Chapter 7
by @maidambu41
Chapter 7
Da sun san waye Uban kowa ba zasu taɓa takowa har cikin gidan ba, da sunan waye a tsaye a gabansu ba zasu taɓa sha'awar zuwa mishi ba. uban kowa fa? Idanunsa ne ya sauka akan Hajiya da take zube a kasa ta zauna dabas tana hawaye ganin yadda suke dukar shalelenta. Ai yau ko kisan kai shalele yayi ba zasu mishi irin wannan dukar ba, Allah sarki yaron da ta tashi cikin maraici, zuwa gabanta yayi yana faɗin." Hajiya tashi kin ji!" Abba Babba da shima abin ya bashi tsoro da al'ajabi. Ya cewa Maamah. " Ku koma ciki!" "To! " Suka bar wurin, Hajiya tana mikewa ta sake tafiya zata zube sai numfashi da haki. "Hmmm ina ganin asibiti zan kaita." " To muje mana!" A wani hargitse ya kalli Abba Babba yana wani taune bakinsa ya ce mishi. "Su kuma matan waye zai tsaya idan baka nan bana nan?" Yadda yayi maganar yana ajiye Hajiya a a jikin motar ya juya ciki da gudu. Bayan kamar minti biyar sai gashi da key. "Zaka iya tafiya?" Shiru yayi yana mai buɗe motar suka saka Hajiya A baya. Ya rufe motar suka bar gidan Abba Babba ya rufe gidanshi, duk wannan abinda yake faruwa Tente Hasiya bata leko ba asalima tsoron tsiya ce da ita.
A bangaren Naanah Asma'u bata iya barci ba, abu goma da ashirin suka tsaya mata a rai. Na farko irin dukan da suka mlshi amma yana da ƙarfin zuciya da ya ce kada su fara abinda suke da niyya, sai Hajiya wanda tasan ba wai don sun ce yana aikata wani abu ne ya sakata a haka ba, sai don kawai sun taɓa shi. Tana kallon lokacin da take ta ƙoƙarin ganin ta shiga tsakaninsu da shi amma suka ture ta. Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon inda take kwance. Goshin asuba barci ya dauke ta, ba zata ce Allah shi kara ba, amma kuma ba zata ce Allah ya sawwaka ba, ita a wa ma zata ce Allah ya ƙara.
Sai da aka fito masallaci Abba babba ya tashe su, domin yasanta da daurawa kanta damuwa. Yana tashinsu ya shirya ya nufi asibitin wanda yasan wahala zai sha tunda Uban kowa bai gaya mishi inda suke ba. Haka yayi ta bin asibiti da suke cikin garin Agadaz, dakyar ya samo su a wani asibiti mai zaman kansa. A bakin kofar dakin da Hajiya take anan ya same shi zaune, shima an mishi treatment. "Ya Hajiya da jikinta?" d'ago kai yayi ya ce mishi. "Da sauki!" Sannan ya mai da kanshi ga kofar kamar idan ya dauke kansa daga kofar wani zai shiga ɗakin saboda yadda jinin hajiyar yayi mugun hawa. Shiru wurin ya ɗauka har zuwa karfe bakwai na safe lokacin da likitan ya zo. Ya mika musu hannu suka gaisa. Sannan ya tambaye su kwanar mai jikin yana me shiga ɗakin, ya jima a cikin ɗakin kafin ya fito daga cikin dakin ya ce musu. "Jininta yana hawa da sauka ina ga zamu riƙeta zuwa lokacin da jinin zai daidaita." Jinjina suka yi Abba Babba ya ce mishi. "Ko zaka tafi gida ka karya sai ka tawo da Rukayyah!" Yana ganin girman Abba Babba domin ya mishi wasu alfarman da mahaifinshi ya gaza mishi yasa ya amince amma da babu dalilin da zai saka ya bar wurin nan idan ba sallah ba. Hajiya ita ce mace ta farko da ta bashi kome a rayuwarshi, ya rasa uwa a lokacin da ya ke buƙatarta, ya kuma rasa mahaifi a lokacin da ya dace ya ji daɗinsa. Ya rasa abubuwa dayawa amma Hajiya da Maamah suka bashi wuri a zukatansu duk da yasan ita Maamah ba tana yi don kawai yana dan kanin mijinta ba, tana yi ne a matsayin uwar da bata samu nata ba, da ta samu nata ya zata juya mishi baya zata yi sai ya ga ba haka take ba. Haka yasa yake ganin girmanta. Mikewa yayi yana tafiya a hankali amma jiri yake kwasarshi. Haka ya daidaita nutsuwarshi. Har ya isa inda motarshi take ya shiga, kifa kanshi yayi yana jin wata wutar masifa ce take ci a ransa. Dakyar ya bar asibitin tafiyar minti shs biyar ya kai shi gida.
Tunda ya fito ya buɗe gate din bangaren Hajiya ya shiga cikin gidan, abin da ya faru a daren jiya yana yawo a kanshi. Ga jini yadda ya bata interlock din yasa shi shiru yana jingine da kofar gate din, kamshin Omo da bleach ya dawo daga dogon nazarin da yake, ita ce rike da tsintsiya tana wanke wurin. Bata san ya shigo ba don ta bawa kofar baya, sanye take cikin riga da wando na barci me kauri pink colour, sai farin hula da ya haska fatarta. Tana rera kira'a, da sassanyar muryanta cikin suratul bakara. Kura mata idanu yayi kafin ya gyara muryansa, bata tsammaci wani zai shigo cikin gidan ba, a zabure ta juya zata bar wurin tsantsin omo ya kwashe ta, ta zube a kasa sosai. Watsa mata harara yayi wanda yasa ta mikewa da sauri zata bar wurin taku uku yayi ya riko rigar jikinta, abinda ya sakata bude baki zata yi ihu ya buge bakin tuni tayi shiru. Jikinta yana rawa, "Uban me nayi da zaki gudu? Mummuna kawai ni ban guje ki ba da wannan mummunar halittar naki." Yayi shiru yana ganin yadda jikinta yake kerma.. ya tsani wannan tsoron wallahi da yana da yadda zai mai da ita mata kunya da yayi, ture ta yayi ta je zata fadi kan bokitin ƙarfen ya kuwa saka doguwar kafarshi yayi ƙwallon da bokitin yana hararanta. "Ki gayawa Maamah ta shirya na kaita!" Gyada kai tayi ta bar wurin da gudu aikin da bata gama ba kenan, ta je ta gayawa Maamah. Can sai ga Maamah da Mairoh har Parlourn Hajiya Mairoh na dauke da abincin suka kawo mishi, yana zaune kanshi ne yake ciwo sosai. Ganin Maamah yasa shi saurin mikewa.."Ina kwana Adam ya mai jikin?" " Da sauki Maamah" ya fada a hankali yana kallon Mairoh da ta ajiye mishi abinci tana faɗin. " Allah ya bata lafiya! " "Amin!" Shiru suka yi yana kallon abincin, kamshin kosai da kunu ya biya ransa. Amma saboda hali irin nasa kada a rena shi ya share, "To Allah ya bata lafiya." Suka mike zasu fita ya ce mata. "Hmm, Abba babba ya ce na kai ki, sai a turo ta ta kwashi kayan Hajiya da zata bukata!" Gyada kai tayi ta ce mishi. "Ga Mairo nan ta shiga ta duba kayan!" Dauke kai yayi ya ce mata. "A'a ta barshi zan duba da kaina!" "Tow bari na turo Uwata!" Wato Naanah Asma'u, shiru yayi bai kula su ba har suka fita. Hararan kofar Mairoh tayi ta ce mata." Ba wani Didih ta zo mugun wani abu zai mata baki ga yadda ta jike ba kayanta duk ya b'aci ba mamaki ture ta yayi!"
" Ita ta ce miki ya ture ta?" Maamah ta tambaye ta, " Maamah ke da bakya son laifinsa, waye bai san yadda ta tsane ta ba ranar da ta dawo konata yayi fa." "Ita ta gaya miki haka? Ko kyautata zaton ga kowa." Shiru tayi bata kara magana, duk maganar da suke yana ji amma bai san yadda zai daina ƙuntatawa yarinyar ba haushi take bashi ya ganta tana farin ciki haushi yake bashi, ya ganta tana abu kamar lusara kara mishi bakin ciki yake yana ji kamar a kashe shi da ransa. Ya tsani ragonta ya tsani lusaranci.
A hankali ya dauki kunun yana sha, yana cin kosan da yayi laushi yana kallon agogon hannunsa. Har y gama sha a gaggauce shi haka Allah yayi shi kome nashi a gaggauce yake yinsa. Bai iya kome a hankali, dakin Hajiya ya wuce bai tsaya jiranta ba ya shiga duba karamin jakarta. Daidai lokacin da ya ji siririn muryanta tana sallama, amma yaji ya tsaya cak a hankali ya ji tana waya tana faɗin. "Hmm!" Shima tsayawa yayi yana jiran ko zata shigo dakin amma sai yaji tana cewa. "Abba Babba yana can, yanzu zasu tafi da Maamah don Abba babba ya dawo ya tafi kasuwa." "Cherry!" Ta furta can kasar makoshinta, yar dariya tayi tana me niman kujera ta zauna. Nan fa soyayya ya ɓalle tsakaninta da Ya Almu. Duk da ba wani abu suke fada ba, daga "hmm" idan ta fada mishi,. Shi kuma ya ce mata. "Uhmm!" Fitowa yayi ya tako ta inda take ya fisge wayar ya buga da bango, a tsorace ta juya tana kallonshi. Zagayowa yayi yana kallon yadda jikinta yake rawa. "Fita ko na karya kafarki!" Kasa motsi tayi tana kallon kasa. "Fita nace!" Ya daka mata tsawan da ta zube a kan kujerar. "Ba cewa nayi ki fita ba?" Gyada kai tayi ta shiga kokarin mikewa ya d'ago tare da fito da ita, ya turo ta waje. Ya koma ya kwaso tarkacen wayar ya watsa mata a bayanta. Don haushinta ma ko magana baiwa Maamah ba ya zuba kayan Hajiya a mota zai tafi Maamah ta fito daga cikin gidan ita da Khamilah, suka shiga baya ya cewa Khamilah.. "ki dawo gaba!" Ba musu ta fita tare da dawowa gaban ta zauna suka bar gidan.
Har suka isa asibitin babu wanda yayi ko tari, haka suka isa dakin da aka kwantar da Hajiya. Duk wani abinda ake bukata ya dauko. Ya shiga da shi Abba babba yana dakin a zaune suka shiga Hajiya tana barci. "Abba ya mai jiki? " " Da sauki Khamilah!" Ya fada yana kallon Maamah."kin kawo min lalita na?" "Eh" ta mika masa, "Adam bari na tafi kasuwa, ina ga zan dawo karfe goma in sha Allah!" Ya fada yana tura takardan da aka rubuta musu wani magani. Gyada mishi kai yayi, yana fita shima ya bi bayansa ya ce mishi. "Abba babba!" juyawa yayi ya ce mishi.. "bani takardan!" Ya fada kai tsaye ba tare da ya kalle shi ba, "ka bar shi wasu allurai ne yanzu zan kawo." "Abba kenan bani kada ka damu hakkina ne na tsaya akan Hajiya domin laifina ne ya janyo haka, zunubina ne don Allah idan ka dauke ni kamar su Khamilah bani don Allah!" Shiru Abba Babba yayi yana jin idan ya bawa Adam takardan gazawarshi ta kai kololuwar gazawa. Murmushi yayi ya ce mishi.. "ni kuma mahaifiyata ce, hakkina ne na kula da ita kayi hakuri ka ji nayi wannan aikin!"
"Abba babba kada ka saya don Allah, domin na rigada na biya kudin kome tunda na kawo ta, idan ka saya zaka yi asarar kudinka ne don Allah kada mu yi haka da kai, ko iya abinci da za a kawo aiki ne balle har magani,. Na sani hannunka bai cudi baya ba!" Wannan kalmar tayi mishi nauyi amma ba yadda ya iya a yanzu idan Abba babba ya fita bashi zai je yayi ta ci, har ya samu ya jefa kanshi cikin wata damuwa. Zuwa yanzu abinda yake da ita duk saboda hajiya nashi tass babu idan kuma ya ce zai taɓa yayi ta bin mutane yana niman rancen kudi karshe ya dauki daya daga cikin amanar da aka bashi ya sayar don Hajiya.. murmushi yayi "Mahaifiya ta ce!"
" Ko ba ka bani takardar ba zan saya da kuɗina, domin zan saka su sake rubuta wa. Allah ya buda maka!" Ya fadawa Abba yana me amsar takardan maganin. Ya wuce cikin abinda ya bar Abba a tsaye. Bai san lokacin da Abba Babba ya bar asibitin ya cewa Maamah. "Bari na amsa magani!" "Shi kenan! A dawo lafiya." Fita yayi daga dakin ya tuna kudin hannun hannunsa sun kare, wanda yake account dinsa bai fito da ATM card din, gida ya nufa.
Lokacin da ya shiga cikin gidan, suna tsakar gidan, matar Abba Babba ta shaƙe Naanah Asma'u. Mamaki ya kama shi ina Mairoh don yasan da tana gidan ba zata bari haka ya faru. "Bani kudin da na baki jiya!" Yadda ta shaketa bai dame shi ba, shi abinda ya kawo shi ya tambaye ta. Yake Hasiya tana shakkar shi sai ta sake ta tana faɗin. "Bata da kunya ne!" Sosa kunnensa yayi yana kallon Naanah Asma'u ya mata wani irin kallo da yasa bata gama shakar iskar da take ta baki ba ta juya zuwa ciki. Taku daya tayi kawai ta zube a wurin. Wani huci yayi ya kalli Hasiya, dama abinda yake so kenan ta shiga ciki ta ci mutuncinta. Bai ce kome ba ya juya kamar zai tafi wani bulogarin karfe ya dauka yana juyawa ya daki gwiwar hannunta, ta kwala wani irin ƙara tare da juyawa tayi tana kallonshi. "Me nayi maka?" Ta fada tana jin kamar hannun baa a jikinta yake ba. Kafin tayi wani yunkuri ya saka kafarshi ya take wuyar kafarta wanda yasa ta jin kamar ba a jikinta yake ba. Dan durkusawa yayi ya ce mata. "Ba yau na gargade ki ba ai idan kin warke sai ki daura daga inda kika tsaya!" Ya nufi inda randar ruwan sanyi yake ya diba a cikin wani bokiti yana diba bai tsaya kawai yana zuwa kan Naanah Asma'u ya juye mata ruwan bakiɗaya a kanta. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke da karfi tana jin saukar ruwan. "Kuɗina!" Ya fada mata yana kallonta. Da rarrafe ta nufi hanyar ɗakinsu. Can kasar gadon ta tsaya tana numfashi saboda asthma da yake son tashi, kallon kofar tayi tana addu'ar Allah yasa ya shigo ya dauka. Shima jin shiru yasa shi takawa zuwa dakin ya samu tana kallon kofar. A hankali ta kai hannu tana jan numfashi ta janyo ƙunshin tare da kifawa akan kayan, tsugunawa yayi ya hankali ya d'ago kanta ta koma ta zube a kirjinsa.. wani irin bugu zuciyarsa tayi ya zuba mata ido. Yana kallon pale face dinta zuwa soft lips ɗinta, da yayi fari kamar me fama da wani ciwon bayan asthma. A hankali ya janyeta daga kirjinsa ya dauki abinda zai iya ɗauka. Sannan ya mai da kudin ya cire bindigarshi har a lokacin kanta yana cinyarshi a kwance yana kin dashen ruwan da ya kwara mata. Yana gamawa ya mike tare da d'agota wanda yayi daidai da shigowar Mairoh dakin, a hankali ya kwantar da ita. "Me ka mata?" Ta fada a tsorace. "Duk abinda yazo ranki ya fada yana ɗaukar bindigarshi ya bude tare da duba harsashin. Shiru tayi ya saita bindigar akan Naanah Asma'u. "Yayarki ko shiru da bakinki?" Idanunta ne ya cika da kwalla ta sha gabanshi yadda yake saita bindigar akan Naanah Asma'u. Ta ce mishi." Shi kenan kada ka cutar da ita don Allah! " Murmushin gefen baki yayi ya sosa kanshi da bindigar. "Kin kwace ta!" Ya ɗauki abinda zai dauka ya juya zai fita ya ce mata."Inhalerta!" Ya saka kai ya fita, yana fita ya kalli Tente Hasiya, ya nuna ta da bindiga. tsoro ne ya kamata. "Idan kika sake na kara ganinki wallahi sai na lalata miki kafarki." Yadda yayi maganar yasa ta sunkuyar da kai, jikinta yana rawa.