MEERAH

03

by @oumfatima33

*MEERAH*

    *OUM FATIMA* 
        ***


      *03*


    Nawaz yayi karatu har matakin degree aiki ne dai har yanzu bai samu ba, saboda yanda ƙasar tamu ta zama. Sai ka gama shan walahar karatu samun aiki ya gagara idan ba wata hanyar ce da kai ba.

   Ya fara waƙa ne tun yana secondary school, sai dai a lokacin bai ɗauki abin da muhimmanci ba. Yana yine kawai a matsayin nishaɗi.

   Abokinsa JB shine ya fara ankarar dashi, kasancewar shi tun yana matashin ya fara harkar studio. Shi ya fara jan ra'ayinsa a kan ya gwada ɗora waƙar.

   Tun baya mayar da hankali har dai wata rana ya amince ya bi JB zuwa studio ɗinsu, wanda asali na yayan JB ɗin ne. Lokacin da ya ɗora waƙarsa ta farko mai taken ƙauna, ba ƙaramin mamaki ya ba wa Jafar yayan JB ba.

   Domin kai tsaye ya fahimci yaron yana da wata irin baiwa, wacce idan ya samu mai tsaya masa ba ƙaramar ɗaukaka zai samu ba.

   Tun daga wannan lokacin ne kuma abin ya fara shiga zuciyarsa, don shi da a burinsa idan ya kammala secondary ya tafi jami'a yayi karatu ya samu aikin da zai taimaki kansa da ahalinsa.

    Lokacin da ya samu iyayensa da batun waƙa da farko basu amince ba, sai da Jafar ya same su har gida ya fahimtar da su irin baiwar da Nawaz ɗin ke da ita a harkar. 

   Ya nuna musu cewa kada su daƙile masa baiwarsa don ba'a san me zai zama ba a nan gaba, sun fahimta sun kuma amince suka bishi da fatan alkairi. Tun daga nan kuma abin ya shiga ran Nawaz ya fara yin waƙoƙi masu matuƙar daɗi, sannan ya gina burin son zama babban mawaƙi wata rana.

   Wannan kenan.


   Da sallama ya shigo cikin gidan nasu da yake a tsaftace an killace komai a inda ya dace, kasancewar mamallaka gidan suna da tsafta sosai. Amsa masa Umma ta yi tana daga Kitchen ta na ƙoƙarin ɗaura tuwon dare.

   Ƙarasa wa ya yi ya zauna saman tabarmar dake shinfiɗe a cikin baranda yana sauke ajiyar zuciya, fitowa Umma tayi ta samu wuri ta zauna a kusa da shi.

   "Sannu da aiki Umma." Nawaz ya faɗa cike da ladabi yana kallon Mahaifiyar tasa, yana jin zuciyarsa na motsawa da tausayin yanda ta fito ta na share hawayen hayaƙin da ta gama shaƙa a kitchen ɗin. Sakamakon iccen da take amfani dashi baya kamawa.

    Yana fata Allah ya cika masa dukanin burikansa na samun abinda zai kyautata rayuwar iyayensa da ta ƴan'uwansa, maganar Ummance ta dawo dashi daga tunanin daya yi nisa a ciki ta na cewa.

   "Yauwa Yayansu, ya aikin? Yau baka dawo Kaci abincin ranar ka ba?." Ajiyar zuciya ya sauke yace.

   "Alhamdulillah Umma, yau na ɗora sabuwar waƙa ta shi yasa na daɗe." 

   "Masha Allah, Allah ya baka sa'a a kan dukkanin abinda ka saka a gaba na alkairi." Umma ta faɗa cike da ƙaunar ɗan nata, duk da dai ta na danne wa tana masa kara kasancewarsa ɗan fari. Don ko sunansa bata kira sai dai tace wannan ɗan, ko kuma tace yayansu.

   Da "Ameen." Nawaz ya amsa yana jin daɗi a duk lokacin da tayi masa addu'a.

   "Ina su Raihana ne?." Ya tambaya sakamakon jin gidan shiru.

   "Duk sun tafi islamiyya." Ta bashi amsa, daga haka ta miƙe ta shiga Kitchen ta ɗauko masa abincinsa a cikin food flask ɗin da ake saka masa kullum.

   Abincin ya fara ci cikin yanayinsa na sanyin jiki da rashin kwaramniya, ya ɗago ya kalli yanda hayaƙi ke fitowa daga Kitchen ɗin. Umma ya kalla sannan yace.

   "Ya aka yi iccen yake hayaƙi sosai kuma yaƙi kamawa yana ta wahalar dake?." 

   "Ka gan shi ban san inda Salman yaje ya sayo min shi ba, ɗanye ne jagab baya cin wuta ko kaɗan sai uban hayaƙi da yake yi." Umma data fito daga Kichen ɗin tana face majina saboda fifita wutar da tayi ta bashi amsa.

   "Bari na kammala cin abincin na fita ko za'a samu busassu sai a kawo maki, amma wannan kafin ki gama ai zai saka makon ciwon kai."cewar Nawaz yana kai laumar abinci bakinsa.

   "Wallahi kuwa ko kaɗan bashi da daɗin amfani,haka a wuya ce Raihana ta ƙare abincin rana da shi." Umma ta bashi amsa lokacin da ta ɗauki buta ta wanke hannunta.

   Cikin natsuwa ya kammala cin abincin ya sha ruwa sannan ya miƙe ya fita, bakin titi yaje inda ake sayar da ita ce ya duba busassu ya sayo ya kawo mata sannan ya wuce filin Ball ɗin su....

*******

  MEERAH 

   A ɓangaren Meerah kuwa bayan fitar Momy wanka tayi ta shirya ta fita cin abinci kamar yanda Momy ta buƙata, a dining ta samu kowa ya hallara kasancewar weekend ne duk samarin Umma suna gida.

  Dady ne kawai baya nan kasancewar yana can Abuja tare da amaryarsa. Yayunta Maza guda biyar tun daga kan Ya Sultan da ya kasance babba. Ya Aryan Ya Maheer, Ya Fadeel da Ya Jawad duk ta same su zaune a dining ɗin.

    Idanu duk suka zuba mata suna kallon ta har ta ƙara so dining ɗin ta zauna a kujerar da Ya Sultan ya janyo mata, kasancewar duk cikin yayun nata tafi shaƙuwa dashi. Duk cewa gaba ɗaya suna sonta, kasancewarta Mace ɗaya ƙwal a cikin su shida da Honorable Abbas Mamman Gwangwazo (Dady) da kuma Hajiya Laylah (Momy) suka haifa.

   Don amaryar Dady har yanzu bata haihu da shi ba, wannan dalilin ne yasa suke yiwa Meerah matsananciyar soyayya. Suka raine ta cikin gata da kulawa.

   Duk abinda ta buƙata a rayuwarta tana samun shi, sai dai abu ɗaya ne suka kasa yi mata. Shine amsar Nawaz a matsayin zaɓinta.

   murmushi ta sakar masa lokacin data zauna a hankali ta furta.

   "Thanks My Yaya." Ta faɗa cikin sanyin murya babu karaɗin da ta saba. Da kulawa sosai ya kalle ta yace.

   "Meke damunki ne Auta?." Yayi mata tambayar yana kallonta cike da nazari. Tsaki Aryan yayi yace.

   "Zai wuce a kan wan can sha-sha-shan yaron, matsiyaci da idanunta suka rufe a kansa, ta kasa ganin banbancin dake tsakaninta da shi!." Ya ƙare maganar cike da takaici, kasancewar sa mai zafi sosai tamkar dai Dady. Sannan ya tsani alaƙar ƙanwar tasa da yaron, don babu ta inda suka dace da juna.

    Kwaɓe fuska Meerah tayi tana kallon Ya Sultan cike da shagwaɓa tana matso hawaye, Ya Sultan ya gir-giza mata kai alamar kar tayi kuka sannan ya kalli Aryan yace.

   "Ya isa haka Aryan, ka bar min yarinya taci abinci cikin natsuwa. Baka ga yanda ta rame bane?." Yayi maganar cike da damuwa yana kallon ƙanwar tasa da yake tsananin so.

   Ƙwaffa Aryan yayi ya ɗauke kai don ya tsani yaron sosai, kwata-kwata bai dace da ƙanwarsa ba. Yarinyar da aka haife ta a cikin gata ta buɗe ido a cikin arzuƙi da daula, suka raine ta tamkar sarauniya.

   Ta yaya suna ji suna gani zasu ɗauke ta su bawa wani matsiyaci, wanda bashi da komai, kasƙantaccen mawaƙin da duniya bata gama saninsa ba.

   "Ya isa haka kukan, maza share hawayen ki tashi kiyi serving ɗin mu." Ya Sultan ya faɗa yana kallonta da kulawa. Cike da shagwaɓa ta ƙara ziraro hawayen tana taɓe baki tace.

   "Allah Ya Aryan ya daina sona a gidan nan, shi yasa na matsu ayi bikinka in tattara in koma gidanka ya daina gani na a gidan!." Tayi maganar tana turo baki gaba irin na shagwaɓabɓun yara.

   "To shike nan sai muyi tafiyar mu can ɗin, dama Love tace tana son Momy ta bata ke." Ya faɗa cike da rarrashi yana shafa kanta.

    Harararta Aryan yayi zai yi magana Ya Sultan ya harare sa yana cewa.

   "Ka rabu da yarinya taci abinci nace." Dole ya haɗiye maganar da zai yin saboda babu musu a tsakaninsu.

    Duk abin nan da su ke yi Momy na kallon su bata tanka musu ba. Sai yanzu da ta kalli Meerah tace.

   "Ki tashi ki yi serving Yayunki." Miƙe wa tayi ta fara zuba ma kowa abinda yake so, koda ta zo kan Aryan sai da ta zumɓura baki gaba  sannan ta zuba masa. Harararta yayi ƙasa-ƙasa yace.

   "Zan kama ki ne yarinya." Baki ta ƙasa tura wa gaba tana ƙun-ƙuni ƙasa-ƙasa, sun saba irin wannan rikicin kasancewar ita ke bin bayan Aryan ɗin a haihuwa.

  Sai dai hakan bai hana soyayya da shaƙuwa shiga tsakaninsu ba, duk da rikicin da suke kwasa kasancewar Aryan mara haƙuri. Ita kuma akwai tsokana, musamman lokacin da take ainahin Meerah kafin ƙaddarar soyayya ta shigo cikin rayuwarta.

  Wanda rashin amincewar ahalin nata ya jefa ta a cikin halin ƙunci da damuwar da take ciki a yanzu....

   Wayar Ya Sultan ce tayi ƙara don haka ya ɗauka saboda ganin wanda ke kiran nasa, sallama ya yi ya ɗora da cewa.

   "Man ya kake, Ya Abuja?." Shiru yayi alamar yana saurare sai kuma yace.

   "Wai yau zaka shigo?." Yanzu ma shiru yayi yana saurare, sai kuma yace.

   "Okay Allah ya kawo ka lafiya, wane time zaka sauka zan zo airport na ɗauke ka."

   "Alright sai ka iso." Daga haka ya ajiye wayar yana mayar da hankalinsa kan abincin da yake ci. Aryan dake kallonsa tun da ya fara wayar, fuskarsa yalwace da fara'a yace.

   "Yaya wai Ya Ajmal ne zai zo?." Amsa ya basa da cewa.

   "Eh yace jirginsa ya kusa tasowa ma."

   "Yes!!!." Mai saita mata shagwaɓaɓɓiyar nan yana hanya." Yayi maganar cike da ɗoki yana kallon Meerah, wacce tunda ya Sultan ya ambaci Man ƴar fara'ar fuskarta ta ɗauke ɗif, don ta ɗan wanda yake faɗa wa hakan.

   Haɗe rai tayi tsaf tamkar wacce aka aiko wa da saƙon mutuwa.....

Bari mu wai-waya baya don sanin su waye zuri'ar Mamman Gwangwazo? waye Ajmal? Menene alaƙarsa da su? Meye a tsakaninsa da Meerah wacce ambatar sunansa kaɗai ya ɗauke farin ciki a saman fuskarta? Ta ya Meerah ta haɗu da Nawaz har soyayya mai ƙarfi ta ƙullu a tsakaninsu. Bayan tarin bambancin rayuwa da suke dashi tako wace fuska?. 

   Mu haɗu a page na gaba don sanin waɗan nan amsoshin.


  Barkanmu da dare.