3
*FARASHIN ABOTA*
*SASAAL*
3
Kwatsam wata rana, labari ya fara yawo ɗan Tani zai kawo mata ziyara..
A ɓangarena sam zancen bai dameni ba, saboda ɓarar gyaɗar kuɗin da na saka a gaba..saɓanin Mairo da ba ta zancen da ya wuce na Ɗan Tani zai zo..
Ranar wata asabar da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe, wanda da ya yi daidai da ranar da aka ce ɗan Tani zai zo, ina tsaka da ɓarar gyaɗa akan buhun da na shimfaɗa, sai jiyo muryar Mairo tana sallama..
Lokacin Inna Asabe tana bakin murhu tana haɗin kayan miyar, miyan kukan da zata ɗora.
Ba yabo ba fallasa ta amsa sallamar Mairo, ba tare ta juyo ba, ta cigaba da abinda take yi, saboda ba kasafai ta cika sakar mata fuska ba..
Dakatawa na yi daga ɓarar gyaɗar da nake yi na miƙe ina washe baki..
Mairo da ke shirye tsaf cikin atamfa mai ratsin ruwan ƙasa, murmushi ta yi, tana takowa cikin yauƙi..
Sai da ta matso daf da ni ta kalleni ta ce;
"Ke kam Hindatu kullum cikin datti, kalli haƙoranki dan Allah"
Gefen kunnena na sosa, na ɗan ɓata rai na ce;
"To ɓarar gyaɗar ma sai na yi mata wanka, na wanke baki? ke ai ƴar gata ce, mu kam ai dole mu nemi kuɗi"
Ɗan ƙaramin bakinta ta taɓe, ba ta ƙara cewa komai ba, ta ƙaraso ta zauna..
Nima komawa na yi na zauna na ci gaba da ɓarar gyaɗata ina kallonta.
Sai dai ta ɗan nisa ta ce;
"Ni fa Mairo gani nake yi kamar irin wannan wahalar ba ta dace dake ba, ki na zama budurwa kina ƙara komawa tsohuwa, uhm bari dai nayi shiru"
Ta ƙarasa faɗa tana kallon gefen murhun da Inna Asabe ta ke..
Murmushi na yi, na ce;
"Mairo kenan, neman kuɗi ai ba wani abun aibu ba ne, duk wannan wahalar da muke ciki, ina fatan wata rana ya zame mana labari, ni da su Inna"
Bakinta ta taɓe ta juya idanunta ta ce;
"Ke da su Inna kuma? uhm Hindatu kenan, ni bara na tashi na koma, idan kin gama kya same ni a gida, kin san yau Ɗan gidan Tani zai zo"
Ban ɗauki furucinta na farko da muhimmanci ba, don haka na ce;
"Mairo da baki da saurayi sai na ce ko son ɗan Tani kikeyi, duk kun bi kun damu kanku da zuwansa..sai ka ce ance zai kawo muku tsaraba"
Ba ta cemin komai ba, ta miƙe, har ta juya ta fara tafiya, na kasa daurewa na ce;
"Au ba zaka yimin sallama ba"
Bata waiwayo ba, kuma bata ce min komai ba, sai Inna Asabe ta da yiwa sallama ita ma kuma Inna Asabe bata amsa mata ba, domin yi tayi ma, kamar ma bata san da ita ba..
Sai da Mairo ta jima da tafiya har Inna Asabe ta gama kaɗa kukarta sannan kammala iya wanda zan yi na miƙe..
Asuwakina na ɗauko, na zuba ruwa a botiki na shiga wanka.. ban fi minti huɗu ba sai gani na fito..
Inna Asabe da ta koma rumfa da tukunyar miyar da ta kaɗawa a gabanta kallona tayi ta kama haɓa ta ce;
"Har kinyi me Hindatu? Na shiga uku ni Asabe, wankan ne har kin yi kin fito? Allah Ya shiryeki"
A rayuwata natsani a kushe ƙoƙarin da nake ganin ina yi..wannan dalilin yasa na turo baki gaba na wuce ɗakinmu..
Kayan da na saka sau biyu, na ɗauko na karkaɗe na mayar da su jikina..basilin na ɗauko na shafa..na tamke kaina tsam da ɗankwali, sannan na fito waje ina maiƙo.
Kusa da Inna Asabe na ƙarasa na zauna, kallona tayi kawai ba tace min komai ba, ta zubomin tuwona na saka hannu na karɓa..ina murmushi.
Tsaf na duƙufa ina gumi na cinye tuwon, na ɗago kwanan ina siɗewa..
Bayan na kammala nayi mata godiya kamar yadda muka saba, na miƙe na kai kwanon wajen wanke-wanke..
Ina cikin wanke hannuna na ji sallamar su Jamila( ƙanena ƴaƴan Inna Asabe)sun dawo daga makarantar Islamiyya..
Ɗaya bayan ɗaya suka gaishe da Inna Asabe nima suka gaisheni kamar yadda ta koya musu..
Su na zama ni kuma ina yi mata sallamar zani gidansu Mairo..
Ba ta hanani ba, sai a dawo lafiya da ta ce..
Kamar ba mace ba, haka nake tafiya.. a raina ina cewa babu bakin da Mairo zatamin gorin ban yi wanka ba..
A bakin ƙaton bishiyar ƙofar gidansu na hangota, ita da Sammani, su na hira..
Da fara'ata na ƙarasa muka gaisa..Sammani ya na tsokanata da abokinsa da ya zo daga Kano jiya da yamma ya hangomu ni da Mairo ce ya na so na..kuma dagaske ya ke aurena zai yi.. a yanayin furucin na Sammani akwai barkwanci da tsokana..amma ga mamakina sai naga Mairo ta ɓata fuska ta ce;
"Allah Ya rabaki da auren ɗan Kano Hindatu, ai kayi aure a ƙauyen da ka taso ai shine aure..ka zauna kusa da danginka"
Ban san zuciyar Sammani ba, amma a tawa zuciyar sam ban yiwa furucin nata wata fassara daban ba, sai na tsantsar son da take yi min..
Sammani ɓata fuska yayi ya ce;
"Kai Mairo, ki rage wannan kishin na ki, ai aure a Kano cigaba ne, Kano fa birni ce"
Manyan idanunta ta zaro ta ce;
" kishi kuma? Da Hindatun? Allah Ya kiyaye"
Su na cikin musayar kalamai akan batun, sai ga mota mai kyau ta gangaro inda muke,.. gilashin baya dana gaba akayi ƙasa da su.
Na gaban motar Dattijo ne, na bayan kuma matashine ɗan tsamurmuri ɗan gayu fari tas mai kyau da shi..
Fuskar matashin a sake ya yiwa Sammani sallama..
Sammani da salon basarwarsa ya amsa..Ni da Mairo muna gefe mun kasa kunnuwar saurarar jin abinda matashin zai ce..
Matashin bai damu da yadda Sammani ya yamutsa fuska ba ya ce;
"Gidan Alhaji Yusufa mai tattasai yake nema, na kira waya network ya hanashi shiga"
Sammani da baya son raini fara yiwa direba kwatacce ya yi..amma matashin ya roƙi alfarma ya shigo dan Allah ya nuna musu hanya..
Sammani bai musu ba, ya yi mana sallama matashin ya buɗe masa ƙofa ya shige..
Motarsu tana barin wajen Mairo tayi tsalle ta dire, ta na cewa;
"Wallahi shi ne, Ɗan gidan Tani ne, jikan Alhaji Yusufa..bari Sammani ya dawo musha labari.."✍🏻
Ku yimin afuwa da jina shiru..