Chapter 8
by @maidambu41
Yadda ya barta a cikin tashin hankali ya mishi daɗi tunda ita ba zata iya kwatar kanta ba. Sai dai kuma tuki yake hankalinsa ya rabu biyu, a halin da ya barta zata farka kuwa? Ko dai ya juya motar ne? To akan me zai damu da ita? Yarinyar da bata damu da rayuwarta ba? Ita kawai ta zauna ana wulakantata. Kurawa hanyar ido yayi yana jin kamar ya koma ko ya cigaba da tafiya ne. Wata zuciya ta tilasta mishi dawowa gidan kamar kiftu sai dai turus yayi lokacin da ya hango Mahmoud dauke da ita, shiru yayi yana kallon yadda Mairoh ta shiga bayan motar bayan ya kwantar da Naanah Asma'u a cikin motar.
Wani abu ya ji ya tsaya mlshi a kahon zuciya, ba wannan bane karon farko da Mahmoud yake mishi shigar sauri ba. Amma na yau har da laifinsa wurin barin ta a cikin wannan halin. Nauyi kirjinsa yayi kamar an danne mishi da wani katon dutse, akan idanunsa suka wuce idan ya ce bai ji haushin Mahmoud ba yayi karya. Tsintar kanshi yayi da bin motarsu, ya ga ba asibiti da ya kai Hajiya Mahmoud zai kai Naanah Asma'u, ba ai kuwa ya kasa hakuri wani irin overtake ya musu wanda yasa saura kiris motarta kifa. Ya kuma tsare musu hanya yadda ba zasu motsa ba. Ba tare da ya damu ba ya fitar da wata wukarshi ya nufi motar tsirara da wukar. Yana zuwa abinda ya fara sokawa a tayar motar Mahmoud. Ai kuwa take iskar tayar ta sace. Ya koma ya bude gaban motar. Ya zo ya shiga kokarin buɗe bayan da take Mahmoud bai kula shi ba, da hannu ya mishi alamar ya bude ko ya fasa glass din motar. Banza Mahmoud ya mishi. Ganin yadda ya koma da baya ya gyara hannun rigarshi ya alamar abinda yake shirin aikatawa ba karamin al'amari ba ne, da sauri Mairoh ta bude motar. Da yake a baya take. "Ina wasa dake? Da bata farka ba, me yasa ba zaki kira ni ba? Kina da wanda ya fi ni ne?" "Don Allah kada ta mutu!"
"Lallai na yarda kai jahili ne, mahaukacin banza wanda bai san ciwon kanshi ba." Mahmoud ya gaya mishi madadin ya ji haushin Mahmoud, dauke kai yayi daga Mahmoud yasa Mairoh ta fito da ita har wurin motarshi ya tsaya sai da ta sakata. Ya shiga ta ɗaya gefen ya kwantar da kujerar. "Zaki shiga ko nayi tafiya ta?" Ya tambayi Mairoh yana hararanta. Ba musu ta shiga baya tana waiwayen Ya Mahmoud ba yau suka saba mishi iskanci da wancan shegen gayen na Austria ba. Ba wanda zai kara mishi iyayi. Har asibitin suka isa, lokacin da Likitan yake tambayar abinda ya same ta. Jan likitan yayi gefe ya mishi bayani, sannan ya juya ya bar wurin. Cikin gaggawa aka saka mata iskar osijin, shi kuma ya je ya sayi maganin Hajiya har zai tafi ya dawo ya samu likitan, " zata farka ta koma gida?" Yadda yake tsare likitan da ido kamar zai ci babu yasa shi cewa. " Zata koma amma yana da kyau a kiyaye abubuwan da zai saka tana samun attack akai akai." Wani cizon bakinsa yayi yana faɗin. "Ina jinka!" "Tana daina yawo babu makarin fuska, ns biyu kada tana shiga iska ko ƙura mata amfani, haka a kiyaye shigarta cikin ruwa ko aiki da ruwa da sassafe. Sannan kada tana saka kaya mai matsatsan wuya. Sai abu na gama a kula da ita kada tana shiga ruwa koda yaushe. Zata farka nan da awa ɗaya. Ka ga damina muke tunkara don Allah kada ta shiga ruwa." Sosa giransa na dama yayi ya ce mishi. "Bayan nan fa?" "Bamu samu wani abu ba, sai dai akwai hoton da zaa yi mata domin naga kamar kirjinsa akwai matsala." "Ba iya asthma ba kenan?" "Eh to daga yanayin farin da bakinta yayi yasa nayi magana, ka duba bakinta da kyau mana." A sanin da yake da shi yana yawan fahimtar lips ɗinta yana haske wato yayi fari kamar wacce take jin ƙishirwa. Yadda ya gama juya kanshi ya d'ago kai da sauri ya ce mishi. "Zuciyarta?" "Ban tabbatar ba," wani cakumo likitan yayi. "Kada ka sake wani yasan da zancen nan ayi duk abinda ya dace zan zo na mai da su gida, kasan Allah kada ka bawa kowa sakamakon na gaya maka." Yadda ya budewa likitan idanuna yasa shi gyad'a mishi kai, sannan ya juya ya fita ya sami Mairoh a zaune tana kallon hanyar da zai fito. Tana ganinshi ta mike tana kallonshi so take ta tambayashi amma yadda bai bata fuska yasa ta leka bayansa tana me maida idanunta kanshi. Dauke kai yayi ya wuce ta bai mata Magana ba. A karon farko a rayuwarshi da ya fahimci me ake kira tausayi. Yana jin yadda take kallonshi amma bai juya ba, yasan kuka take. Tafiya yake cikin nutsuwa da jarumta yadda kasan toron giwa. Haka ya b'acewa ganinta, zama tayi tana shashekar kuka. Fitowar likitan da wasu Nurse biyu suna tura ta a keke yasa ta mikewa. "Didih!" Kasancewar har lokacin bata san waye akanta ba. Yasa bata san me Mairoh take fada ba. Haka suka shiga da ita wani daki aka rufe ɗakin, sun fi minti talatin a cikin dakinki kafin suka fito daga cikin dakin.
A kofar dakin ya sami Mairoh tana jingine da jikin ɗakin tana jiransu. Yana xuwa bai wani wata wata ba, ya tura kofar ya shiga ya same su suna ta daukar hoton kirjinta. Bakiɗaya suna tsaye amma sun kasa yarda da abinda sakamakon ya bada ba. "Fita don Allah!" Wani kallon banza yayiwa Nurse din ya cewa likitan. "Ina da degree a human anatomy, degree biyu gaya min meye kake ɓoye min!" Jin haka yasa likitan ya mika masa laptop ɗinsa duk da saninsa akan dan adam amma ya kasa fahimtar komai akan sakamakon. Mika mishi yayi ya zuba mishi ido yayi masu cike da tsoro. "Gaya min!" Shiru likitan yayi yana kallon yadda yake kallon Naanah, "Kanwarka ce ko matarka ce?" D'ago fararen idanunshi masu kama da na mage ya kafe shi dasu yayi. "Dame ka ga na dace a gare ta?" Shiru yayi yana kallonsu yanayinsu ya nuna kamansu ta wani gefe kuma sun fi dacewa Ma'aurata. "Matarka!" Murmushi yayi wanda tunda yake a rayuwarsa wannan ita ce kalmar da tafi bashi dariya ya shafa kanshi. Tare da sosa giransa na dama. "Hmm!" Ya faɗa yana kallon fuskarta yana jiran abinda likitan zai faɗa. "Ina jinka!" "Ko za muje office dina ne?" Takaici ne yasa ya watsawa likitan wani kallon banza yana faɗin. "Zaka gaya min me yake faruwa ko sai na hana kowa sakat a cikin asibitin nan?" "Shi kenan, amma nime wuri ka zauna!" Ya nuna mishi wuri ya zauna, amma saboda rashin mutunci irin nasa ys ce mishi. "Ka ga nayi kama da wanda zai razana?" Ya tambayi likitan, girgiza kai likita yayi kafin ya ce mishi. "To shi kenan!" Shi sai ya nime wuri ya zauna. "Ina jinka kana bata mana lokaci ne fa!" Shiru likitan yayi yana mai mikawa Nurse din laptop din ta mika mishi takardun da aka gama printing. "Wannan takardun na binciken da nayi ne, ciwon da yake damunta bai da alaka da asthma, asalima tsakanin Asthma da ciwon kamar tazarar mai nisa ne." Mika mishi tap nurse din tayi ya mika mishi. "Wannan zanen huhunta ne lafiyarsu lau, shi kuma inda yake ciwon kirjinta ne gefen hannu inda zuciyarta yake, zaka ga ƙarfin zuciya zuciyarta yake da shi, wanda akalla zai iya kaita shekara daya zuwa uku, bamu ke da rayuwa ba amma mara lafiyarka damar da take da shi bai wuce kaso 35% ta rayu ba, bakiɗaya zuciyar tayi rauni ta kusan mutuwa bakiɗaya daga gangan jikinta. Idan haka ya faru to ita zaku rasa bakiɗaya." Ji yayi duniyar tana wani juyawa ne ko girgiza take yaji kamar zai faɗi ƙasa. Bai san lokacin da ya dafe gadon da take ba, yana jin wani irin ciwon kai mai ƙarfi kamar kanshi zai tsage.
Likitan yayi maza ya rike shi, zufa yake kamar an watsa mishi ruwa. Likitan ya ce. " Bani kujerar can! " Buge hannunsa yayi ya tsaya da kafarshi ya juya yana kallon fuskarta. " Tun yaushe take da shi?" " Gaskiya yadda ya samu wuri a jikinta nan, ya jima sosai a tare da ita abinda ban fahimta ba shine ƙwayoyin halitta sun ki barin musamman cewa shin haihuwarta akayi da shi ko daga sama ta same shi?"
"Yanzu babu maganin da zai warkar da ita ne?" Girgiza kai likitan yayi ya ce mishi." Maganin shine a nisantata da duk wani abun tashin hankali. Sai magani amma asalin warkewarta shine a bata wani zuciyar." "Zai kai kamar nawa?" Shiru likitan yayi kafin ya ce. "Gaskiya ku tanadi kudi me yawa, domin zaku iya kashe CFA Miliyan goma haka!" Murmushi yayi ya ce mishi. "Ana samun zuciyar?" Girgiza kai likitan yayi yana faɗin. "Ana samu amma yana da wahala domin ba kowa yake yarda ayi wannan aikin da sassan jikin dan uwansa ba. Sai dai ko zaku fitar da ita kasar waje." Wani irin bugawa zuciyarsa tayi kamar zata fasa kirjinsa.
Wani irin tausayin Abba babba ya kama shi, idan ya ji wannan labarin ya zai dauka? A hankali ya ja kujerar ya zauna yana mai saka hannunshi a kanshi kamar wanda aka ce ya tabka asara mai girma. Shiru ɗakin ya ɗauka ya mike." Ubangiji ya shiga lamarin!" Ya d'ago ta ya daura a kujerar da aka shigo da ita dakin. Ya shiga tura ta a hankali. Ya fito da ita yana kallon Mairoh da tayi zuru-zuru tana kuka. "Ya Adam!" "Muje gida zan karɓo duk wani abinda ake buƙata." A hankali take tura kenan har waje ya amso ledojin maganin sannan ya zo wurin motar ya taimakawa Mairoh suka sakata a cikin motar. Sannan ya zaga ya shiga motar ya saita madubin motar yana kallon fuskarta har suka bar asibitin, a hankali ya ce mata. "Mairama!" D'ago kai tayi tana mamakin yadda ya san sunanta."Idan muka je gida zaki musu abinci, zan dawo na ɗauka. Ita kuma ki saka idanun a kanta. Sannan kada ki yi nisa da ita." Shiru yayi kafin ya ce mata. "Kada ki gayawa Abba Babba da Maamah, zan bar kome zamu biya mu dauki sadisu ya saka mata kome. Ku tayata da addu'a bata da lafiya sosai." Rufe bakinta tayi tana kuka, tunda ya faɗi haka ya tabbatar mata Didi bata da lafiya Didih dinsu mai sonsu. " " Ya Adam asthma ce?" Girgiza kai yayi yana kallon hanya har suka isa kofar shagon sadisu ya futa ya miishi magana ya zo ya shiga gaban motar suka nufi gidan da su, haka suka fita Mairoh ta kasa riƙeta , zuwa yayi ya dauke ta cak yayi cikin gidan. Har zuwa cikin dakinsu ya kwantar da ita ya gyara zaman rigarta. Ya cewa Sadisu. "Bari ta sauya mata kaya ko?" "Ba kome!" Fitowa suka yi Mairoh ta sauya mata kayan, saboda har yanzu a jike suke. Motsin da tayi da hannunta Mairoh ta ce mata. "Sannu Didih" bude ido tayi sai kuma ta rufe, haka ta gama ta gaya musu cewa ta farka. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Sadisu. Suka shiga dakin haka ya saka mata ruwan. Da kome Sadisu ya ce mishi. "Ko za a taimaka a nimo monita da zai taimaka mata wurin numfashi?" "Zai kai nawa?" "Eh tow ina ga zai kai dubu dari bakwai, kuma yana aiki ne da wuta fa!" "Sai me?" "Su kenan sai nurse!" "Shi kenan xan iya samu a yau?" Gyada mishi kai yayi ya ce mishi. "Zai zo amma irin daren nan!"
"Shi kenan muje zan zo yanzu!" Fita Sadisu yayi ya kalli Mairoh sannan ya durkusa Kasan gadon, ya janyo kayanshi ya shiga cire kudin sannan ya mai da su. "Idan kina buƙata ki dauka abinda zai miki!" Daga nan ya fita, shiru tayi tana mamakin yadda ya koma kuma? Abinka da kwaya. Fita tayi kitchen, ta rasa me zata dafa can sai gashi dauke da manyan ledojin nama da kayan miya. Duk ƙoƙarin Abba Babba sai ta ga ashe akwai wanda yake irin wannan aikin. A da can kallon mahaukaci take mishi, sai dai yau daya ya sauya kome abinda bata taɓa gani ba.
Duk da rufin asirin da Yan uwan Abba babba suke da shi amma kiri-kiri suka nuna shi ba kowa ba ne. Sai wurin karfe uku ta gama lokacin ya dawo ya amshi na asibitin ya wuce da shi. Lokacin da ya isa ya samu Babarshi Hajiya Atikah ta zo."Uban kowa wai me ya faru ne? Na tambayi Rakiya tayi tace Hajiya ce ta fadi kawai!" "Karya tayi kenan? " Ya tambaye ta yana kafe ta da idanunsa da suke hargitse." A'a na dai yi mamaki ne! " " Tunda kin zo Maamah ko zaki koma gida ke da Khamilah wancan yarinyar jikinta ya motsa itama!" "Naanah ko?" Gyada kai yayi mata, sannan ya ajiye ya juya wurin Hajiya da take ta barci. Shafa kanta yayi ya cewa Maamah. "Ta farka kuwa?" "Eh ta farka ta sha ruwa ta koma!" "Alhamdulillahi!" Ya furta yana kallon Hajiyar ya gyara mata kwanciya da zaman mayafin da aka lullubeta da shi. Sannan ya cewa Hajiya Atikah. "Zaki zauna sai dare Turai zata zo domin na gayawa Jamil ya gaya mata zata zo!" "Muje Maamah!" Suka dauki kwandon safe wanda Hajiya Atikah tana zuwa ta cinye tas. Sannan suka fita daga dakin yana gaba suna binsa. "Jikin Didih dai na rasa me yake faruwa? Ta dawo lafiya amma ciwo cikin kwanaki biyu yana tashi a kai a kai!" Da sunan me yake damunta ba zasu fadi haka ba.. haka suka iso har Khamilah ta fita ya juya ga Maamah. "Maamah dama tana da wani ciwo bayan asthma ne?" Girgiza kai tayi ta ce mishi. "Ta dai ce min kirjinta yana ciwo dai!" Shiru yayi kafin ya ce mata. "Kuma baku je asibiti ba?" "Wai na ga ko asibitin muka je maganar asthma suke fada mana!" Shiru yayi yana auna maganar kafin ya ce mata. "Shi kenan! Allah ya bata lafiya!" Fita tayi zata shiga gidan Mahmoud ya zo shima. Jan motar yayi ya bar gidan. Har unguwar,
Fitowa Mahmoud yayi ya nufe ta. " Yaron can bai da mutunci, Maamah! " " Kai dai tun yarinta naka bai hadu da Adam ba ne amma yana da kirki! " Ta fada suna shiga cikin gidan, bai gaya mata abinda ua faru ba, amma yadda yake mita ya tabbatar mata sun yi arangama. Lokacin da suka shiga cikin gidan, jikinta yayi sanyi parlourn suka shiga a parlourn ta samu Khamilah tana tambayar Mairoh. " Me ya same ta? " " Wallahi ban sani ba, sai dai dukkansu har Tente Hasiya abin ba dad'i. " Shiru Maamqh tayi ta shiga cikin dakin ganin yadda aka saka mata ƙarin ruwa yasa jikinta yayi sanyi. Ko ba a gaya mata ba abinda ya faru da Naanah Asma'u yana da nasaba da Hasiya. A saninta kiyayyar da Adam yake nunawa Naanah Asma'u bai kai yadda zata shiga wani hali ya kyale ta ba, sannan ba zai iya barin ta cikin mugun yanayi ba, Hasiya tayi mata wani abu ne. Bata san wacce irin kiyayya Hasiya take yiwa Naanah Asma'u ba, domin tasan yarinyar ba ruwanta da ma Mairoh ce ko Khamila zata ce basu da kirki amma Naanah Asma'u fa......