SOYAYYAR ZUCI

Chapter 29&30

by @deeyamerh10

πŸ’–πŸ’– SOYAYYAR ZUCI πŸ’–πŸ’– 
(Love and Romantic story)
               Written 
                     By
              Deeyamerh 
07070647236
Page 29&30
Cocktail πŸŽ‰πŸŽ‰
Sosai gun ya kawatu domin wasu irin Decorations style DEEYAMERH~LUXERY ta kawata musu,Domin wasu irin combination light ne kawai suke kyalkyali wajan,gefe guda wasu irin Tables ne a ajere masu makutar kyau,kowacce chair da irin colours followers masu kyau da daukar hankali,inda amarya zata zauna ango shi kansa abin kallo ne,Sosai gurin ya kawatu Domin Indai decorations ne to a barwa Deeyamerh kayanta.
Sosai yan mata kesha da fita domin ganin komai ya tsaro kafin amarya da ango suzo,domin da kawayan amarya dana ango suma sun tsara bazatar da zasu yimusu.
8:pm na dare motocin kawo kawayan amarya suka fara zuwa,kai abin dai sai wanda ya gani domin iya ankon da yake jikin su abin kallo ne domin kaff din su colour iri daya hakama Ι—inkin ga colour din da suka zaba me kyau maroon colours sosai tayi masu kyau.inda mazan suka ci ado cikin milk Suit sosai suka bada kala.
A harabar wajan cocktail din suka tsaya domin jiran amarya da ango,Daya daga cikin Friend din ango ne yace "Har yanzu fa Boss be karasu ba ai na fada wa Habib ba lallai yazo amma ya kafemin akan zaizo".
Dariya duk sukayi domin sunsa halin kayansu India Boss ka gaji da jira,sosai suke hira a wajan domin su rage lokaci inda suka koma shirya kansu domin Habib din ya ce musu sun kusa karaso wa.
Yadda sukai shirin zaka san an hada yan gayu da wayayyu a gun,Dan ba wata rawar kai ko jin ai nakai magana ake ta ya'yan masu fada aji.
Haskene ya dallare musu ido,inda suna ganin haka Friend din Ango suka Hau ihu domin sun san mutum dayane ke musu haka wato Boss,Parking yayi inda yake kallon duk abinda yake faruwa ta cikin motor kafin abokan nasu suxo inda kake,murfin motar ya bude a hankali yasako kafarsa daya wacce take dauke da shoe,kai nagana ganin takalmin kasan da kudi aka siya,shima dai irin ankon da sukai shine a jikin Amma sai ka dauka nasa da ban yake domin ba karamin hawa da shi yayi ba.
Gaisawa suka fara shi da abonka masu tsokana nayi masu murnar sun dade basu ganshi ba sunayi,Sosai ya sake dasu yana hira dan bazaka ce wani ne a wajan ba,duk da jiki da yanayi ya nuna amma haka ya mai da kansa kamar su.
Wata motarce ta sake tsayuwa a gefen su,mai da kallonsu sukai gareta dan a tunaninsu motar ango ce tazo Amma sai me a tare suka bude murfin motar nan fa hankalin wanda baya kansu suna hira fa ya dawo da su kansu.
Fituwar suhaima ya dai dai da dagowar idanun Boss kanta inda itama tana fitowa idanuwanta cikin nasa,sosai zuciyarsu ta buga a tare Domin abune ya zowa kowa a bazata,bakwai kwalliya tayi me yawa ba Amma Kayan da ke jikinta sun kasance na musamman. An zaΙ“e su da kyau, an yi musu dinki cikin salo na zamani, kayan sun yi mata kyau sosai kuma sun zauna a jikinta.
Da yawan abokan ango kallonta suke Amma ita kallo daya tayi musu ta dauke kanta daga gun,Fatima ce tazo gunta tace"bari naje na cewa Mc yafara sakin Kidi muci kudin mu"Dariya sukai a tare har da tafawa.
Cik suka shiga inda suka cewa Mc ya sake musu slow music masu dadi,ai tunkan su bar gurin aka fara da music masu motsa zuciya.
Fita sukai inda kuka tarar da ango da amarya sunzo,sosai suka tsara kansu inda aka wasu daga cikin abokan ango da na amarya a gaba sai amarya da ango a tsakiya bayama suka sake sa abokan, sosai suka bada tsari me kyau.
Tafiya suke a tare inda wakar perfect take tashi agun,suna shigo akahau ihu da tafi dan wllh zakai tunanin Boss da suhaima ne ango da amaryar,takawa suke a hankali cikin aji da yanga.haka suka kai amarya da ango har gun zamansu,tsakiyar filin taro suka tsaya sosai akasha picture da video kafin kowa yake gun da aka tana da domin zamansu.
Muryar MC ne kukaji yana fadin"Ladies and gentlemen... ku ba mu hankalinku kaΙ—an. Amarya da ango sun iso!”
Ihu gun yasake karewa da shi jin haka kawai Mc ya saki waka habawa sai ga kawayan amarya an fito ana juyi Fatima ce kan gaba gun shiga filin.
Suhaima kuwa kasa tashi tayi dan tana kusa da Boss zaune haka kawai naji sanyi na shigarta,a jikinta take ji idonu na yawo a jikinta,haka kawai take jin kamar mahadinta yana kusa da ita,ina ma yadda take ji ace SECRET LOVER din tane a kusa da taga soyayyar da ya dade yana tanadi.
Tunda suka zauna kallonta yake domin ji yake kamar ya bude kirjinta ya sata kowama ya huta,bata kwalliya tayi ba Amma Ni yake kamar ya dura hannu a ka yayi ihu kallo taya yaji kawai yana sonta 
Suna cikin zaman kurame sai ga Fatima tazo ta janyeta har ajiyar zuciya ta sauke dan ba karamin takura tayi ba.
Sosai suka sha rawa abinsu dan ance ai party matane, tsabar rawa sai da dan kwalinta ya cire,Ai dagowar da Boss sai akan suhaima wanda take kiciniyar yadda zata mayar da daurinta.A haka har kanin fatima yazo wanda idan baka sani ba sai kai tunanin ya girmesu zuwa yayi yana mata magana akunne,kai take dagawa alamun tanajin me yake fada ganin tana ta gyara kawai yasa hannun wajan karbar daukwalin sai ya bata mayafi ta yafa akan ta ai ta can tana rawa batasan ta kamo hannunsa bata juyashi akan dole sai yayi rawa nan fa ya fara tawa sai tafiya da sowar ce ke tashi domin After party yafi dadi.
Tunda ya kafe ta da ido take kallonta duk abinda sukai akan idonsa,har wasu hawayene suke taruwa a idanun dan kishi,idan rawar take so tayi da shi mana dan me zatayi da wani har da tabashi,yadda take agunsa kome tace tana so zai mata indai zai sata a farinciki.
Tunda ya mike ya dushi gun masu rawar friend dinsu wanda basa rawar suke kallonsa,yana isa wajan yasa hannunsa ya kamu nata tunda ya fara tafiya da ita bai aje ta ko ina ba sai cikin motarsa zagayawa yayi wajan zaman driver yaja suka bar holl din tafiya suke amma bai ko kalli inda take ba,wani duka da yayiwa steering sai da ta matsa takure kanta tayi domin sai wani irin huce yake.
Ba irin kiran da Abokan basuyi masa ba amma yaki dagawa haka ma Fatima ba kiran ta batai mata amma tsoro yahana ta.
Tunda ya dauke ta bai ajeta ko ina ba sai kofar gidan su Fatima ,tsabar tsoratan da tayi ko motsi ta kasa,ko lokacin tunani bai barta tayi ba taji muryar cikin amo yace mata"Out"cikin sauri ta bude motar ta fita garin fita ne ta yar da wayarta,da dugu ta shiga cikin gidan a farfajiyar da ake aje motoci ta tsaya sai kuma ta juya da sauri ta leka wajan ko ta ga yatafi sai dai me tana lekawa suna hada ido da shi ai a 360 ta mai da kofar ta wuce ciki.
Shi abin ma dariya ya bashi wato lekowa take taga ya tafi ko yanan,cikin motar ya koma sai sauke a jiyar zuciya yake Why my princess?Ina kishinki fa a cikin nan Allah ya halittamin sonki da kishinki fa sosai ya dafe saitin zuciyarsa domin ji yake kamar zata fito.
Tofa sahaima kin shiga uku yeseen anya gobe da ke za'ayi dinner kuwa?
To kubiyo Ni domin jin yadda zata kaya.......