Chapter 2
PAGE 2
Na saki jikina na nuna kamar na yarda da shi komai ya wuce, muka ci abinci, muka yi fira sannan muka kwanta. Da asuba alarm ya tashe ni, na tashe shi, ya yi juyi kawai bai tashi ba, na idar da sallah ina zaune ina lazimi na tuna da wayar tasa, na tashi da sauri na ɗauki wayar dake kusa da filonsa a hankali na fice daga ɗakin, falo na shigana zauna bugun zuciyata na bugawa saboda fargabar abin da zan iya samu, da farko call long na shiga, na ga yana waya da mutane da dama, maza da mata, na dawo na shiga massage nan na sha mamaki, duka rabi da kwatan saƙonninsa na mata ne, a na farko-farko nan maganganu aka fi yi masa akan aurenmu, da yawansu sun nuna masa fusatarsu da auren, wasu kuma mamaki, suna ta cewa ya yaudare su, duk dai ban ga yana replay ba, a tsofaffi saƙonni kuma yawanci ya ba da amsa, sannan ba sa wuce yaushe za mu haɗu? Ko su matan su ce yaushe zai shigo musu, kalaman soyayya dai da na jan hankali kala-kala haka suke aiko masa, na ajiye gwauron numfashi, na shiga whatsApp, cikin massage ɗin da na gama karantawa na wata Safna duk ya fi yawa, har akwai inda ta turo masa da cewar wallahi tun da ya yaudare ta ya cuce ta wannan auren na shi ba zai ci Talata ba ballantana Laraba, saboda haka na dubo sunanta, aikuwa na tarar da saƙonninta kaca-kaca, har da wanda bai kai ga buɗewa ba, duka dai magana take yi masa akan ya yaudare ta, tsofaffin saƙonnin kuma fira ce suke yi ta masoya, amma fa masoyan bariki, don wasu zantukan ko ni da nake matarsa zan ji shakkar yin su.
Nan na shagala da bibiyar chart ɗinsu, ina ta sauraron voice ɗinta, amma ban ga hotonta ko ɗaya ba, har gari ya yi haske a kan lambarta nake, sai kawai na je na mayar masa da wayarsa yadda take, na koma falon na zauna na zuba tagumi, zuciyata tana ta zugi, kaina ya cushe na ma rasa yadda zan yi, idan jiya ya yi mini ƙaryar alaƙarsa da ƴar shila to wannan Safna ko me zai ce idan na tambaye shi? Hmm na sauke numfashi, ina tuna lokacin da ya fara zuwa neman aurena, mutane sun yi ta kawo maganganu a kan sam ba mu dace ba, saboda ba shi da kamun kai, wanda a lokacin muka ɗauki zancen a ƙanzon kuregi, Baba ne ma kaɗai ya gasgata, don ba a son ransa ma aka yi auren ba, Salman sam bai kwanta masa ba, ni ma kuma a baya ina da masoyi kafin zuwan shi, ƙaddara dai da rabo ita ta sauya komai, da fari na yarda ƙazafi ake yi masa, tun daga kan yadda shagalin aurenmu ya kasance sai nake zargin anya kuwa ban yi ganganci leƙawa ramin kura ba?
A sanyaye na tashi na shiga kitchen, sai da na gama haɗa abin karyawa na yi wanka, ina cikin shiryawa ya tashi, na yi masa kallo ɗaya na kau da kai, ga shi dai fari kyakkyawa, mai yawan kyauta ga kowa, amma yana da naƙasu ta ɓangaren addini, kamar bai ɗauki sallah da muhimmanci ba, ya ƙaraso ya riƙe ni da murmushi yake cewa"Babu gaisuwa?"
Na ce"Ka fara gaida mahaliccinka, don sai an gaida shi ake amsa gaisuwa, hakan na ga manya suna yi".
"Ok" Kawai ya ce, ya fita zuwa banɗaki, ni kuma na gama na koma falo na zauna, tunanin abin da na tarar a wayarsa ya tsaya mini a rai.
Na yi jarumtar danne damuwata sosai, na sakin fuskata muka karya kamar yadda muka ba, sai na shigo masa da zancen ina gajiya da zama ni kaɗai, kaɗaici yana damuna, ina son na dinga shiga maƙota, tun da yaransu ma suna ta shigo mini, nan take ya amince ya ce ai babu matsala. Akwai wata buduruwa Saudat da ta shigo min ya kai sau uku, gidansu ne na kusa da gidana, don haka nan na fara shiga, muka gaisa babarta tana da kirki sosai, ina zaune ma mijinta ya fito muka gaisa, ya yi mini Allah Ya sanya alkhairi, har da nasihar haƙuri, nan na shantake muka sha fira hakan ya yi mini daɗi, to da yamma ma da na yi wanka, ina zaune na gaji da zaman gidan, sai na fita nan bayan layinmu kaɗan, akwai wata mata mai fara'a da ta shigo min, muka yi fira har nake jin ita ƴar eriyarmu ce, unguwarmu babu nisa da unguwarsu, sai na ga tun da aure ya haɗa mu waje ɗaya ya kamata mu yi zumunci, na shiga gidanta, ta tarbe ni hannu biyu-biyu, sunanta Hajiya Hadiza, fira muka yi sosai, na saki jiki da ita, tana ta ba ni shawarwarin zama da miji ɗan sanda da kuma yanayin aikinsu, wani abun ma sai na ji kamar ta san damuwata, har maganin mata ta ba ni sai da na ji kiran sallar magriba na tafi gida.
To fa tun daga ranar sai na daina zaman kaɗaici, nake shiga maƙota ina rage lokaci, yanzu duk gidajen mun san juna, suna shigo mini su ma, musamman dai Hajiya Hadiza da kuma maman Saudat, wacce mijinta ogan mijina ne a wajen aiki, yana da kirki sosai.
Tun daga ranar da na duba wayarsa ban sake dubawa ba, sai dai idan an kira shi na ga sunan mace ne nakan ɗaga don na tabbatar, wata idan na ce matarsa ce sai ta kashe, wata kuma ta zage ni, wata ta yi mini barazanar sai na bar gidan.
Akwai wata rana da ba zan taɓa mantawa da ita ba, da safe Salman ya fita aiki, na gama duk ayyukan gida ina zaune sai na ji ana ƙwanƙwasa gidana, na tashi na je na buɗe, na ga wata mace ce mai bugun, na yi mata kallon rashin sani, tun da yanzu duk na san matan unguwar sannan shi ba ma ɗan garin ba ne, ballantana na ce ko wata ƴar'uwar tasa ce, "Ke ce kika buga gidan?" Na tambaye ta.
"E ni ce, yi haƙuri ba ki gane ni ba ko?" Cikin yanayin maganarta mai kama da tsiwa da cakwaikwaiwa ta faɗi hakan, nan take na gane muryarta, Safna ce wacce na bibiyi chart ɗinsu, kuma wacce ta fi yawan kiran shi a waya.
Gabana ba da rass, na dake na saki murmushi na ce "Sannu da zuwa, ki shigo".
Ta shigo muka tsaya a zaure, tana yauƙi ta ce"Amarya ya amarci? Angon ba ya nan ne?"
Na ce"Amarci kam ga shi nan ana kan sha, Alhamdulillah, ango ya tafi aiki".
Ta jinjina kai, ta kai hannu ta dafa kafaɗata, har sai da na tsorata don na ji abun banbarakwai, ta fara maganganun da suka kusa tarwatsa zuciyata, ta ce"Na so na samu Salman a gida, amma tun da ba ya nan zan faɗa miki abin da yake tafe da ni sai ki sanar masa, tuni ne na zo yi masa, don Allah ki faɗa masa ya zama wajibi ya zo fa mu tattauna a kan wannan matsalar, mu san yadda za a yi da wannan cikin na jikina, domin kullum ƙara ƙwari yake yi, idan kuma ya zaɓi na haihu na kawo miki ɗan ko ƴar to sai ya yi bayani".
A hanakali na zame hannunta daga kafaɗata, kaina ya shiga juyawa na ji kamar zan zube a wajen, "Ciki! Kina nufin ciki ne da ke?"
Ta yi mini makirin murmushi ta ce"Shi mai cikin ne zai tabbatar miki". Daga haka ta juya ta yi tafiyarta, ta bar ni a daskare.
Zuciyata ta dinga bugu, tuni ƙwalla ta kawo idona, tashin hankalin da na shiga a lokacin ba ya misaltuwa, mijina da auren ko wata biyu bai yi ba wai wata tana ɗauke da cikinsa? Da sauri na saka hijjabi, na fito, cikin rashin sanin abun yi na faɗa gidan Maman Saudat, ina shiga muka yi kiciɓus da mijinta a tsakar gida, nan take na rushe da kuka, a razane ya ce"Subhanallah! Zinatu mene ne ya faru?"
Cikin kuka na ce"Wata ce, wata ce yanzu ta zo ta faɗa mini Salman ya yi mata ciki".
Ya ce"Tana ina?"
"Ta tafi" Na faɗa ina share hawaye, duka na ruɗe.
Ya ce"Ki kwantar da hankalinki, ba lallai ya zama gaskiya ba, idan ta sake zuwa kuma ki kira ni, ki tafi gida ki yi shiru kar ki kira shi Salman ɗin, za mu san abun yi in sha Allah!".
Na koma gida, na zauna na ci kuka na gode Allah, ruwa kaɗai na wuni ina sha, na kasa cin komai, don ban ma yi girkin ba, can da yamma, ina zaune sai ga bugun gida, na yi zaton ma yara ne, na je na buɗe, kawai sai na ga Safna ce dai ashe ta dawo, "Me kika dawo yi kuma?" Na tambaye ta da ƙarfi.
Ta ce"Tuni na dawo, don ina so ki san abun ba na wasa ba ne, lallai lallai ki tabbatar masa da ya zo mu tattauna, don ciki kullum ƙara girma yake yi, ba zai yiwu ya cuce ni ya yaudare ni ba, ya yi aure ni kuma ya bar ni da wahalar cikinsa.
"Oga!" Na ƙwalawa baban Saudat kira, wanda ya fito cikin shirin tafiya aiki.
Sai ya taho da sauri, har karkarwa nake wajen faɗin"Ga ta nan ta dawo, ita ce ta zo ɗazun".
Oga ya ce"Ke saboda ba ki da mutunci shi ne za ki za ki zo har gida da zancen banza?"
Da tsiwa ta ce"A'a ka ga yallaɓai dakata! Ciki ne ya yi mini na zo fa na tabbatar musu".
Ta juya za ta tafi, ya sha gabanta, ya sauke mata mahaukacin mari, ta dafe kunci ya ce"Kin san da wanda kike magana kuwa? Tsugunna a nan!".
Ba ta tsugunna ba amma ba ta sake yunƙurin tafiya ba, ya ciro waya ya kira Salman, ya ce masa ko me yake yi maza-maza ya katse ya zo gidan yanzun nan.
Babu jimawa kuwa sai ga motar Salman ta shigo layin, yana ganin Safna ya fara ƙanƙance ido, a fusace ya ce"Uban me ya kawo ki gidana!?"
Ta ce"Maganar cikin da yake jikina na zo mu yi".
"Ciki! Ni ne na yi miki ciki?" Ya tambaya ransa a ɓace.
Ni kuwa kallon shi kawai nake cike da takaici da fargabar anya kuwa zan iya cigaba da zama da shi?
Oga ya ce masa"Salman da gaske take?"
Da sauri ya ce"Wallahi ƙarya ne, ƙarya take yi mini, na dai santa, amma babu wani zancen ciki".
"Ku shige mu je!" Cewar Ogan yana kallonmu ni da ita.
Salman ya koma mota, Oga ya buɗe gidan baya ya shiga, zaraf ta riga ni buɗe gidan gaba ta shiga ta zauna. Wani sabon kishi ya turnuƙe ni, a fusace na ce"Dalla malama fito ki koma baya!".
"Ki shiga bayan ki zauna, don ni na saba zama a gaban shiyasa". Ta yi maganar tana yi mini kallon tara saura kwata.
Sai da suka zazzage ta, sannan ta fito ta koma bayan, na shiga gaba ya ja mota, sai da muka fita daga barikin muka hau titi sannan Oga ya ce"Police station ɗin Fage za ka kaimu".
Na yi mamaki don na yi zaton na inda suke aiki za mu je, sai na bar shi a ba a son tonawa Salman asiri ne a wajen aiki, har muka ƙarasa zuciyata zafi kawai take yi, ga kuma fargabar abin da zai faru, idan da gaske tana da cikinsa ya zan yi? Ko wacce hujjar zai kawo mini don ya kare kansa? Lallai a ranar na yarda namiji ɗan kunama ne.