RU'UYAA (The dreams we never lived)

4. ...baƙin mutane...🖋️

by @autum17




har aka tashi break ina tunanin abinda aka koyar da mu, shine karo na farko da akayi karatu naji na fahimta kuma naji abun ya taɓa zuciya ta,duk abinda ta faɗa ya shafe ni....sai dai taya zan zama mai high sef istim? abun yanada sauƙin faɗa amma aiwatarwar ne da wahala, nasan dacewa yanzu na rage nuƙu nuƙu cikin hijabi kamar yanda ta faɗa, amma har yanzu ina matuƙar jin kaina a takure musamman idan ina gaban maza

ranar ina wucewa ta filin ƙwallo,akwai mata da yawa da suka wuce kafin ni kuma ko wace mace idan ta wuce mazan dake wurin sai sun bita da kallo suna maganganun da basu dace ba...ina zuwa naji wani na faɗin '' wannan kamar sandar sluka (snooker)... idan mutum ya rungumeta ciwon ƙirji zata sashi!" abun ya bala'in yimin zafi kunya ta rufeni lokacin da suka kwashe da dariya naji kamar ƙasa ta buɗe ta haɗiye ni,duk yanda naso in bashi martani kasawa nayi dole nabar wurin zuciya ta na tsananin zafi..

Numfashi na sauke ina kalle kalle, kwanakin nan Asma'u ta dena zuwa amsar kuɗin break ɗinta sai nata neman ta kafin inganta bayan da ba haka bane to Meya sauya? rashin amsa yasa na miƙe na fara neman ta na zagaye makarantar duka har bayan masallaci na tafi amma bangan ta ba

'' Habeeba kinga Asma'u?" na tambaye yar ajinsu '' tana wurin Macijin sari ka noƙe !" tabarni tsaye a wurin da tsananin faɗuwar gaba! meya kai ta  wurin ɗan iskan nan dan Allah? bata yimin alƙawarin bazata sake zuwa wurin shiba? kodai ƙarya take basu rabu ba?
 
da wani irin sauri ƙafafuna suke tafiya har na shigo office ɗin shi,samun shi nayi tsaye dab da Asma'u dake maƙe da bango idonta sun fito tsabar tsoro hannun shi riƙe danata yana Magana cikin kashe murya '' I love you...kin san hakan kema bansan dalilin da yasa kike wahalar da zuciya ta ba ma'u...'' katse shi tayi  a tsorace ''  Abeeda tace...tace in dena...kulaka!" fushin dake cin shi ya danne yana  ƙara matso ta kafin ya ɗaura hannunta a ƙirjinshi 

ƙoƙarin cire hannun  take daga jikin shi ya riƙe da ƙarfi yana mata wani ɗan iskan kallo yace '' kina kuwa jin yanda zuciya ta ke bugu saboda soyayyar ki ma'u?" ɗago idonta tayi tana kallon shi kafin da sauri tayi ƙasa da su ya cigaba da faɗin '' yayar nan taki burinta ta raba mu dan taga kin fita kyau da zubi bake kika faɗa min cewa babu wanda ya taɓa cewa yana sonta ba?" gyaɗa kai Asma'u tayi... nikuwa naji wani irin abu ya soki zuciya ta,kenan Asma'u...kafin in gama tunanin naji yana sake faɗin '' kuma kikace akoda yaushe sai ta haɗa kanta dake ba?" nan ma kai ta gyaɗa..naji ƙafafuna sunyi sanyi... wannan sirri nane kuma abinda ya shafi rayuwar mu taya zata faɗa masa wannan?

'' kishi take na faɗa miki baki so kiji idan mun rabu na tabbatar zata zo tace tana sona! kin san yan mata nawa kuwa keson mu'amala dani amma na zaɓe ki ma'u? ki saki jikin ki dani kinji!" yayi maganar yana ƙara jawo ta jikinshi duk da a tsorace take bata hanashi ba

hakan ya tabbatar min dacewa maganganun shi sunyi tasiri akan ta, idona suka ɗau zafi cike da hawaye akan komai dana gani kuma naji 

'' Tsohon ɗan iska munafiki,dallah sake ta!" a wani irin firgice su biyun suka juyo suna kallona musamman ita, wani irin kallo nake binsu dashi su biyun amma dayake ɗan iska ne sai Kallon ta yayi yana faɗin '' Babe kinga ni ko? na faɗa maki kishi take dake!" 

'' Rufe ma mutane baki!!!" na daka mashi tsawa idona suka ƙara duhu..farin ciki ya rine, '' babu abinda ka iya sai lalata yaran mutane kawani riƙe ta a kwana kana cusa mata maganganu... wallahi tallahi idan har baka fita daga harkar Asma'u ba zan iya kashe ka nima daga baya a kashe ni!" zaro ido yayi yana kallona hannun shi dafe da bakin shi dan yagani a idona Abinda na faɗa ɗin da gaske nake...

'' Abeeda ki den...'' kafin ta gama faɗar abinda zata faɗa na wanke fuskar ta da mari shock rubuce a fuskar ta take kallo na,ni kuma ina kallon ta cike da fushin cin amanar datayi min'' akan wannan ɗan iskan zaki gaya min magana har kike kira na Abee..''hawaye na sauka a idonta a tsawace tace 

'' eh! an kiraki Abeeda ba sunan ki bane? ina son shi shine yasa kika gan mu tare ki dena shiga rayuwa ta..da gaskiyar mutane kishi na kike kawai ba wani abu ba..so kike in rabu dashi don ke ki samu ki maƙale mashi kuma bazan rabu dashi ɗin ba!" ta fita daga office ɗin kamar zata tashi sama nabi bayanta da kallo...

dariyar macijin sari ka noƙe ce ta dawo dani daga shock ɗin da har yanzu Ban dena jin shiba 

zagayowa yayi ya tsaya bayana ya ranƙwafo yana wani hura min iska a fuska '' huɗubata tayi aiki ko? yanzu zaki iya raba mu? ki sani sai na samu Abinda nake so daga ƙanwarki iya karki kallo don babu wani abinda zaki iya yi akai!" kasa cewa komai nayi tsabar yanda jiki na da zuciya ta suka min nauyi 

tureshi nayi daga hanya ta na fita ina layi hawaye suka ciko idona..da gudu na ruga na ɓoye bayan masallaci ina risgar kuka duk dacewa an koma aji...yau Asma'u da bakinta ke irin wannan maganar? ashe dama ƙarya take da tace zata rabu dashi? Kuma dama itama tun tuni tana gani na a matsayin mai kishi da ita har take faɗar sirrika na mawani banza can? zuciya ta ta karye fiye da zaton mai karatu 

har aka tashi short break ina kuka sai dai na canja wuri saboda masu zuwa wurin...sai lokacin Sallah na gama kukan idona sunyi luhu luhu sun ƙanƙance sunyi jawur.. alwala nayi na shiga Masallacin mukayi sallah 

da aka gama ban koma class ba sai lokacin tashi naje na ɗauki jakata ban jira kowa ba nayi gaba abuna...wata doguwar hanyar danake bi a duk sanda rayuwa tayi min zafi ko nake buƙatar kaɗaici nabi ina tafiya ina tunani zuciya ta na ƙara ƙuna a duk sanda na tuna abinda Asma'u ta faɗa min '' laifi nane!" na faɗa da shaƙaƙƙar murya ina goge hawayen da suka silalo min...da ace na iya son kaina a yanda nake ..da ace inada ƙwarin guiwa..da ace na gode Allah yanda yayi ni..da babu wanda zai faɗi maganar da zata sosai raina...hawaye kamar ruwa suke kwaranya daga idona sai dai nake sa bayan hannu na ina sharewa 

wurin ƙarfe uku da rabi nakai gida samunta nayi tsaye kusa da bishiyar mangoro tana jirana dan bazata iya shiga ita kaɗai ba... ina ƙarasowa ta miƙe muka cigaba da tafiya babu wanda yace uffan cikin mu har muka shiga ciki

Muka iske Mama  tsakar gida riƙe da hijabi fuskar ta ɗauke da damuwanmu muka  tsaya   kallonta jin tsayuwar mutum yasa ta juyo ganin mune ta sauke ajiyar zuciya '' ina kuka ts..'' kafin ta gama magana na saki jakata na ruga na rungumeta tareda fashewa da kuka mai ƙarfi ''Maamaaaa!" zuciyata na ƙara karyewa hankalin Mama ya tashi sosai hakama Asma'u ɗago Ni daga jikinta  tayi duk ta daburce baiwar Allah'' meya faru yar Mama faɗa min!" take  share min hawaye na da suka kasa tsayawa... wani irin rauni da baƙin ciki ke ɗawainiya da zuciya ta...

Mama a ruɗe take tambaya ta cigaba da tambaya ta da ƙarfin hali irin na uwar data ga yarta cikin damuwa   '' hum...dama wasu ne suka yi mata abinda suka saba!" da sauri  Asma'u ta faɗa kanta tsaye hakan yasa na ƙara ɓoye fuskata  a ƙirjinta, rungume ni tayi tana lallashina Muryar ta na rawa na tsani inji muryar Mama a irin haka, zuciya ta karaya take..duk da akwai sauran kuka cikina sai na haɗiye kawai 

Mama ta ɗagoni tana share min hawaye tace '' Abeeda dan Allah ki dena saka kanki a damuwa ki tuna cewa duk wannan abun lokaci ne sannan kyaun jiki dana sura suna ƙarewa banda na hali...ki zama mace me kyakkyawar zuciya shine Abu mafi muhimmanci!" gyaɗa kaina nayi kawai babu wanda ke ganewa ko kuma zai gane sai wanda ke cikin yanayin..... Asma'u daga gefe tayi tsaye bata ce komai ba yanayin ta ya nuna bata ji daɗin abinda ya faru ba mema ake kiran kalmar da turanci....uhmm..

Autumn: guilty 

ta kasa cewa komai..

riƙe hannayen mu Mama tayi  ta shigar damu ɗakin mu dake ƙamshin tsintsiyar ƙamshi ta zaunar damu sannan ta fita 

matsowa tayi da niyar magana sai kuma me ta tuna oho ta matsa baya nasan maganganun macijin sari ka noƙe ke yawo a kanta...

cire hijabina nayi tareda rigar uniform ɗin na ɗaura zane na zauna ƙasa bayana jingine da bango ido lumshe...bina da ido tayi,tasan maganganun ta ba ƙaramin...uhm..mema ake cema kalmar da turanci? yawwa...

Autumn: emotional breakdown 

...eh.. kalaman ta sun ruguza ɗan sef istim ɗin dana samu daga malama Hafsah..da ina da low sef istim...amma yanzu shima low ɗin ƙila ya koma kwata ko babu ma duka 

Kayan ta itama ta cire ta ɗaura zane ta zauna nesa dani tana wasa da yatsunta saboda wannan gilti ɗin datake ji..Mama ce ta shigo da plate ɗin shinkafa da miya ta ajiye..  da lafiya lafiya tashi zanyi inyita tsalle tsalle amma banda yau...baƙin ciki ne fal a raina abincin ma ya fita daga raina...

'' matso ga shinkafar nadafa tuwo!" Mama ta faɗa itama dai har yanzu bata wartsake ba,na tsani inga Mama cikin damuwa badan naso ba na matso mu duka muka fara cin abincin 
bawai dan inajin daɗin abincin abakina ba nake ci...

Bayan mungama miƙewa nayi na fita ruwan sanyi na ɗiba daga drum na shige bayi nayi wanka minti talatin na fito na wuce ɗaki Vaseline na ɗauka ina shafawa ahankali a hankali ina kallon kaina ta madubi 

Mama da Asma'u suka bini da ido, bayan na gama da wannan tsohuwar wardrobe ɗin mu na buɗe na ɗauki uniforms ɗin wurin aikin mu, baƙaƙen riga da wando da hijabi half sunna nidai nawa ya wuce ƙirji... ƙaramar singlet irin ta yara da pant pink color na ɗauka na matsa can gefe na saka kayan sannan na dawo na ɗauki hula fara itama na saka 

yau shiru nayi babu mita babu kompilen,kwalli na shafa a idona dayasa suka ƙara fitowa da kyau naɗan shafa man baki wanda ni gaba ɗaya kwalliya bata dame ni ba,a ganina ni ba mace bace ban kaiba shine yasa banayi ko lip gloss ɗin bana shafawa...

duk da yanda nakeji na juyo da murmushi na kalli Mama nace '' Naga kinsa hijabi akwai inda zaki ne?" ajiyar zuciya ta sauke tace '' gidan Haule zanje ɗanta sale ne ya goce a ƙafa..''

'' subhanallahi! Garin yaya?" nida  Asma'u muka tambaya '' wai an aikeshi shine kiken shi ya samu matsala wurin taka birki suka game da me mashin " ta bamu amsa cike da alhini '' bari idan anyi Sallah sai mu tafi tare daga nan in wuce wurin aiki!" na faɗa mata gyaɗa kai tayi nikuma na shiga neman wannan abun da ake laƙa ma mutum da suna a uniform mema ake kiranshi da turanci..uhmm... yawwa nem tag ( name tag) ganin shi nayi a ƙasan wardrobe na zuƙuna na ɗauka na kakkaɓe kafin na maƙala shi a gaban riga ta sunan dake jiki ' A.Tuwo' wato Abeeda tuwo juyowa nayi naga Asma'u ta kafe ni da ido rage girman idona nayi zuwa rabi...hakan yasa zuciyar Asma'u tsinkewa...tunda muke Abu irin wannan bai taɓa haɗamu ba...bana saurin warkewa daga gori...idan har aka goranta min akan abu ko kuma akayi anfani da ammm...mema ake kiranshi da turanci idan mutum na tsoron Abu...yawwa..insikiuritis (insecurities) toh yana matuƙar wahala in manta kuma bama dawowa daidai da koma wane ne yayi min hakan...

Bayan la'asar tare muka fito mu duka muna tafiya muna hira hakan ba ƙaramin rage min abinda ke zuciya ta yayi ba..ina matuƙar son Mamar mu ita kaɗai Banda Asma'u...uhh... shike nan dai.. itama   ina sonta amma yanzu nayi fushi da ita

koda muka isa gidan Haule akwai mutane da yawa ga Saleh nan zaune da ɗauri a ƙafar shi,shima shekarun mu ɗaya,ana kiran hakan da turanci...?age mates!

nida shi bamu shiri ko kaɗan duk dashi bai taɓa kushe niba amma yana hararata gaisuwa aka fara tsakanin manya kafin aka fara magana akan Asma'u don ita duk wanda yaganta saiya maganta,tayi ƙasa da kanta tana murmushi jin ana yaba kyaunta'' oh harda ke aka zo kenan?" ya buɗe idonshi daga jin murya ta,kuma fa bacci yake..zama nayi gefen mama nace '' daga jin murya ta sai ka buɗe ido?" gyara zaman shi yayi yace '' yo na sani ko zuwa kikayi ki ƙarasani?" murmushi nayi nace '' ai saida daddare zaka ga wata mage me irin idona to nice!" tuf tuf yayi tareda faɗin '' li'ilafi ƙuraysh,aniyar moɗa tabi randa!" mutanen dake sauraren mu sunata dariya banda Asma'u...nima dai dariyar nayi 

Mama ta miƙa gaisuwa nima na miƙa tawa da sauri yace '' ankarɓi ta Mama, ba'a karɓi ta Tuwo ba!" miƙewa nayi na taɓe baki tare da faɗin '' kadai ji dashi nan..ƙafarka ta karye kowa ya miƙo gaisuwa karɓa ake don ayi saurin tashi kai kana dawo ma mutane da gaisuwar su... toh nitawa karɓaɓɓace ehe!" nakai zauren gidan naji yana faɗin '' gocewa nayi fa ba karyewa ba!" aka saka dariya nima sai na murmusa... duk da bamu shiri da Saleh wallahi ina matuƙar ƙaunar shi fisabilillah 
Kuma shima yana ƙaunata idan muka samu Abu sai mun bawa juna.. kuma bama rabuwa da cacar baki sai dai idan bamu ga juna 

da sauri sauri na kawo bakin gate ɗin Maina granda hotel... gaidar da masu gadin nayi kamar koda yaushe sannan na shiga daga ciki,ƙaton hotel ne mai haɗe da restaurant,hotel ɗin ya haɗu ya gaji da haɗuwa dan 7 star hotel ne babba kenan 

ta ƙofar baya na shiga na gaida head chief ɗin mu ko hakane sunan ta koba haka ba oho... faɗa ta balbale nidashi wai nayi latti... tafiya ta nayi nabarta da ɓaɓatu 

cikin restaurant ɗin na shiga na samu abokan aiki na suna aiki nima sai na bisu ina karɓar order,Ina matuƙar son aiki na mafiyawanci duk ɓacin ran dana kwaso anan yake kwaranyewa idan na haɗu da abokan aiki... wurin a raye da surutun mutane ƙasa ƙasa ga hasken wannan globe ɗin me kama da sarƙa da ake kira da  turanci uhmm.....candaliya ( Chandelier) ga sanyin ac da kuma Ƙamshin turaruka daban daban..duk da yau akwai sanyi dan Haryanzu rana bata fito ba,hakan bai hana a kunna ac ba

tuntuni na lura da yanda wasu dake zaune a table No. 6 suke  kallo na suna lasar baki suna maganganu amma ban bi takansu ba...kirana suke zasu bada order naƙi zuwa na jawo zainab nace '' ga wasu can kije ki karɓa '' tafiya tayi ni kuma na matsa zuwa ɗayan table ɗin 

Bayan mun gama karɓar order kowa yaje ya amso wanda ya karɓa, saboda zainab ta tafi toilet dole ni na karɓi order no.6...tura baron abincin nayi wanda ake kira da turance 🛒 cart... wannan na riƙe ba sai nayi tunani ba.. abubuwan da suka yi order shinkafa da mai da yaji,yajin cikin wata ƙaramar roba fara,sai salads da lemu, boza (burger)da tabarma (shawarma)da sauran su..

fuska a matuƙar ɗaure na isa gabansu na fara sauke musu abincin '' ji mana yan mata!" wani farin saurayi daka ganshi kaga bafulatani yayi maganar,sauran suna  kallon kallo suna magana da ido,banza nayi dashi ina cigaba da sauke abincin '' kayan jikin ki sun burgeni! musamman daga ƙirji'' yayi maganar  da shaƙiyanci, abokansa na taya shi

ji nayi kunya ta fara rufe ni jikina yayi sanyi musamman danaga kamar mu ake kallo, naji kamar insa hannu in kare ƙirjina amma konayi hakan abanza hijabin ƙarami ne

'' faɗa min bra size ɗinki in siya maki." plate ɗin dake hannuna na dire da ƙarfi jikina ya fara rawa kaɗan idona sukayi ja,na  ɗago nakejin fushi na tasomin na kalleshi, sun ɗan tsorata kaɗan'' warin bakinka na damuna ko zaka iyayin shiru?" galala sukayi su dukan su.... mutanen wurin suka kwashe da dariya..wai an kunyata ɗan gaye

a fusace ya riƙe hannu na '' dan ma kin samu a na maki magana? me zanyi da flat board like you? da mumm....'' kafin ya ƙarasa maganar na ɗauki cokali na cika shi da yaji na tura masa a baki...

mutane suka hangame baki suna kallona shiko nan take idonshi suka yi jawur jijiyoyin wuyan shi suka miƙe...abokanshi suka kasa motsi 

salad plate na ɗauka na kife masa akai na kalli cikin idonshi'' Flat board? a haka sheɗaniyar zuciyar ka take ƙawata maka ni...kuma kake yimin magana! nafi ƙarfin ka!" na faɗa ina warce hannu na nabar wurin.. tari yafara da ƙarfi ,da sauri ƙawayenshi suka dinga bashi ruwa yana haɗiye wa saboda azaba... idonshi sunyi ja dayaga abun bazai ƙare ba ya wani kwasa da gudu kamar mahaukaci salad na reto akanshi 

mutane sai dariya suke ƙawayenshi suka ajiye mana kuɗin mu a. table suka bar restaurant ɗin...



***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️