Wutar ƙaiƙayi

Chapter 4

by @sadiyaabdulrazak954

PAGE 4


   
   Sannu a hanakali na fara gudanar da karatuna, har na saba da mutane, akwai wata ƙawa da na yi mai suna Habiba, muna mutunci da ita sosai, sai dai ban fi sati uku da fara zuwa ba, laulayi ya yi mini sallama, rashin lafiya ya sako ni a gaba, kasala, amai, yawu, ciwon kai duka suka haɗar mini, gabaɗaya sai makarantar ta so fita a raina, Salman ne ya tsaya tsayin daka ya dinga nuna mini muhimmancin karatun, don da cewa na yi ni na haƙura da makarantar, haka dai na daure na cigaba da haƙuri da baƙon yanayin tun da Salman yana ƙoƙari ko ban yi girki ba, ba ya damuwa zai siyo mini duk abin da nake so na ci, haka ma maƙociyata Hajiya Hadiza tana aiko mini abinci, ko na je gidanta na ci, ita ma mun ƙara sabo sosai da ita, ban manta ba akwai ranar da Salman ya nemi shawarata kan kawai a zubar da cikin nan, saboda wahalar da nake sha, ni kuwa duk wuyar ban ji zan iya haka ba, don haka ban amince ba, da Allah Ya taimake ni na samu sassaucin abun, kuma a lokacin ne Babana ya yi mini hanya na samu gurbin koyarwa a wata makaranta primary, wacce take private kuma ta Arabic ce, na fara zuwa koyarwa, a can unguwarmu gidan iyayena makarantar take, nan ma dai Salman ba ya gajiya, shi ne yake kai ni, na kame a gaban mota, ga shi dama ya haɗa mini kayan lefe na gani na faɗa, saboda haka duk suturata masu kyau ne da tsada, idan mun ƙarasa ƙofar makarantar shi yake buɗe mini mota, ya ɗakko mini jakata, ya ɗauki kuɗin kashewa ya ba ni, wannan yana yi mini daɗi, har wani fashewa kaina yake yi, yana da kyautatawa musamman a gaban mutane, sosai yake nuna shi mijin-tace ne, har ta kai ƴan unguwarmu sun fara ƙananun maganganu a kan irin son da yake yi mini, ana cewa na auri mijin marainiya, haka a Sa'adatu Rimi ma ƙawayena suna yawan tsokanata da na mallake mijina, wasu kuma su ce amarci ake sha shiyasa, ni dai murmushi kawai nake yi don da sun san halinsa da ba su fara yi mini murna ba.

 A haka rayuwar ta cigaba da tafiya, nakan ɗauki wayarsa na bincika, ban fasa ganin ƴan'matansa ba, kuma ban fasa tuhumarsa, tun yana yi mini ƙarya don kare kansa har ya daina, sai dai ya yi mini shiru, a da idan na ɗauki fushi yakan rarrashe ni, amma yanzu sam ya daina, sai dai shi ma ya ɗauki gaba da ni, mu yi ta zaman kurame.

To yanzu idan yana aikin kwana wannan buduruwar ta maƙwabtana Saudat nake kira sai ta taya ni kwana, indai aikin kwanan gaske ya tafi sai safe yake dawowa, idan kuma yawon club ya tafi ina ganewa, tun da tsakar dare yake dawowa gidan, sai Saudat ta koma falo, mu kwanta tare da shi, daga baya sai ya tsiri wani sabon hali, idan zai dawo tsakar daren nan sai ya dawo da wani abokinsa, wai shi ma zai kwana a gidan, saboda dare ya yi, a ƙa'ida kamata ya yi su kwana da shi tare a falo, ni kuma mu kwana da Saudat a beadroom, sai Salman ya ce sam ba zai yarda ba, sai dai Saudat ta koma falon, sai na ba ta bargo ta shimfiɗa a ƙasa ta kwanta, shi kuma abokin nasa ya kwanta a kujera, tsakani da Allah wannan tsarin bai dace da musulmai ba, mace buduruwa da namiji zabgegen saurayi su kwana ɗaki ɗaya? Saboda haka tun da haka ya faru sau biyu Saudat ta daina zuwa taya ni kwana, idan ba ya nan sai dai na kwana ni kaɗai, tun ina jin tsoro har na saba da wannan.

 A hankali miyagun halayensa suka dinga fitowa fili, yanzu duk ranar Lahadi sai Sabi'u ya yo masa canjin sababbabin kuɗi wanda za su yi liƙi idan sun je club, akwai wani babban club fitacce a Kano wanda duk wani riƙaƙƙe a harkar bariki ya san wajen, to duk Lahadi sai ya ɗauki wanka sun tafi da Sabi'u, wataran su kwana a can, wataran ya dawo tsakar dare, tun ina damuwa ina yin ƙorafi har na sare na barwa Allah komai, na duƙufa karatuna da koyarwata, kuma ina rainon ƙaramin cikina.

Idan damuwata ta fara yi mini yawa Hajiya Hadiza nake faɗawa, ta ba ni haƙuri ta ba ni shawara, sai ma ta saka na fara bussines, na fara da haɗa magungunan mata, ina ba ta sari tana siyarwa, da yake ni mai yawan karance-karance ce, wasu ma a littafai nake samun yadda zan haɗa, makaranta ma na fara tallatawa da kuma ƙawayena, nan da nan harkar ta fara gara mini, ina samun ƴan canjina. 

Yanzu duk watan duniya sai na je Jigawa gaida mahaifiyar Salman, idan aka yi albashi ya jibgo min kayan abincin nan, haka zan auni shinkafa na ɗibi taliya da macaroni, mai da magi, komai sai na ɗiba, sannan na ce ya kawo kuɗin tsarana, na shiga kasuwa na siyo musu tsaraba omo, sabulu har ma da kayan ciye-ciye, da yake yana da yawan siye-siye haka kawai yakan siyo mini atamfa mai tsada, duk da kayan lefena suna nan a ajiye ban gama ɗinka su ba, to wani lokacib sai na ɗora da atamfa na kai wa Umma, haka nake zuwa da kaya niƙi-niƙi duk wata, ta yi ta shi mini albarka, haka ƴan uwansa ma duk suna so na, sai guda ɗaya cikin ƙannensa ce na lura tana yi mini gani-gani.

To fa bayan mun zama jiki ni da Salman sai abubuwansa suka ƙara ta'azzara, ta kai yanzu sai ya yi sati ɗaya cir bai zo gida ba, idan mun yi waya ya ce mini aiki ne ya yi masa yawa, haka zai bar ni babu cefane, idan na yi girkin na ajiye masa washegari sai dai na zubar, idan bai lalace ba na ɗumama, da daddare na ci kwalliya ina jiran miji, sai dai na farka na cire kayan kwalliyar, to ni ma sai na daina yin girkin kullum, idan na dawo daga koyarwa sai na sauka a gidanmu na ci abincin rana, sai na ji Mama tana ta shi wa Salman albarka, ashe yana yawan zuwa gidan, har ma ya zauna ya ci abinci, ko ya ce a aika masa police station, ni kuma ya bar ni babu cefane, a lokacin babu wanda ya gane yana ƙuntata mini.

Duk ranar da ya waiwayo ni, zai jibgo mini cefane, kaji, jan nama, kilishi, da dangin kayan ruwa lemoka kala-kala, ko kuma ya turo min kuɗi ta account ya ce na je na yo mana cefane, to idan ya zo ɗin nan shi fa ya fi so kar na wani yi masa ƙorafi, kawai na karɓe shi hannu biyu-biyu, na faranta masa kamar ba a yi komai ba, da na yi ƙorafi sai ɗauki fushi, ƙila ma daga ranar ya sake tafiyarsa, saboda haka wataran na nuna fushi wataran kuma sai na bawa zuciyata haƙuri na sake da shi, a haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya. Ga dai abinci a gidan, amma sai na dinga ramewa saboda damuwa, tun da ba ni da wata kwanciyar hankali.

Na fara zuwa awo, nan ma shi ne yake kai ni, ya ba ni kuɗin kashewa. Akwai lokacin da wayata ta faɗa cikin randa, ta sha ruwa sosai kafin na ankara, ta ƙi kawowa, ya karɓa ya ce zai kai mini wajen gyara, bayan sati ɗaya sai ya zo mini da sabuwar waya fil a kwalinta, da sabon layi, na ce masa ina tsohon nawa ya ce wallahi bai gan shi ba, ya ɓata, haka na haƙura na fara amfani da sabon, na sassaka lambobin da nake da su kwafe a takarda, ciki har da lambar tawa da ya ce layin ya ɓata, na yi saving da my number.

Watarana ina kitchen dawowata daga makaranta kenan, zan ɗan tafasa taliya, na ji ƙarar wayata, na duba, mamaki ya kama ni ganin sunan da ya bayyana, wato my number, hmmm ashe wata ƙaddarar ce ta bankaɗo mini labule sanadin wannan tsohon layin nawa.


***