RU'UYAA (The dreams we never lived)

5. ...na tsira...🖋️

by @autum17



Bayan barina restaurant ɗin toilet na wuce na sha kuka sosai ina fitowa kuma akace manager na kirana..tsaye nake gaban shi yanata surfafa min bala'i akan abinda ya faru a restaurant yana magana akan wasu etik and etike (ethics and etiquette) '' taya za'ayi kima customer ir..."

 '' uban etik and etike manager...taya za'a yi kafaɗi irin haka? kasan abunda yayi min ne? idan ƙanwarka ce wani ya riƙe mata hannu yana mata maganganun banza zaka ce haka?..." nan nashiga sauke mashi bala'i ta inda nake shiga bata nan nake fita ba,dafe kanshi yayi kafin ya fara bani haƙuri... dan kuka nake kamar raina zai fita ina sheshsheƙa, zaunar dani yayi a ɗaya daga cikin kujerun dake office ɗin shi ya ɗauko ruwa ya miƙa min ya tsuguna gabana yana bani baki...bayan nasha ruwan na ɗan rage sheshsheƙa ya ƙara bani haƙuri sannan yace intafi hotel inyi aiki in bar restaurant ɗin 

gyaɗa kaina nayi na miƙe na fara tafiya '' na gode '' na faɗa sannan na iyarda fita, elevator na shiga ya ajiye ni a floor ɗin kitchen.. gani nayi chefs ɗin suna ta kai komo daga gani sauri suke suyi subawa kowa order shi

'' ke zo ki ɗauki wannan abincin ki kai ma room no 207 !" wani daya juyo ya ganni yayi maganar yana nuna min cart ɗin da aka shirya komai ciki.. yatsine fuska nayi kafin na ƙarasa naja cart ɗin na shiga elevator na danna 2nd floor kafin ƙofar ta rufe sai ga Abeed ya shigo yana min murmushin shi mai kyau har saida dimple ɗinsa ya fito tsayawa yayi kusa dani hannunsa ɗauke da wani rufaffen plate 

'' yau ba magana name sake?" ƙin kallonshi nayi,yayi yar ƙaramar dariya, wani abu ya zaro daga aljihunshi ya miƙo min,saida na kalli abun dake ɗauke cikin ƙaramar kwalbar nace '' meye shi?" hannuna ya riƙe ya samun a tafi...yace '' sunan shi Usma grass root,ranar naji kina tambayar abinda zai sa gashin mutum ko girar mutum da eyelashes suyi tsawo su ciko da sauran su shine na kawo maki...amma kibi ahankali idan ya shiga ido akwai zafi sosai!" ya ƙarashe maganar yana kashe min ido, juya abun nayi a hannu na kafin na ƙara kallon shi nace '' ina ka samu?"

'' siya nayi " ya bani amsar '' nawa?" na sake tambaya '' dubu sittin!" zaro ido nayi wannan albashi nane na wata uku,kuma shima haka 

'' ko baki so?" ya tambaya yana ɗage min gira '' girgiza kai na nayi...sai kuma nace '' meyasa zaka kashe kuɗi masu yawa don ni bayan kai ma ji da kanka kake?" murmushin gefen baki yayi min wanda bansan ma'anar shiba '' kada ki damu,kedai kiyi amfani dashi kawai!"

'' meyasa kake kulani?" na tambaya hannu naɗe a ƙirji na juyo ina kallon shi,ya shafa ƙeyarshi'' son ki nake!" waro ido nayi da farko sai kuma na fara dariya kamar mahaukaciya harda ɗaura hannu akai...'' bana son wasa... me yasa kake kulani?" nayi tambayar fuska a tsuke, ajiyar zuciya ya sauke ya koma serious yace '' saboda kece the most authentic person Dana taɓa gani a rayuwa ta!" kallon shi nake cikin rashin fahimta bangane me yake nufi da wannan kalmar ba,gane hakan da yayi yasa ya fara min bayani,'' idan akace mutum authentic,ana nufin yana abu da gaske,baya ɓoye ɓoye,baya yin abu dan mutane su gani..da zuciya ɗaya yake abu!" yake juya ido kamar mace

'' Oh..'' na furta ahankali, na faɗawa duniyar tunani da gaske ni...mema nene kalmar? aidai kunji Abinda ya faɗa ko da gaske ni haka nake? '' keep being yourself,zaki gani wata rana akwai wanda zai soki dan hakan kawai..zai soki a yanda kike batareda ya nemi ki canja wani abu game da kanki ba!" 
 

buɗewar elevator yasa yayi gaba batareda ya sake cewa komai ba,ganin idan na cigaba da tsayuwa elevator zata rufe dani a ciki yasa na fito ina tafiya a hankali ina tura cart ɗin da gaske akwai wanda zai soni a yanda nake batareda na zama mai kyau har na fitar hankali ba? naga yanzu mazan sun iskance idan har baki da wa'yannan kyaun zuciya bazai sa su kulaki ba!

Na sauke ido tare da danna ƙaraurawar ɗakin na ɗari biyu da bakwai...da turanci aka amsa '' come in..'' taɓe baki nayi ina faɗin ' yan wulaƙancin ' a raina 
tura ƙofar nayi na shiga wani irin daddaɗan ƙamshi na dukar hancina da kuma sanyin Ac, ɗakin yayi min kyau sosai king size bed ne me ɗauke da jan zanen gado kamar wani ɗan tsafi sai dogon benci mai katifa..aidai kun gane shi irin wanda ake ajiye wa gaban gado ko? wanda masu kuɗi tsabar iyayi suke ajiyewa bayan bashida wani amfani 

Sai jan carpet me ratsin fari a gaban gadon,daga gefen dama na ɗakin idan an shigo TV ne sai wardrobe dake kallon ɗayan bangon daga Tsakiyar ɗakin akwai kujera zaman mutum biyu da table a gaba sai labule masu nauyi suma jajaye 

painting ɗakin kamar fari kamar yellow bansani ba sai toilet...ɗakin ya burgeni sosai duk da ba wannan ne karo na farko da nake shiga ɗakin hotel ba

wani saurayi ne zaune a saman kujerar daga shi sai ƙaramin wandon da ko rabin cinyarsa bai kai ba,askin kanshi low cut kyakkyawa ne sosai ban taɓa ganin wani me kyau irin nashi ba duk rayuwata fuskar sa ɗauke take da manyan laɓɓa (full lips) na ƙasa yayi pink irin na Asma'u amma na sama kalar fatar jikinsa ce wato ruwan ƙasa( brown) hancinsa dogo mai kyau haka ma idanun shi farare masu ɗauke da ƙwaya brown kamar zuma..yana da ƙaton jiki.. '' kutumelesi!" kalmar ta fito daga baki na batareda na shirya ba,amma wannan anyi babban ɗan iska! wane irin iskancine wannan? ji nayi na fara tafasa daga ciki ni kyaun shi bai wani burge Ni ba kokaɗan 

gefen wando na na taɓa naji turaren yajina na nan.. gyaɗa kai nayi tsaye daga bakin ƙofa '' ga abincin na kawo'' na faɗa batareda motsawa ba daga inda nake... ɗagowa yayi ya kalleni tareda sakar min Murmushi mai kashe zuciya sai dai ni tawa zuciyar bata mutu ba!

 ya tashi zaune yana shafa kuncin shi yace '' kece wacce ta cika ma wani baki da yaji ko?!" sai dana harare shi nace '' ko kaima kana so ayi maka fiye da nashi ne?" Naji kamar in share wannan banzan murmushin dake fuskar shi...taya ma ya sani? munafukai masu kwana da ido ɗaya a ko ina...

'' to ƙaraso ciki mana...''ya share abinda na faɗa


dogon numfashi naja tare da juya idona a kaikaice jin yanda zuciya ta take ingizani da inyi mashi wanka da turaren yaji amma sai na dake na tura cart ɗin har zuwa gabanshi na fara sauke abincin duk abunda nake inajin yanda idonshi ke yawo a jikina hakan ya ƙara hasala ni miƙewa nayi tareda ɗaura hannuna a ƙugu a matuƙar tsiwace nace '' wai Malam kallon bai isa haka ba? ko kai maye ne aniyar moɗa tabi randa!" Takaici duk ya isheni...bai dena kallo na ba
sai ma kamar dariya nabashi '' meye sunan ki?" ya tambaya '' ba faɗin suna nazoyi anan ba!" na bashi amsa a zafafe daga gani me kuɗi ne kuma ni banason masu kuɗi

'' sunana Ibrahim '' 

'' ban tambaye ka ba!" gyaɗa kanshi yayi yana riƙe dariyar shi, da alamu wannan ne karo na farko daya haɗu da masifaffiyar yarinyar da kyaun shi baisa ta rusuna ba lashe bakin shi yayi,'' zamu iya zama abokai?" yayi maganar yana miƙo hannu mugaisa 

'' sunana ba chidera ba dakake miƙo min hannun ka,nan kano ne garin hausawa idan kana buƙatar abokai mata katafi Lagos! !" nayi maganar ina sauke abu na ƙarshe dake saman cart ɗin na miƙe zan tafi ya riƙe hannu na..shima ya miƙe,ji nayi zuciya ta tana bugu da mugun ƙarfi, jan hannu na nayi a tsiwace nace'' dalla sake min hannu dan niba yar iska bace!" amma ko gezau sai ma ƙara riƙe hannun da yayi yana murmushi, wallahi tsoro naji ya saukar min irin wanda ban taɓa ji ba...na kuma san saboda ba kayane a jikinshi 

ƙwace hannu na nayi ina matsawa baya shima yana matsowa har muka dangane da window yayi min runfa da faffaɗan ƙirjinshi,ji nayi numfashina nafita sama sama,ya saka idonshi cikin nawa Haryanzu da murmushi a fuskar shi '' ww...wai...mmm..meye..haka?" nayi maganar a tsorace ina damƙe turaren yaji na idan naga abu yaci tura in watsa masa inyi gaba, ahankali cikin raɗa ya matso da fuskar shi dab da tawa yana faɗin '' to waye ɗa iska?" Yawu na haɗiye ina nadamar abinda na faɗa.. 

'' banda amsa yanzu kam!" na kawar da fuskata gefe dan yanzu ba shine lokacin rashin kunya ba...yayi dariya daga ƙirjin shi tare da danne leɓenshi da fararen haƙoranshi...

Hakan ya ƙara tsorata ni sai ƙoƙarin basarwa nake kamar bana jin tsoro amma ƙafafuna sai rawa suke..harda ɗan ƙaramin fitsari nayi a wando...

 murya na rawa nace '' nidai matsa min in wuce!" maƙe min kafaɗa yayi yana kallon idona.. pepper spray ɗina zan jawo yayi saurin ɗaura hannun shi mai bala'in laushi a nawa...ɗan ƙaramin sauti ya ƙwace min a razane nayi hiri hiri da ido...tawa ta same ni,yana kallon cikin idona da manyan nashi, da zurfaffar murya yace '' meye sunan ki?" zuciya ta kamar zata fita daga ƙirjina tsabar yanda take bugu...har so nayi in ture shi amma ina zan taɓa a jikin nashi daba kaya?

Runtse idona nayi na ɗaura hannayena a ƙirjinshi ina turawa da duk ƙarfin da Allah yayi min amma bai ko matsa ba sai dariya da naji yana yi '' wato abun ya kai har da cin zarafi ko?"

Ya tambaya murya ƙasan maƙoshi... buɗe idona nayi suka shige cikin nashi,da sauri na ɗauke su na mayar akan hannayena dake manne da ƙirjinshi...gefe da gefe...saman kan baƙin abun nan da maza da mata suna dashi...yawu na haɗiye zan janye hannu na ya riƙe....

saura kaɗan zuciyata ta fito ta baki na...murya na rawa nace '' n ...nifa...ka rabu..da..Ni...baka gani mayya bace...zan iya shanye maka..jini... ka barni in fita..toh!" wannan barazana ko ƙaramin yaro aka yiwa ita tsaf zai kwashe da dariya bare babban mutum...yake kallona kamar abinda na faɗa shine mafi girman wasa daya taɓa ji...

'' oh.. Allah sarki...so you're a witch?" Ɗaure fuska nayi dan bana jin turanci can can...kuma ban gane abinda ya faɗa ba...sai na gyaɗa kai kawai ..na ɗauka ya rabu dani...ƙara matso ni yayi..nima na sake shigewa cikin bango..ƙafafuna manne da bangon...yanda yayi min runfa da jikinshi idan mutum ya shigo bama zai san da akwai ni a wurin ba...


'' i surprisingly have a thing for witches with gray eyes...can I kiss you?" Batareda na fahimci abinda ya faɗa ba na shiga gyaɗa kai kamar ƙadangare nidai kawai ya barni in tafi...tsawon shekarun dana kwashe ina aiki a hotel ɗin nan ba'a taɓa rutsani har haka ba...sai dana haɗu da wannan kyakkyawan ɗan tashan...har lokacin idona sunƙi komawa dai dai..duk na gama tsora ta...na ɗauka nan ne ƙarshe yanzu kawai zai yi dariya ya juya ya koma wurin abincin shi amma a mamakina sai 

ya sauke yatsan shi saman laɓɓana yana kallon cikin idona wani irin abu naji yana min yawo tun daga tsakiyar kaina har yatsun ƙafafuna kuma naji kamar jikina ya mutu, karkace kanshi yayi tare da lumshe ido zai sumbace ni,

wata irin gigitacciyar ƙara na saki,tare da buga mashi guiwata tsakanin ƙafafun shi na kwasa da gudu..nabar shi da durƙushewa ƙasa yana zagi da turanci...yau kallon fim ɗin China yayi min rana...
Kamar makauniya naji naci karo da mutum ..kuma wannan mutum ɗin bai yi komai dan taro ni ba lokacin da nayi tangal tangal kafin ɗuwawuna su sha ƙasa 

runtse idona nayi saboda zafi, kafin na buɗe su ina kallon mutumin dake tsaye gabana,saye da ƙananan kaya riga mai dogon hannu ash color wando baƙi ya ɗan tattare shi daga ƙasa fuskar shi sakaye da face mask...sumar kanshi baƙa wulik ga wani sihirtaccen ƙamshi da yake zubawa...yana kallona da baƙaƙen idonshi kamar na maijin bacci da sauri na miƙe ina kallon shi a masife nace '' baka ganine? baka ga ka ture niba?idan wannan ramen dake fuskarka bai aiki,abunda xaka iyayi dan taimakon kanka da kowa ma shine ka zauna cikin ɗaki basai kazo kana bangaje mutane ba!'' na ɗanyi nadamar yanda na zage shi amma ban bashi haƙuri ba..sai ma

nayi tsammanin yabani haƙuri amma sai cewa yayi '' Get.Out.of.My.Way!" yayi maganar da wata irin ƙatuwar murya idonshi suka ƙanƙance a kaina...daga yanayin maganar shi zaka san ba ɗan Nigeria bane ..abinda ya faɗa aiko wanda baije makaranta ba aka cema get out yasan abinda ake nufi gyara tsayuwata nayi gaban shi nace '' bazan matsa ba ka..!" ban gama sentence ɗina ba ya wani bangajeni gefe saura kaɗan in faɗi yayi tafiyar shi.. sakin baki nayi kafin naja wata gora dake saman wani cart ɗin abinci da aka aje a hanyar na saita bayan kanshi na jefe shi...sai ga ƙeya.. juyowa yayi yana kallona, hannu dunƙule kamar zai naushe ni

gwalo nayi mashi kafin na kwasa da gudu ina dariya aini ɗin bata wasa bace... ganin lokacin sallah yayi yasa na wuce masallaci bayan na shiga Baye nayi tsalki saboda yanfa mutumin nan yasa nayi fitsari a wando,ana gama sallah na dawo na cigaba da aiki..sai ƙarfe tara shift ɗina ya ƙare har nayi sign out naga Macijin sari ka noƙe da wata mata zaune a wani table....jinayi haushi ya kamani dole inyi wani abu akan abinda ya faɗa min ɗazu 

tare suke saukowa daga stairs cikin shiga iri ɗaya baƙaƙen riguna da baƙar jacket a sama sai baƙin wando jeans suna zuba ƙamshi, har yanzu da face mask baƙi a fuskar shi Ibrahim kuma magana yake masa idonshi ya sauka akan tuwo data karɓi plate daga hannun wani waiter tana tafiya kamar bada gangan ba ta juye duk abinda ke cikin plate akan Macijin sari ka noƙe dake riƙe da hannun yarinyar da suke tare...daga gani yarinyar bazata wuce sa'ar Tuwo ba... tsayawa sukayi su biyun suna kallo... Macijin sari ka noƙe ya wani miƙe kamar wanda aka watsa ma ruwan sanyi '' Abeeda wannan wane irin rashin hankali ne?" kukan ƙarya Tuwo ta fara tana faɗin bada gangan bane amma ya zaƙe sai faɗa yake mata

ganin irin kallon da mutanen wurin ke masa kamar na wani mara tausayi yasa ya shanye fushin shi sai kuma a fusace yabar restaurant ɗin yarinyar da yazo tare da ita ta matso wurin Abeeda '' Nagode!" ta raɗa ma Tuwo a kunne kafin ta bar wurin 
'' i like that girl!Ro..?" Ibrahim ya faɗa ma gayen dake kusa dashi amma koda ya juyo yaga wurin babu kowa... murmushi yayi yabi bayanshi..

Batareda wani damuwa ba nima nafita daga restaurant ɗin ina tafiya ina tsalle tsalle iskan hadarin na ƙara ratsani,ni tuni ma na mance da wannan mutumin da muka haɗu dashi a hotel '' hi kyakkyawa '' naji Muryar shi daga bayana da sauri na juyo ina kallon shi dan harabar hotel ɗin akwai haske sosai kamar rana..take na gane shi, haɗe rai nayi na juyo a masiface nace '' yawwa ɗazu dana shigo ɗakin ka shine zaka wani yimin runfa kana laguda ta ko? toh bari kaji niba yar iska bace idan wani abu ya sake haɗa mu ka taɓani sai na tsinka ma mari a fuska !" Ya shafa fuskar shi tare da matsowa dan dani ba shiri naja baya

'' ai saida na tambaya idan zan iya sumbatar ki,kika ce eh remember?" ɗaure fuska nayi

'' taya ni ban tuna ba?"

'' not my fault if you have short memory!" ya kashe min ido...naji kamar in soka mashi yatsa cikin ido...naja tsuki ƙasa ƙasa zan bar wurin ya jawo ni ya rungume da ƙarfi 


da duk ƙarfin da Allah yayi min na gantsara mashi cizo a gefen wuya 

'' ahhh!!" ya sake ni tare da ja baya...da wannan damar nayi amfani zan gudu ya damƙo hijabina,ba shiri na ƙame ƙam...

''ki gudu mana!" Ya raɗa min a kunne..oh ni tuwo na shiga uku waye wannan mutumin wai? gabana sai faɗuwa yake...ƙamshin turaren sa ya dabaibaye ni kamar ni na shafa.. iska na haɗiye ina kalle kalle koda Allah zai sa wani ya kawo min ɗauki 


'' ashe ke vampire ce? a freaking vampire...'' sai yayi dariya tare da sakina ya zagayo gabana hannu a aljihu...


Autumn: what an absolute moron!

Abeedah: ashe kin gane...ji nayi kamar in naushi muguwar fuskar shi

'' Meye sunan ki'' ya dawo dani daga duniyar mafalkin dana shiga..ko kaɗan bai burgeni ba..na ɗage mashi kafaɗa

'' nima ban sani ba!" na amsa ina ja baya..hannu ya miƙa zai ɗage min hijabi 

'' wai meye haka?" na faɗa murya a sama 

'' sunan ki nake so in gani...''

''.sunana Khadijah!" Na faɗa mashi sunan daya faɗo raina...gyaɗa kanshi yayi ya zaro wayarshi daga aljihu ya miƙa min

'' your digits!" Daga shi har wayar tashi binsu nayi da kallo ƙwaƙwalwa ta na loading a 360...tunda muka haɗu sai turanci yake ni kuma baji nake ba...

'' lambar ki!" Ya ɗan waro min idonshi...ɗauke nawa nayi nasa mashi lambar da ban san kota waye ba..nufa bamu da waya..sai ta mama dake ringin sau ɗaya a shekaru masu yawa...har da saving na mashi cikin style 

''Cardy..I like the sound of it..sai munyi waya..goodnight ..Khadija!'' ya sakar min Murmushi kafin yayi gaba ya barni tsaye...

ajiyar zuciya na sauke tare da fashewa da dariya '' ace wacce zai kira ɗiyar soja ce...kuma babanta ya ɗauki wayar a wannan lokacin?" wata sabuwar dariya na kwashe da ita kafin nabar wurin kada ya dawo ya same ni 


koda na koma gida Mama na zaune a tsakiyar gida suna hira itada da Asma'u na kuma san ni suke jira '' salama alaikum '' nayi sallama na shiga '' wa'alaikumssalam '' Mama ta amsa da sauri nazo na faɗa jikinta '' Mama antaso!" '' maraba maraba!" Mama ta amsa min, miƙewa nayi na shiga kitchen na zubo abinci Batareda na cire hijabin ba nashiga ci..

 su biyun suka kafeni da ido...''.akwai wani abu ne?" 

'' ina kika samu wannan turaren...ƙamshin sa irin na maza?" Mama ta ƙanƙantar da idon ta...sarƙewa nayi da abincin dake cike a bakina...da sauri Asma'u ta kawo min ruwa amma naƙi sha...kamar zan mutu amma kuma tunanin ƙaryar dazan sharara nake..mutumin nan ya gama dani wallahi 

Mama taƙi dena kallo na...sai dana gama tarin ido jawur nace '' zainab ta kawo..ba yayanta ne...'' 

saida mama tayi min irin kallon da ban san ma'anar shiba ta gyaɗa kai..
ina tsaka dacin abinci aka fara ruwa ba sallama,da sauri muka faɗa ɗaki '' ruwa ba sallama ba iska". inji Asma'u Mama tace '' shikuma hadarin da yake nan baki gani ba ko?"...saida na cinye abincina tass sannan na ɗauki zane na fito waje rataya zanen nayi a bakin taga na kwaɓe uniforms ɗina ya rage daga Ni sai pant da singlet na shiga cikin ruwa...ina tsalle tsalle 

'' waini Allah yaushe Tuwo zata girma?" inji Mama tana shafa kan Asma'u dake saman cinyarta...sai wurin ƙarfe goma sannan na cire pant ɗin da singlet na ɗaura zani na shiga ɗaki ina rawar sanyi Mama ta bini da ido kasancewar fitilar da aka kunna yasa nake ganin inda nake saka ƙafa...wata doguwar riga rabin cinya nasa na saka pant na faɗa saman gado,Mama ta gyara ma Asma'u kwanciya sannan ta rufe mana ƙofa ta kwanta... matsawa nayi kusa da ita na riƙo hannunta '' ke wai yaushe zaki girma?" ta tambaya tana ƙwace hannun ta,turo baki nayi '' to Ni ban iya bacci saina riƙe wani abu!" tsuki taja ta juya min baya kawai sai na rungumeta tabaya...lumshe idona nayi inaji yanda ruwa ke dukan kwanon mu...har bacci yayi gaba dani 

har ma tsawon kwanaki nida Asma'u bamu dawo daidai ba da Mama tagane hakan ta tambaya sai cewa tayi '' Ni Na gaji da yanda Tuwo takeyi ta karɓi kanta yanda Allah yayi ta amma saita ta gwada kanta dani bana jin daɗi!" tayi maganar ne yanda duk mai saurare zai ɗauka abinda nakeyi ne bata so,amma a zahiri bataso in faɗama Mama abinda ya faru... murmushi nayi na miƙa ma Mama ruwan shinkafar dana ɗauko na zauna gabanta ta fara shafa min batareda tace komai game da abinda Asma'u ta faɗa ba...niko tunani kawai nake yaushe Asma'u ta iya makirci har haka? duk dan saboda wancan makirin mutumin ne ko dai dama haka take? haɗa ido mukayi ta sakar min harara 

lumshe ido na nayi... Asma'u ba haka take ba saboda mutumin nan ne na tabbatar... amma saidai akwai wani sashe na dake faɗa min dama haka take nice dai bansani ba...ture tunanin gefe nayi nace '' Mama ranar Lahadi zamuyi wanki ko?" '' Eh'' ta amsa '' daga nan sai kimin kitso in gani idan gashina ya ƙara tsawo!" jinayi Asma'u na faɗin '' gashin ki nanan yanda yake,tsawon nan dai bazai ƙaru ba!" kamar ba ita tayi maganar ba tacigaba da assignment ɗinta Wanda nima ina dashi amma bazanyi ba

'' yau bazakije aiki ba?'' Mama ta tambaya girgiza kai nayi '' hutu nake '' na bata amsa 
************

Yan kwanakin nan Asma'u ta sauya sosai a gida idan gaban Mama ne saita dinga yama ake cema kalmar a Turanci.... pretending! Sai ta dinga pretending kamar ina wani abun da bata so, a makaranta ta dena zuwa wuri na kuma a bayyane take kai kanta ga Macijin sari ka noƙe... sannan take ƙarayin komai dan tasani inji ba daɗi game da kaina...take ƙara nuna min abubuwan data fini dasu,tafini kyau, tafini gashi,ta fini ƙwaƙwalwa....kuma tayi sa'a don kuwa emotional break down ɗina ya dawo sabo fil kullum sai nayi kuka safe da rana da daddare kuma hakan ba ƙaramin faranta mata yake ba,duk dani ban fahimci hakan ba,na ɗauka duk dan saboda Macijin sari ka noƙe ne sai na ƙara himma wurin son nuna mata shi wane irin mutum ne amma bata koso taji....

***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma ₦800

Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️