MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 37

by @maimunabala209

MATAR GIDA 037



SHUUKRAN/022




P37




Ammi ta fito daga ɗaki hannunta riƙe da wata roba cike da dambun nama sai wani ledar turaren wuta, jiya aka aiko mata daga Zamfara,a jiya ta fara amfanin da turaren ta ji dadinsa sosai hakan yasa ta ɗiban ma Unaisa,bayan fitarta daga ɗaki bata ga Unaisa ba a tunaninta tana kitchen tare da ƴan aikinta hakan yasa ta kwallawa ƴar aikinta kira ta tambaye ta ko Unaisa na tare da su,nan ta cewa Ammi bata kitchen ɗin mamaki ya cika,tana tunanin dalilin da zai sa Unaisa ta aikata haka,kawar da tunanin ta yi lokacin da ta tuna Unaisa jinin Fulani ce  wata zuciyar ta ce ''ƙila kunya ne irin na fulani'' bayan Ɗalha ya ajiye Unaisa a gida wani babban pharmacy ya wuce inda ya samu wani matashi ya yi masa bayanin rashin lafiya Unaisa bayan ya gama jero bayanai ne ya mayar da dubansa ga matashin ya ce ''na kai ta asibiti an haɗo mata magunguna so ina son ka bani magani da zai kare ni daga kamuwa da sanyin da ke jikinta'' shiru matashin ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya ce ''amma likitar da ta duba matarka bata baka magani ba'' Ɗalha ya ce ''ba ta ba ni ba'' daga haka bai sake cewa Ɗalha komai ba ya shiga haɗo masa magunguna bayan ya haɗawa Ɗalha magunguna ne ya mayar da dubansa ga Ɗalha kafin ya ce ''za ku ɗagawa juna ƙafa kasan in ana shan maganin sanyi ba a kusantar juna sai an gama sha'' cike  da gamsuwa Ɗalha ya ce ''eh haka ne na fahimta'' daga haka ya biya ƙudin magunguna,Unaisa ce kwance cikin ɗaki hannunta riƙe da waya tana chating tun fitarta daga ɓangaren Ammi take kwance har an kira sallar magrib tana nan kwance,Ɗalha na zaune cikin parlourn Ammi ya ƙorawa TV ido gaba ɗaya hankalin sa bayan kan TV kallon kawai yake amma gaba ɗaya hankalinsa baya kan TV,tun shigarsa parlourn ya tarar da Ammi tana waya hakan yasa ya zauna yana jiran ta gama,Ammi dake zaune kan kujera dake fuskantar wanda Ɗalha ke zaune a kai ta mayar da dubanta garesa bayan ta ajiye wayar hannunta ta ce ''har an idar?" sai a sannan Ɗalha ya cire idonsa daga TV ya mayar da su kan Ammi yana gyara zama ya yi magana cike da girmamawa ya ce ''barka da yamma Ammi'' Ammi ta ce ''yauwa barka'' ta faɗa tana mayar da idonta kan TV shiru ne ya biyo baya na wasu ƴan sakanni can Ammi ta mayar da dubanta ga Ɗalha ta ce ''ɗazu Unaisa ta shigo mun gaisa..ashe dai haka take da kunya gaba ɗaya ta ƙasa sakin jiki da ni''Ammi ta yi magana fuskarta dauke da murmushi ta ce ''baƙunta ta ce da an kwana biyu zata sake jiki..ka san Amirah ma haka ta yi ta jin kunyata farkon aurenku gashi yanzu ya zama tarihi,ita ma zata sake'' shi dai Ɗalha ya yi shiru bai ce komai ba bai yi tsammanin Unaisa zata shigo wajen Ammi ba murmushi ya ƙaƙalo ya ce ''haka ne'' Ammi ta daura da ''in ce kuna da komai na girki a can bangaren ku'' Ammi ta ƙare magana idonta kan Ɗalha amsa Ɗalha ya bata ya ce ''eh Ammi'' gyara zama Ammi ta yi kafin ta ce ''ina ganin gobe amarya zata fara girki'' shiru Ammi ta yi na wasu ƴan sakanni can ta ce ''aiy ta yi sati ko'' cike da girmamawa Ɗalha ya ce ''eh Ammi'' nan Ammi ta daura da ''da ka koma ka faɗa mata kaga gobe sai ta tashi da shiri'' Ɗalha ya jinjina kai ya ce ''haka ne Ammi,Allah ya saka da alkairi ya ja kwana ya ƙara lafiya'' Ammi ta amsa da ''ameen'' daga haka Ɗalha ya yi wa Ammi sallama ya miƙe hannusa riƙe da ledar magani Ammi ta bisa da ido har ya fita daga parlourn

















Unaisa ce zaune kan darduma hannuta riƙe da waya har sannan tana sanye da hijab ɗinda ta yi sallah da alama bata dade da idar da sallah ba,sallama dauke bakin Ɗalha ya shigo ɗakin,a hankali ta ɗago ta kafesa da idanunta kafin ta amsa sallama,Ɗalha ya samo waje ya zauna bakin gado tare da ɓalla buturan rigarsa,nan kan gado ya ajiye ledar magani tashi Unaisa ta yi daga darduma ta kwaɓe hijab ɗin jikinta ya rage daga ita sai kayan bacci riga da wando,riga ya ɗan mata yawa haka ma wando ko kaɗan bai matseta ba,ledar magani ya dauko ya ciro magunguna ya kalli Unaisa da ke shirin hawa gado ya ce ''dan bani ruwa na sha magani'' babu musu ta miƙe ta fita daga ɗakin zuwa parlour ta dauki ruwa gora ɗaya ta kawowa Ɗalha ƙarɓar ruwa ya yi tare da yi mata godiya bayan ya gama shan maganin ne ya cewa Unaisa dake kwance ''za ki fara girki gobe'' ya yi magana a takaice hannusa riƙe da wayarsa zumbur Unaisa ta miƙe daga kwanciyar da ta yi ta ce ''me girki? ni a'a wallahi ba zan iya ba,girki kwana takwas da aure na shiga kitchen gaskiya ba zan iya ba'' ta ƙare magana tana juya ido a hankli Ɗalha ya waigo ya mayar da dubansa gareta ya ce ''ba za ki iya ba ki ka ce?" Unaisa ta ce ''eh ba zan iya ba'' numfasawa Ɗalha ya yi kafin ya ce ''to ya ki ke so a yi? ba za a sake aiko mana da abincin ba daga ɓangaren Ammi ba,so ki ke mu zauna da yunwa?" matashi dake gefenta ta dauko ta daura a kafa tare da langwabar da kai ta ce ''ba za mu zauna da yunwa ba siya mana za ka riƙa yi'' gyara zama Ɗalha ya yi idonsa kanta ya ce ''so ki ke na riƙa yawon siyan abinci baya muna da komai a gidan nan?" taɓe baki Unaisa ta yi tare da gyara zama kafin ta ce ''kamar yadda na faɗa maka ba zan yi girki sati ɗaya da aure ba'' ta kare magana tare da kwanciya shiru Ɗalha ya yi gaba ɗaya ya gaji da halaiyyar Unaisa ya dauki a ƙalla mintina huɗu zauna yana tunani can ya sauke ajiyar zuciya yana mayar da dubansa gareta ya ce ''Ammi ta ce kin shiga kun gaisa'' banza Unaisa ta masa kamar bata ji abinda ya faɗa ba can dai Ɗalha ya fita daga ɗakin hannusa riƙe da ledar maganinsa,bayan shigarsa ɗaki rage kayan jikinsa ya yi ya wuce bathroom ya yi wanka,bayan fitarsa daga bathroom ya shirya kansa cikin wata jallabiya mai laushin gaske ruwan ɗorawa bai tsaya ɓata lokaci ba ya yi kwanciyarsa kan gado,wayarsa ya dauko ya kira layin Amirah gaba ɗaya yau basu yi waya ba har jin kansa yake wani iri, Allah Allah yake ya gama abinda yake ya kirata ya ji muryar ta sosai yake samun nitsuwa in ya ji muryar Amirah ba kamar Unaisa ba da bai taɓa zama tare da ita minti biyar bata masa rashin kunya ba bugu biyu Amirah ta amsa wayar cike girmamawa ta gaishi shi ya amsa mata murya sake ya tambayeta lafiyar yara Amirah ta ce duk suna lafiya,Ɗalha ya je gaba ɗaya bazai iya cigaba da ɓoyewa Amirah  kewarta da ya yi ba sosai yake bukatarta kusa da shi gyara kwanciya ya yi kafin ya yi magana cikin sanyin murya ya ce ''Amirah'' a natse ta amsa masa ta ce ''na'am'' numfasawa Ɗalha ya yi kafin ya ce ''bana jin zan iya cigaba da rayuwa ba kya kusa da ni'' shiru ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya ce ''zan zo Kaduna gobe'' maganar ya zowa Amirah a ba zata da tsantsan mamaki,a kullum tana ƙara mamakin Ɗalha,saita nitsuwarta ta yi kafin ta masa magana cikin kwantar da murya ta ce ''baban Sudais..yara sun fara jarabawa yau'' shiru ta yi kamar yadda shima ya yi shiru yana sauraron ta can ta ce ''da sun gama zamu taho Kano kamar yadda muka saba a can muke hutu wajen Ammi..sai nake ganin ka yi zaman ka kawai na ƙara maka sati ɗaya ko ka manta ne?" numfasawa Ɗalha ya yi kafin ya ce ''ban manta ba ina sane Amirah'' shiru ya yi maganar da yake son yi ya maƙale a makoshinsa ya ƙi fita da kyar ya iya furta ''na yi kewar ki ne l miss everything about You khamsin ki girkinki kamshin ɗakin ki''ya yi magana a rarrabe kamar yaro me koyun magana gaba ɗaya ya gama kunce mata lissafi har ta fara tunanin ko wani abun marar kyau ne ya same shi tana cikin wannan tunanin ya ce ''akwai wata ni'ima da salama da nake tsintar kaina ciki duk sanda na ke tare da ke'' muryarsa na rawa ya ce ''a nan babu wannan sai hayaniya da damuwa l'm tired Amirah na gaji'' sai a sannan Amirah ta fahimce inda ya dosa  kenan faɗa ya yi da amaryarsa yasa yake son dawo gareta a hankali ta shiga furta ''no..no..no way'' shiru ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta saita nitsuwarta ta ce ''amm baban Sudais ina ganin ka yi zaman ka a can har zuwa lokacin da hutun ka zai ƙare ni da yara muna lafiya'' murmushi mai sauti Ɗalha ya yi kafin ya ce ''oky is fine zan zauna'' Amirah ta yi shiru ta ƙasa furta komai can Ɗalha ya ce ''good nigth'' daga haka ya kashe waya ya rufe ido yana mayar da numfashi sosai ya yi kewar Amirah ya gaji da azabar Unaisa ƙazanta rashin kunya rashin addini murya can ƙasa ya ce ''ya ilahi''  can wajen Amirah kowa kusan raba ɗare ta yi tana tunani maganganun da Ɗalha ya yi mata bata sani ba ko da gaske yake ko dan amaryarsa ta ɓata masa rai ne 












SHUUKRAN