14
*FARASHIN ABOTA*
*NAFISATU_SASAAL*
***
14
A daidai lokacin ya ƙara tsulamin bulalar akaro na biyu da iya ƙarfinsa..
Tsabar azaba da ya ratsani muryata har disashewa ya yi na kasa ihu.
Baba bai ƙyaleni ba, sai da ya yimin dukan tsiya..duk haƙurin da Inna ta yi ta bashi bai sauraramin ba, sai da ya gaji da kansa.
Wannan dare zan iya cewa shine dare mafi tsananin da na taɓa gani a rayuwata a wannan lokacin, jikina kamar an watsamin ya ji saboda azabar da nake ji.
Raɗaɗi biyu ne suka tsawaita wannan dare a gareni, na farko rasa Umar, na biyu dukan da Baba ya yi min.
★washe gari Inna bata bar ni nayi aikin komai ba, ta ce naje ɗaki na huta.
Idan lokacin tafiya makaranta ya yi, na shirya na wuce, kar na ƙara tunzura zuciyar Babanmu.
Jamila ce ta kawomin koko da wainar rogo har ɗaki, tana yi min sannu..
Kaɗan na iya sha, na miƙe na zura kayan makaranta...bayan na kimtsa har ɗaki na je na gaishe da Baba.
Bai fasa ba ni kuɗin kashewa ba, amma ko gefena bai kalla ba.
Ba iyakacin tunani ba, gaba ɗaya mantawa na yi ma da batun Mairo a duniya.
Tare da su Jamila muka tafi, ko da na isa aji, ban nemi jin ta bakin ƴan ajinmu ko Mairo ta zo ko ba ta zo ba, na yi zamana na fitowa da littafina na fara karatu..
Ina zaune sai gata ta shigo..ba ta ji nauyin zama a kusa da ni ba, har da cemin;
"Amma Hindatu baki da kirki, ke fa na zauna jira amma na ji ki shiru"
Jin na yi shiru, yasa ta taɓoni ta ce;
"Hindatu kin san menene? jiya na ji labarin Saifi abokin Sammani zai tafi makarantar horon ƙwallon ƙafa, abokanan aikin Kakansa suka ɗauki nauyinsa"
Har ga Allah na manta wanene Saifin da take nufi, wannan dalilin yasa ban motsa ba, ban kuma ɗago na kalleta ba, balle na saka ran samun amsa daga gareni.
Shan jinin jikinta tayi ta ƙara cewa;
"Yanzu Hindatu saboda sharrin da Sammani ya yi min jiya shine kike jin haushina?"
Kamar dutse haka na yi shiru..
Har aka tashi, Mairo ba ta samu kalma ɗaya daga gareni ba.
Ko da na zamu tafi gida, ban tsaya na jera da ita ba, kamar yadda ban saba tafiya tare da su Jamila ba, haka nayi tafiyata ni kaɗai..
A raina na ke jin cewar ba dole sai da ƙawa zan yi rayuwa maidaɗi ba..rayuwa tana zuwar maka ne a yadda ka ɗauketa, da kuma mutane da ka wajibtawa kanka kai dole sai ka yi rayuwa da su...
Ko da na isa gida, kamar kullum a rumfa na samu Inna tana raba abincin rana..
Sannu da gida na yi mata, ta amsa tana nunamin gefenta, alamar na matso na zauna.
Haka kuwa na yi, a tunani abincina zata miƙomin..amma sai na ji ta fara yi min nasiha da na daɗe ina kallonta akai kafin Mairo ta wargazamin tunani a kwanakin da suka gabata..
Nasihar na ko yi cewa; "A'A" akan duk wani abu da ya saɓawa daidai tayimin.
A cewarta nasarar bawa ta na tabbata ne a lokacin da ya san kansa..
Sannan ta ƙaramin da bata shiga lamarina ƙawancemu da Mairo ne saboda a dalilin ƙawacenmu aurenta ya so mutuwa shekaru masu yawa baya..
Saboda ta na matsamin tun ina ƙarama akan na rabuwarmu da ita, maƙota suka fara gulmar saboda ba ita ta haifeni ba..a ƙarshe Babanmu ya yarda har ta kai ga samun saɓani a tsakaninsu..
Daga wannan ranar tayi alƙawarin daina saka baki a duk wani abu da ya shafi ƙawacenmu.
A ƙarshe ta ce ba ta na son ta rabani da Mairo ba ne, tana dai yi min gargaɗin na kiyayeta, ba kuma komai zata ce min na yi, na yi ba.
Maganar Umar kuma na ajiyesa a gefe, dama can Allah bai ƙaddara mijina ba ne, domin jiya danginsa sun cewa Baba ya yi min tsakani da ɗansu..domin babu yadda za'ayi ɗan birni irin Umar ya auri mace iri na.
Kai na jinjina mata, na yi mata godiya, ta miƙomin abincina, na ɗauka na matsa can gefe na zauna na fara ci..
Ina gamawa na tashi na yi wanka, na yi alola na yi sallah.
Ban kwanta barci ba, na fito na yiwa Inna sallamar zan je tambayo kuɗin ɓarar gyaɗar da na yi, sai a lokacin su Jamila suka yi sallama..Inna ko kallonsu ba ta yi ba, saboda takaici.
Ina zuwa gidan na ke yiwa ɓarar gyaɗa suka biyani haƙƙina tare da haɗoni da wata gyaɗar na kamo hanyar gida.
Ina shiga gida ko zama ban yi ba na ajiye gyaɗar na shige ɗakinmu na ɗauko bankin da nake tara kuɗi...na zura kuɗin a ciki na mayar da shi maɓoyarsa..
Fitowa na yi na shimfaɗa buhu na zauna..na juye gyaɗar na fara ɓara muna hira da Inna.
Da yamma ta yi Baba ya dawo, gaban ƙafafunsa na je na durƙusa ina ba shi haƙuri..
Bai hantareni ba, sai nasihar da ya yi min kan na kiyaye mutuncina..batun Umar kuma ko da wasa baya son ya ƙara jin shi, Allah Ya haɗa kowa da rabonsa..
Kai na ɗaga masa, na miƙe na shige ɗaki..
A wannan dare ma, na yi kuka kamar babu gobe, domin har cikin raina Umar ba ƙaramin kwantamin ya yi ba, ba wai don kasantuwarshi ɗan Birni kaɗai ba har da kyawawan halayyarsa.
A kwanakin biyun da suka biyo bayan nan, haka muke rayuwar kurame ni da Mairo a makaranta..
Tun tana yi min magana har ta gaji ta haƙura, haka zamu zauna shiru, har ƴan aji suka fara gulmarmu..
Ba na biya mata makaranta, itama ba ta biyomin, ana tashi zan kama hanyar gida, da zarar na isa gida na ci abinci, na yi wanka na yi sallah, zan shimfiɗa buhun ɓarar gyaɗata..
A cikin kwanaki biyu, har haske na yi, saboda babu zaman ƙofar gidansu Mairo, kuma kullum sai na yi wanka.
A daidai wannan gaɓar muka fara shirye-shiryen zana jarabawar Qualifying ta aji biyar ɗin sakandare.
Ba laifi mu kan ɗan yi magana da Mairo ta dalilin karatu shima ba sosai ba.
Cikin sa'a muka fara zana jarabawarmu, mu ka gama lafiya ƙalau..bayan nan muka yi hutu, bakunan mu ɗauke da addu'ar samun nasara.
Ko da akayi hutu ban nemi Mairo ba, Ita dai tayi ƙarfin halin zuwa gidanmu ita da Sammani sau ɗaya, amma na ƙi fita, domin na san da wahala idan na fita Sammani ba zai yi min zancen Umar ba..
Kwana uku da zuwansu, sai ga Mahaifin Mairo Alhaji Idi ya zo wajen Baba..akan batun meyasa na daina zuwa gidansa shin wani abu ya haɗani da Mairo ne bai sani ba?
Baba bai ɓoyemasa komai ba, duk da ya san labari abinda ya faru tsakaninsa da iyalan gidan Alhaji Yusufa ya je masa, amma ba lallai ya san da ƴarsa a rakiyar abinda na aikata ba..
Har labarin irin dukan da ya yi min sai da ya bashi.
Faɗa Alhaji Idi ya fara yi, ya sa Baba ya kira masa Jamilu, ya turashi gida ya kira masa Mairo, sannan ya biya gidansu Sammani ya kira masa shi su taho tare..nima Baba ya kirani na fito
Sammani ya riga Mairo zuwa, domin tare suka taho da Jamilu...
Kamar yadda ya faɗa ranar, haka ya ƙara maimaitawa su Baba akan Mairo tasan komai ya faɗa mata, kawai ƙetace yasa tayiwa Hindatu rakiya.
Mairo tana zuwa ko gama daidaitar tsayuwarta ba ta gama yi ba, Alhaji Idi ya zari biyu daga cikin siraran itacen darbejiyar da Inna ta zube a soro tana jiran su bushe ta fara amfani da su, ya fara lafta mata..
Kaina na sunkuyar ƙasa ina dariyar jindaɗin da rabona da irinsa har na manta..
Da yake Alhaji Idi a tsaye yake, ga jiki ga tsaho, kafin Baba da maƙotan da suka jiyo ihun Mairo su samu damar karɓarta a hannunsa ta ji jiki..kamar ma har gigicewa tayi, domin lalube ta fara yi kamar makauniya..
Shi dai Sammani ya na tsugunne a gefe kansa a ƙasa.
Tsawa Alhaji Idi ya daka mata, a take ta nutsu tayi shiru a gefen maƙocinmu, jikinta yana karkawar dukan da ta sha.
A gaban mutanen wajen ya ce;
"Shi har cikin ransa, babu wanda yake jin yaƙinin idan bayan babu ransa zai iya duba Mairo a cikin ƴaƴansa kamar Mallam Adamu( Baba) amma shine zata ci amanar dake tsakaninta da Hindatu?
Ya na so jama'ar wajen su zama shaida duk ranar Mairo ta ƙarayin wani abu makamancin irinka haka bai yafe mata ba"
Haƙuri aka fara ba shi, bai saurari kowa ba, ya kama hanya ya bar soron..
Baba haɗamu ya yi, ya yi mana nasiha.
Ni dai a ɓangarena ba na jin zan ƙara yarda da Mairo, amma a zahiri sai na nuna masa komai ya wuce..
Tare muka yi mata rakiya har da Baba, a ƙofar gida muka samu Mahaifinta..
Daƙyar Baba ya shawo kansa ya haƙura..shima ya ƙara yi mana nasiha muka kamo hanyar gida da Baba..
★washe gari labarin mutuwar Alhaji Idi ya karaɗe Yankinmu.
Idan na ce ban ji mutuwar mahaifin Mairo ba na yi ƙarya, Baba shi kansa zama ya yi yana kuka a tsakar gida, Inna da mu gabaki ɗaya muna tayashi..
A labarin da aka samu daga amaryarsa da yake ranar girkinta ne, ta ce lafiya ƙalau ya dawo daga masallaci sallar asuba, daga cewa bari ya ɗan kishingiɗa shine bai tashi ba, rai yayi halinsa.
Kowa ya kaɗu da mutuwar Alhaji Idi, musamman waɗanda suka ƙwaci Mairo a hannunsa..
Lokacin da muka je gidan nayi ido biyu da Mairo, sai da zuciyata ta tsinke, tausayinta ya maye gurbin duk wani haushinta da nake ji..
Ta yi kuka, ta yi surutai, domin mahaifinta dai shine mai tsaya mata akan komai, dangin mahaifiyarta talakawane liƙis masu son zuciya, domin ko nemanta ba sa yi..
A ranar mutuwar a gidansu Mairo Baba ya ce na kwana..
A daren ranar sai na ji kamar tana waya da wani, ko da na farka washe gari da asuba, ban ga alamar komai ba, sai na bar hakan a matsayin wataƙila mafarki na yi..
Sai dai abinda ya ƙara bani mamaki shine; zuwan Khalil a ƙatuwar mota, da wasu abokanansa biyu, da wani mutum ɗaya da ka gani kasan ɗan uwansa ne..
Babu irin tambayar da ban yiwa Mairo ba, akan ya ya akayi Khalil ya san Mahaifinta ya rasu?
Kafewa tayi akan kawai ya zo ne akan gaɓa, banda abuna ina taga hanyar gayawa Khalil rasuwar da aka yi mata..
Zuwansu Khalil da irin kuɗin da suka bayar a matsayin sadaka, ba ƙaramin barin baya da ƙura ya yi ba..
Bai kuma ɓoyewa dangin Mairo shi masoyinta ba ne..
Hango daula a tattare da shi yasa kowa ya ja bakinsa ya yi shiru, ba su sanar da shi batun Sammani ba.
Sammani kasa haƙuri ya yi, da daddare ya yi, ya turo aka yi masa sallama da ni..
Ko da na fita, ban ɓoyemasa gaskiyar yadda Mairo ta haɗu da Khalil ba, a ƙarshe na ce masa, wataƙila Khalil ya je Yankinsu Inna ne ya biyo tana nan, shine ya zo akan gaɓa..
Ba don Sammani ya gamsu ba, ya jinjina kai muka yi sallama..
Ni ma ina shiga nayi mata sallama, zan koma gida, ga mamakina bata nuna wani alamar jimami ba, balle ta hanani tafiya..har ƙofar gida ta rakoni tana yimin godiya..
Haka kwanaki suka shuɗe har akayi sadakar bakwai, kullum Inna idan tayi shinkafar rana, da tuwon dare sai ta zubamin na kaiwa Mairo..
Ana cikin haka, muka koma makaranta.. sakamakon jarabawarmu ta fito..
Sai dai babu sunan Mairo a waɗanda suka yi nasara..
Tun a makaranta ta fara kukan ta shiga uku..Nima kasa haƙuri na fara tayata..
Haka muka dawo gida muna kuka...
Ko da na isa gida na shaidawa Inna..
Jimamin ina Mairo zata samun kuɗin zana jarabawar kammala sakandare ta fara yi, acewarta gashi Mairo ba iya sana'a tayi ba..su ma kuma babu wadata balle su taimaka mata..
Shima kuma Sammani fafutuka yake yi balle a saka rai da shi..
Ko abinci ban tsaya ci ba, na ɗauki nawa na juye a waje ɗaya da nata na nufi gidansu..
A ƙofar gidansu na sameta ta ci kuka, ko kayan makaranta ta bata cire ba, Sammani na zaune a gefenta..
Ina jin sanda yake ce mata, ta kwatar da hankalinta ko bai samu kuɗi ba, zai kira Saifi ya taimaka masa.
Daƙyar ni da Sammani muka lallasheta ta ci abinci..
Daga wannan rana na ɗauki haramar yin aikatau kala-kala, nice har da dakar barkono duk domin na tara wani abun daga cikin kuɗin jarabawar Mairo...✍🏻