MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 38

by @maimunabala209

MATAR GIDA 038




SHUUKRAN/022




P38





Washegari tun bayan sallar asubah Amirah ta ƙasa taɓuka komai bayan ta idar da azkar ɗin safe tunanin Ɗalha ya hanata sukuni maganganun da ya faɗa mata daren jiya ya riƙa mata yawo a zuciya gani take kamar bata kyauta masa ba da ta hanasa dawowa yau kamar yadda ya faɗa,what if saboda ya samu saɓanin da amaryarsa yake son dawowa gareta,nan take Amirah ta ji gaba ɗaya kanta ya kulle,daga gefe ɗaya kuma kusan kullum sai yara sun yi tambayar babansu sai ta ce masu ya yi tafiya da anty su,Allah ya taimaka ta zaunar da yara duka ta yi masu bayanin babansa ya ƙaro aure harda basu da wayun fahimtar ƙarin aure sai ce masu ta yi babansu ya samu masu Anty zata riƙa zama tare da su a gidan,itama Mumyn su ce,haka jiki babu kwari Amirah ta daure ta shiga yiwa yaran shirin zuwa makaranta,karfe bakwai da mintina arba'in na safe Amirah ce tsaye cikin parlour tana sawa Fauziyya socks daga gefenta kuma Aina'u ce tana zugewa Suhail zif ɗin jakar makarantarsa bayan ta mayar masa da littatfansa cikin jakar,Amirah ta haɗa kan yara zuwa makaranta yayin da ita kuma Aina'u ta shiga gyaran gida bayan dawowar Amirah daga kai yara makaranta bathroom ta faɗa ta yi wanka kafin ta fito ta yi breakfast,bayan ta gama ne ta shiga kitchen ta daura abinci,karfe ɗaya da mintina arba'in Amirah na zaune cikin ɗakin bayan ta idar da sallah Aina'u ta shigo ɗakin bakinta dauke da sallama waje ta samu ta zauna tana kallon Amirah da ta ɗaga hannu tana addu'a bayan Amirah ta shafe addu'a ne ta mayar da dubanta ga Aina'u ganin haka yasa Aina'u gyara zama tare da faɗin ''kin yi baƙo yana parlour'' fuskar Amirah dauke da mamaki ta ce ''baƙo kuma'' Aina'u ta ce ''eh wai Kabir daga Kano'' nan take Amirah ta sake murmushi cike da murna ta ce ''ikon Allah Kabir zuwa babu sanarwa ki faɗa masa ina zuwa'' ta kare magana tana tashi daga kan darduma,bayan fitar Aina'u Amirah bata tsaya ɓata lokaci ba ta cire hijab ɗin da ta yi sallah,ta nufi saif ta buɗe tare da ɗaukar mayafi ta rufe jikinta,fuskarta dauke da murmushi ta shiga parlour,gidan ya yi shiru baka jin motsin komai sai kwanuka da Aina'u ke goge a kitchen bayan ta gama wanke wanke bakin ta dauke da sallama ta shigo parlour Kabir dake zaune hannusa riƙe da waya ya ɗago ya kalleta yana amsar sallamar da fara'a zama Amirah ta yi a kujerar dake fuskantarsa har sannan fuskarta a sake ta ce ''zuwa babu sanarwa'' Kabir ya yi murmushi bai ce komai ba yana kurɓar lemo da Aina'u ta kawo masa bayan ya ajiye kofin ne ya gyara zama kafin ya gaishe Amirah cike da girmamawa,amsa gaisuwar Amirah ta yi tana tambayar sa gida ya ce mata kowa lafiya,bayan sun gama gaisawa ne Kabir ya ce ''daga gidan su Yasmin nake ta ce a gaishi ke'' sai a sannan Amirah ta fahimci dalilin zuwan Kabir Kaduna gyara zama ta yi ta ce ''yanzu na ji zance ka ce dai wajen Yasmin ka zo'' Kabir ya yi murmushi bai ce komai ba Amirah ta daura da ''ok shi yasa Rumaisa ta kira ni ɗazu na shiga alwala na fita naga miss call ɗinta ai kuwa zan kirata'' daga haka sun cigaba da hirar su,suna nan zaune Aina'u ta sawa Kabir abinci ta kawo masa a cikin hirar nasu ne Amirah ta cewa Kabir tana son fara sana'a sai dai bata san wata sana'a zata iya yi daga gida ba,numfasawa Kabir ya yi kafin ya ce ''me sai sa baza ki yi irin wanda na ke ba kina zaune gida sai dai a riƙa tura maki riba'' cike da gamsuwa Amirah ta ce ''ok kana nufin harkar hatsi?" Kabir ya ce ''eh ana samun riba sosai musamman in kina da babban jari'' Amirah ta jinjina kai kafin ta ce ''ok na fahimta,yanzu kamar nawa ya kamata na bada'' Kabir ya ce ''ko nawa ma za ki iya sai dai zai fi kyau ki fara da kamar miliyan biyu haka zuwa sama''shiru Amirah ta yi shiru na wasu ƴan sakanni tana tunani gaba ɗaya abinda ta mallaka naira miliyan biyar da rabi ne asali tana da miliyan uku da wani abu nata na kanta sai kuma miliyan biyu da rabi da Ɗalha ya bata sanda zai auro Unaisa matsayin kuɗin fadar kishiya 

















Gyarar murya Amirah ta yi kafin ta ce ''in na bada miliyan biyu da rabi zai yi?" Kabir ya yi murmushi kafin ya ce ''zai yi mana Anty wasu da dubu ɗari biyar suke fara'' Amirah ta jinjina kai kafin ta ce ''ok Allah ya taimake mu'' Kabir ya ce ''ameen'' Amirah ta daura da ''yaushe zan baɗa kuɗin?" Kabir ya ce '' zan faɗa maki in lokaci ya yi saboda yanzu kuɗo nake aika hatsi in na saro,and na riga na aika na wannan satin sai sati mai zuwa..za mu yi waya kafin nan'' Amirah ta ce ''to Allah ya kaimu'' daga haka sun cigaba da hirar su Kabir bai bar gidan Amirah ba sai karfe huɗu bayan ya yi sallar la'asar,tsaraba me yawa ya yiwa su Sudais kayan ciye ciye ne da sauran tarkace,karfe biyar da rabi Amirah ta je makarantar su Sudais ta kwashe su yau ma kamar kullum bayan dawowarsu gida wanka ta yi masu kafin suka ci abinci kamar dai yadda suka saba sun yi ta sa ta magana wanka kawai da cin abinci sai da an kusa kiran sallar magrib kafin ta gama masu bayan idar da sallar magrib malamin su yazo ya yi masu karatu,kamar yadda Unaisa ta faɗa cewar ita baza ta yi girki ba hakan kuwa ya faru,bayan wayewar gari karfe tara daidai Ɗalha ya shigo ɗakinta ganinta ya yi kwance hannuta riƙe da waya kamar dai yadda ta saba waje ya samu ya zauna ba tare da kallon inda take kwance ba ya ce ''me ki dafa?" fuskarta kan waya ta ce ''babu'' daga haka Ɗalha bai sake cewa komai ba ya tashi ya fita daga ɗakin zuwa nasa bayan shigarsa ɗaki wanka ya yi kafin ya fita juction ya siya masu abin kari soyayyen dankalin turawa haɗe da soyayyen kwai ya siya masu take away biyu,daga haka ya wuce wani shagon provision inda ya siya masu lemo kwalba daga nan ya wuce gida,bayan dawowarsa gida zama ya yi nan parlour ya ci abincin sa bayan ya gama ci ya fita daga gidan gaba ɗaya bai kara bi ta kan Unaisa ba,ita ko Unaisa misalin ƙarfe goma da rabi ta fito daga ɗaki dalilin yunwa da ya hanata sukuni hakan yasa ta fita daga ɗaki ba shiri,ganin take away a parlour yasa ta zauna ta fara ci abinda ke ciki bayan ta gama ci ta dauki take away ɗin ta kai shi dusbin, da dare misalin tara da rabi Ɗalha ne kwance kan gado hannusa riƙe da waya yana kiran layin Amirah har kiran ya katse ba'a ɗaga ba,Amirah na kwance tana kallon kiran Ɗalha har kiran ya katse bata ɗaga ba sake kiran layin ya yi a karo na biyu nan ma ba'a ɗaga ba,a hankali Ɗalha ya sauki ajiyar zuciya tare da ajiye waya daga haka ya gyara kwanciya yana karanto addu'a bacci a can wajen Amirah kuwa kafe wayar ta yi da ido cikin zuciyarta tana addu'a Allah yasa ya sake kira,ta dauki a ƙalla mintina takwas a haka ganin bazai kira ba yasa ta ajiye wayar a hankali ta kifa fuskar wayar a hankali ta rufe idonta da niyyar bacci,ta dauki a ƙalla mintina biyar tana ta juye a gado can dai ta tashi zaune a hankali ta kai hannu ta dauki wayarta ta shiga wajen tura sakonni lambar Ɗalha ta danna ta yi rubutu da bai wuce layi biyu ba ta tura masa,daga haka ta yi kwanciyarta,washegari Laraba bayan Amirah ta kai yara makaranta misalin karfe goma ta je salon gyaran gashi bata dauki lokaci ba da dawo bayan an gama mata gyaran gashin kasancewar Amirah ba ma'abociya son lalle ba ce yasa ta yi gyaran gashi ta dawo gida,bayan dawowarta gida ta shiga haɗa kayan yara da nata gobe alhamis yaran za su gama jarabawa juma'a da safe za su wuce Kano wannan dalilin yasa Amirah ta fara haɗa masu kaya tun yau gudun kar su manta wani abu,bayan yaran sun dawo daga makaranta da kanta ta wankewa su Ummu Abiha suma kasancewar duk kayan gyaran gashi tana da su a gida,washe gari Alhamis Aina'u ta yiwa Amirah kitso me mugun kyau ƙananu sosai a ranar kuma ta yiwa su Ummu Abiha bayan sun dawo makaranta yaran mazan kuma Amirah ta kai su aski,tun ranar Laraba Amirah ta faɗawa mallam Abdullahi da ke zuwa yiwa yara karatu cewar za suyi tafiya wannan dalilin yasa bai sake zuwa ba sai sun dawo daga Kano zai cigaba da zuwa,Aina'u ba ita ta gama yiwa yaran kitso ba sai sha biyu na dare,inda Amirah na sa masu lalle bayan ta jera masu stickers,kamar wasa sune har ɗayan daren suna parlour,karshe dai a nan parlour suka kwana har Aina'u,bayan Amirah ta daura masu net,ta kashe gaba ɗaya wutan parlourn haka ma fanka iya AC kaɗai ta bari a kunne,hasken wutan daining area dake shiga parlour yasa parlourn bai yi duhu sosai ba,karfe biyu na dare Amirah na kwance Fauziyya na gefenta inda ta yi lamo jikin Amirah,Amirah ta dauki wayarta kamar yadda ta yi tsammani saƙonni kusan huɗu Ɗalha ya aiko mata ba komai yake rubuta mata sai hot romance messages duk wanda ta karanta sai ta ji gaba ɗaya ta shiga wani irin yanayi tun ranar da ya ce mata zai dawo Kano ta ce a'a bata sake ɗaga kiransa ba,in tana bukatar wani abu sai ta tura masa saƙo hakan yasa shima ya daina kiranta gaba ɗaya sai dai ya tura mata saƙon da zata uni tsigan jikinta na tashi,ita kuma bata iya hakuri da ya tura sai ta buɗe ta karanta yanzu haka ma saƙonni take karantawa,bayan ta karanta na karshe da wani irin sauri ta kifa wayar kamar ba ita kaɗai take karanta sakon ba







SHUUKRAN