04
by @oumfatima33
*MEERAH*
*OUM FATIMA*
*04*
WACECE MEERAH ?
Cikakken sunana shine Hafsat Abbas Mamman Gwangwazo, ana kirana da Meerah ne saboda sunan Mahaifiyar Dady aka saka min. Shine Momy tayi min alkunya da AMEERAH.
Lokacin dana fara girma kuma friends ɗina suka zamanartar da sunan ya koma MEERAH, wanda dashi kowa yake kira na a yanzu.
Mahaifina Honorable Abbas Mamman Gwangwazo ɗan siyasa ne wanda ya riƙe muƙamai da dama a gwamnati, yanzu haka yana riƙe da muƙamin Ministan sadarwa ne.
Ɗan Asalin Gwangwazo ne dake Tudun Wazirchi, ward Kano Municipal LGA. Asalin zuri'ar gidansu nada alaƙa da sarautar Kano, tun asali Kakanninsu suke ɗaura rawani wa Sarakuna da sauran masu matsayi a fada.
Babbar zuri'a ce mai asali da tushe wacce ake ganin mutunci da ƙimarsu sosai sakamakon alaƙar da suke da ita ta kai tsaye da Masarauta.
******* Kakan Hon. Abbas Mamman Gwangwazo Alhaji Basiru Gwangwazo shi ya fara ajiye harkar naɗi ya shiga karatun boko, ta hanyar wani Bature da aka kawo yake koyarwa a makarantar primary da aka buɗe a yankin nasu.
Yayi karatu har matakin ƙarshe a wan can lokacin da taimakon wannan dai Baturen daya fahimci baiwar ilimin da yake da ita. Don da farko zama yake nesa da inda ake koyar da karatun yana kallonsu cike da sha'awar abin.
Tun Baturen Malamin nan bai lura da shi ba, har ya gane shi. Hakan yasa ya janyo shi cikin ɗaliban da yake koyarwa, ya kuma je har gidansu ya sanar da Mahaifinsa sha'awar da yake ita a kan Karatun. Wannan ne mafarin samun duk abinda ya samu.
Wanda hakan ya zama abin magana a wurin dangi ake ganin ya ajiye al'ada da sana'ar da suka gada tun daga Kakanni, ya biye wa koyarwar da Yahudawa suka zo da ita.
Hakan bai dame sa ba kasancewar yana son abin, don haka ya mayar da hankali a kan abinda ya saka a gaba, tun da ya samu goyon bayan Mahaifinsa.
Mahaifiyarsa ce taso ƙin amincewa da farko, sai da ya zauna ya fahimtar da ita cikin natsuwa sannan ta amince masa.
Bayan kammala karatunsa ya samu aiki mai kyau da albashi mai tsoka, wanda ya janyo ƴan'uwansa da suka ƙi karatun suka fara yi masa hassada ganin irin ci gaban daya samu.
Alhamdulillah rayuwarsa ta ƙara yin kyau sosai inda ya samu ci gaba fiye da sauran ƴan'uwansa, yayi aure ya hayayyafa yana kula da ƴa'ƴansa da Matarsa, da zuri'arsa baki ɗaya.
Yaso duka ƴa'ƴansa suyi karatun boko don su ma rayuwarsu tayi kyau kamar tasa, amma sai wasu suka ƙi amincewa bisa zugar Kakanninsu da har yanzu ba kowa ya yarda da karatun bokon ba.
Mamman wanda shine ɗa na biyar a wurin Alhaji Basiru Gwangwazo shine ya gaje sa a harkar karatu, don duk yafi ƴan'uwansa mayar da hankali. Hakan yasa Mahaifinsa ke ji dashi ya kuma tsaya masa yayi karatu mai zurfi.
Don sauran ƴan'uwansa iya secondary suke yi su koma sana'ar gado, wasu ko secondary ɗin ma basa kammalawa suke watsar wa. Babu yanda Alhaji Basiru ya iya dole ya ƙyale su kowa yabi ra'ayinsa, sai dai ya mayar da hankali sosai a kan Mamman don ya fahimci shine photo copynsa....
****** Alhamdulillah Mamman ya samu ilimi sosai, inda ya karanci harkar kasuwanci. Hakan yasa bayan kammala karatunsa ya tsunduma harkar Kasuwanci da taimakon Mahaifinsa, wanda yake matuƙar alfahi da shi. Hakan kuma ya janyo masa tsana a wurin sauran ƴan'uwansa, don suna ganin kamar Mahaifinsu ya fi son sa.
Mamman shi ya fara barin cikin gidansu, lokacin da yayi auren fari ya fita wata unguwar ta masu kuɗi ya tare da amaryarsa Hafsat wacce ƴar wani Malaminsa ne na makaranta.
Ganin irin ɗaukakar daya samu yasa ƴan'uwansa da suke ƴan uba fara yi masa hassada, kamar yanda ya faru da Mahaifinsa. Rasa yanda zai suyi dashi yasa suke yaɗa jita-jitar cewa.
Ya ajiye al'ada da sana'ar da suka gada ya biye wa koyarwar yahudawa, sun sauya masa tunani gashi nan yafi ƙarfin zama a gidansu na gado tamkar yanda kowa ke yi a cikin zuri'arsu.
Bai bi ta kansu ba yaci gaba da al'amaransa yanda ya saba, tun da da amincewar Mahaifinsa ya fita ɗin. Sannan kuma bai manta tushe ba yana shiga duk wani abu daya tashi a cikin dangi, yana kuma bayar da gudummawa sosai.
Haihuwa ta farko da matarsa Hafsat tayi ta haifi Namiji wanda yaci sunan Mahaifinsa Basiru, amma suna ce masa Bashir ne.
Haihuwa ta biyu mace ta haifa aka saka mata suna Safiya, haihuwa ta uku ne ta haifi Abbas wan da bayan haihuwar Abbas ɗin Alhaji Mamman ya ƙara aure. Inda ya aura a cikin danginsu mai suna Maimuna.
Bayan Abbas Hafat ta sake haihuwar yara biyu Mata Ramatu da Zuwaira, inda ita ma Maimuna amarya ta haifi nata yaran guda uku Maza biyu Abdurra'uf da Abdullahi, sai Macen Asma'u.
Waɗan nan sune zuri'ar Mamman Gwangwazo Yara takwas kenan, Maza huɗu Mata huɗu. Inda Uwargida Hafsat keda biyar Maza biyu Mata uku. Amarya Maimuna nada uku Maza biyu Mace ɗaya.
Alhaji Mamman Gwangwazo ya raini yaransa cike da kulawa, ya basu ilimin boko dana addini. Don har yarasa Mata sai da ya saka su a Makarantar boko.
Sai dai su iya secondary school suke gama wa yake aurar dasu, Mazan ne suke zarce wa Jam'a domin yana da burin su samu ilimi sosai wanda zai amfane su, ya amfani zuri'ar da zasu haifa.
Rayuwa taci gaba da miƙa masa inda ake damawa dashi sosai a harkar kasuwanci, ya buɗe Companysa na kansa yana gudanar da Kasuwancinsa cikin gaskiya da amana. Wanda sune tushen duk wata nasara daya samu.
Ganin irin sanuwar da yayi a harkar kasuwanci yasa wani Uban gidansa, wanda ya fara janyo shi cikin kasuwanci ya bashi shawarar shiga siyasa.
Bai amince ba sai da yaje ya nemi shawarar Iyayensa, sun amince suka saka masa albarka sannan ya fara. Cikin amincewar Ubangiji ya shiga siyasar da ƙafar dama ya riƙe muƙamai da dama.
Yaransa Maza duk sunyi karatu har matakin degree, inda Babban ɗansa Alhaji Bashir ya gaje sa a harkar kasuwanci. Bayan kammala degree ɗinsa ya tafi kasar London yayi master's ɗinsa duk a kan Kasuwanci.
A can ya haɗu da Matarsa mai suna Na'imatu ƴar wani babban ɗan Kasuwa, sun ƙulla soyayya mai ƙarfi don tunda ta ƙyalla ido taga Bashir ta kamu da soyayyarsa mai zafi.
Bata wani sha wahalar shawo kansa ba don shima ya ƙyasa, ya riga ta kammala karatu ya dawo ya barta a can zata kammala nata. Sai dai koda ya dawo Mahaifinsa ya masa maganar aure ya sanar da shi cewa ya samu Mata.
Lokacin daya sanar dashi wacce yake so ɗin, sai aka ci sa'a ƴar abokin Alhaji Mamman ɗin ce da suke harkar kasuwanci. Wannan dalilin yasa ya same shi da maganar, shima yayi farin ciki don haka babu wani ja aka bayar da sadaki aka ajiye ranar aure daidai da lokacin da zata kammala karatunta. Don ita ma tana gaba da gamawa.
Bayan kammala karatun Na'imatu aka sha shagalin bikinsu ta tare a gidanta, Bashir yaci gaba da gudanar da Kasuwancinsa. Don shima tarihi ne ya mai-maita kansa, cikin ƙan-ƙanen lokaci ya samu shaharar data fi ta Mahaifinsa.
Manyan Company biyu ya buɗe waɗan da yake shigo da manyan motoci daga kasashen waje, ɗaya a nan Kano, ɗayan kuma a Abuja. Inda ya tare da matarsa wacce ta haifi yaran ta guda huɗu, Babbar ƴarta Mace ce mai suna Zinat. Sai ɗansu na biyu Ajmal, sai Sulaiman sai auta Fatima.
******
A fannin Siyasa kuwa Abbas shine ya gaji Alhaji Mamman, don bayan kammala karatunsa ya fara harkokin siyasa. Inda ya fara daga ƙananan muƙamai har zuwa muƙamin da yake kai yanzu.
A fannin iyali shima ya auri Matarsa ta farko mai suna Hajiya Laylah wacce ƴar Yayan Mahaifinsa ce ya gani yana so aka yi ƴar gida. Ita ce ta haifa masa duka yaransa shida, Maza biyar sai autar su Mace wacce taci sunan Mahaifiyarsa Hafat ake mata laƙaɓi da MEERAH.
Bayan dogon lokaci ya auri Matarsa ta biyu Hajiya Hasiya ƴar Uban gidansa a siyasa wacce har yau Allah bai bata haihuwa ba.
**** Sauran yaran Alhaji Mamman Maza na ɓangaren Amaryarsa Maimuna duka aikin gwamnati suke yi inda suke da manyan muƙamai a gwamnati.
A ɓangaren Ƴa'ƴansa Mata kuwa duk sun yi aure, ko wacce kuma ta auri mai kuɗi ne, wasu ƴan Kasuwa. Wasu ma'aikatan gwamnati.
Zuri'ar Mamman Gwangwazo zuri'a ce mai haɗin kai da ƙaunar juna, domin kuwa Alhaji Mamman bai yi ƙasa a gwiwa ba wurin haɗa kan iyalansa, da nuna musu muhimmancin zumunci.
Don yana fatan ko bayan ransa su kasance a dunƙule wuri ɗaya cikin haɗin kai da ƙaunar juna.
Wannan kenan.
___________
Shaƙuwar dake tsakanin Alhaji Bashir da ƙanensa Hon. Abbas ta bambanta da kowa a gidan, don tun suna yara ƙanana suke matuƙar son junansu. Kusan ma duka rainon Abbas ɗin Alhaji Bashir ne Ya yishi.
Har girmansu kuma basu daina ƙaunar junansu ba, wannan yasa suka yi ƙoƙarin haɗa kan iyalansu. Sai dai inda aka samu matsalar Na'imatu matar Alhaji Bashir tana da wani irin ji da kai, hakan yasa take ganin tafi ƙarfin yin mu'amala da Hajiya Laylah.
Sai dai duk da haka kawunan yaransu a haɗe yake, don suna matuƙar son junansu tamkar dai iyayen su Maza dake ƙoƙarin haɗa su, ta hanyar zuwa hutu a gida ɗaya duk da cewa wurin zama ya raba su.
Shi Alhaji Bashir yana Abuja da nasa iyalan, shi kuma Hon. Abbas yana nan a Kano a unguwar Nasarawa GRA.
Muƙamin Ministan sadarwa daya samu ne ya mayar dashi Abuja, inda ya tafi da amaryarsa ya bar uwargidan a nan Kano tare da yaranta.
Hon. Abbas yana matuƙar son Ajmal yaron Yayansa na biyu don tunda aka haife sa yake son shi sosai, tamkar dai yanda Yayansa ya so shi tun yana yaro. Hakan yasa tun yana ƙarami yake ɗauko sa yazo yayi kwana biyu musamman idan ya samu hutun weekend.
A haka ne Momy (Hajiya Laylah) ta shaƙu da yaron sosai, wanda daga ƙarshe riƙonsa ya dawo hannunta ta haɗa su da yaronta na farko Sultan wanda zasu zo sa'anni.
A hannun Momy yayi karatunsa tun daga nursery har zuwa Secondary School, sai dai in an yi hutu a kai sa ya gano iyayensa.
Mahaifiyarsa Hajiya Na'imatu ba son zamansa take a can ba, amma ba yanda ta iya saboda koda ta samu Abby (Alhaji Bashir) da maganar faɗa yayi mata sosai. Yace.
"Ko duka ƴaƴan dana haifa Abbas ya nema zan iya mallaka masa su, ba wai yaro ɗaya ba. Kar na sake jin irin wannan maganar a bakin ki. Don ni da Abbas duk ɗaya ne."
Lokacin da yayi wannan maganar ta shiga ɓacin rai sosai, amma sai dai soyayyar da take masa da sanin data yi masa baya magana biyu yasa ta ƙayale.
Sai dai tayi alƙawarin janyo yaronta jikinta a hankali har ta shawo kansa, ya buƙaci komawa gabanta da kansa. Don Ajmal shine yaro mafi soyuwa a zuciyarta, kaf cikin yaranta........
Barkanmu da dare