SHI SO DABAN YAKE

Babi na sha biyu

by @dijensy

12



 Jidda ce kwance ta cusa fuskarta a cikin pillow tayi luf tunda suka komo daga banɗakin ta ƙi sake yarda su haɗa ido hoton abubuwan da suka faru take ta tunawa tana ji tana kallo ta kasa wanke jikinta bayan tayi using toilet sai Hassan ɗin ne yayi mata wannan buguwar hannu bata kyauta mata ba take ta tunani a ranta ga bacci yaƙi zuwa mata kamar yadda bata yi bacci ba haka shima ya zauna sai wajen sha biyu bacci ya ɗauketa wuraren ƙarfe uku ta sake tashi tana ankare da hannun nata ta kallo inda take tsammanin Hassan ɗin na nan ta ga sallah yake yi ta ɗauka subh tayi ta ɗauki wayarta daga gefe ta ga ƙarfe ukun dare nafila  yake rufe ido tayi tana ɗan jin zugi hannunta amma ba kamar ɗaxu ba ta koma baccinta.Washegari da sassafe ta kira Anty baby ta faɗa mata ta yi buguwan ƙashi gida zata dawo Umma ta karɓi wayar tace bazata dawo ba haushi ya isheta da wajen ƙarfe shaɗaya suka xo duba ta Anty da Umma da su Abdallah har da yarinyar maƙotansu da suke mutunci aka kawo mata ita ta tayata aiki inbanda tasan zata moreta ba abinda zai sa ta yarda don haushin yaran makotansu take a cewarta kwadayayyu ne yarinyar bata fi sha uku ba ita kuwa sai murna take,sabida yanayin aikinsa hassan ya sa bai iya zama gida ba sai dai da sassafe yana mata aikin da ya saba kafin ya fita ya barta da yarinyar idan ya dawo haka zai cigaba da kula da ita duk motsin da zatayi sai ta ce wash shikuma kamar a ruhin jikinsa.Yau da ta tashi tace masa ita farfesu take so ta gaji da cin duk abubuwan da yake siyo mata ,Neema yarinyar da aka kawo ta zauna mata ta kalla bayan fitar Hassan ɗin “Ke kuma ki tashi ki feren dankali”.Ta buƙata da hannu daya take danna wayarta Neema tace toh tana tashi ta fita kitchen dankali ta soya mata ta kawo mata parlour “Dakkon kofin tangara da flask na shayi”.Neema ta tashi ta je ta taho da flask kawai ya subuce ya faɗi kwalba ta fashe “Da kyau”.Jidda ta furta jin ƙarar fashewar abu  ta kirata a tsawace ta shigo ɗakin “Flask ɗin kika fashe min sabida tsabar rawar jiki saurin me kike?rawar takashi na ƙwaɗayi dankalin ne baki taɓa ci ba ko me?zo kiyi kneel down”.Jidda ta buƙata haka Neema ta durƙusa tana ɗaga hannu sama “Gobe zaki haɗa kayanki daman ba wata uwa kike tsinanamin ba rainonki kawai nake”.A yadda take Hassan ya shigo ya kalleta ya kalli Jidda yana tambayarta me ya faru ta turo baki tana faɗa masa me tayi ya yi murmushi “Ayi haƙuri bazata sake ba indai flask ne zan siya maki wani”Hassan ya faɗa yana sa Neema ta tashi Jidda ta harari hannunsa ta ga ƙullin ledar sai da ya sake ɗora mata ruwan shayin ta cika plate kamar bazata iya ci ba haka ta tashesa a ɗan bowl ta sammata ba ruwanta da tambayarsa ko zai ci ta ajjewa kanta ragowar fafesun. Anyu kwana takwas kafin Jidda ta cigaba da sabgoginta kamar da ,Neema kuwa ta tafi tuni Jidda ta saita mata hanya.Yau bayan fitar Hassan aiki koda ta karya ta jiyo mai sayar da yoghourt awaje Jidda ta ɗakko kuɗi ƙanƙara take son sha tana sauri ta fita da ɗankwalin atamfarta ta yafa a ka kofar ta datse lock ya shiga gashi bata fito da makulli ba ta juya tana ƙoƙarin buɗewa ko wayarta na ciki ta ja tsaki yafi biyar ta zauna kofar gidan tana tunanin ya zatayi can ta tashi ta leƙa bayan layi ta hangi wani matashin saurayi ta tsayar dashi “Dan Allah kofar gida ne ce ta rufe ba wani a ciki kuma ko zaka taimaka min da wata dabarar?”Ya dubeta sama da ƙasa yace mata to Jidda ta taho yana biye a bayanta suka tsaya ƙofar gidan ya kalleta ya dubi ƙofar “Sai na samo ɗan wani ƙarfe ko zaki shiga makota ki zauna zanje titi na dawo sai na miki magana kizo a bude kofar ko tunda ba kya ta tsaiwa a waje ba kina matar aure ga ko mayafi babu”Ya faɗa Jidda ta giɗa kai ta kalli gidajen kusa da ita da ko shiga bata taɓa yi ba na gefen ta ta kwankwasa matar ta buɗe matashin ya zagaya Jidda na shiga gidan ya dawo ya kalli gefe da gefe ba kowa ya haura gidan yana sauri ya shiga parlour wayar Jidda ya fara gani ya ɗauke  ya shiga dakinsu ya bude sif Atm da wasu agogon hannu na Hassan ya zuba aljihu ya kalli fankarsu sabuwa ya kunce yana shiga kitchen kaf kayan da yasan zai iya squeezing ya zuba a buhu da ke drawer kitchen sai da ya dauka ya haɗa da cyɗinder gas nasu ya haura ta baya kango ne ya jefa su yana haurawa ya dira ya saiti hanya Jidda tana ta jira sun gaisa da matar gidan yarinysrta daya a goye Jidda ta fara gajiya da jira har sha biyu shiru daga baya dai ta tashi matar na kallonta tace “Ai irin wannan ko number mai gidan kya haddace da ko kiransa sai kiyi da wayata”.


“Wlh fa zan duba naga”.Jidda ta leka waje ba kowa ƙarshe sai mai gidanta ta kira makociyar yace suna da group ai na magidantan unguwar a haka ya samu number Hassan ya kirasa yana gurin aiki ya taso ,koda ya ƙaraso Jidda ta fito daga gida ya kalleta ta haɗe rai “Nasha zama walhi”.Ta faɗa tana bashi labarin saurayin da ya mata alkawarin dawowa Hassan ya buɗe ƙofar ya kalleta “Shi yace maki ki shiga gidan?”Ya tambaya ta jinjina kai suna shiga gidan parlour ta nufa kai tsaye inda ta ajje wayarta ta kalla wayam ta shiga ɗaki ko anan ta ajje ba waya ba alama fanka ma haka Jidda ta ɗora hannu aka tana kuka Hassan ya shigo yana kallonta “Wayata!”Hassan ya lumshe ido yana buɗewa ya kalli fanka babu ya ga sif ɗin ma a buɗe take kafin ya fara jin alert ana tsirare masa yan canjuka a account dubu sha takwas da ke account ɗinsa ya karar Jidda kuwa ta wayarta take ya rasa ma mai zai ce ga rana da ake kuma yau azumi yake  hannunta ya kamo ya zaunar ba tare da faɗa ko hayaniya ba ya shiga bata haƙuri  yace zai bata tashi kafin ya sake mata ,gas cylinder kuwa a yanzun ya fita ya sayo sabo ya ɗuro mata ya kawo kafin ya koma wajen aiki don hour daya aka bashi wajen aiki wunin ranar Jidda a sanyaye ta tsinewa barawo albarka yafi a kirga.A washegari Hassan ya kaita tayi swapping layin ya cire layinsa daga samsung nasa ya saka layin Jidda ya bata ta sa hannu ta karɓe keypad techno ya saya ya saka layinsa suka komo gida ta ga an kawo bulo an ajje kofar gida ya kalleta yace mata za a ƙara katangar gidan nebsabida gujema faruwar irin hakan.Jidda a hankali ta dawo da komai nata wayar Hassan tana kallon apps nashi duk islamic apps ta taɓe baki ta shiga duba message ba wani message sai na MTN nan ma baki ta tabe gallery sa ma banda takardu da hotunan dalibansu sai video na sauka da sukai wancen lokacin sai su Usman da wata sallah ya musu hotuna duka hotunansa uku ta gani kawai a ciki ta shiga wano folder daban rututu ta ga hotunanta da mamaki take ta budewa yawanci duk bata sani ba sai wasu tana bacci harda videos Jidda kawai ta jinjina kai don ya bata mamaki ta shiga tunanin kalla yake zama ya tayi kenan?ta tabe baki sai da taji kamar ta goge don shi ba ruwansa da tayi kyau ko bata yi kyau ba kawai dauka yake ita kuwa idan zata ajje hoto sai ya fita sosai haka dai ta rufe ta barshi ta karasa sauke abubuwan da take so.


       *******


   Yau tayi waya da Anty baby take faɗa mata an saka ranar bikin ya Ibrahim wata hudu biki Jidda ta shiga tambayar ko wace budurwar.


 “Ina ruwanki da ita dole sai kin santa in tazo kya ganta”.cewar Anty baby.


“Yaushe zai dawo to ya gama karatun masters ɗin ne?”Ta tambaya Anty baby tace “Saura kaɗan baki da labari ya samu aiki ai acan biki zai zo kawai ya koma daga baya matar ta bisa”.Cewar Anty baby Jidda ta saki baki “Abubuwa ake gidan bakwa sani lissafi ciki ? Shikenan”.Jidda ta faɗa cikeda jin haushi “Ai har yanzu baki gama hankali sosai ba idan kinyi za a saka ki ciki”.Baki ta turo sabida tsabar haushi da wuri ta mata sallama ta lalubo number ya ibrahim da suka daɗe ma basi magana ba  ta tura masa da voice note tana masa korafin ya dena kulata aka ci sa a yana kusa ya mata reply.


 “Biki ai naku ne Jidda sai yadda kukai na wakiltaki komai ki rabu da anty baby zan turawa amarya number ki kece wakiliyar ango”Ya faɗa wani daɗi taji ta sake tura masa da reply ya kirata sun jima suna waya ta faɗa masa zata fitar da ankon bikinsa haka sukai sallama ta tashi tana dauko earpiece na hassan ta saka tana shiga group na novel ta kunna audio tana ji sama da hour ɗaya bacci ya ɗauketa Hassan da ya shigo ya sameta kwance da earpiece ya duqa kusa da ita yana cire mata kafin ya zare daga cikin wayar ya kara kunnenaa yana ji ya daukesa yan mintina kafin ya gane ba radio bane littafi ne murmushi yayi ya tsayar da audio yana sa mata wayar a charge ya ajje earpiece ɗin yana gyara mata kwanciya ya mata addua kafin ya tashi ya cire kayansa yana shiga banɗaki ya yi wanka ya sa kayan bacci ɗazu ya ci abinci kafin ya fita makarantar dare ba wani yunwa yake ji ba sabida haka kwanciyarsa yayi.



     Washegari da safe yana off ya roƙeta da ta shirya zasu je duba Anty Ruƙayya bata da lafiya harda ƙarin  ruwa aka mata ,bayan sun je shi ya wuce tahfiz sai bayan an tashi ya zo suka tafi gida a hanya ya tsaya suka sayi kayan cefane girki kafin su dawo gida shinkafa kawai ta ɗora amma shi ya ƙarashe girkin,gama cin abincin rana ta ɗakko kibiya tana zaunawa parlour ta saka earpiece a lallai tana saurarar book tana tsifa da ta sunkuya sai ya zare yana kallo tana ta tsaki ya rufe islamic littafin da yake karantawa ta ga ya taso yana zaunawa kujerar kusa da inda take zaune a carpet “Kin gaji?”Ya tambaya yana kallon gashin nata ko kwara uku bata tsefe ba shiru tayi don daman ta gaji ta tsani tsifa kuma yawanci Anty baby ke tayata ko Umma Hassan ya karɓi kibiyar ta gyara zamanta ya fara yi mata hankali kwance take jin novel ɗinta ta shagala sai murmushi take yana kallonta yana mata tsifar har ya gama Jidda ko sani bata yi ba ashe har taje mata yayi taji ya taɓa mata kafaɗa “Ina abinda zaki packing ko aske shi za ai?”Ya tambaya cikeda zolaya Ta juyo ta sa hannu ta shafa kan ta ɗaga cinyarta tana zaro ribbon ɗin ta miƙa masa ya ɗaure mata harda tufke mata gashinta akwai yawa tsaho ne ba sosai ba dai dai gwargwado yake ya kalleta ta tashi tana tattare comb ɗin da kibiyar ta tafiyarta ɗaki bata ce komai ba ya kasa dena murmushi.Da yamma hadari ne ya haɗu ruwa ya sauko maghriba ma a gida yayi ta Jidda tunda ta ci abincin dare ta shiga ɗaki tana ta latsa wayarta sai wajen goma da rabi ta shiga banɗaki ta yi wanka ta fito tana buɗe sif wata sara da ta tsara da ta yi wanka ta balbala turare da bata yi amma tunda ta gwada daga cikin turarikan da aka kawo mata wani ɗaɗi yake mata a hanci har a darduma take shafawa da hijab din sallah ,ta gama bulbula shi ta zira rigar baccinta doguwa tana faɗawa kan gadon ta zira earpiece a kunne tana jin book ɗinta ta juya baya har ya shigo ya gama nashi shirin kwanciyar bata sani ba ya kasa dena jin yadda turarenta yake cika masa hanci ga wani irin yanayi da yake jinsa ya rufe rabin window ɗakin feshin ruwa yana shigowa kaɗanya komo ya kwanta yana ƙurama cieling ido  ya mirgina gefe yana kallon Jidda ta juya baya komai nata ɗaukan hankalinsa yake tamkar mai jin ƙishir ruwa ya ganshi ya gangaro daf da ita earpiece ɗin ta ji an zare mata ta saurin juyowa tana sauke idonta a kan fuskarsa “Mai ake cewa a ciki?”Taji ya tambaya ta turo baki tana kai hannu zata karɓe ya riƙe mata hannun a hankula ya haɗe tafin hannunsu “Ki bani labari inji nima”.Jidda tayi ƙasa da ido “Maza basa ji”Ta faɗa ya murmusa Hassan yana sake kwanto da kanshi suna jin numfashin juna ya kasa ɗauke ido daga gareta “Sirri ne na mata a ciki ?meyasa baza a raba da mazan ba uuhmm ..Amirahtaaa”.Taji ya ja sunan ya faɗesa da wata siga wani yarrr ta ji a jikinta ta kuma kasa motsawa sai jin hannun hassan tayi yana shafa hannunta ya gangaro wuyanta numfashinta yana ƙara gudu kafin ƙanƙanin lokaci ta   ga ya mata rumfa haɗi da fara romancing ɗinta baƙon yanayi na shiga jikinta tana sa hannunta a hankali ta ɗora a ƙirjinsa ai kamar xugashi tayi ya ƙara ƙaimi rigar baccin nata ta ji ya zame mata ita yana raba ta da ita wani tsoro ya shigeta taji ya haɗe bakinsu wani zazzafan kiss yake mata bugawar zuciyarta na ƙaruwa ta ji bakinsa inda bata taɓa tsammani ba tana dai karantawa a novel amma a aikace yau ne karo na farki jikinta ya soma mazari maganganun Anty baby take tunawa tana so ta tureshi amma zuciyarta na gargaɗarta sannan kuma wasu daga cikin system na jikinta suna maraba da sakonnin  gangar jikin gabaɗaya ta damka masa ta mallaka masa kafin ta ji wani sabon salon da ya ɓullo dashi ta matse kafafunta ta ji hannayensa kan cinyarta yana ƙoƙarin buɗawa zuciyarta tana tabbatar mata da wannan abun zai mata da labarinsa take ji cikin kunnenta take jin yana karanto adduar saduwa ta shiga kame jikinta tana ƙoƙarin hanawa wani tsoro da firgici ya shigeta lokaci guda taji bazata iya ba sabida ƙarfin riƙon sa “Hassan pls….Ta ja s ɗin a kunnenta ta ji muryarsa kamar ba tashi ba “Jidd …pls ..i wont hurt….y..ou..let ..me in…


“Umm…..”Ta kurma uban ihu ya toshe mata baki wani irin kakkarwa jikknsa ya dauka kamar zai mutu haka yake ji idan bai samu hanya ba ,jidda nema take wannan Hassan ɗin da ta sani ya dawo jikinsa don bata yarda shine a wannan lokacin ba wani azaba take ji ta fitar hankali da bata taba ji ba na ratsata har ta gwammacewa buguwar da tayi a hannu da wannan azabar da Hassan yake gana mata ta kira Umma yafi sau ashirin harda Anty baby sai da ta kira hakan bai sa ya fasa shiga ba yana faɗawa wata duniyar da bai taɓa sanin akwai irinta ba tsahon mintina kafin ya dawo cikin hayyacinsa ya kankameta kamar ya sata cikinsa ya shiga shashafata yana shi mata albarka yana gode mata ko saurarsa da kyau ba tayi gani take kamar idan ta motsa zai sake mata wani abun ya sa ta yi luff tsahon minti ashirin ta ji ya kira sunanta da muryarsa da ta sani a tausashe “Jidda”.Da sauri ta yi yunkuri tashii daga kan katifar taji azaba a ƙasanta ta fasa ƙara “Wayyo Ummana!”Hassan wata damuwa ta dabaibayesa  ya tabbata yayi losing control bashi da niyyar ya wahalata haka ya shirya ya mata komai cikin sauki bai san me ya fisgesa ba  ta rukunkume pillow tana rufe kirjinta yana dafa kafadarta ta sigar lallashi “My Jidda kiyi hakuri na miki laifi ,ko ma kneel down ne ki sani amma yanzu ki bari na baki kulawa kin ji”.Hawayenta ta shiga gogewa ya gama goge mata hadda batasan haka abin yake ba in banda mugunta ta ya za a aura mata Hassan yanzu ta tuna ya kai 10yrs tazararsu watakila shiyasa ta sha wuya don in ba haka ba ba wacce zata zauna da namiji.Jidda da kyar da roko ta tashi don sai da ya fara tsarkake kansa ya dawo bayan ya canja kaya ya taimaka mata da kyar take takawa ya dauketa ta ki yarda su haɗa ido wanka ya mata daman bata wanke gashinta ba ɗazu ya haɗa duka ya mata ta ƙi cangaz da kyar ta xauna a bahon ruwan dumi kamin su dawo ɗaki bai bari ta ga  stain din jinin katifar ba kar hankalinta ya tashi kafin tafito ya gyara wajen bata tarar da komai ba a kan katifar ,Hassan kamar ƙwai haka ya shiga tarerayar Jidda sai cin magani take taki ko kallonsa bakin maganar tata ma ya mutu ya ciro mata kayan yace zai sa mata ta fizge da kanta ta saka kayan tana kamewa gefe yaga kamar sanyi take ji ruwa ya dauke sai yayyafi ake ya rufe window gabadaya ya dawo yaki daina bata hakuri sai da ta tashi zata bar masa ɗakin ya kyaleta ya ce ta kwana shi zai kwana a parllour ta rifo kofar dakin tana takawa ta kwanta taki cire tunanin abubuwan da suka auku a ranta hassan da yake sumi sumi shine ya zage ya mata wancen abubuwa?Take ta faɗa a rai daga baya bacci ya dauketa mai nauyi…..




*Book on Arewapen🥰 masoya bazan yi disappointing ɗinku ba kawai ku bada himma da comment da share and like*



***