12
*SASAAL*
***
12
"A'a Hindatu kawai dai ina farin ciki ne Umar zai kiraki da daddare a gabana, na ji irin kalaman soyayyar da kike bani labarin yana gayamiki..
Ina fatan dai kin sako wayar a jaka?"
Ban ji wani abu mara daɗi game da furuncinta ba, sai ma murmushi da na yi na kama haɓa na ce;
"Ai ba zan iya barinsa a gida ba, indai ba so nake yi, Yaya Umar ya kasa barci ba, kin ganshi nan na sakoshi, a gefen kayana"
Na ƙarasa faɗa ina nuna mata gefen jakar bayana.
Baki ta saki tana kallona, kafin ta ce;
"Yaushe Umar, ya koma Yaya Umar ba ni da labari, lallai soyayya daɗi"
Juya idanuna na yi na ce;
"Ke ma dai lura ne bakya yi, yaushe rabon da na ambaci sunansa, ai tun da muka saba, ya kwaɓeni da ba'a kiran sunan mutumin da ya girmeka kai tsaye, sai an sakaya, balle shi da zai zama mijina da zarar mun yi candy"
Guɗa Mairo ta saki tana dariya ta ce;
"Hm bakina da goro, amma indai namiji ne, muna nan zaki ba ni labari"
Ɓata fuska na yi na ce mata;
"Labarin me kuma zan baki, ni dai bana son mugun baki"
Jakar makaranta da ta zuba kayanta a ciki ta ɗauko zata rataya, na ga ta fasa ta tsaya tana kallona, cikin mamaki ta ce;
"Lallai Mairo! soyayya ta buɗe miki baki, ina faɗa kina faɗa, hm Allah Ya sa mu dace"
Shiru nayi mata, na yi hanyar fita..ina jinta tana cigaba da mita ban ce mata komai ba.
Har muka isa tasha muka samu Mota bata ce min komai, nima ko kallonta ban yi ba.
Ba mu jima ba, motar mu ta kama hanya..sai a lokacin ta fara jana da hira ƙasa-ƙasa har na saki jiki muka cigaba da hira..
Ba mu jima ba, muka isa tashar ƙauyensu Inna, da yake motar da muka hau ba laifi akwai gudu..
Muna sauka a tasha, wata mota itama ta faka ɗauke da matafiya..
Ɗaya daga cikin matasan da suka sauko daga motar ne, ya ƙaraso kusa da mu.
Ka na ganin lafiyayyen akwatin kayansa da ya riƙo da kyan fatarsa kasan daga birni yake.
Sallama ya yi mana, ya na tambayarmu sunan gidan da ina ji, na san gidansu Inna yake nufi..
Ban nuna masa can muka nufa ba, na yi masa bayani yadda zai gane.. godiya ya yi mana, har ya juya zai fara tafiya sai kuma ya juyo ya ce;
"Dan Allah idan babu damuwa ko zan iya sanin sunanki"
Ya faɗa yana kallon Mairo..
Mairo wani irin murmushi ta yi ta ce;
"Sunana Maryam, kai fa?"
Ɗan gemunsa ya shafo ya yi murmushi ya ce;
"Sunana Khalil daga garin Kaduna, hutu na zo yi wajen kakannina, idan babu damuwa ko zan iya samun lambarki?"
Kamar wayarta haka Mairo ta juyo tana kallona ta ce;
"Hindatu ba ni wayar nan"
Gudun kar na yarfata ya sa na zamo jakar bayana, na zuge zif na fito da wayar na miƙa mata.
Karɓa tayi ta miƙa masa..
Ai kuwa nan take ya saka lambarsa ya kira, ya miƙo mata wayar ya na cewa;
"Na gode ko kyakkyawa, sai kin ji kirana"
Ya faɗa yana nuna alamar kira da yatsunsa biyu..
Wajen masu babura ya ƙarasa, ban ce mata komai ba, sai na jira ya samu abun hawa ya tafi tukunna..
Ta waiwayo kenan zata yi min magana na rigata;
"Mairo ki ka ce bakya son ɗan birni?"
Dariya ta kwashe da shi ta ce;
"Hindatu kenan, yadda kike faɗar soyayyar da Umar yake miki, ai dole na sauya tunani, yanzu ga ba shi har koya miki mutunta manya ya yi ba, shi fa Sammani, tun da nake kiran sunansa bai taɓa cewa a'a ba"
Wani irin kallo na yi mata na ce;
"Ban fahimci me kike nufi ba?"
Kai tsaye ta ce min;
"Gwadawa zan yi ko za'a dace"
Na san ba zata ɗauki gaskiya ba, don haka na yi gaba na barta a baya..
Machine ɗaya muka hau zuwa unguwarsu Inna..
Ba mu sha wahalar samun gidansu ba..
Tarba ta musamman akayi mana, kamar za'a goyamu..
Ga abinci masu daɗi da aka gabatar mana har da siyo mana pure water, da lemo.
Bayan mun huta, na kira Baba na shaida masa mun sauka lafiya ƙalau.
Ɗan autansu Innata ne ya yi mana rakiya har zuwa gidan da ake yi mata magani.
Ba shi da nisa sosai da gidansu..
Da na yi ido biyu da ita, sai da na zubar da hawaye, haƙiƙa tana jin jiki, duk ta rame ta zama wani iri, ko maganarta baya fita da kyau.
Ina gidan Umar ya yi ta kirana, na ƙi ɗagawa na ce sai mun dawo gida..
A nan muka ƙarasa wuninmu ba mu dawo gidansu Inna ba, sai bayan mun yi sallar magriba.
Tun muna kan hanya, Khalil ya kira waya..
Dole ba ni da zaɓi na miƙawa Mairo wayar..
Muna tafe su na hira, sai kashe murya take yi..ai kuwa daf da zamu shiga gidansu Inna muka hangosa a zaune, kan bencin mai sayar da kayan provision ɗin da yake ƙofar gidan.
Tasowa ya yi fuskarsa da mamaki, itama Mairo mamakin ganinsa take yi, saɓanin ni da nasan dama ba zai wuce a nan haka gidan kakannin na sa yake ba..
Maimakon Mairo ta miƙomin wayata, sai ta ƙanƙamesa a hannunta kamar na ta..
Har muka gama gaisawa da Khalil hankalina ya kan wayar.. ba na so ya gane ba wayarta ba ce kamar yadda ta nuna masa, don haka na shige gida, a lissafina ba wani daɗewa za tayi ba.
Kamar wasa haka na zauna zaman jiran shigowar Mairo har na akayi sallar Isha'i ba ta shigo ba, har abincin daren da na ci na rage mata ya huce salam.
Kasa haƙuri na yi, na taso daga makwancin da aka bamu na fito waje domin na duba ko lafiya..
Ina fitowa ga mamakina, a soron gidan na hangota a maƙale a tsaye..tana ta kore saurayen da suke ta cizonta saboda duhun wajen..
"Mairo me kike yi anan?"
Na tambayeta ina zare ido.
Sosa ƙeya tayi ta ce;
"Wallahi kin ga chajin wayar ce ta ƙare, shi ne na rasa yadda zan shigo na yi miki bayani, nasan ba zaki ji daɗi ba"
Ajiyar zuciya na sauke, duk da ban yarda da batunta ɗari bisa ɗari ba.
Kamo hannunta na yi ina cewa;
"Babu komai da safe sai mu nemi shagon caji mu kai, kafin mu kama hanya"
Haka muka kwana, shiru, saboda takaici ko tambayarta yadda suka yi da Khalil ban yi ba..
★washe gari, bayan mun karya, mun yi wanka. Na cewa Mairo bari na yiwa ƙanin Innata magana ya yimin rakiya na kai wayar caji kafin mu tafi.
A take Mairo ta fara mitar, gara kawai mu je muyiwa Inna sallama mu ɗauki hanyar gida yaushe wayar tayi caji..yaushe muka koma gida? Dare sai ya yi mana a hanya
Fahimtar gaskiya a cikin maganarta yasa dole na haƙura..muka nufi ka ƙara dubo Innata daga nan mu yi mata sallama..
Mun samu jikinta da ɗan sauƙi ba kamar jiya ba, sai saka mana albarka da muryarta ta ba ta fita dakyau take ta yi.. alƙawarin zan ƙara dawowa idan Baba ya yarda na yi mata..sannan muka yi bankwana.
Kamar jiya da daddare da muna dawowa a ƙofar gida muka samu Khalil ya yi gayunsa irin na wayayyun ƴan birni..
Daga gaisuwa babu abinda na yarda ya ƙara shiga tsakanina da shi na shige gida na bar Mairo a tsaye..
Ba ta jima ba, sai gata ta shigo, da kuɗi a hannunta..
Ban nuna na ga kuɗin ba, sai da ta taɓoni tana nunamin..
Dariya na yi na ce;
"Mairo kenan ke da kike da Sammani ina ke ina amsar kuɗin wani"
Dariyar jindaɗi ta saki ta ce;
"Ki ka san me Allah zai yi? Amma wacce mace ce ki ke ganin zata ɗauki Sammani ta bar Khalil?"
Banza nayi mata kamar ban ji ta ba, na saɓa jakata na yi hanyar waje..
Yayyen Inna da ƙannenta babu wanda bai yi mana alheri ba..
Har ƙofar gida iyalansu suka rakomu.
Kamar yadda muka zo, haka muka ƙara hawa machine ɗaya zuwa tasha..
Muna isa tasha muka samu mota..mu na ciki a zaune, ana jiran ragowar fasinja ɗaya kawai na ce bari na gwada kunna wayata na gani?
A daidai lokacin aka samun cikon fasinja..
Fakon idon Mairo dake kusa da ni nayi, lokacin hankalinta ya kan direba, da ƴan kamashon da zai sallama.
Ina kunna wayar bayan ya ɗauki lokaci, ya kawo..wani irin duhu ne ya ziyarci idanuna na ɗan lokaci.. sakamakon chajin da na gani akan wayar har 80%..ina shiga wajen kira na ga kiran Umar babu iyaka..
A take hawaye ya cikamin ido..na zura wayar a cikin jaka..na kwantar da kaina akan kujera..a daidai lokacin motarmu ta fara tafiya.
Tambayar kaina na fara yi, kenan Mairo tana sane ta kashemin waya? To meyasa za ta yimin haka? ita da ta ce tana son Umar ya kira a gabatan ta ji irin kalaman soyayyar da yake gayamin.
To ko dai kishi take yi, a'a wata zuciyar ta kwaɓeni da cewa saboda me zata yi kishi bayan itama ga Khalil ya ce yana sonta?
To ko dai bata san kan wayar ba ne, shiyasa ta maƙale taƙi shigowa jiya kar na ce ta lalatamin waya?
Babu irin zancen zucin da ban yi ba, amma na kasa samun amsar dalilin da yasa Mairo tana sane zata kashemin waya..
Babu kalar hirar da bata jani da shi ba, amma na yi shiru, saboda na rasa wani irin hukunci ya kamata na yanke..
Yanzu abinda zan fara yi shine, idan muka isa gida zan kira Umar na lallaɓashi na ba shi haƙuri ya sauko..
Motar mu ta ɗan lalace a hanya har na ajiye jakata na je na kama ruwa..kafin a kammala gyara.
Ko da na dawo a yadda na bar jakata haka na sameshi.
Lalacewar motar yasa mun ɗan lokaci kafin mu iso gida..
Ban tafi gida ba, sai da na yiwa Mairo rakiya har gida, tana ta tambayata wai me yake damuna ne haka duk na bi na canza?
Murmushi na yi na ce mata babu komai..
Da wani irin sauri na nufi hanyar gida..burina na isa na keɓe na kira Umar..
Ai kuwa ina zuwa na yi sa'a babu kowa a gidan sai Jamila, a tsakar gida tana wanke-wanke wai Inna ta tafi gidan gandun su Baba dubiya..
Ɗaki na shige hannuna ya na rawa na zamo jakata..
Zuge zip na yi, na kai hannuna saitin inda na saka wayar amma sai na ji wayam..
Jikina yana rawa, na zazzage jakar ban ga komai ba..
A take na fashe da kuka ina ƙara ɗaga jakar ina karkaɗewa....✍🏻