Chapter 5
*RIKICIN DUNIYA...*
©️ Meenat A. 'Yandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
CHAPTER 5
..."Malam! Me nake gani haka? Wariyar launin fata da kake nunawa Nadiya, yau har ta kai mu ga haka. Ko ita ba kaine ka haifeta ba?"
Kallonta ya yi bai yi mamakin abin da ta fada ba
"Wannan kuma ke ce za ki fadi eh ko kuma aa"
Rass? Gaban Inna ya yanke ya fadi. Saurin kawar da zancen tayi
"Gaskiya abin da kake mata a gidan nan ya yi yawa, yarinya tsaye take bakin kokarinta tana kyautata maka amma kullum cikin sakata a damu kake. Yau kai ne har ta kai ku ga duka"
"Wace kyautatawa kike magana? Ko kudin maza da take amsa, ko kuma kina magana ne akan wancan yaron dake zuwa wurinta bada izinina ba? To bude kunnuwanki ki jini da kyau, na fada zan kara fada ni mai gadin primary ne. Ban dauki kaina na kai can inda kuke tunani ba, don haka ku fitar da duk wani shirme da karya daga cikin rayuwarku. Sannan ke kuma ki bude kunnuwanki da kyau ki jini, daga yau na haramtawa yaron nan zuwa kofar gidana matukar bai turo magabatan shi ba"
A yanzu kam hannu biyu ta ɗora bisa kai tare da fashewa da kuka.
"Kawai a fito a koreni a gidan nan idan haka aka yi niyya, wallahi bazan rabu da Kasim ba."
Tana kaiwa nan ta ruga da gudu ta shige daki.
"Ka ga abin da nake fada maka ko? Yanzu har ta kai Nadiya ta gane kafin son wannan munafukar a kanta”
"Ba sonta ne bani yi, ba halinta ne bani so. Sannan kema kin sani ke ce Ummul aba'isin faruwar duk wani abu da kika san ya faru"
"Ni me nayi? Ka ga Malam. Kada ka daura muni jakar tsaba kaji su bini"
Murmushi takaici ya yi. "A tunaninka duk abin da kuke yi a cikin gidan nan ke da Nafiya ban sani ba ne? Ba shakka kinyi kuskure domin zuba maku ido nayi ina kallonku, saboda har wurin da nake aiki labaran kaf abubuwan da kuke yi ya ke iskeni"
"Cewa za kayi munafukai 'yar unguwar nan ta mu su suke zugaka ba tare da kayi bincike ba ka hau ka zauna"
"Wannan kuma damuwarki ce. Allah ma shaida ne na ba Nadiya tarbiyya yadda ya kamata ke ce ke bi lungu da saƙo kina rusheta." Ya na gama maganar ya fada daki.
"ke kuma bak'ar munafuka na dawo kanki, za ki shige dakinku ko kuma sai na barki kwance a wurin nan?"
Da gudu Jamila ta fada ɗauki tana shasshekar kuka.
Bata jin dadi idan ta ga yadda mahaifanta ke samun sabani ko ince matsala saboda ita. Duk da dai tasan akan gaskiyar ta take amma har ga ranta bata jin dadi..
Da wannan damuwar takwanta baccin da zata iya kira da ƙuntatacce kuma mara daɗi.
Da asuba ta tashi yayi sallah, sai dai tana tsoron tayar da Nadiya dake sharar bacci ko alamar tashi bata yi ba. Tana gudun ta tayar da ita cibi ya zama ƙari, daure wa ta yi ta kai zuciyarta nesa tana fara kiran sunanta tana bubbugata.
Buɗe ido tayi tare da watsa mata kallon banza.
Tsoki ta doka tana mai laluben wayarta.
"Anti gani nayi har gari ya waye baki yi Sallah ba..."
"Ke dakata mini!"
Ta daka mata uwar tsawa.
"Me ye haɗinki da yin Sallah ta ko akasin haka, kabarinmu daya dake ne. Wato ba za ki daina shiga harka ta ba ko”
“Kiyi hakuri, gani nayi ko zaman gaba muke yi dake idan lokacin sallah yayi kamata ya yi a ce na tayar dake”
“To bani bukata. In ba haka ba zan shayar dake mamaki”
Ta karasa maganar tare da ficewq a dakin. Ba sallar ta nufa ba ruwa ta diba sai da tayi wanka sannan ta yi alwallah.
Bayan ta gama sallah komawa ta yi ta kwanta sakamon sai karfe tara suke da exam.
Jamila kamar yadda ta saba mikewa ta yi ta dora masu koko. Bayan ta gama ta amso masu kosai da waina.
Wainar kawai nadiya ta ci ta karasa shiryawa ta fito ta nufi gidansu Wasila. Sai dai abin da ya bata mamaki shi ne wayar gari da ta yi babu sakonnin Kasim bare kiran waya. Kamar yadda ya saba Da wannan tunanin ta karasa gidansu Wasila.
Canjin da Wasila ta gani a wurin Nadiya shi ya tabbatar mata da tabbas aikinsu ya fara ci.
Farin ciki mara misaltuwa ta tsinci kanta.
Haka suka yi exam din ranar suka gama duk da ba su rubura wani abij arziki ba amma sun sani da first class zasu fito.
Wasila so take ta tambayi Nadiya abin da ke damunta, sai dai tana tsoron ta bar wata kafa wadda zata gane shirinsu. Don haka bakinta ta kulle.
Har suka karasa gida jikin Nadiya sukuku.
Da farin cikinta ta fada gida. "Umma! Umma!!"
Ta hau kwala mata kira.
Da gudu Umma ta fito domin a tunaninta wani mugun abun ne ya faru.
"Umma albishirinki"
Goro fari ƙal"
"Aikinmu ya fara ci"
"Ke don Allah"
"Wallahi kuwa Umma sai ma kinga Nadiya yau sukuku take na so in tambayeta, sai dai na ji tsoron kada ta gane shirinmu"
"Kinyi kyan kai haka nake so ki iya tuggu da kissa, saboda asiri kadai baya ci ba tare da kissa ba ko gidan miji kika shiga"
"Umma shi ya sa na basar nayi kamar ban gane halin da take ciki ba"
"Yanzu sai mu je ga shirinmu na gaba"
Umma ta fada tana mai gyara zama.
"Shiri kuma? Wane irin shiri ne wannan bayan wanda muka yi wurin Boka Bakurmi"
"Wurin Malam Bawa za mu je"
Jin abin da Umma ta fada ya saka Wasila dafe ƙirji.
"Malam bawa kuma? Ko dai kina nufin Boka bakurmi?"
"Kamar dai yadda kunnuwanki suka ji miki, haka na fada. Kin tuna da wata magana da kika fada mini a baya gane da Malam Bawa da Nadiya?"
"Eh ban manta ba"
"To da ita za muyi amfani mu ƙara dulmiyar da Nadiya"
Fiddo ido waje Wasila tayi cike da firgici.
"Kai Umma! Abun sai ya yi mata yawa. Ga rasa Kasim ga kuma wata babbar musibar, Umma ki tausaya mata saboda idan muka jefata cikin waccan masifar rayuwarta ta gama lalacewa"
Mugun kallo Umma ta watsawa Wasila.
"Tausayi? Ba shakka na kula baki da wayo ba ki san inda ke miki ciwo ba. Bude kunnuwanki da kyau ki saurareni shi abokin gaba ba a ɗaga masa bare har ta kai ga jin tausayinsa. Wuta ake bude masa ta ko ina don haka abin da na ce shi za a yi ko baki so"
"Hmm! Ina son mallakar Kasim amma wallahi halin da Nadiya zata shiga naji ba dadi har cikin zuciyata"
"Abu ne mai sauki ki haƙura da Kasim har abada mu rayu cikin baƙin talauci har abada"
"Aa, ba zata zaɓu ba. Bindiga a ruwa. Ko mutuwa ne na amince tayi indai burina zai cika"
"Yanzu na ji batu"
"Amma Umma ina da wata shawara"
Wasila ta fada.
"Ina saurarenki"
"Me zai hana muke wurin Bakurmi ya yi mana aikin"
"Kinji ji da wata magana kuma, shi Malam Bawa shi ne zaiyi aikin da kansa"
"To shikenan ba matsala da yaushe zamu tafi?"
"Zuwa an jima domin ba a bori da sanyi gwuiwa"
Kamar yadda suka fada haka suka kama hanyar gidan Malam bawa. Ba karamin farin ciki yayi ba da wannan aiki da suka kawo masa. Amma inda gizo ke sakar sai sun kawo ɗan kamfai wanda Nafiya ke amfani da shi.
Da wannan tunani suka dawo gida cike da farin ciki, domin ta san ba zai yi mata wahalar samu ba.
Bayan magriba suna zaune ita da Umma karamin yaro yayi sallama "ance ana sallama da Wasila In ji wani"
Yamutsa fuska tayi. "Ka je ka ce bata nan"
Wasila ta fada.
"Kai yaro je ka ce gata nan zuwa"
Umma ta yi saurin ba yaron amsa.
"Kai Umma! Yanzu haka fa bata wuce faƙiran samarin nan ne masu fama da kansu"
"Koma dai wane ne je ki ganewa idonki.”
Turo baki tayi tana gungunai ta dauki mayafinta ta.
Kamshin daya dakar mata hanci ne ya saka ta kara sauri.
Mutuwar tsaye tayi sakamakon wanda na mujiyarta suka nuna mata tsaye ya na sakar mata murmushi...
Meenat A. 'Yandoma