MATAR GIDA PAGE 36
MATAR GIDA 036
SHUUKRAN /022
P36
Gaba ki ɗaya yaji ya gaji da rashin wayo da kuma rashin hankali haɗe da rashin kunya irin na Unaisa,bai sake cewa komai ba yaja motarsa,ita ko Unaisa tun ba yau ta tsani Ammi tun sanda suka samu labarin yadda Ammi ke son Amirah ta ji gaba ɗaya ta tsani Ammi saboda a tunanin ta Ammi baza ta so ta ba,tafiyar mintina talatin ne daga gidansu zuwa asibiti,bayan tafiyarsu asibiti reception Ɗalha ya je Unaisa na biye da shi wata nurse ya tarar zaune,sallama ya yi mata ta amsa kafin ya ce mata yana son ganin likitan mata,ƴan danne danne cikin computer ta yi kafin ta mayar da dubanta ga Ɗalha ta ce ''kuɗin ganin likita naira dubu ashirin'' Ɗalha ya fito da ATM card ɗinsa ya miƙo mata ƙarɓa ta yi ta cire kuɗin kafin nuna masu wasu kujeru da aka tanadarwa masu zuwa ganin likita ta ce su zauna za'a kira su, basu daɗe da zama ba nurse ɗin ta nuna masu wani office ta ce su je likita na jiran su,bayan shigarsu likitar mace ce ta nuna masu wajen zama ta ce ''bismillah'' bayan sun zaune ne ta tambaye su abinda ke tafe da su,Ɗalha ya cire kunya ya yiwa likita bayanin komai yadda kaikaiyi ya hana Unaisa bacci daren jiya da kuma abinda ya gani a jikinta,a karshen zancen sa ya daura da ''gaba ɗaya satinmu ɗaya da aure''ba tare da ɓata lokaci ba likita ta rubutawa Unaisa wasu gwaje gwaje kusan guda biyar cikin harda scan amma kafin nan saida ta duba Unaisa a ɗakin da aka tanadar dan duba marasa lafiya,daga haka Unaisa ta tafi lab dan bayar da sample ɗinta,bayan fitar sakamakon gwajin likita ta kira Ɗalha da Unaisa zuwa opishinta,bayan shigar su ciki likita ta mayar da dubanta ga Unaisa fuskarta dauke da murmushi ta ce ''amarya kin sha khamshi'' Unaisa ta ƙaƙalo murmushin da bai kai cikin ba ta mayar wa likitan numfasa likitan ta yi tare da gyara zama ta mayar da dubanta ga Ɗalha ta ce ''ango abinda yake damun amaryar ka infection ne wato sanyi,sai dai na yi mamaki da ka ce min amaryar sati ɗaya ce'' mayar da dubanta ta yi ga Unaisa ta ce ''amarya'' murya can ƙasa Unaisa ta amsa kamar wata mutumiyar arziƙi ta ce ''na'am sosai likitan ke ƙare mata kallo can ta ce ''an ba ki magunguna kafin bikin ki?" nan ma ta amsa cikin kwantar da murya ta ce ''eh'' likita ta ce wasu irin magunguna ne?" Unaisa ta ce ''cewa aka yi maganin sanyi ne da na gyaran auren'' numfasawa likita ta yi kafin ta ce ''ina nufin maganin gargajiya aka ba ki ko na asibiti? Unaisa ta ce ''gargajiya ne,wasu itatuwa ne haɗe da saiwa'' cike gamsuwar amsar da Unaisa ta bata likita ta ce ''good'' daga haka ta mayar da dubanta ga Ɗalha ta ce ''sakamakon gwajin da muka yi mata ya nuna cewa matarka tana da infection a jikinta tun kafin aurenku saboda babu yadda za a yi ta kamu da wannan mugun infection sati ɗaya da aure,magungunan da aka bata a gida da sunan maganin sanyi su suka ɗaga mata sanyi'' shiru likita ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta daura da ''ka san magungunan gargajiya ɗaga ciwo suke kafin su yiwa mutum magani shi yasa a ko da yaushe muna jan hankali mutane kan yawan shaye shaye magungunan gargajiya,abu na gaba kuma shine rashin tsafta'' mayar da dubanta ta yi Unaisa kafin ta ce ''ki dage da tsaftace wajen nan'' ta faɗa tana buga biro kan tebur ɗinta har sannan idonta kan Unaisa ta ce ''a gaskiya ba kay kula da tsaftar wurin alamu sun nuna'' mayar da dubanta ta yi ga Ɗalha kafin ta ce ''zan so muyi magana ni da ita'' ɗage kafaɗu Ɗalha ya yi ya ce ''ba matsala'' likita ta daura da ''sannan abinda yasa na rubuta mata scan shinne da yawa yawan mata suna kamuwa da ciwon sanyi har ya taɓa masu mahaifa ba tare da sanin su ba shi yasa na rubuta mata scan,alhamdulillah mahaifarta lafiyarta ƙlau'' mayar da dubanta tayi ga Unaisa ta ce ''har yanzu kina shan magungunan?" Unaisa ta bata amsa ta ce ''a'a'' rubuce rubuce likitar ta yi cikin wata farar takarda kafin ta miƙawa Ɗalha ta ce ''za a siya mata waɗan nan magungunan sannan ta kula da shan ruwa sosai insha Allah za ta samu sauƙi sosai'' magunguna masu mugun tsada ta rubutawa Unaisa saboda infection dake jikinta ba na wasa bane karɓar takardar Ɗalha ya yi kafin ya fita daga opishin bai tsaya ko ina ba sai pharmacy dake asibitin Allah ya taimaka duka magunguna ya same su nan cikin asibiti,bayan fitar Ɗalha likita ta yiwa Unaisa bayani sosai kan muhimmanci tsaftar mace ta cewa Unaisa ''duk sanda mijin ki ya neme ki dan Allah da kun gama ki je ki yi tsarki ki wanke wajen da kyau ko baza ki yi wanka lokacin ba,sannan banda amfani da ruwan sanyi ki daure ki riƙa amfanin da ruwan ɗumi,wata roba me kama da matancin mace likita ta dauka ta ajiye gaba Unaisa ta shiga nunawa Unaisa yadda ya zata riƙa wanke wajen
Bayan komawarsu gida Unaisa ce ta fara fita daga mota bata tsaya ko ina ba bangarensu hannunta riƙe da ledar magani,tun daren jiya da Ɗalha ya sa ta shiga ruwan ɗumi bata sake jin kaikayin ba sai yanzu amma ba kamar daren jiya ba yanzu da sauƙi,ba tare da ɓata lokaci ba ta kwaɓe kayan jikinta ta wuce bathroom ta haɗa ruwa cikin bathtub ba tare da ɓata lokaci ba ta shiga cikin bathtub ɗin hannu ta sa wajen ta wanke shi tass tun daren jiya da Ɗalha ya wanke mata wajen ta samu sauƙin zafi da yake mata hakan yasa yanzu ta sa hannu ta wanke ko wanne lungu da saƙo kamar yadda likita ta nuna mata ɗazu a asibiti,sau biyu ta canza ruwan kafin ta fita ta daura towel,bayan fitarta ta shirya kanta cikin wata ɓakar doguwar riga sabuwa wanda ta dauko daga kayan lefen ta,da kadan rigar ta wuce gwaiwarta,hula ƴar yayi da dauko ta rufe sumarta da shi arabain cap,daga haka ta fita daga ɗakin zuwa parlour ruwar gora ta dauko ta koma ɗaki,wayarta da ta jefar kan gado ɗazu ta dauka ta sa charji kafin ta dauko ledar maganin kamar yadda aka zana jikin kwalayin magungunan ta cire magungunan ta sha daga haka ta dauki wayarta ta kunna data,misalin ƙarfe biyar na yamma ta fito daga ɗaki yau ma kamar kullum bayan fitarta daga ɗaki ta ga basket ɗin abinci a parlour bata tsaya ɓata lokaci ba ta sama waje ta zauna ta zubawa kanta abincin farar taliya ce da miyar kifi sai lemon abarba,a natse ta ci abincin bayan ta gama ci ta sha lemo daga haka ta kai plate da kofin da ta yi amfani da su kitchen ta wanke,bayan fitarta daga kitchen ta nufi hanyar ɗakinta, maganar da Ɗalha ya yi mata ɗazu ya faɗo mata inda ya ce ya kamata ta je ta gaida Ammi taɓe baki ta yi kafin ta shiga ɗaki ta cire rigar jikinta,ta dauki wanda tasa ɗazu da zasu tafi asibiti ta sa, turare ta dauko daga lefenta ta fesa daga haka ta fita daga ɗakin zuwa kitchen inda ta dauki basket ɗin da aka sa masu abincin safe ta fita hannunta riƙe da basket ɗin bayan fitarta bangaren Ammi ta nufa ta shiga parlour bakinta dauke da sallama,Ammi dake tsaye kofar kitchen tana magana da ƴan aiki ta waigo ganin Unaisa yasa ta saki murmushi tare da amsa sallamar fuskarta dauke da murmushi,a natse Unaisa ta karasa shiga parlour tana murmushin da bai kai ciki ba,Ammi ta samu waje ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun parlour idonta kan Unaisa da ke zaune,a mutunce Unaisa ta gaishi Ammi,Ammi ta amsa mata fuskarta dauki da fara'a ɗaya daga cikin ƴan aiki Ammi ta kirata ta ce ta zo ta ɗauki basket da Unaisa ta shigo da shi ba a dau lokaci ba ƴar aikin ta shiga parlour ta dauki basket ta koma kitchen,Unaisa da Ammi zama suka yi shiru ita dai Ammi idonta kan TV Unaisa kuwa sai wasa take da gyalen dogon riga dake jikinta can Ammi ta miƙe tana mayar da dubanta ga Unaisa ta ce ''ni zan shiga ciki ina zuwa'' Unaisa ta ce ''to'' da ido ta bi bayan Ammi tare da taɓe baki bayan shigar Ammi Unaisa kamar jira take ta tashi ta fita daga ɓangaren zuwa nata
*SHUUKRAN