Chapter 3
PAGE 3
Oga ne ta shige gaba wajen shigar da ƙara, sannan aka neme mu, muka shiga mu duka, na ƙi yarda mu haɗa ido da Salman, saboda yadda nake jin zafi idan na kalle shi, na yi musu ƙarin bayani sosai, aka tambayi Safna ta fara zabure-zabure tana rashin kunya, nan fa suka dinga fesa mata mari aka yi mata fatata, aka ce mata idan za su yi barikinsu su yi can tsakaninsu, babu ruwan matarsa, kar ta sake ko a waya ta sake nemanta, aka ce sanda aka yi mata cikin na sani ne ballantana ta ce ta zo yi mini tuni? Shi kuma Salman yana ta rantsuwar ƙarya take yi, ba ta da ciki, ƴan sandan suka ce za a je asibiti a yi gwajin ciki, idan aka gano ƙarya take yi, daga nan kotu za su wuce. To fa da Safna ta ji matsin lamba sai ta fashe da kuka, ta ce"Don Allah ku yi haƙuri, ni ba sai an yi gwaji ba ma, wallahi ƙarya nake yi ba ni da ciki".
"A kan me kika yi ƙaryar!?" Ɗan sandan ya daka mata tsawa.
Ta share hawaye ta ce"Saboda na haɗa su faɗan da zai yi sanadin mutuwar auren, Salman ya yaudare ni, yana ta yi mini ƙaryar zai aure ni, kawai sai na ji ya je ya yi aurensa".
Nan ɗan sandan ya ce wannan case ɗinta ne da shi, kar ta sake saka matarsa, ko da wasa ta sake zuwa gidansa ko ta kira matarsa a waya sai ta sha mamaki, suka ƙara da faɗin yanzun ma ba za a barta haka ba, dole sai ta yi sati ɗaya a kulle, wannan somin taɓi ne, idan ta sake gwada hakan ta sani a gidan kaso za ta zauna, nan aka yi mana tsakani, aka shigar da ita aka kulle.
Mu kuma muka fito daga wajen, muka shiga mota, wannan karon Oga ne ya shiga gaba, ni kuma na shiga baya, muka ɗauki hanya, a hanya ya sauke Oga don ya ƙarasa wajen aiki, ni da shi muka nufi gida, motar shiru babu wanda ya kula wani har muka ƙarasa. Yana tsayawa a ƙofar gida na yi saurin ficewa, dama da mukullin gidan a hannuna, na buɗe na shige, na shiga falo na zauna har lokacin zuciyata a cushe take, sai dai zan iya cewa na samu ɗan sassauci da jin babu zancen ciki, duk da na san wannan bai kai dalilin da zai saka hankalina ya kwanta ba, don indai yana bin matan to kuwa tabbas wataran cikin na gaske sai ya tabbata, na share hawayen da suka sakko mini, ni sai yanzu ma na fara zargin ko dai wannan ne ya haddasa rabuwarsu da matarsa ta farko?
Ina cikin wannan tunanin kawai sai na ji tashin motarsa, ya wuce shuuu, mamaki bai kashe ni ba sai da na yi saurin tashi na leƙa windo na ga kuwa tabbas shi ɗin ne ya fice daga barikin, zuciyata ta sake kumbura, ni nan na kame na tsare gida ina jiran shigowarsa na ji ta inda zai fara ba ni haƙuri, ya kuma yi mini alƙawarin ya daina ko da kuwa ba da gaske yake ba, ashe shi bai ma ɗauki hakan a wani babban abu ba, tun da har zai iya ficewarsa bai ba ni haƙuri ba? Na rasa yadda zan yi, na rasa wa zan bawa labari ko zan ji nauyin zuciyata ya ragu. A ranar kasa yin girki na yi, wajen ƙarfe takwas ina zaune ina kallon tv, wanda hankalina sam ba a kanta yake ba, na ji tsayuwar motarsa, sai da ya daɗe yana buga gidan sannan na danne zuciyata na je na buɗe, na wuce na koma ɗakin ba tare da karɓi ledojin hannunsa ba, ya shigo ya zauna yana cewa "Zeena lafiya dai na ga ko sannu da zuwa ba ki yi mini ba?"
"Sannu!" Na faɗa ba tare da na kalle shi ba.
Ya janyo ledar yana cewa"Ga kajin nan, har da kilishi na siyo miki, ga kuma yougurt mai sanyi, anya ma kuwa ba zai saka ki mura ba? Ko za ki ɗan saka shi a ruwa ya huce?"
Wani takaici ya turnuƙe ni, na kumbura kamar zan fashe, na ƙi kallonsa, ya tashi ya fice ya je kitchen ya ɗakko faranti da kofuna, ya dawo ya juye kazar, ya zuba yougurt ya ƙaraso inda nake ya kai kofin bakina, na kau da kai ina danne zuciyata don kar na surfa masa zagi.
"Zeena ya dai? Akwai abin da ya faru ne?" Ya faɗa yana ajiye kofin.
Na juyo ina yi masa kallon mamaki, na ce"Da gaske? Da gaske tambayata kake yi Salman?"
Ya ce"E mana, to ni na ga duk kin jagule mini, kina son kilishi, na ga yau ko kallon shi kin ƙi, ki ga fa ya yi faɗi" Ya faɗa yana ɗakko falle ɗaya ya kai bakinsa.
Na ce"Salman zuwa yanzu na fara tunanin wai wa nake aure? Kana ta ba ni mamaki, ka ba ni tsoro, wanda wannan zai iya kawo saɓani da tsana a tsakaninmu, ƙarshe kuwa ka san me hakan zai haifar, yanzu duk abubuwan da suka faru a yau ba su kai ka gane ka yi mini ba daidai ba? Ko ban cancanci haƙurinka ba ai na cancanci zama ka yi mini bayanin da zai kare ka, ni fa matarka ce, wacce ta aure ka ba tare da sanin kana neman mata ba, yanzu kuma ta tabbata na sani, babu wata hujjar aikata hakan da za ka kawo mini? Kana nufin duk tashin hankali da zubar da hawayen da karuwarka ta saka ni a yau ya tafi a banza, shikenan har komai ya wuce a tsakaninmu na saki jiki da kai na faranta maka a yau ɗin?"
Ya ce"Zeena kenan, ni kina ba ni mamaki, to wai ba ya wuce ba? Ni da na ga an yi komai a gaban idonki, ga shi kin ji ta ƙaryata da bakinta ai za ki yi mini uzuri ki san ya wuce ko? Ko ba ki ji maganarta ba? Ta ce so take ta raba mu, duk fa don na daina kula ta ne ya kawo hakan, idan a baya na yi neman mata yanzu ai na tuba, Allah ma yake karɓar tubanmu ballanta kuma matanmu? Yau da ban daina ba, ai da ba ki ji duk wannan ba, ta sanadin aurenki na daina komai, sannan ke ce za ki ƙarfafa tuban nawa, ta hanyar nuna kin yarda da ni, ba wannan fushin da kike yi ba, haba, wannan ai ba wayewa ba ce sam".
Na yi shiru ina ta kallon shi, na kasa cewa komai, ya ce"Haba, ki bar komai ai ya wuce, ungo nan ki ji sanyi a ranki". Ya miƙo mini kofin, na ƙi karɓa.
Sai ya ƙyale ni, ya fara cin kazarsa hankali kwance, ni kuma zuciyata ta cika da wasi-wasi, dama na sani can shi Salman ba mutum ba ne mai saurin fushi, yana da raha sosai, amma a ganina wannan ai ya wuce abun wasa, can na tsinkayi muryarsa ya ce"Yawwa Zeena, dama ina so na faɗa miki, ina ta cuku-cukun sama miki gurbi a makarantar gaba fa".
Wani farinciki ya yi mini dirar bazata a zuciyata, ina matuƙar son karatu, a ƙa'idar yadda Babana ya tsara sai na yi NCE za a yi mini aure, to ganin na samu mijin tun kafin Candy sai kawai aka yi auren bayan an yi yarjejeniya da shi zan cigaba da karatuna, kuma idan na samu aiki zan yi.
"Da gaske kake?" Na tambaye shi.
Ya yi ƴar dariya ya ce"A'a da wasa, Allah kuwa na sa a duba, Sa'adatu Rimi nake so ki yi, tun da kin ga Arabic kika karanta sai ki ɗora kawai, idan kuma za ki canza cos to sai ki yi bayanin wanda kike so".
Kamar komai bai faru ba na ce"E hakan ma ya yi, zan yi Arabic ɗin, Allah Ya sa dai a samu".
Ya ce"Za a samu in sha Allah! Kin ga ke ma kya rage zaman kaɗaicin nan, na yi miki alƙawarin zan dinga kai ki, ko da aikina zan iya katsewa, zan dinga ɗakko ki idan na samu dama, idan kuma ban samu ba zan ba ki kuɗin mota, duk wani nauyin karatunki yana wuyana, har ki kammala ba zan gaji ba in sha Allah!".
"Da na ji daɗi kuwa,na gode sosai Allah Ya sa".
Ya ce"Ni kuwa sam ban karɓi wannan godiyar ba, sai kin ci kazar nan".
Ya taso ya dawo kusa da ni, na ci sosai, muna taɓa fira akan karatun, sai na watsar da komai na haushin shi da nake ji, muka gama muka kwanta cikin nishaɗi.
Kwanan Safna biyu a kulle sannan aka fitar da ita. Muka cigaba da zamanmu lafiya da Salman, mutum ne mai kyautatawa sosai, yana da bushasha, cefane har yawa yake yi, babu nau'in kayan abincin da bai ajiye mini ba, nama kuwa kullum da shi nake yin girki, a rana ɗaya sai ya siyo kaji ya siyo naman kai, sannan ka ga ua haɗo da kifi, sannan sam babu ruwan shi da kulle ko saka ido a fitata, irin na wasu mazan, shi da kansa yake ba ni kuɗi na shiga kasuwa, na yo siyayyar gida da ta amfanina.
Yanzu idan yana aikin kwana Saudat ce take shigowa ta taya ni kwana, mu sha fira sannan mu yi kwanciyarmu.
Ya cika alƙawarin da ya ɗauka, ya yi mini komai na karatuna, zan fara zuwa ne kawai, saboda haka ranar na ce masa zan je gida don na sanar musu, ya siyo kaji manya uku, na soya na yi farfesu, na yi haɗaɗɗen girki na zuba a kula, ya ɗauke ni da yamma ya kai ni, ya ce bayan isha'i zai zo ya ɗauke ni, ba Mama da dama ita ta fi son aurena da Salman ba, hatta Baba ya yi farincikin jin zan cigaba da karatuna, suka dinga saka masa albarka, nan fira ta kaure tsakanina da ƙannaina, aka yi raha, aka bi ƴan gida da abincin da na kawo, kowa ya saka albarka, ana ta yi mini murnar na dace da miji.
Bayan sallar isha'i ya zo ya ɗauke ni, muka tafi bayan ya bawa Mama kuɗi a rabawa ƙannaina. Kafin mu tafi Mama ta yi mini nasiha sosai kan kyautatawa danginsa, da yawan ziyartarsu, saboda haka muna ƙarasawa gida na faɗa masa zan je Jigawa na gaida Umma, nan take ya amince, ya ba ni kuɗi na je na yi siyayyar tsarabar da zan kai, ya saka ni a mota ya ce na gaishe su.
To dama mun saba muna gaisawa da su ta waya, sannan ƴar autarsu Nana ta taɓa zuwa gidanmu tun kafin auren, har ta yi sati ɗaya, suka tarbe ni hannu biyu-biyu, mahaifiyarsa tana so na, tana da kirki sosai, kwana biyu na yi na baro Jigawa bayan ta haɗa mini tsaraba, na dawo da fura da nono mai yawa, don su ɗin fulani ne, na rabawa maƙota da ƴan gidanmu.
A ranar da zan fara zuwa makaranta, zo ka ga farinciki da zumuɗi, tun sassafe na yi wanka na shirya, ɗaya daga dogayen rigunan kefena na saka, na naɗa mayafin, da ya shirya ya fito yana yaba yadda na yi kyau, shi babu ruwansa da shigar da zan yi idan zan fita, inda a gidanmu ne ban isa na fita a haka ba, don saka hijjabi kowa ya san yana cikin dokar matan gidanmu, wanda Babana ne ya assasata, gyale duk girmansa indai sunan shi gyale ba ka isa ka yafa shi ka fita ba, ƙarshen zance dai har ranar aurena da hijjabi na ci biki, don haka yanzu nake jin daɗin yadda na samu ƴancin yafa gyale.
Tsarin karatun Asabar da Lahadi na zaɓa, har cikin makarantar ya shiga da ni, ya ɗauki dubu uku ya ba ni, duk da ya san na yi girki na taho da shi, ya yi mini sallama da fatan nasara ya tafi.