MATUKAR INA RAYE

Matukar Ina Raye 17

by @mrsisham12


MATUKAR INA RAYE

(As Long as I’m Alive)

Writer — MRS ISHAM
*** WhatsApp.

Page 17

Tsaye suke a falo cikin shirin fita, kowa ya shirya tsaf. Daddy ya dubi Zannor.

“Kana ganin ba za mu tashe shi daga bacci ba kuwa? Kasan His Excellency zai ji daɗin ganin sa.”

Cikin hanzari Mamie ta ce, “Haba Almusthapha, kana gani fa, yaron nan jiya da ƙyar muka samu ya yi bacci saboda ciwon sa da ya tashi. Mu bar shi a gida ya huta.”

Duk suka yarda da maganarta, domin jiya ciwon BK ya tashi, inda ya sha baƙar azaba, da ƙyar baccin wahala ya ɗauke shi.

“Shikenan, mu tafi kawai. Gimbiya Sima ita ma ba za ta samu zuwa ba, da ciwon kai ta tashi.”

Cewar Daddy, yana yin gaba, a yayin da Mamie ta taɓe baki ta bi bayansa. Nan duk suka fito harabar gidan, inda motocin suke a fake suna jiran fitowar su. Ba a ɗauki lokaci ba suka shiga motocin, suka bar gidan.

Tana tsaye a bakin window ɗakin ta, tana kallon su har suka bar gidan aka rufe gate. Wani irin makirin murmushi ta sake, sannan ta bar bakin window ta nufi gaban mirror. Ta ɗauki kwalban magani, sannan ta fita daga ɗakin. Ma’aikatan da ke aiki a kitchen ta kira ɗaya daga cikin su.

Bayan ta zo ne ta ce, “Ina kayan karin kumallon BK? Ko an kai masa ne?” Ta yi maganar tana tsare gida.

Jiki na rawa, mai aikin ta amsa da, “Ah ah, Hajiya Sima, ba a kai masa ba. Ga su can a dining tare da na ki duka.”

“To, yayi kyau. Ki koma kitchen ɗin, zan neme ki.”

“To,” ta faɗa tana barin gurin da sauri, don ta san halin Sima yanzu; sai ta mata zagin cin mutunci, ko ma ta yi ƙoƙarin kai mata hannu.

Dining ɗin ta nufa. Tana buɗe flask ɗin tea ɗin ta tsiyaya, ta haɗa tea, sannan ta zuba maganin cikin kwalban ta gauraya.

“Saratu!” Ta kwala kiran mai aiki.

Tana riƙe da kofin, mai aikin ta iso tana cewa, “Naam, Hajiya.”

Yatsina fuska ta yi.

“Ki kai wa BK tea ɗin nan, ki ce Mamie ta ce ya tashi ya sha kafin a kawo masa breakfast ɗin sa.”

Da mamaki ta ke kallon ta, domin ta san hakan bai taɓa faruwa a gidan ba. Ko da yaushe Mamie ce ke ba da umarnin a kai wa BK abinci idan ba zai samu fitowa dining ba.

“Amma, Hajiya…”

“Amma uban me?” Sima ta dakatar da ita, tana watsa mata muguwar kallo.

Hakan ya sa ta karɓi kofin ta nufi sashen BK.

Can sai ga ta nan ta dawo. Cikin ƙaguwa Sima ta nufeta tun kafin ta gama saukowa ƙasa.

“Kin ba shi?”

“Eh, Hajiya, na ba shi.”

Ta kuma cewa, “Kin tabbata ya sha?”

“A gabana ya sha, kusan rabin kofi.”

Ta saki murmushin jin daɗi, sannan ta ce, “Za ki iya tafiya.”

Komawa ɓangaren ta ta yi, ta sheƙa wanka, sannan ta saka wasu kayan bacci masu jan hankali. Ta feshe jikinta da turaruka masu ƙamshi.

Tafiya take a hankali, fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi. Kallo ɗaya za ka mata, ka fahimci tana cikin farin ciki. Hannunta riƙe da ledar kosai, dayan kuma wani farin roba ne cike da tuwon madara da ta yi wa BK. Saboda kwanaki ya ce mata yana son tuwon madara sosai, hakan ya sa jiya da Mallumjoo ya ba su kyautar kuɗi, shi ne ta sayi kayan haɗin. Salma ta tayata haɗawa.

Dama so take ta ba shi bazata. In za ta kai kosai, sai dai ya gan ta da tuwon madara, ta san zai ji daɗi sosai.

Bayan ta shiga gidan, kai tsaye falon ta nufa, amma babu kowa. Sai ta doka sallama, sai ga mai aikin ta fito suka gaisa. Nan ta ba ta kosan da ta kawo.

Har ta juya za ta koma kitchen, Waheeda ta yi saurin dakatar da ita.

“Don Allah, ina BK yake? Na kawo masa saƙon sa ne, ina so in ba shi hannu da hannu.”

Ba tare da tunanin komai ba, ta mata kwatancen sashen na sa.

“Na gode,” ta faɗa tana nufar stairs ɗin.

Sima da take tafiya cikin yanga ta nufi sashen BK, tana tauna cin gam, yana ba da sauti kamar wata kilaki. Har ta isa bakin ƙofar part, ta ɗaura hannunta a kan handle ɗin, za ta murɗa, sai kira ya shigo wayarta.

Tana dubawa ta ga sunan Sweet Sis ya bayyana a kan screen ɗin. Sai da ta ɗan ja tsaki kafin ta yi picking.

A mugun zabure ta ce, “What! Mama ta rasu? Wayyo, na shiga uku! Na lalace! Kuna ina yanzu? Gani nan zuwa.”

Ta gama maganar tana fashe da kuka, sannan ta katse kiran ta bar gurin da gudu. Bangaje juna suka yi, amma ko waiwayowa ba ta yi ba, balle ta ga wadda ta buge.

Waheeda da ta ji zafin bugun ta bi bayanta da kallo kafin ta ce, “Ban yafe ba,” cikin ɗaga murya.

Ƙofar da ta gani ne ya sa ta fahimci nan ne inda mai aikin ta kwatanta mata. Hakan ya sa ta buɗe ƙofar ta shiga, sai dai babu kowa a falon da ya gaji da haɗuwa, ga manyan hotunan BK a ciki.

Tafiya ta ci gaba da yi tana kiran sunan Besty, amma babu amsa. Ƙofar ɗakin da ta gani a buɗe ta shiga.

Kwance ta same shi a kan gado, sai juyi yake yi yana riƙe da kansa da hannu, ga zufa ta jika masa jiki sharkaf.

“Besty…” Ta kira sunan a hankali. Ganin bai ba ta amsa ba ne ya sa ta isa gaban gadon tana faɗin,

“Ni kake sharewa saboda na zo gidan ku ko? Ni dama tuwon madara na kawo maka.”

A kasalance ya buɗe baki ya ce, “Ki ajiye a gurin.”

Ajiyewa ta yi, ta saki murmushi.

“Wai ba ka da lafiya ne? Me ke damunka?”

“Jikina ne yake min ciwo ta ko’ina,” ya ba ta amsa da ƙyar, har lokacin idanunsa a rufe suke.

Waheeda da ta zuba masa ido ta marairaice, jin baya jin daɗi.

“Sannu. Bari in tafi gida, kar a neme ni. Ka samu ka tashi ka sha magani, in ba haka ba kuma jiki magayi.”

Hannu ya miƙa mata, ya buɗe idanunsa da suka yi ja sosai.

“Mika min kofin tea.”

Dube-dube ta yi, nan ta ga kofin tea ɗin. Ta ɗauka tana kallon yadda madara ta yi biyayya cikin tea ɗin, har wani kauri-kauri yake yi.

“Ko za ki sha ne?”

Da sauri ta girgiza masa kai alamar a’a.

“Kar ki damu, ki sha ki ba ni sauran.”

Tana tsattsare shi da ido ta ce, “Ka tabbata?”

Kai ya jinjina mata a hankali. Hakan ya sa ta yi kurba biyu zuwa uku, sannan ta miƙa masa kofin. Ta ga ya miƙe zaune da ƙyar, ya sha, sannan ya ajiye kofin a ƙasa, duk tana tsaye a kansa.

Buɗe baki ta yi za ta yi magana, nan ta ji kanta ya wani irin sarawa. Da sauri ta dafe kan, nan ta fara ganin abubuwa bibbiyu, ga hajijiya da ke dibarta. Kafin ta ankara, ta faɗa saman gadonsa, wanda shi ma yana zaune a kai, amma bai san inda kansa yake ba.

“Salma, ni kam ina Waheeda ta maƙale ne? Daga zuwa kai kosai har yanzu shiru. Ko za ki dubo mini ita?”

Cewar Ummah, wadda gaba ɗaya ta shiga damuwa saboda rashin dawowarta. Kusan awa ɗaya da rabi kenan da fitarta.

“Ummah, kin san fa Waheeda sarai. Yanzu haka ta wuce gidan su Safara’u ne.”

Daga nan suka bar zancen, amma lokaci zuwa lokaci tana duban ƙofa.

Mamie da Zannor ne suka dawo gida saboda mantuwar da Mamie ta yi. Hakan ya sa Zannor ya dawo da ita. A tare suka shigo falon.

“Sannu da dawowa, Mamie,” cewar Saratu, mai aiki.

Ba ta amsa sallamar ba, sai ta ce, “BK ya fito ya yi breakfast kuwa?”

“Ah ah, Mamie, bai fito ba, amma dai ya tashi. Ɗiyar gidan masu kosan nan ta kawo masa saƙo, zai yiwu suna hira a sashensa.”

Da tsananin mamaki da al’ajabi, Mamie ta furta, “What! Tun yaushe ta zo?”

“Eh, dazun ta zo, ta ɗan jima dai. Don tana gidan ma Hajiya Sima ta fita tana kuka, alamu rasuwa aka yi mata.”

Jinjina kai ta yi bayan ta gama saurarenta, sannan ta nufi stairs ɗin, Zannor na a bayanta. Har suka shiga sashen BK.

Falon babu kowa, nan suka nufi bedroom ɗinsa. Abin da suka tarar ne ya sa suka ji zuciyoyinsu na kokarin rabewa biyu saboda tsananin tashin hankali.

Dafe kirji Mamie ta yi tana faɗin, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Zannor, menene idanuna suke nuna min haka?”

Zannor da ya rufe bakinsa da tafin hannu ne ya sunkuyar da kansa. Ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba.

Goge hawayen fuskarta Mamie ta yi, ta ƙarasa shiga ɗakin. Tana isa gaban gadon ta hau tashin Waheeda ta hanyar bubbuga kafaɗarta tare da kiran sunanta.

A hankali ta buɗe idanunta, waɗanda ta ji sun mata bala’in nauyi. Ganin fuskar wadda ke tsaye a gabanta ne ya sa ta fara ƙoƙarin miƙewa a zabure, amma hakan ya gagara saboda yadda yake riƙe da ita. Kai, idanunta kansa ta yi, nan ta ga kusan rabin jikinsu na manne.

Da ƙyar ta mike zaune, tana jin zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Ba wai don ta san abin da ya faru ba, sai don ganin su Mamie a kanta da ta yi ya ba ta mamaki.

Cikin tsare gida Mamie ta jefa mata tambaya, tana bin ta da muguwar kallo.

“Me ya kawo ki sashen yarona?”

“Tuwon madara na kawo masa.”

Kallon roba ɗin suka yi duka, kafin Mamie ta maida dubanta kan BK, wanda ke kwance babu riga, sai iya dogon wando. Yana bacci, bai ma san inda yake ba.

“Tashi ki fita ki bar min gida, baƙar munafuka.”

Kallonta sosai ta yi, jin sunan da ta kira ta da shi, amma sai ba ta ce da ita komai ba. Ta sunkuya ta ɗauki hijabinta, ta soma tafiya don barin ɗakin.

Zannor ta gani tsaye a bakin ƙofa, idanunsa sun sauya kala, tashin hankali ya bayyana ƙarara a kan fuskarsa. Zuba wa juna ido suka yi, kafin ya matsa mata ta wuce.

Har ta kai bakin ƙofa ta ji muryarsa.

“Bestyn BK…”

Cak ta dakata da tafiyarta, ta juyo ta dube shi. Taku biyu ya yi ya iso gare ta, ya ce,

“Ki faɗa min menene abin da ya faru a ɗakin nan? Me ya faru tsakanin ki da Bestyn ki har kika yi bacci a kan gadonsa?”

Ɗaga kafaɗa ta yi alamar ba ta sani ba.

“Samun sa na yi ba shi da lafiya, shi ne zan tafi. Ya ce in ba shi sauran shayin da ke wancan kofin kafin in ba shi na sha. Tunda na sha, sai na dinga ganin biyu-biyu. Sai yanzu da na farka na gan ku, na ji dama-dama.”

Ba iya Zannor da take ba wa labari ba, hatta Mamie ta fahimci ba ta san girman abin da ya faru ba. Shi ya sa ba ta damu ba, saboda yadda ta faɗa ya nuna alamu daga ita har shi ba sa cikin hayyacinsu.

Runtse idanunsa ya yi, ya furta,

“Shikenan, za ki iya tafiya.”

Sai da ya tabbatar da ta fita ne ya yi saurin zuwa ya ɗauki kofin da ta nuna, ya kai hancinsa ciki. Tabbas ya ji wani irin ƙamshi daban a cikin shayin.

“Mamie, duk yadda aka yi wani ne ya sanya wani abu a cikin abin shan ɗan uwana. BK ba zai taɓa aikata haka ba, ni na san wane ne shi.”

“Na shiga uku na ni! Hiyana!” Ta faɗa tana daura hannu biyu a kai cikin tashin hankali.

“Yanzu meye abin yi? Duk wanda ya aikata haka yana so ne ya lalata wa yarona rayuwa. Dole in yi wani abu tun kafin lokaci ya ƙure.”

Shiru suka yi, suka zuba wa BK da ke kwance ido, sun ma rasa abin yi.

A firgice Mamie ta kuma faɗin, “Na samu solution. Tunda abu aka sanya masa a abin sha, ina da tabbacin bai san abin da ya faru ba, kuma ko ya farka ba zai iya tunawa da komai ba, kamar yadda ita ma yarinyar ba ta tuna ba.”

“Me kike nufi, Mamie?”

Cikin tsawa ta ce, “Abin da nake nufi kam ɗaya ne, ai Zannor. Ko ta halin ƙaƙa, BK ba zai taɓa sanin abin da ya faru a wannan rana ba. Ba ma shi kaɗai ba, babu wanda zai san wannan abu daga ni sai kuma kai. Wannan sirri ne tsakaninmu biyu. Wallahi, duk sanda maganar nan ta fita, Zannor, ba zan taɓa yafe maka ba, sai na tsine maka albarka, in har twin ɗin ka  ya san da wannan sirri. Ka ji na faɗa maka.”

Jikinsa ne ya ɗau rawa. Cikin matsanancin tashin hankali yake kallonta, sannan ya hau girgiza mata kai.

“Ah ah, Mamie, ba zan iya ɓoye wannan sirri ba. Ita yarinyar fa? Wannan tauye hakki ne. Ba zan bar ki ki yi abin da zai iya cutar da BK ko kuma yarinyar mutane a gaba ba.”

Damƙe ƙwalarsa ta yi, tana zare masa idanunta da suke zubar da hawaye.

“Zan iya yin komai a kan ɗana. Kalli idanuna, Zannor, kuma ka yarda da abin da zai fito a bakina. Na maka alkawari, babu abin da zai je ya dawo. Ina yin komai ne saboda rayuwar ɗan uwanka ta yi kyau. Ka sani, in wani abu ya fita, to kai ne nan ka lalata rayuwar ɗan uwanka da kanka. Ka sa wannan a cikin kwakwalwarka.”

Nan take ya ji gabansa ya faɗi, jin wannan tsattsauran kalma daga bakinta. Ji ya yi komai ya tsaya masa. Ta yaya zai so abin da zai ruguza rayuwar ɗan uwansa da hannunsa?

Kai ya girgiza.

“Babu abin da zai faru da BK, Mamie. Zan aikata duk abin da kike so,” ya faɗa yana sanya kuka kamar ƙaramin yaro, yana jin yadda zuciyarsa take ƙara tsananta bugawa.

Rungume shi ta yi, tana bubbuga bayansa, har yanzu idanunta na kan BK.

A saitin kunnensa ta furta, “Dole BK zai bar wannan ƙasa. Ya tafi ya cika burinsa na zama ɗan wasan ƙwallon ƙafa da yake so.”

Duk da wannan kalma suke ta jira shi da BK daga bakinta, amma yau da ya ji ta, sai ya ji ta salam sam bai ji wani armashi ba, domin ya san ba don Allah Mamie ta amince ba, sai don son kare BK daga laifin da ya aikata.

Lokacin da Waheeda ta dawo, ba ta samu Ummah a gida ba. Ta shiga Makota yin gaisuwar rasuwa. Salma ce ta dube ta a tsanake.

“Ke kuma, me ya sa kike tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki?”

“Babu komai, jikina ne yake min ciwo.”

Ta gyada kai, tana maida hankali kan wayarta, ta ce, “Ba dole ba, kin je kin biye wa kawarki Safara’u, kun yi wasan banza. Na daura ruwan zafi a murhu, sai ki sauke ki yi wanka da shi. Saura kuma, kar ki zuba min wani ruwan a tukunya.”

Ruwan ta juye ta maida mata da wani, sannan ta yi wanka, ta saka wasu kayan, ta hau gado ta kwanta.

Da gudu Salma ta faɗa ɗakin, ganin Waheeda ta kwanta.

“Ke, ke, ke! Me za ki yi? Ba dai bacci ba ko?”

Tura baki ta yi gaba.

“Rana ya faɗi, zan iya bacci, Yaya Salma. Ki duba lokaci mana.”

“Anya ba shaye-shaye kika je kika yi ba kuwa? A gidan uwar wa yanzu yamma ta yi? Karfe sha ɗaya ce fa, mandiya!”

Salma ta faɗa tana wurgawa Waheeda harara.

Ta ƙara da, “Dallah, tashi!”

Ko motsawa ba ta yi ba, ta ce, “Ai ba ki ga na soma baccin ba balle ki sako ni a gaba.”

“Ya dai fi, don ba ma bari zan yi ki yi ba,” ta faɗa tana zama a kan gadon, ta kunna musu Indian Hausa suka fara kallo.

Farkawa ya yi kwatsam, ya ga kansa a ɗakin Zannor. Sosai ya yi mamakin yadda aka yi ya ga kansa a ɗakin. Babu wani abu da ya zo masa. Ya mike zaune, yana jin kansa da jikinsa na masa nauyi, tamkar an aza masa dutse.

Da ƙyar ya shiga toilet ya yi wanka ya fito. Sai a yanzu ya ji ya fara dawowa hayyacinsa.

Bangaren Mamie ya je. Nan ya same ta ita da Zannor. Rungume ta ya yi yana sauke ajiyar zuciya. Shafa kansa da ke ɗauke da lallausan suma ta yi tana murmushi, ta ce,

“Barka da tashi, yarona BK.”

“Thanks, Mamie,” ya faɗa yana kai dubansa kan Zannor, wanda yake kallonsu, damuwa ƙarara shimfiɗe a kan fuskarsa.

“Zauna da kyau, ina da albishir ɗin da zan maka.”

“Albishir…” ya furta a hankali.

Ta ɗaga masa kai. Ya dubi Zannor ko zai ba shi haske, amma ya ɗage masa gira sama, alamar shi ma bai sani ba.

Wani envelope ta miƙa masa tana murmushi.

“Buɗe ka gani.”

A hankali ya soma buɗewa, kamar yana jin tsoron abin da zai gani a ciki.

Idanunsa ne suka sauka a kan abin da ke rubuce a cikin takardar. Da ɗan ƙarfi ya furta,

“Nooo way…”

Dariya ta yi ta ce, “Congratulations, my boy!”

“Mamie, wai da gaske kike? Allah Ya sa wannan ba mafarki ba ne.”

Shafa kansa ta yi tana faɗin, “Ba mafarki ba ne. Wannan ticket ɗin ka ne na trip to Paris. Sannan a yau da ƙarfe bakwai na dare jirgin ku zai tashi zuwa babban birnin Paris.”

Rungume ta ya yi da ƙarfi. Rungume ta yayi da ƙarfi. Yau ba ƙaramin farin ciki ta sanya sa ba. Cike da jin daɗi ya furta, 

“Thank you, Mamie. I love you so much.”

Zannor ido kawai ya zuba musu, yana kallon wasan da mahaifiyarsu take bugawa.

Murmushi ya kirkiro ya daura a fuskarsa, sannan ya matso ya dafa kafadar BK.

“Congrats, twin. Ina taya ka murna.”

Nan suka rungume juna cike da so da ƙauna.

“Zannor da sauran ma’aikata sun riga sun gama shirya maka duk wani abu da za ka buƙata. Abin da ya rage yanzu shi ne, nan da awa biyu mu raka ka airport.”

Cewar Mamie tana murmushi.

“Shikenan. Kafin lokacin ya cika, zan je in yi wa ƙawar nan tawa sallama.”

Fara’ar da ke kan fuskarta ta ɓace lokaci guda.

“Wace ce kawarka kuma? Yaushe har ka yi ƙawa ban sani ba?”

Shafa gashin kansa yayi cikin jin kunya, sannan ya furta 

“I mean, ƙawar Nini, Waheeda.”

“Ba ka da wannan lokacin. Daga baya ko Nini za ta sanar mata.”

Kamar dai ita, murmushin da ke kan fuskarsa ya kau. Ya ce

“But, Mamie…”

Dakatar da shi ta yi ta hanyar cewa

“Ka san ba na son musu ko?”

“Ki yi haƙuri.”

Daga haka suka bar zancen, suka ɗauko wani batu daban.

Follow me for more interesting chapters 🥰🤌🏻