MATAR GIDA PAGE 35
daMATAR GIDA 035
SHUUKRAN/022
P35
Da wani irin sauri Ɗalha ya ɗago kansa tare da rufewa Unaisa jiki bazai iya cigaba da kallon wajen ba,numfasawa ya yi kafin ya mayar da dubansa gareta tana ƙokarin tashi zaune bayan ta zauna ta mayar da dubanta ga Ɗalha tana gyara hular kanta ta ce ''cuta ta kamani ko babe?" Ɗalha da ya yi nisa cikin tunani ya kalleta tunani yake yaya amaryar da bata yi sati biyu a gidan miji ba ta kamu da irin wannan sanyi,yana da tabbacin ba daga jikinsa ta samu ba sai dai in dashi ta zo gidan,kallon ta ya yi na wasu ƴan sakanni gaba ɗaya ya rasa abin faɗa kawai ya ce taso muje babu musu ta bi bayansa yana tafe tana biye da shi har cikin bathroom ɗinsa,nan ya nuna mata bathtub dake cike da ruwan ɗumi ya ce ''oya bismillah shiga ki zauna'' jiki babu kwari Unaisa ta cire riga sai nunnuƙiwa take a dole tana jin kunya bayan ta zauna cikin ruwan ne Ɗalha ya umurce ta da ta sa hannu ta wanke wajen ta marairaice fuska ta ce ''zafi yake min'' kallonta Ɗalha ya yi na wasu ƴan sakanni kafin a hankali ya sunkuyo ya kai hannunsa ya fara wanke wajen,wani ƙara Unaisa ta sake amma bai saurareta ba ya mayar da hankali wajen wanke wajen,lungu da saƙo Ɗalha ya sa hannu ya wanke tun Unaisa na tura masa hannu har ta hakura ta daina gaba ɗaya ta nime zafin ta rasa hakan yasa ta sake jiki ta zauna cikin ruwan,sau biyu ya canza ruwan kafin daga bisani ya yi mata wanka tsaf ya dauki clean towel dake rataye cikin bayin ya dauko ya miƙa mata,karɓa ta yi tare da daura a ƙirji,tare suka fito tana manne da shi ɗakinta ya nufa da ita bayan shigarsu ɗakin ɗaya daga cikin akwatunan lefin ta Ɗalha ya buɗe ya dauko riga da wando na bacci ya ɓare daga leda kafin ya miƙo mata babu musu Unaisa ta karɓa ta sa,sosai ta ji daɗin jikinta a wannan daren wannan zafin da kasanta ke mata ta ji gaba ɗaya ya daina kamar an cire mata ciwon haka taji Ɗalha dake zaune bakin gado yana ƙare mata kallo har ta gama sa kaya bayan ta gama ne Ɗalha ya jefo mata tambaya inda ya ce ''ba a ba ki maganin sanyi bane a gidan ku? shiru Unaisa ta yi tana binsa da kallo so take ta fahimce inda zancen sa ya dosa ganin irin kallon da take masa yasa ya gyara zama idonsa cikin nata ya ce ''ina nufin irin gyaran da ake yiwa amare kafin a tura su gidan miji ke ba a yi maki bane?" shiru Ɗalha yana jiran jin amsa daga bakin Unaisa har sannan idonta a kansa ganin da gaske bata fahimta ba yasa ya ce ''ina nufin magunguna haka irin na sanyi da sauran su ba a baki ba?" numfasawa Unaisa ta yi sai a sannan ta fahimci abinda yake nufi hakan yasa ta gyara tsayuwarta idanunta cikin nasa ta ce ''har maganin zafi in akwai to fa an bani,kusan wata guda ana banka min magunguna iri iri..shiru ta yi na wasu ƴan sakanni tana shirin hawa gado ta ce ''me yasa ka tambaya?'' shiru Ɗalha ya yi bai ce komai ba yana ƙare mata kallo mayar da dubanta ta yi garesa sanda ta ja bargo tana rufe jiki AC da ta bare a kunne yasa ɗakin daukan sanyi ta ce ''bacci zan yi yanzu..kai fa ina zaka kwanta?" ta kare magana tana haye gado zuwa yanzu Ɗalha ya daina mamakin halaiyar Unaisa kallonta kawai ya ke cikin zuciyarsa ya ce ko godiya bata yi min ba,numfasawa ya yi kafin murya can ƙasa ya furta Allah shi kyauta,daga haka ya fita daga ɗakin zuwa nasa,bayan shigarsa ɗaki idonsa ya dauka kan wannan zanin da Unaisa ta shigo da shi ɗazu taɓe baki Ɗalha ya yi kafin ya kai hannunsa na hagu ya dauki zanin, fita ya yi daga ɗakin zuwa kitchen,bayan shigarsa kitchen idonsa ya sauka kan kwandon shara da aka sa bakar ledar zuba shara a ciki jefar da zanin Ɗalha ya yi cikin kwandon kafin ya daura bakin ledar,daukar ledar ya yi ya fitar daga part ɗin gaba ɗaya babban robar zuba shara dake can kusa da gate ɗin gidan ya jefar da ledar ciki,daga haka ya koma part ɗinsu,bacci mai nauyin gaske ne ya dauki Unaisa da kyar Ɗalha ya samu ta tashi ta yi sallar asuba bayan ta idar da sallah ta koma ta kwanta
Karfe tara daidai Ɗalha ne zaune gefen Unaisa, kallonta ya rinƙa yi yana tunanin ina ta samu wannan mugun sanyin a hankali ya kai hannu ya fara bugun matashin da ta daura kanta a kai tare da kiran sunanta a hankali Unaisa ta buɗe idonunta dake cike da bacci inda ta sauke su fuskar Ɗalha,sanye yake cikin wata farar jallabiya murya can ƙasa ya ce ''ya jikin?" yunƙurawa Unaisa ta yi ta tashi zaune kafin ta ce ''da sauƙi sosai'' ta faɗa tana gyara zaman rigar bacci dake jikinta Ɗalha dake zaune bakin gado ya kai hannunsa fuskarta yana shafa ita dai sai kallonsa kawai take can ya ce ''ya kamata mu je asibiti a duba ki,ki tashi ki shirya nima zan je na shirya'' ya faɗa tare da miƙewa tsaye da to Unaisa ta amsa daga haka ya fita daga ɗakin zuwa nasa,bayan fitar Ɗalha a hankali Unaisa ta sauki kafafun ta ƙasa kafin ta sauka daga gadon nan cikin ɗaki ta cire nigth wear da Ɗalha ya bata kafin ta wuce bathroom da kanta ta tara ruwa cikin bathtub kamar yadda Ɗalha ya yi mata daren jiya fita ta yi daga bathroom zuwa kitchen inda ta dauko gishiri,hannuta riƙe da gishirin ta wuce bathroom ɗinta kamar yadda ta ga Ɗalha ya yi jiya haka ta yi bayan ta gama haɗa ruwa ta shiga cikin ta zauna yau dai ta daure ta wanke wajen sosai kamar yadda Ɗalha ya wanke mata daren jiya har yanzu wannan farin abu bai daina fita daga jikinta ba sau uku ta canza ruwan kafin daga bisani ta yi wanka,sosai taki dadin jikinta daren jiya bayan Ɗalha ya sa ta zauna cikin ruwan ɗumi wannan dalilin yasa ta haɗowa kanta ruwa,bayan fitowarta daga wanka wajen da aka zuba mata akwatunan kayan lefenta ta nufa ɗaya daga cikin akwatunan ta buɗe ta ciro wata doguwar riga egyptain kore daga haka ta dauki farar gyale da farin takalmi ba tare da ɓata lokaci ba ta shirya kanta cikin wannan doguwar rigar sosai rigar ta yi mata kyau abin ka farar mace,man shafawarta kawai ta shafa shima sama sama ba ta shafawa fuskarta komai ba ta yi rolling gyale,fita ta yi daga ɗakin hannuta riƙe da wayar,a nan parlour ta tarar da Ɗalha zaune yana cin masa da miyar ganye wanda Ammi ta aiko masu da shi,tuni ya gama shiri sanye yake cikin wata farar shadda da aka yiwa ɗinki zariya sosai ya yi kyau kana ganinsa kaga ango, amma wannan ƙiba da angwaye ke yi shi bai yi ba, waje Unaisa ta samu ta zauna kusa da shi ta sawa kanta masa kwara biyu rak kafin ta dauki kofi ta zuba ruwan sanyi yau ba a masu kunu ko zobo ba,bayan sun gama ci ne Unaisa ta kwashe kwanuka ta kai su kitchen,bata bar kitchen ɗin ba saida ta wanke kwanuka da suka yi amfani da su kafin ta fito,bayan fitarta ta tarar Ɗalha har fita hakan yasa ta bi bayansa kulle kofar part ɗin ta yi da makullen da ta gani jikin kofar,daga haka ta wuce compmund, compund ɗin gidan babu kowa sai tsirarun busassun ganye dake baje a ƙasa,bayan isarta wajen mota kofar gaba ta buɗe ta shiga ta zauna inda Ɗalha ya je buɗe gate,bayan ya buɗe gate ya dawo ya shiga mota ya fitar da motar kafin ya koma ya kulle gate
Asibitin ƙudi Ɗalha ya kai Unaisa a hanyarsu ta zuwa asibitin ne ya mayar da dubansa ga Unaisa ya ce ''ya kamata ki je ki gaida Ammi in mun dawo daga asibiti'' wani irin kallon raini Unaisa ta yiwa Ɗalha kafin ta ce ''kamar ya na je na gaida Ammi ciwo take?" shiru Ɗalha ya yi na wasu ƴan sakanni tare da ɓoye ɓacin ransa kafin ya ce ''lafiyarta ƙlau gani na yi tunda aka kawo ki baki shiga kun gaisa ba ƴan'uwanki sun yi kwana huɗu kafin sun tafi yau kwana huɗu da tafiyarsu ƙinga satin ki ɗaya da kwana ɗaya amma ba ki taɓa zuwa kin gaishi ta ba,sai nake gani ya kamata ki je in tana da wani aiki ki kama mata'' ya kare magana idonsa a kanta mayar da hankalin sa ya yi kan tuƙin da yake,taɓe baki Unaisa ta yi kafin ta yi magana cikin isa da rashin kunya ta ce ''na ga kai na aura ba Ammi ba saboda haka kai zan yiwa biyayya kuma kai zan ma hiɗima ba wata Ammi ba'' da wani irin sauri Ɗalha ya saukar da mota gefen kwalta ya yi parking bayan ya paka mota ne ya mayar da dubansa ga Unaisa da ta wani haɗa rai cikin ɓacin rai Ɗalha ya ce ''me ki ka ce?" gyara zama Unaisa ta yi tare da mayar da duban ta kan hanya tana kallon motoci da ke kaiwa da komuwa sosai ran Ɗalha ya ɓaci ya ce ''anya kuwa kin san abinda ki ke?kin san me ake nufi da aure?" Ɗalha ya karasa magana idonsa kannta babu alamar wasa tare da shi mayar da dubanta ta yi garesa kafin ta ce ''ni ce kuwa na san aure,aiy auren kenan na maka biyayya,kai kaɗai Allah ya ce ya kyautata maka ba wani ba'' ta kare magana tana murguɗa masa masa baki wannan kalmar kai kaɗai Allah ya ce na yiwa biyayya na kyautata maka yasa Ɗalha ya ji jikinsa ya ya yi sanyi ya ƙara tabbatar cewa Unaisa bata san abinda take ba,sannan bata san ma'anar maganar da ta yi ba kyautatawa mahaifiyarsa kamar shi ta kyautatawa biyayya kuma da take faɗi shi kaɗai zata yiwa biyayya yanzu da ya ce ya kamata ta je ta gaida mahaifiyarsa kamata ya yi ta ce masa to ba tare da wani ƙorafi ba wannan shi ne biyayya amma rashin sanin cewon kai da kuma ma'anar yiwa miji biyayya yasa ta bijirewa umurninsa, ya gama yanke hukunci da sun koma Kaduna zai sa ta a islamiyya
SHUUKRAN