FARASHIN ABOTA

16

by @nafisatusasaal01

*NAFISATU_SASAAL*
       ***


               16


"Na gode da irin sakayyarki, ga dubu biyu nan na baki kyauta"

Daga haka na zura wayata da kuɗina a 
 jaka na janyo mata ƙofar ɗakinta na bar gidan.

Ina tafe ina mamakin ƙarfin halin Mairo da son zuciyarta.

Ina zuwa gida na ga gidan a kulle, na san ba zai wuce Inna tana gidan gandun su Baba.

Juyawa na yi zuwa gidan. 

Na kuwa yi sa'a samunta a zaune tana hira..cikin raha na saki fuskanta muka gaisa da kowa.

Inna miƙomin ɗan mukulli ta yi, ta  yimin bayanin abincinmu yana nan a rumfa tasa baho da rufeshi.

Ƙarɓa mukullin na yi na ce mata; "toh" na yi musu sallama na bar gidan.

Tsabar sauri kamar zan faɗi, ba ni da burin da ya wuce na isa gida na buɗe wayar na ga menene a ciki.

Ina isa gida na yi  sauri na buɗe na shige sannan na zura sakata kar tumaki su shigo, su yiwa Inna ɓarna.

kai tsaye ɗakinmu na nufa, jakata kawai na zame daga bayana na kunna wayar..

Sai dai a garƙame yake, ta saka mukulli.

Da farko sunanta na fara gwadawa ya ƙi yi, na gwada na mahaifinta shima ya ƙi yi.

Shiru na yi a zaune, zuciyata tana suya, kamar na ɓare wayar gida biyu..

Har na miƙe zan tashi, sai na yi tunanin bari na gwada saka sunan mahaifiyarta..

Ai kuwa ina sakawa wayar ta buɗe, hamdala na yi, ina sauke ajiyar zuciya.

Wajen kira na fara shiga, anan na ga lambar da akayi saving da "Mijina"

Ban wani san kan  waya ba. Don haka na yi ta shige-shige..

A wajen tura saƙo ne, na ga saƙunan lambar da aka yi saving da Mijina, ya na ta lallashinta akan rasuwar mahaifinta.

A take naga ne Khalil ne.

A nan na ga saƙunan kuɗin da yake tura mata, ciki har da kuɗin Jarabawa.

Ban san meyasa ba, a raina ban ji haushin kulashin da take yi ba..

Dalilina kuwa shine, shi Sammani ya dage sai da ƙwallon ƙafa zai ci abinci, yaƙi ya nemi sana'ar kansa, sai dai idan ya ga dama yaje kasuwa ya ta ya mahaifinsa sayar da kayan koli..

Shima kuɗin da zai samo akan suturar gwanjo da turare ɗan ɗuri suke ƙarewa, sai Mairo da yake ɗan bawa..wannan dalilin yasa da wahala idan kuɗi suka ɗara dubu biyar ka sameshi a wajensa..

Ba shi da labari sai idan ya samu hanyar tafiya ƙasar waje, gaba ɗaya mutanen ƙauyenmu sai sun ji daɗi..

To amma meyasa Mairo take zaluntarsa ba zata fito ta gayamasa gaskiya ba ya kama gabansa?..

A take zuciyata ta bani amsa da;

"Ke ma da take aminyarki ta zalunceki balle shi"

Har zan yi laluben lambar Umar, sai kuma na tuna zancen Baba..murmushi na yi na ajiye wayar ina shanye ƙwallar da yake shirin zuwar min.

Tsakar gida na fito na wanke hannuna. na shiga rumfa na ɗauko abincina.

Ina ci, ina tambayar kaina;

 "anya Mairo tana da zuciyar imani kuwa?"

Ina cikin wannan tunanin na ji ana bubbuga ƙofar gidanmu.

Ban tambayi ko waye ba, saboda nasan ba zai wuce su Jamila ba.

Tashi na yi, na buɗe.

Mairo na gani a tsaye, kafin tayi magana, na yi sauri zan mayar da ƙofar na kulle, sai dai na makara, ta riga ta kutso jikinta.

Sakin ƙofar na yi, ina runtse idanuna saboda ba na son ganinta.

Juyawa na yi zan koma rumfa, kalamanta suka dakatar da ni;

"Hindatu ki ba ni wayata da kuɗina da kika sace min a ɗaki"

Murmushi na yi, kamar wata babbar mace, ba tare da na juyo ba na ce;

"Ki zo ki ƙwata ƙarfi ya cinye"

Kamar mahaukaciya sabuwar kamu, haka ta saki ƙara, ta na cewa;

"Wallahi sai kin fitomin da wayata, tunda ke ɓarauniya ce, ma ci amana"

Kalmominta na ƙarshe su suka kawoni wuya.

Ai kuwa na sunkuya da ɗebi ƙasar randar da ke gefena na juyo a zafafe na nufeta.

A zahiri Mairo ta fi ni jiki, amma ba zata gayamin ƙwari ba.

Siraran ƙafafuwa na saka da iya ƙarfina na kwashe mata ƙafafuwanta.

Tim! ta faɗi ƙasa saboda ba ta zaci haka daga gareni ba.

Kafin ta yunƙura, na saka hannu na matse fuskarta da iya ƙarfina har ina ciye haƙora.

Saitin bakinta na kai ƙasar hannuna, na dirje bakinta da shi..tana ihu da yunƙurin ƙwatar kanta.

Wannan ihun nata shi ya janyo hankalin maƙota suka shigo..na saketa.

Sai dai ina sakinta ta kamo ƙafafuwana na zube ƙasa..anan fa muka kaure da dambe.

Ina jin sanda ake cewa aje a kira Inna da Baba.

Duk yadda aka so rabamu abin yaci tura, saboda yadda muka matse juna, tana mintsinina ina mitsininta.

A haka Inna ta shigo ta same mu, su Jamila ma suka dawo daga makaranta.

Inna ce tayi min tsawar na saketa.

Ina kuwa sakinta ta fara kawomin duka, tana cewa;

"Wallahi baki isa ba, muguwa kawai, sai kin fitomin wayata"

Ban yi ƙasa a gwiwa ba, nima na zage karfina na fara kai mata duka..a take  damben mu ya dawo sabo.

Daƙyar yayyenta da aka kira suka rabamu.

Duk da haka, ba ta daina ihun na fito mata da wayarta.

Faɗa babban yayansu ya fara yi mata, amma ta kafe ita dole babu inda zata je, sai na fito mata da wayarta.

A daidai lokacin Sammani ya shigo tsakar gidanmu..ko minti biyu bai yi ba, sai ga Baba shima ya shigo hankalinsa a tashe.

Matsowa Baba ya yi kusa da ni, ya na yi min kallon mamaki..

Muryarsa a tausashe ya ce;

"Hindatu menene ya haɗaki da Mairo, meyasa zaki ɗauke mata waya?"

Kasa magana na yi, saboda wani irin kuka da ya tahomin.

Tsit kowa ya yi, ban jima ina yi ba..na yi shiru ina shesheƙa, sannan na fara bayanin abinda ya faru.

Tun daga kan zuwarmu ƙauyensu Inna har zuwa bayanin da Exam ofisan mu ya yi min, da ƙaryar da ta yimin ta biya kuɗin.. har  zuwa kan wayata da kuɗi da na gani a jakarta..

Abun ɗaya ne ban faɗa ba, shine hirarsu da Khalil.

Sammani kasa magana ya yi, kamar wanda kwai ya fashewa a ciki haka ya juya ya bar gidan.

Baba juyowa ya yi kan Mairo ya na ce; ta yi na ta bayanin ya na jinta

Mairo tsuru ta yi a tsaye, ta kasa magana...

A take maƙota su ka fara Allah wadai da ita..

Yayyenta matsowa suka yi su na bawa Baba haƙuri...

Baba murmushi ya yi, ya ce;

"Haba ai babu komai, duk yiwa kai ne..ku jata ku tafi gida, Allah Ya kiyaye gaba"

Mari babban yayansu ya tsinka mata, ta yi gaba su ka rufamata baya.

Bayan Inna ta tabbatar kowa ya fita, ta saki guɗa har shewa tana cewa;

"Ohh ni Asabe, yanzu har ni ku ke munafurta domin ku farantawa wannan mujiyar(mairo), ai dama na sawa raina komai daren daɗewa sai gaskiya ta bayyana, yanzu ai gashi ta nuna muku halinta"

Baba cikin barazana ya ce;

"Asabe wai meyasa kike haka ne? Ke da zaki taushi Hindatu, ai niyyarta zaki duba, ba wai abinda Mairo ta yi mata ba..

Yanzu ko bayan ranmu ai mun san Hindatu zata kula da bayanmu"

Da alama furucin Baba sun sanyaya mata jiki..kamoni tayi zuwa jikinta, ta fara takawa da ni zuwa rumfa.

Baba da su Jamila bayanmu suka biyo..

Nasiha Baba ya yi min akan kar na damu da abinda Mairo tayi, kanta ta yiwa, Allah zai dubi niyyata ya bani ƙawa ta gari mai irin halina.

Sai da na tabbatar Baba ya gama min nasiha, sannnan na miƙe, na nufi ɗaki.

Wayar da kuɗin  na ɗauko na fito da su, na bawa Baba, kai tsaye na ce a siyar wayar..

Baba ya so ya ce; "a'a" amma Inna ta nuna masa hakan shine daidai..rigimar ta mutu gaba ɗaya.

Layin aka cire, Jamilu ya kai bayan gida ya jefar. 

Na bi komai na cikin wayar, irinsu saƙo da sauransu na goge, tunda dama babu hotuna a kan wayar..

Barcin da na yi, na wannan rana na musamman ne, domin ji nake yi, kamar na yada ƙwallon mangoro na huta da ƙuda.

★washe gari da ƙwarin gwiwata na shirya na tafi makaranta..kuma nayi alƙawarin ba zan canza wajen zama ba, sai dai ita ta canza.

Ai kuwa ina zuwa na hangota a wata kujerar daban..ban ji komai a raina ba, na yi zamana.

Ko da aka tashemu haka na tafi gida ni kaɗai. 

Ina isa gida, bayan na ci abinci na yi sallah.

 Na duƙufa yin aikatau ɗin kuɗin da muka saba..domin wasu lokutan har da wankau mu ke haɗawa.

Daga ranar da Sammani ya bar gidanmu, ban ƙara jin labarin halin da yake ciki ba, kuma ban nemi ji daga bakin kowa ba, domin shima laifin Mairo ya shafe shi a wajena.

Haka na yi ta rayuwata ni kaɗai har ranar zuwa ranar da zamu fara Jarabawa..

A ranar ne *Fatima Muhammad Gamsarka*, baƙuwar fuskar da ta zo zana jarabawa a makarantarmu ta shigo rayuwata dalili lambar jarabawarmu da ya zo kusa da na juna.

Ban taɓa ganin fuskarta a Yankinmu ba.. wannan yasa na cika da mamaki na dinga satar kallonta.

Ba ta da yawan magana, sannan kyakkyawace a fuska, mai sanyi muryar da babu hayaniya..sannan ga ƙoƙari.

Ko da muka fito daga ɗakin Jarabawa kowa sai so yake yi yayi mata magana, amma ta na biye da ni a baya.

Bayan mun baro cikin mutane, kasa haƙuri na yi na kalleta na ce;

"Dan Allah kuma anan garin kike"

Murmushi ta yi, ta ce;

"A nan nake mana, sai dai makarantar kwana nake zuwa a garin Kaduna, ciwo ne ya kwantar da ni, watanni biyar baya..kin san gidan Fulani?"

Kaina na ɗaga mata da sauri, kalmar filti(Filthy) da Saifi ya dangantani da shi na dawowa ƙwaƙwalata.

Murmushi ta yi ta ce; "to nan ne gidan kakanni na"

Murmushin yaƙe na mayar mata. Daga haka na janyo littafina domin fara shirin tukurar jarabawa ta gaba.

Ina karatu ina satar kallon fatarta da babu datti, sai na ji na ƙwaɗaitun da son nima nawa ya zama haka, wataƙila ma da zan dage da tsafta har kyau sai na fita.

Dariya na bawa kaina, ina jin nishaɗi a cikin raina, domin duk da rashin mayar da hankali da nake yi a kan jikina, ba zaka taɓa kirana da mummuna ba..to ina ga kuma ina yin wanka akai-akai da shafa mai, mai kyau?...kasa riƙe murmushina na yi.

Abinda ya ƙara birgeni da Fatima shine rashin surutunta, tuna yanayin ɗan uwanta yasa na fara tunanin waƙila nutsuwa halittar su ce.

Muna nan zaune, wani ɗan matashi mai tsananin kama da Saifi ya kawo mata abinci, a mazubi mai kyau..

Abinda ya bani mamaki shine yadda ya sakarmin fuska har da tambayata yaya karatu; 

Ina amsa masa na ji wani irin daɗi ya kamani..

Shima satar kallon ƙafarsa da ta fi fuskarsa haske na yi, tsaf da ita a cikin takalmi.. a take na ji na ƙara ƙwaɗaituwa da son zama ƴar gayu nima.

Ya na tafiya babu jimawa Jamila ta kawomin abinci nima a kwanon siliba mai kyau.

Babu wanda ya ci na wani a cikinmu, duk da bismillah da muka yiwa juna.

Bayan mun gama muka yi sallah sannan aka fara haramar shiga jarabawa ta biyu.

Ko da muka gama muka fito, Fatima tana tare da ni.

Ina jin ƴan makarantarmu su na gulmar ashe ƴar gayu na samu shiyasa na watsar da Mairo.

Daga wannan ranar sai ya zamana duk ranar da zamu yi jarabawa tare muke tafiya da Fatima..

Ranar da ta fara biyomin mamaki ne ya kamani, na tambayeta ta yaya akayi ta gane gidanmu..

Buɗar bakinta sai cewa tayi ai Sammani ne ya kwatanta mata..daga haka ban ƙara tambayarta ba saboda ba na son jin komai da ya dangance  su, shi da Mairo.

Ranar da muka yi jarabawa ta bakwai Yankinmu ya ɗauka..masu arziƙi daga birni a cikin manyan motoci har gudu uku, sun zo tambayar auren Mairo...✍🏻