SOYAYYAR ZUCI

Chapter 31&32

by @deeyamerh10

💖💖 SOYAYYAR ZUCI 💖 💖 
  (Love and Romantic story)
              Written
                By
         Deeyamerh
07070647236
Page 31&32
kai wajan rabin Awa agun ko zata sake fitowa amma shiru,sai da motocin da suka dau yan mata suka fara dawowa sannan yaja tasa ya bar wajan dan ba yasan idon sani ya ganshi.
Sosai tasha tambayoyi abun yan matan familyn,ko wacce da abinda ya burge ta,haka kawai taji duk wata macce da zata ya beshi tana jin haushinta to hakan me yake nufi wai?ganin ba tada amsar bayarwa yasa ta cigaba da sangarta,Abinda yake daure mata kai har yanzu Fatima ba ta tambayeta waye ba?akan me yayi mata haka?ko ta sanshi ne?sosai kanta ya dau zafi akan sanin waye shi,yanzu ina zata sake ganinsa wayarta tana cikin motarsa sosai ta damu cikin wannan dare dan duk yadda yan matan suka so tasaki jiki a shirya Dinner gobe kasawa tayi.
Har sai da Fatima tazo tace mata"suhaima wanna guy din gaskiya yana sonki irin wanna kishi haka" dariya tasa tana zama kusa da ita tace"oya bani labarin yaushi soyayyar tai karfi haka bansani ba?
Ke dalla can nima fa bansan shi ba,yadda kiga yayi mun haka nima nagani Ni damuwata daya ce wllh wayata yana cikin motarsa fa idanunta har suna kawo ruwa dan haushi.
"Innalillahi kibar gayamun haka dan Allah yanzu to gashi ke biki sanshi ba,bare nemusa Amma kinsan me ina tunanin kamar Abokin yaya Abdul Indai kuwa haka ne to tabbas zaizo dinner gobe,dan haka ki kwantar da hankalinki dan dai bayi maka da mutumin banza ba.
Sosai Fatima ta bata baki har tasake ana ta shirya Dinner yadda zasu dan wllh sai tayi rawar da tafi ta jiya ma idan ma wai rawar yake mata bukulu to fa sai tayi,abu kadan sai tasaki murmushi domin yanayin da suka kasance yana kawatar mata,ina ma haka SECRET LOVER din ta yake ai kwana zatai a zaune tana kallonsa wanna madarar kyau haka oh oh oh.
Sosai suka shirya yadda abin zai tafi yadda zasu bawa Kowa sha'awa a gun, har  rawar da zasuyi a wajan a daran haka shirya ta,Ni kuwa nace idan kinkiji bakya kigani ba ko.
___________
Washe gari tun 7:30am duk wanda zai je Makeup aka tafi domin sunce duk waje daya zasu tunda Dinkinma duk iri daya ne,inda manya masu Aure suka kira akai musu nasu a gida.
Sosai yan matan sukai kyau domin ko wacce ta tsaso kyauta domin ta burge mai sonta wacce bata da saurayi kuma Allah ya bata wajan irin su Sahaima😂.
Karfe 8:00pm motocin abokan ango suka zo daukar su amma sbd da sun ce sune karshan shiga suka ce musu ai ba'agama dan haka su jirasu.
Sai da aka fara kiransu A waya Sannan kowacce ta fito a shigarta sosai suka burge mazan domin tun a cocktail wasu daga ciki suka tafi da zuciyar wasu. Ko wacce da kawarta haka suka shiga Mota sai wajan Dinner
✨ THE KANO ELITE GALA NIGHT
Ba wai  wajan dinner yara bane a'a Annual Elite Gala Night ne inda manyan businessmen, attajirai, doctors, politicians, CEOs da manyan family names da suka halarci wannan Dinner,
An shirya taron a wani grand ballroom mai girman gaske. Daga bakin ƙofa har cikin hall ɗin, komai yana nuna an zuba kuɗi.
Babban chandelier ɗin crystal yana kyalli daga sama, yayin da soft golden lights suke haskawa a bangon hall ɗin. Tebura zagaye ne, kowanne an lulluɓe shi da farin tablecloth mai tsabta, a tsakiyarsa kuma akwai tall crystal centerpiece ɗauke da white roses da touches na gold.
A gefe guda kuma akwai babban stage da aka yi masa black-and-gold luxury backdrop, yayin da smooth instrumental music ke tashi a hankali.
Baƙin suna shigowa ɗaya bayan ɗaya cikin formal outfits—mata cikin dogayen gowns masu tsada, maza kuma cikin perfectly tailored tuxedos da suits.
A wannan daren.
A harabar wajan aka sauke inda aka sanarwa da Mc cewar Kawayan Amarya fa sun iso a basu nasu taken,nan da Mc ya bazama nemu musu waka domin ba karamin burgeshi sukai jiya ba.
Ba  karamin kyau sukai ba domin duk wanda ya kallesu sai ya kara.A jere suka fara tafiya sai da suka je bakin Holl din sannan suka tsaya domin suna jiran wakar dan da rawa zasu shiga har inda Ango da Amarya suke.can na hango suhuma cikin wata doguwar gown wadda ta sa duk wanda ya kalle ta ya sake kallonta.
Amma daidai lokacin da take suke sha cikin hall,Sai ƙofar babban entrance ɗin ta buɗe, nan kallo yadawo kan su domin suma abokan ango ne suma jere.
Dagowar da suhaima zatai sai idanuwanta cikin na Boss wanda ciki 
Baƙar tuxedo ce jikinsa, white shirt a ciki, black bow tie, sannan wristwatch ɗinsa yana kyalli ƙarƙashin hasken chandelier.
Tsayinsa, yadda yake tafiya cikin nutsuwa, da confidence ɗin da yake ɗauke da shi suka sa wasu daga cikin mutanen da ke kusa suka juya suna kallonsa.
Suhaima kuwa Da zarar idonta ya sauka kansa, sai ta tsaya cak,Fatima ta lura da hakan ta matso kusa da ita rada tai mata a kunne "Suhaima... kina kallon wa haka?"
Suhaima ta yi saurin kawar da idonta.
"Nobody."
Fatima ta ɗan yi murmushi.
"Hmm... Nobody ɗin nan kuwa yana kallonki."
Kallonta yake ta gefen idonsa,dan ba karamin mamaki tabashi yayi tunanin abinda yayi mata jiya basai ya bude baki ya fada mata abinda yake nufi ba Amma yaga alama a aikace  yake so,nan danan yanayi yinsa ya sauya,lumshe blue eyese din sa yayi ,domin ji yake kamar yakashe duk wani namiji da yake kalle masa Princess dinsa.
 Muryar MC sukaji yana fadin "Ladies and gentlemen, we are waiting for the bride to make her grand entrance into this hall.”take wakar Until I Found You ta farà tashi.
Cikin takunsu na yan mata masu ji da kansu suka fara motsawa sai ihu da tafi domin ba karamin haduwa sukai ba,a haka har suka je inda Amarya da ango suke sai picture kawai ake sosai kowa yayi abinda yake so Sannan MC yake ce wa suna so Daya daga cikin Friend yazo ta bada Tahirin Amarya.
Sosai akaci kasa nan fa Mc yafara sakin zafafan wakoki,tunda ya zauna idonsa yake kanta Amma ta nuna kamar ma bata ganshi ba harkar gabanta yake yi,ai bai sare da lamarin ta sai da yaga sun hada kai sunyi cikin filin nan fa aka fara barin kudi kace me,yadda suka tsara rawar haka sukayi ta nan da maza ta mata kafa fara musu liki,dan wani daga cikin family Mama tunda ya yaje kanta ya bude rafar 1k yake juye mata,ita bama tasan yanayi ba kawai rawar suke dika.
Da yadda ya mike ya nufi wajan shi kadai ya isa yasa ka kauce masa domin yadda ya koma kamar wani mayunwacin zaki bai tsaya bin ta kankan kowa direct hannu yasa akwai ya sabata a kafada kamar ya dauki yar tsana,yadda yake takonsa kasan ran maza ya baci.
Tunda ya fito da ida bai direta ako ina ba sai wajan motarsa,kafin ya bude murfin ta cijeshi a hannun ta kallesa ido cikin ido tace"idan jiya kai mun na rabu da kai to yau bazaka batamin biki ba,ko wanda ya isa da Ni bazai mun wanna takamar ba bare kai".kallon ta yake kamar yasa mu tv domin yarasa wani irin hukunci zai mata, har tana da bakin budewa tace masa wanda ya isa da ita to waye?tana da wani saurayin ne?
Hannun biyu tasa domin da tunkude shi. Amma yasa hannunsa wajan rike nata,yadda taji hannunsa yana rawa yasa tadago da kallesa,da sauri ta sauke nata domin tashen hankali kawai ta hango a cikin kwayar idanunsa.
Wallahi kika sake kika koma cikin holl dinan duk wani namiji da yarabe ki to wllh sai na kashe shi kuma na kashe banza domin ke tawa ce Ni daya,dani aka halinci ki,idan rawa kikaso muje ki zauna a gaba kina yi amma bazan lamunci ganin kina juya abinda ya haramta ga duk wani namiji ba,MY cikin wani irin salo yaki sunan kafin ya dora hannunta akan saitin zuciyarsa yace"Idan har zata kara gudun da take a kirjina to ki hasaso yadda zan kashe duk wani abu da zai shiga tsakanin mu.
Kallon baka da hankali take masa kafin cikin tsiwa tace"ka kashe mana ina ruwa na kai ma kasheka za'ayi dan Allah kamatsa Ni naje naji dadin rauwata kuma yanzu ma zanje na na rungume wani eh dan kaji sai dai ka mutu ku.....ai bai bare ta karasa ya hade bakinsa da nata domin wllh da taci gaba da fada masa zata rungume wani Gara kowa yazo ya gansu wannan yanayin.
Idanuwa tazora hannu tasa tana dukan sa domin ya cika ta Amma yaki,tsotsar bakinta kawai yake cikin fushi da fusata,hango Fatima tayo inda suke yasa tafara kokarin turesa Amma ina ina jinduk abinda take masa.
Suhaima wai lafiya ne kike wa Bros Sha'ayan ne......ai maganar makalewa tai ganin yadda yake tsotse mata baki,domin yasan waye bros Sha'ayan,cikin karfin da yazo mata tas hannu ta tunkude shi, da sauri tai wajan Fatima yana kuka domin jitake kamar ai Hauka baki ta buɗe watau mata magana ya riga ta"Teema ki fada maka zan iya mutu idan ta rungume wani ba bani ba,ki fada mata Sha'ayan natane ita kadai nabata ragamar rauwata taja ina biye da ita Please I can't naka maza na kallonta ita din Tawa ce.
Cikin sauri ya bude motarsa yashiga yabar wajan a 360 sai dai Allah ya kiyaye.
Kallonta Suhaima take Amma hawaye ke zuba,rumgume ta Fatima tayi tace"Sorry Besty banso daga bakina zaki fara jin wasu abubuwan ba sona komai yazo daki bayan daki amma Kashhh kunsa dole zan fada Miki lokaci da nake so yazo bai zoba.
Tirkashe me Fatima yake boyewa sahaima ne??