RIKICIN DUNIYA

Chapter 4

by @meenatyandoma

*RIKICIN DUNIYA...*

©️ Meenat A. 'Yandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

CHAPTER 4
...Takalman da suka gani a kofar ɗakin ne ya tabbatar masu akwai wata a ciki. Gefe guda suka tsaya suna faman jira musamman Wasila dake ji tamkar tayi tsuntsuwa ta ganta a gaban Boka Bakurmi.
"Umma ji nake kamar aikin nan za a samu matsala. Yau da muka je wurin Malam Bawa ya tabbatar mana da aiki ya ci, sai yadda Nadiya tayi da Kasim."
"Dadina da ke wani lokacin ke sakara ce. Ko a wurin sunayensu ya kamata ya yi ki gane, wancan Malam Bawa aka ce wannan kuma Boka Bakurmi. Ba mallaka ba ko auren Kasim tayi sai ya lalace in dai Bakurmi na raye"
Murmushin da bata san ya kubce mata ba tayi.
"Umma shi ya sa nake masifar kaunarki. In babu ke ina zan saka raina, ji dai yadda kika tsaya mini akan wannan matsalar. Dole ki huta ki je Umrah kije hajji, kaf kasashen duniya sai kinje yawo"
Dariya Umma tayi.

"Shi ya sa na tsaya miki kai da fata ganin kin mallakesa, saboda nasan har abada ba zaki taba guduna da arziki ba"
"Wace ni Umma, Ni din banza"
Rufe bakin Wasila yayi daidai da fitowar matar dake cikin dakin.
Kutsa kai suka yi tare da a bajewa gaban bokan.
Ba su ce uffan ba face fiddo kasar daya bukata.
Katon faifai ya dauko ya hadeta da yar uwarta, daga bisani yayi wani Surkulle kasar ta raba kanta ko wace tayi gefe guda tamkar a mafarki.
Zabura Wasila ta yi.
"Na shiga uku!"
Ta furta a gigice muryarta na kyarma.
Tuntsurewa da dariya Bakurmi ya yi "wanda ya shirya ɓata bai kamata a ce karamin abu ya na gigita shi ba. Leko nan ki gani"
Ya karasa maganar ya na mai nuna mata ƙatuwar kwaryar dake gabansa.
Togewa tayi ilahirin jikinta na kyarma. 
"Umma ki leƙa a madadina"
Ta karasa maganar cikin tashin hankali.
"Ki leko na ce"
Ya daka mata uwar tsawa da ƙatuwar muryarsa mai kama da rugugin aradu.
Cikin rikicewa ta mike da rarrafe ta karasa a gabansa.
Ita da Kasim ta gani zaune a cikin tamfatsetsen falo suna ta annushuwa.
Dafe ƙirji Wasila ta yi. "Ni....Ni....ni ce da Kasim"
Dariyar da tafi ta farko ya yi, daga bisani ya turɓune fuska.
"Indai muka saka abu a gaba, to fa tabbas sai mun cimmasa duk rintsi. Amma ina hango duhu a cikin aurenku tabbas akwai matsala"
Ya karasa maganar ya na kallonsu da daka-dakan idanuwansa.
"Koma wace matsala ce muna da kai, don haka ba matsala ba ce"
Umma ta fada.
Dariya ya sake babbakewa da ita a karo na barkatai.
"ki je ki fara shirye-shiryen auren Kasim saboda da kanshi zai dawo gareki."
Sauran kudin da Kasim ya bata suka ware wanda boka ya kayyade za a bayar suka baro wurin, Wasila tafi kowa farin ciki Saboda ji take ina ma ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.
Gaf da magriba suka dawo gida, tun daga yanayin gidan suka tabbatar da Malam Ɗayyabu ya yi ciniki. 
Kara washe baki Umma ta yi saboda yau ji take tamkar an biya mata hajji...

Gidansu Nadiya
Tun bayan dawowarsu a makaranta take faman kiran layin Kasim amma baya shiga.
Abin duniya duk ya ishe ta zuciyarta ta fara yi mata wasiwasin anya Malam Bawa ya yi aikin yadda ya kamata?
Ƙarar wayarta ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula.
Sassanyan murmushi ta saki tana mai kanga wayar a kunnenta.
 "Sorry Wasilata Bani kusa naga kinyi mini missed call."
Rass! Gaban Nadiya ya yanke ya fadi.
Jin abinda Kasim ya fada
"Baby! Me Ka ce, ni kake kira da Wasila?"
Daburbucewa Kasim ya yi tamkar ya na a gabanta.
"Yi hakuri kinsan ina da wata kanwa mai sunanta. To yau sun zo gidanmu ne shi ne ta matsayin sai na kaita shan ice cream, Amma BA da niyya nayi ba kiyi hakuri"
Duk da wata zuciyar gargadinta take yi akan kada ta yarda da shi, tsagi daya na zuciyarta tuni ya aminta da Kasim.
Hirar soyayya suka sha sosai da Kasim, daga bisani ya kashe wayar.

Ba tare da tasan dalili ba samun kanta tayi da jin faduwar gaba.
"Wasila! Wasila"
Ta shiga maimaita sunan tamkar mai koyon magana.
"Shalele! Lafiya naji kina ta faman nanata sunan Wasila ko wani abu ya faru ne?"
Inna ta fada tana mai shigowa dakin ta zauna.
"Inna! Kamar fa akwai matsala"
"Matsala kuma ? Wace irin matsala, fada muni har kin saka na ji gabana ya yanke ya fadi"
"Kasim ne fa ya kira Ni da sunan Wasila abin da bai taba yi ba, kuma fa hujjojin da ya bani na cewa kuskure ne basu gamsar da ni ba"
"Kai har naji hankalina ya kwanta. Wannan sokuwar yarinyar ita da uwarta da ke fama da bakin talauci, me zasu iya yi bare har su kwace miki saurayi. Ki kwantar da hankalinki ko baku je wurin Malam Bawa ba ne?"

"Munje har ma ya tabbatar mini da sai yadda nayi da Kasim. Sannan na ga alama saboda duk da a waya ne ba a gabana yake ba naji yadda ya rude"
"Yawwa ko ke fa? Yanzu abin da nake so shi ne ki kwanta kiyi baccinki, ba gobe kika ce mini zaku fara jarabawar karshe ba?"
"Eh"
"To maza kwanta yadda za ki tashi da wuri, a matse nake ku gama ko Kasim ya aiko ayi maganar aurenku"
Ji Nadiya ta yi kamar an tsomata cikin aljannah., Inna ɗakinta ta koma sakamakon Mahaifin su Nadiya na kwala mata kira.
"Anti!"
Jamila ta Kira sunanta cikin sanyin murya.
"To shugabar Mayu ta kaf Africa. Me ya faru?"
Nadiya ta karasa maganar cikin masifa tana mai yarfa hannuwa.
"Don Allah kiyi hakuri da abin da zan fada, na sani Ni ban isa in Baki shawara ba. Amma duk da haka zan tuna miki da wani abu, ke da Wasila duk kuna tafiya ne a cikin duhu ba tare da sanin inda kafafuwanku ke sauka ba"
"Ban gane a cikin duhu ba, fito fili kiyi muni magana don kada ki fake da alaye kina zagina a kaikaice"
Ajiyar zuciya Jamila ta yi
"Anti me ye amfanin zuwa wurin bokan da kuke yi, mijin da zaki aura fa ne..." Ba tare da ta karasa maganar ba Nadiya ta luka ashar.
"Ke ni kike fadawa wadannan maganganun? Yaushe nayi lalacewar da za ki saka ni a gaba kina fadamin abinda kika ga dama?"
Murmushin takaici Jamila keyi, wannan abu shi ya kara tunzura Nadiya hannu ta ɗaya ta tsinketa da mari.
Zafin marin ya saka Jamila mikewa rike da kumatu.
"Me nayi miki, daga fadar gaskiya?"
"Ke har kin kai wadda zata kalli tsabar idona ta ce tana fada mini gaskiya, wacece ke akwai wanda ke bukatar a fada masa gaskiya sama da ke? Kin maƙalewa wancan shashashan Ustazun wanda bazai amfane ki da komai ba sai baƙin talauci"
A yanzu kam Nadiya ta kawo Jamila karshe.
"Aa fa, anzo wurin da bazan iya jurewa ba. Shi ɗin malamina ne don haka bazan bari wani abu ya je kusa da mutuncinta ba bare har yayi kokarin taɓasa. Alhamdulillah! Na gode Allah da talaucinsa tunda bai sakani a hanyar ɓata ba bare har in je gidan wani mushiriki akan ya yi min aiki a kansa"
A fusace Nadiya ta yi kan ta da mugun nufi.
Bata bari ta karaso ba ta fice da gudu.
Hayaniyarsu ita ta fito da mahaifansu.
"Jamila me ke faruwa haka, abin da baki taba yi ba yau kece ke aikatawa?"
Cewar mahaifinsu.
Hawayen da yaga tana yi ne ya tabbatar masa ita ce da gaskiya kamar yadda ya zata tun farko.
"Ke Nadiya me ya faru duk da na san ko ba a tambaya ba laifinki ne"
Cikin tijara da rufewar ido ba tare da la'akari da wanda ke yi mata maganar ba ta hau zazzage tijara.
"Ni dama a gidan nan nasan ba a sona, kome nayi ban iya ba. Karamar yarinya tayi mini rashin kunya amma a rika bata gaskiya. Na gode ma Allah da ya saka aurena zanyi in bar muku gidan"
"Me Jamilar tayi miki nasan ba mutumci ne da ita ba "
Inna ta fada tana kokarin kamo Jamila.
"Kul na kara ji kin aibata mini ɗiya."
Hannu Nadiya ta kai da zummar cafko Jamila da ke boye a bayan mahaifinsu, Malam Amadu data kawo shi har wuya hannu ya daga ya wanke ta da mari dama da hagu, ji da ganinta daukewa suka yi na wucin gadi. Inna kuwa salati da sallallami ta hauyi tana rirrike Nadiya...

Meenat A. 'Yandoma
***