Ɗanɗano
by @legendspen
*DA JININSA NAKE RAYUWA*
_ƊANƊANO_
"Ke wai wace irin banzar yarinya ce da ba ta san ciwon kanta ba, Husna?!"
Muryar Mama ta karaɗe gidan tamkar ƙarar tsawar da ke barazanar tsaga benen gidan. Husna ta riga ta yi nisa a cikin kukan da take yi, gwiwoyinta a haɗe da ƙirjinta yayin da take zaune a kan lallausan kafet ɗin ɗakin. Babu abin da Husna ke ji sai wani irin raɗaɗi mai zafi da ke daskarewa a cikin zuciyarta.
"A ce gida kamar wannan, gidan da ake taƙama da addini da tarbiyya, gidan malamai gaba da baya, amma ki dage sai kin ɗauko abin kunya kin yafa mana! Wai ke Husna kece zaki buɗe baki ki ce mana kina son wanda ba musulmi ba? Arne? Mutumin da ko yankan farce ba za mu haɗa da shi ba a addinance da al'adance?"
Mama ta faɗa tana ci gaba da masifa tana kai da komo a tsakiyar ɗakin, fuskarta ta yi jajir saboda ɓacin rai. Duk wata kalma da take furtawa tana sauka ne a jikin Husna kamar ana zuba mata ruwan ɗanyen dalma.
A hankali Husna ta ɗaga kanta wanda ya yi mata wani irin nauyi, hawaye na wanke mata fuska, ta ce.
"Mama, ba za ku gane ba ne..." muryarta ta fito a kausashe kamar ba ita ke gunjin kuka ba. "Ba zan iya rayuwa babu shi ba. Idan na bar shi, tamkar na ci amanar rayuwata ne! Mama, jininsa ne fa yake gudu a cikin jijiyoyina. Da jininsa nake rayuwa!"
Kafin Husna ta rufe bakinta, ta ji saukar wani zazzafan mari a kuncinta wanda ya sa ta ga wasu taurari na wani ƙanƙanin lokaci. Wannan shi ne marin farko da Mama ta taɓa yi mata a duk tsawon rayuwarta, domin Husna ta kasance yarinya mafi soyuwa a zuciyar kowa da ke gidan, yarinyar da ake so ake kuma alfahari da ita, tun daga kan Abba, Mama, yayyenta maza har da ƙaninta ma Ashir.
"Rufe mini baki, shashasha mara tunani!"
Mama ta faɗa cikin tsananin ɓacin rai tana nuna ta da yatsa.
"Wannan jinin da kake iƙirari ba shi ya halicce ki ba! Allah ne Ya ƙaddara jininsa zai shiga jikinki ya zama silar rayuwarki, kuma bai ci ki ce zaki sayar da addininki da mutuncin zuri'arki saboda shi ba! Ke yarinya ce mai taurin kai. Mahaifinki ya riga ya gama yanke hukunci, kuma babu abin da zai canza. Don haka ki goge wannan haukan daga ƙwaƙwalwarki, domin kuwa ko raba ki da rayuwar za a yi, ba za ki taɓa auren wanda ba musulmi ba!”
Kalaman Mama suka kusa dakatar da numfashin Husna, a hankali ta kwantar da kanta a kan gwiwoyinta ta sake rushewa da wani irin matsanancin kuka. Akwai ciwo mai tsanani idan mutanen da suka fi kowa ƙaunarka a duniya su ne ke ƙoƙarin raba ka da jinin da ke buga zuciyarka. Amma ita dai ta san har yanzu ba azo wani dalili da zai hanata bawa zuciyarta abin da take so, na menene ma wai za a ce ba za ta auri wanda take so ba, ita a yanzu kukan nan da take yi ma, ba na duk faɗa da nisihar da Abba ya yi mata kafin ya fita ba ne, cewa da ya yi ba za ta auri wanda zuciyarta ke muradi ba shi ya sanya ta kuka, dan ita ko kaɗan ba tason jin wannan kalmar, mutuwa kaɗai ce zata raba ta da abin da take so.
*********
Sai da ya ɗan matsa gaba da ita, daidai yaddaa rana zata rage mata ganin fuskarsa, kamar yaddaa ya yi mata lokacin farko da suka yi doguwar magana da shi, cikin amon muryarsa mai sanyi ya ce.
"Husna, kin kasance mace ta farko da ta shiga rayuwata ta hanani zuciyata sakat, komai na ke yi tunaninki nake, ba zan iya cewa ga adadin son ki da yake cikin zuciyata ba, ke ɗin ta daban ce.
Ina son ki, ina son komai naki, murmushinki ka ɗai abun ya isa ya dauwamar da rayuwata cikin farin ciki, rigimarki abar soyuwa ce a gareni.
Sai dai ƙa'idojin rayuwa sun sanya shamki a tsakaninmu. Ina tsoron kar soyayyarmu ta kai mu matakin da zamu rasa kowa namu."
"In dai ina tare da kai, banƙi na rasa kowa ba, kai nake so kuma kai zan so yau, gobe, jibi, har numfashina na ƙarshe."
Husna ta katse shi, sabida ba tason ya zo gaɓar da zai furta mata kalmar rabuwa, ya yi wani irin murmushi mara daɗi, ya ce.
"Ina tsoron kada na karɓi zuciyarki, sannan a tsakiyar tafiya al'ada da addini su sa mu miƙa wuya, mu bar zuciyoyinmu a tarwatse.
Ban koya miki darasin lissafi domin ki kasa yin lissafin makomarki ba."
Sai da ta matso kusa da shi, ta tsaya gab da shi ta zarar ta kasance mara yawa, har tana jin yaddaa zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi, kaman yaddaa tata take. Asibiti ne, amma ita ji take kamar wani fili ne aka ware na masoya, ba ta jin komai ba ta jin motsin kowa sai shi, a hankali ta yi magana cikin wani irin salo mai bayyana zallan abin da ke zuciyarta.
"Ni Husna, in dai ina da rai ina da numfashi, kai zan so. Da jininka nake rayuwa, da sonka zan rayu."
***********
"Amma ai naga ke mata ta tace."
Ya faɗa cikin cool voice, idonsa a lumshe, sai da Husna ta ƙare masa kallo tana ja da baya, sannan ta ce.
"Ni matarka ce? Matar da ba ta kai ba, matar da ba ta isa, matar da ka aura da mugun nufi."
A hankali ya buɗe fitinannun idanunsa da suka yi jajir ya kalleta, shi zai iya jure duk wani juji na ta, zai iya jure wa duk wannan rashin kunyar na ta, Fatansa ɗaya a ce ta zauna tare da shi, tazo kusa da shi. Yana matuƙar son jinta a jikinsa, yana son ya ji jikinta cikin na shi fiye da yaddaa yake son jin jikin Jamila a tare da shi, tun ranar da ya faɗa ruwa ta yi warming na shi da jikinta, ya kamu da matsananciyar shawar jikinta a tare da shi, bai sani ba ko ita ɗin ce ya fara so, ko jikinta na ta ya fara sha'awa, amma zai iya yin komai domin ta zauna a tare da shi.
"AS'MAhhhhhh."
Ya ja sunanta, shi ka ɗai ya san irin yanayin da yake ji a yanzu, ya sake runtse idonsa, ya ce.
"Dan......" sai kuma ya yi shiru, sai can ya ce. "Allah"
"Dan Allah mene?"
Husna ta faɗa tana mamakinsa, yafi ƙarfin ya ce ma ta dan Allah, shine zai zauna yana rarraba ma ta magana, ita wane karen haukan ne ma ya cije ta za ta sake haɗa jiki da shi? Daga yi ma sa abun arziƙi ya matse ma ta jiki sai da ya sanya ta jinya, duk wannan girman na sa ya dinga daddaneta har da hawa kanta, shine yanzu da yake saratu ce ita shine za ta sake ba shi jikinta? A wanne gidan mahaukata ta so? Ita ba ta ma san me ya kaita akaita wannan abun ba, Mutumin ma da ta kwana ta tashi da sanin cewar ta tsane shi har cikin ranta, amma kwana biyu ta fara rasa kantax tana shishige masa wanda gaba ɗaya ba haka ta tsara zaman gidan ba, ko nufinta gorin da Jamila ta yi mata ne ya sa ta fara haka? To ita ina ma ruwanta da shi da matarsa, wanda take so shi take so, kuma shi za ta ci gaba da so, dole ne ta bar gidannan cikin 'yan kwanaki ko da kuwa Abba zai kashe ta sai dai ya kashe ta.
"As'mah."
Ya sake kiran sunanta, yana matsowa inda take, da sauri ta ja baya gudun kar ya fisgota, tun da ta san ita da shine kaɗai cikin gidan, matarsa ta tafi gantalin da ta saba, ga wannan As'mah ɗin da yake kiranta kwata kwata ba ta son sunan, jinsa take yi har jijiyoyin jikinta inda ya kira. Buɗe ido ta yi ta gan shi gab da ita yana ƙoƙarin sa hannu ya fisgota, ba shiri ta ƙwalla ƙara.
Daidai lokacin da Jamila ta yi parking motarta a compound ɗin gidan.
Wani banzan kallo ta watsawa part ɗin Husna ta ci gaba da tafiya, sai dai kuma idonta ya kai kan Blue benz ɗinsa, a fili ta ce.
"What? Bai fita ba?"
Nan take ƙwaƙwalwarta ta hasaso mata shi ne dalilin da ya sa Husna ƙwalla ƙara.
"Unbelievable!”
Ta faɗa tare da nufar part ɗin, daidai lokacin ya kai hann yana ƙoƙarin taɓa towel ɗin jikin Husna, ita kuma ta runtse idonta, sabida ya gama kai ta ƙarshe bangon ɗakin.
************
Dukkansu suna tsaye kowa ya yi carko carko, fuskarsu duk ta nuna ɓacin ran da suke ciki, cikin wata irin muryar da ba su taɓa ji ba, Abba ya ce.
"To wallahi ba a gidana ba, Asma'u."
Ba kalmar ba a gidana ba ce, ta ƙara tsorata su ba sunan Asma'u da Abba ya ambata shi yafi basu mamaki, ba su ba kowa ya san Abba ba ya kiran Husna sai dai ya ce Nanata, idan yana son yi mata faɗa ne ma zai ce. Nana Husna, to amma yau ainahin sunan ma ya kira.
Husna da ke cikin ɗaki a zaune hantar cikinta na faman kaɗawa ta tashi ta fito tsakar gidan, kanta a ƙasa ta durƙusa.
"Tun da abin da kika zaɓa kenan, daga rana mai kamar ta yau na yafeki cikin 'ya'yana, na haƙura da ke har duniya ta naɗe, soyayyar da nake miki Allah Ya bani wata 'yar da zata so ni ana gaba, dan haka ina son ki haɗa duk wani abu naki ki tafi ko ina ma zaki, abin da kika zaɓa kin Samu."
"Dan girman Allah Alhaji, dan soyayyar da kake wa Annabi Muhammadu a'a."
Mama ta faɗa tana zubewa a gaban Alhaji, Yaya Abdul ma ya zo kusa da ita ya zube a take Walid da Alhaji ma suka zo suka zube har da Ashir, suka kama ƙafar Abba, Yaya Walid ya ce.
"Abba karka hukunta tata a haka, Abba wannan hukuncin dukanmu ka yi wa har da kai ma, kar ka je fa rayuwarta a wani hali na daban, Abba dan Allah kar ka watsar da tarbiya da ka shafe shekaru kana yi mata, Abba dan girma Allah ka yi haƙuri."
Kuka ya ciyo shi har ya kasa ƙarasa maganar da yake yi, Mama ta sake cewa.
"Idan ka ce Husna ta tafi ina zata? Mun bata dama kenan ta yi duk wani abu da take so, Husna so take ta zama zakkah a cikin zuri'armu, ta ɗauko abun kunya ta yafe mana ta ƙarfi da yaji."
"Mama ba wannan zaku yi magana ba dan Allah, ku yi magana a kan yanda zata dawo hanyar da ake so."
Alhaji ya faɗa, sabida baya so kalaman Mama su ƙara tunzura Abba da har yanzu bai ce musu ya haƙura ba.
"Ta je ko ina nema, abun ta nema ne ta samu, Allah Ya sani bangaza wajen tarbiyarki ba, a kullum ina yi koƙarina wajen kare duk wani haƙƙinki da 'yan uwanki, Allah Ya gani kuma zai shaideni a ranar gobe, ba zan miki baki ba Husna, amma zan barki da abin da kike so."
Yana kaiwa nan ya fice, tabbatacciyar shaida ta bai haƙura ba, Husna sai ta bar gidan.
"Kinga ni Husna, idan kika kasheni, kika kashe shi sai ki ji daɗin duniyar."
Mama ta faɗa, bata so ta yi kuka, ko ƙwalla bata fatan ta yi wa wani cikin 'ya'yanta, amma Husna ta dage ta tirji, ina za ta sanya ranta ta ji daɗi.
"Yanzu Mama mene abun yi? Yanda Abba ya fita dai yana kan bakansa."
Kallon Walid da ya yi magana Mama ta yi, bayan ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Mene abun yi, ita gwanar baka ga ko a jikinta ba, ba taƙi yanzu mu bata hanya ta fita ba."
Kallonsu suka mayar ga Husna da take kallon su ido ƙir, kaman ba a kanta ma ake magana ba.
*************
Tun da ta ajiye masa coffee din ta zauna kusa da shi, so take ta faɗa masa abin da ke ranta, amma ba ta san ta inda za ta fara ba. Ita har ga Allah matsalal Husna da ta ɗauka ƙarama tana shirin zamar mata babba. Bata ƙaunar yarinyar nan ko kaɗan. A yanda take gani tsaf zata iya ƙwace mata soyayyarta a wajen mijinta, namiji da aka ce ɗan kunama, kwata kwata ba kunya na ce da shi.
"Jamsy."
Ya kira sunanta ganin ta yi nisa cikin tunanin da take yi, shi ba mutum ba ne mai nuna kulawa a zahiri, amma kuma zuciyarsa tana damuwa idan ya ga wani a cikin damuwa, kawai buɗe baki ya yi magana ne abin da ke matuƙar wahalal da rayuwarsa.
Murmushi ta yi masa, sannan ta kama hannunsa ta buɗa, ta kwanta a ƙirjinsa ta fara magana a hankali.
"Honey."
"Uhm."
Ya amsa mata, tana jin yanda zuciyarsa ke bugu, sai da ta daidaita nutsuwarta sannan ta ce.
"Wannan za ta iya zama alfarma ta ƙarshe da zan nema a wajenka, dan Allah ba dan ni ba ka yi kokari a kai."
Ya gyaɗa mata kai, ta sake cewa.
"Ban san ta yanda zan faɗa ma ba, ina sonka ka sani, duk da bani da tabbaci a kan so da kake min, amma a kwanaki ka sanar da ni da baka sona zuwa yanzu ba ka tare da ni, na ji na yarda da hakan. Dan girman Allah."
Sai kuma ta miƙe ta durƙusa kusa da ƙafafuwansa.
"Dan Allah, dan Allah ka rabu da Husna, ka sake ta, wallahi ganinta ka dai hanani nutsuwa yake."
Ta ƙarashe maganar kamar za ta yi kuka, da wani irin mamaki ya ɗago kai ya kalleta. He can't believe abin da take cewa, wai ya saki Husna, Husna da ya fara jin sonta a duk wata tsoka ta jikinsa!
Gani na dawo muku da sabo, bayan ajiye Sartse. Kamar koyaushe ban ce babu marubutan da suka fini ba, amma na sani cewa alƙalamina yana da wani irin salo na musamman wanda muddin ka fara karanta shi, ba za ka so ka ajiye ba. Kun saba gani na da salo mai ratsa jiki, kamar yadda muka yi a SARTSE, kuma a wannan karon ma na zo muku da abin da ya fi kowane lokaci.
Ina roƙonku da ku ba ni kyakkyawar shaida da yaƙini, ni kuma zan ba ku nishaɗi da darussan da kuke buƙata in sha Allahu.
Na gode da soyayyarku da amincewarku a kan rubutuna. Allah ya haɗa mu a Aljannar Firdausi. Amin.
#Da_jininsa_nake_rayuwa
#lovetriangle
#loveandheal
#unexpected_love
#legendspen