MATUKAR INA RAYE

Matukar Ina Raye 18

by @mrsisham12

MATUKAR INA RAYE

(As Long as I’m Alive)

Writer — MRS ISHAM
*** WhatsApp

Page 18

Yau tun da gari ya waye, haka nan Waheeda ta farka ba ta da wani walwala. Hatta Ummah sai da ta fahimci hakan. Babu irin tambayar da ba ta yi mata ba, amma ta ce babu abin da yake damunta. Hakan ya sa Ummah ta rabu da ita, ta zuba mata ido kawai.

Har aka gama kosai, Salma suka fita. Waheeda ba ta leƙo tsakar gidan ba, tana nuƙe a ɗaki kamar sabuwar amarya.

Muryar Ummah ta ji tana kiran sunanta, tana cewa ta zo ta kai kosai gidan Mai Dawah, amma ta yi muƙui kamar ba ta cikin ɗakin. Ummah za ta sake magana ne, sai muryar Nini ta dakatar da ita.

“Ina kwana, Ummah. Na zo karɓar kosai.”

Ummah ta amsa mata cikin fara’a, sannan ta ƙara da cewa

“Kun ji shiru ko? Ƙawarki ce ta ƙi fitowa daga ɗaki tun dazun da kawo kosai ɗin, kuma babu yara a gidan, duk sun tafi makaranta.”

“To, shikenan.”

Jin muryar Nini ne ya sa Waheeda ta lallaba ta fito. Suna ganin juna suka saki murmushi.

“Me yake damun ki, ƙawata? Ko don Bestyn ki ya tafi ne yasa kika fara ciwo?”

Cikin rashin fahimtar inda zancen nata ya dosa, Waheeda ta ce:

“Ya tafi? Ina ya je to?”

Da mamaki Nini take kallonta.

“Wai ba ki sani ba? Jiya jirginsu ya tashi zuwa ƙasar Paris. Sai nan da shekara uku zuwa huɗu zai dawo. Kin san ɗan ƙwallo ne shi.”

“Shekara huɗu…”

Ta tsinci kanta da maimaitawa.

Nini ta gyada mata kai.

“Eh, haka dai na ji Daddy da Mamie suna faɗa jiya.”

Wani irin bala’in sanyi ya ratsa jikinta nan take. Ta ji hawayen da ba ta san na meye ba sun ciko mata ido. Ta yi ƙoƙarin shanye su, amma ta kasa, sai da suka zubo.

Ummah ta tsaya tana kallon ikon Allah, tana jinjina kai.

“Yanzu a madadin ki yi masa addu’a, Allah ya ba shi abin da ya je nema, shi ne za ki tsaya yin kuka, Auta?”

Ba ta kula da Ummah ba. Ta koma ɗakin da ta fito, ta kwanta a kan gado, sannan ta soma kuka mara sauti. Sosai take kuka, amma sam ba ta san takamammen abin da ya sa take kukan ba.


Shiru ya mamaye majalisar.

Kowa ya zuba mata ido, ganin ta yi shiru daidai inda BK ya bar ƙasar a cikin labarin. Sai da suka shafe kusan mintuna biyar babu wanda ya iya cewa komai, saboda yadda jikinsu ya yi matuƙar sanyi.

Duk yadda suka yi zato, ba haka ne abin ya kasance ba. Rabuwarsu ta zo musu a bazata. Na biyu kuma, kukan da mai ba su labarin take yi ya fi kashe musu jiki, har ya sa suka fara tambayar kansu. Menene ya faru a gaba da har ya sanya mai ba su labarin kuka?

Ko kaɗan ba su yi ƙoƙarin dakatar da ita ba. Duk da ba su san alaƙarta da mutanen cikin labarin ba, sun matuƙar tausaya mata. Domin su kansu, da labari kawai ake ba su, sai da suka ji tamkar su zubar da hawaye.

Sai da ta yi kuka sosai sannan ta saka gefen mayafinta ta share hawayen idanunta.

“Ku yi min afuwa, amma labari ya ƙare daga nan.”

Jiki a sanyaye, Baba ya ce,

“Labari bai ƙare ba, yarinyata. Alamu ma sun nuna yanzu ne aka zo tsakiyarsa, wajen da ya fi ko’ina taɓa zuciya. In ba haka ba, da ba ki yi kuka irin haka ba. Ki daure ki karasa mana, ko da a gurguje ne.”

Rufe fuskarta ta yi da duka tafukan hannunta, ta sauke ajiyar zuciya.

“Tabbas, a yanzu ne aka zo shafi mai taɓa zuciya a wannan labari, kuma mai tayar da hankali. Bayan tafiyar BK da watanni huɗu…”

Ci gaban labari…

Ummah ce take ba Labiba, wadda ta dawo gidan da zama, magungunanta, saboda yanzu jikinta ya tsananta. Laulayi yake damunta sosai, musamman da yanzu cikin yake neman watanni takwas.

Baba Karami na kan kujera ya buga ta gumi, ya zuba musu ido. Har da ɗan ramewa sai da ya yi saboda ciwon Labiba sosai ya tsaya masa a rai. Kafin daga bisani ya miƙe ya fita daga gidan.

Mama Sadiya na tuka tuwon dare, yayin da Mama Jamila kuma take share bakin ƙofar ɗakinta. Sai Ya Ado da ke gefe guda, shi da su Salma, suna hira.

Da gudu suka ga fitowarta. Ta tsuguna ta soma sheƙa amai kamar za ta amayo hanjin cikinta.

Duk da idanu suka bi ta da kallo, kafin Zuwairah da Salma su isa gare ta, suna mata sannu tare da dafa ta.

“Haka kawai Ummah ta ji kirjinta na bugawa da bala’in ƙarfi. Sake maganin da ke hannunta ta yi, suka zube a kan tabarma. Ta miƙe, hannunta na rawa, har ta kasa isa inda Waheeda take tsugunne tana amai. Sai Mama Jamila da ta jefar da tsintsiyar da ke hannunta ta nufe su. Ta ɗago Waheeda tsaye, ta kalli aman da ta yi a wajen, sannan ta ja hannunta ta buɗe mata idanu sosai. Nan take ta ji gabanta ya faɗi.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Me zan gani haka? Waheeda, ciki?! Waye ya yi miki ciki? Yau mun shiga uku!”

Maganar Mama Jamila ta sa duk wanda ke kusa da su ya daskare.

Ummah, wadda har yanzu hannunta ke rawa, ta kasa motsawa daga inda take. Kallanta ya koma kan Waheeda, sannan kan Mama Jamila, kamar tana ƙoƙarin fahimtar abin da kunnenta suka ji.

“Me kika ce?” ta tambaya cikin wata murya mai rauni.

Mama Jamila ta kasa amsa mata. Ita kanta fuskarta ta sauya, idanunta suka cika da mamaki da tashin hankali.

“Na ce… Waheeda ciki gare ta.”

“Ciki?”

Ya Ado ya maimaita kalmar a hankali, sannan ya miƙe tsaye daga inda yake zaune.

Salma da Zuwairah suka kalli juna cikin firgici. Babu ɗaya daga cikinsu da ya samu damar furta komai.

Waheeda kuwa tana tsaye tsakanin Mama Jamila da Salma, jikinta a sanyaye, fuskarta cike da ruɗani.

A hankali ta furta

“Ummah…”

Ummah da har yanzu idanunta ke kanta ta ce

“Zo nan, Waheeda.”

A hankali ta isa gabanta, domin ba wani ƙarfi take ji a jikinta ba.

“Mamana, don Allah ki karyata abin da Jamila take faɗa a kanki. Ki karyata cewa babu wani ciki da kike ɗauke da shi.”

Ta zuba mata ido na wasu daƙiƙu kafin ta ce:

“Na… na ɗauki ciki? Irin wanda Anty Labiba take da shi?”

Tambayar ta fito kamar wadda ba ta ma san ma’anar kalmar sosai ba.

Mama Jamila ta dafe kirjinta.

“Allah na gani, Maimuna, yarinyar nan ba ta ma san abin da muke magana a kai ba!”

“Ki yi min shiru, Jamila! Ina magana da ’yata ce.”

Ta faɗa a tsawace, nan take gidan ya yi shiru.

Ta dawo kan Waheeda ba tare da alamun wasa ba ta ce

“Faɗa min gaskiya. Kin taɓa kasancewa da wani namiji?”

“Ah-ah, Ummah, ai kin hana ni. Kin ce min kada in bari namiji ya riƙe hannuna, saboda zan ɗauki ciki.”

Salma cikin damuwa ta riƙe hannun Ummah.

“Don Allah ki kwantar da hankalinki. Ba lallai ya kasance ciki ba, Ummah. Waheeda har yanzu ƙarama r yarinya ce.”

Mama Sadiya ta yi saurin cewa

“To, in ba ciki ba, wannan aman na menene?”

Rai a ɓace Salma ta amsa mata

“Amai kaɗai ba ya tabbatar da ciki, Mama Sadiya.”

Ya Ado ya katse su.

“Hakane, Salma. Kuma tunda ita kanta ba ta san komai ba, gwaji ake buƙata kafin mu ce wani abu.”

Waheeda, wadda bacci ke cin idonta, sai bin bakunansu da kallo take yi, tana son ta fahimci abin da suke nufi da tana da ciki.

Ummah ta sulale ta zauna a ƙasa, domin ji ta yi kanta na jujjuyawa. Babu abin da take yi da ya wuce addu’a, tana roƙon Allah ya sa ba abin da kowa yake tunani ba ne.

Ummah da ƙyar ta iya cewa

“Salma, kira min Yayanku a waje.”

Tana gama faɗin haka ta riƙe hannun Waheeda suka shiga ɗaki.

Ba a daɗe ba, Baba Karami ya shigo gida, ga Salma a biye da shi. Yadda ya ga kowa tsaye jugum-jugum ya san akwai ƙaton damuwa. Hakan ya sa kai tsaye ya nufi ɗakin Ummah.

Nan ya same ta ta saka Waheeda a gaba tana kuka.

Hankali a tashe ya durƙusa a gabanta, yana jin kololuwar tashin hankali.

“Ummah… me yake faruwa? Me ya sa kike kuka? Wani ne ya mutu?”

Nuna masa Waheeda ta yi, wadda take bin su da dara-daran idanunta, kafin ta ce

“Wai Waheeda ake zargin tana ɗauke da juna biyu, Sadam.”

Wani irin faɗuwar gaba ya ji a sukwane. Ya dubi Waheeda da Ummah ke nuna masa.

“Mene? Ciki kuma, Ummah? Kuma wai Waheeda?”

Ya tambayeta cikin rawar murya.

Gyada masa kai ta yi tana ci gaba da kuka.

Tsananin daburcewa ya sa Baba Karami bai san lokacin da ya ce

“Wannan ba gaskiya ba ne, Ummah. Waheeda ɗin nan fa ƙaramar yarinya ce da za a ce tana da ciki.”

“Nima fatan da nake yi kenan. Ya sa zargi ne kawai. Ka ɗauke ta ku je asibiti a yi mata test.”

Shi dai har yanzu ya gaza yarda da abin da kunnuwansa suke ji game da ƙaramar kanwarsu. Maganar ta matuƙar ɗaga masa hankali.

Salma ce ta shigo ɗakin, jiki a sanyaye, ta same su suna magana a kan zuwa asibiti domin tabbatarwa.

A marairaice ta ce

“Ummah, ya kamata ku je tare. Ke ce mahaifiyarta, za ki fi samun kyakkyawan bayani daga bakin likita.”

Jinjina kai Baba Karami ya yi, ya amince da maganar Salma. Hakan ya sa suka shirya, har da ita Salma. Su huɗu kenan suka tafi.

Bayan wasu ’yan gwaje-gwaje da aka yi wa Waheeda, aka ce su jira a bakin ƙofa domin jiran sakamako.

Bayan kamar mintuna ashirin, sai ga likita ya leƙo yana kiran Ummah da Baba Karami. Cikin ofishin suka shiga, suka bar Waheeda da Salma a zaune.

Sai da ya gyara zaman gilashin idanunsa kafin ya yi ɗan gyaran murya, yana kare musu kallo. Ya ga damuwa karara a fuskokinsu.

“Ke ce mahaifiyarta?”

Kai kawai ta samu damar gyada masa.

“Na fahimta. Wannan kuma ɗan uwanta ne, saboda kamannin juna.”

Baba Karami bai kula da shi ba, saboda ba wannan jawabin suke son ji daga bakinsa ba. Ganin sun ƙi kulasa ne ya sake gyaran murya, ya ɗaga takardar sakamakon ya soma dubawa.

“Mun yi mata gwaji, mun gano yarinyarku tana ɗauke da ciki na watanni huɗu daidai a jikinta.”

A rikice Ummah ta dafe kirjinta saboda wani azababben bugawa da yake yi mata, ga tsoro da ya lullube ta lokaci guda. Ta nemi nutsuwarta ta rasa.

Babu abin da take furtawa da ya wuce

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…”

Tunda take a rayuwarta, wannan shi ne tashin hankali mafi girma da ta taɓa shaida da idanunta. Ya ya ta san za ta fuskanci wannan al’amari da ya riske su a lokacin da ba su shirya ba?

Nan ta ji wasu azababbun hawaye masu zafin gaske suna saukowa saman kumatunta.

“Ki yi haƙuri, ki yi haƙuri, Ummah. Wannan jarabawa ce Allah ya aiko mana.”

Baba Karami ya faɗa yana rungumeta, amma shi kansa dama kawai yake nema domin ya fashe da kuka. Abubuwan sun haɗu sun yi masa yawa. Tashin hankalin da yake ciki ya rasa ma da wanne zai fara ji.

Ga rashin lafiyar Labiba, wadda yanzu ko magana ba ta yi saboda tsananin azabar ciwon da take fama da shi. Ga kasuwarsa da ta tsaya masa cak, shagon nasa ma kayan sun ƙare, babu komai sai ’yan kalilan. Sannan ga wani abu da ya taso musu yau kwatsam na Waheeda. Ya rasa da wanne zai ji.

Sai da ta yi kuka sosai sannan ta ɗago daga jikin Baba Karami ta dubi likitan da kumburarrun idanunta.

“Yanzu likita, akwai yadda za a cire mata wannan cikin? Yarinyata ’yar ƙarama ce. Na yi imani Waheeda ba za ta iya haifar da abin da ke cikin ta ba.”

Likitan, wanda tausayi ya cika zuciyarsa a kansu, ya furzar da iska mai zafi kafin ya ce

“A zahiri, ciki a jikin yarinya ’yar shekara goma sha huɗu yana buƙatar kulawar likita sosai. Idan kuma aka yi ƙoƙarin cire shi, musamman idan bai kammala ba ko kuma aka yi hakan ta hanyar da ba ta da aminci, matsalolin da za su iya faruwa sun haɗa da zubar jini mai yawa, kamuwa da cuta, ragowar kayan ciki a mahaifa, da kuma rauni ko huda mahaifa. Gaskiya hakan babban haɗari ne ga rayuwarta.”

Baba Karami ya tambaya cikin rawar murya

“Me kake nufi da haka, likita?”


“Abin da nake nufi shi ne, tana cikin yanayin da zai iya zama mai haɗari idan aka samu zubar jini mai yawa, ko kuma cikin ya zube ba tare da kulawar asibiti ba. Haka kuma akwai yiwuwar kamuwa da mummunar cuta idan wani abu ya rage a mahaifarta bayan zubar cikin.”

“Kana nufin zan rasa ’yata ne fa, likita? Sadam, kana jin abin da yake faɗa ko?”

Ummah ta faɗa tana riƙe Baba Karami, jikinsa ya gama mutuwa.

Likitan ya yi saurin girgiza kai.

“Ba ina cewa za ta mutu ba ne. Amma ina gaya muku gaskiya ne domin ku fahimci muhimmancin lamarin. A yanzu, abin da ya fi muhimmanci shi ne kada a yi mata wani abu a gida, ko a ba ta wani magani ba tare da umarnin ƙwararren likita ba. Idan ta fara zubar da jini da yawa, ta suma, ko ta fara samun matsanancin ciwon ciki, ku gaggauta kawo ta asibiti.”

Baba Karami ya sunkuyar da kansa, hannunsa na rawa.

“Mun gode, likita. Tashi mu tafi, Ummah.”

Da ƙyar ya iya ɗaga Ummah, wadda take jin tamkar za ta mutu saboda nauyin da take ji a zuciyarta.

Tunda Salma ta ga yanayin da suka fito daga ofishin likitan, jikinta ya ƙara macewa. Ta san a wannan lokacin abin da suke tsoro ya riga ya tabbata. Da sauri ta nufe su, ta riƙe hannun Ummah suka zaunar da ita.

“Me ya sa, Waheeda? Me ya sa za ki aikata min haka? Duk irin wahalhalun da muke ciki ba kya gani, sai da kika sake jawo mana wani? Abin da za ki saka min kenan?”

Ummah ta faɗa tana rushewa da sabon kuka. Kasancewar babu kowa a waiting area ɗin, hakan ya sa babu wanda ya lura da halin da suke ciki.

Baba Karami ya durƙusa gaban Ummah, shi da Salma suna ta ba ta haƙuri, amma ta gagara tsayar da kukan da take yi. Hakan ya sa Waheeda da Salma su ma suka fara kuka.

Rai a ɓace ta ce

“Sadam, ka gaya wa ƙanwarka ta faɗa maka wanda ya aikata mata wannan ɗanyen aikin. In kuma ba haka ba, zan datse duk wata alaƙa tsakanina da ita.”

Hankali a tashe, Waheeda dake kuka ta zube a kan guiwowinta a gaban Ummah. Ta dafa ƙafafunta tana girgiza kai.

“Wallahi, Baba Karami, ni ba ni da ciki. Babu wanda ya riƙe min hannu.”

A fusace ya juyo ya sharara mata mari.

“Ɗan uban ki! Likita da duk gwaje-gwajen da aka yi miki duk ƙarya ne kenan, ki ke nufi?”

Zafin marin da ta ji ne ya sa ta ƙara sautin kukanta, tana dafe da kuncinta.

“Ka yarda da ni, Baba Karami. Babu wanda ya riƙe min hannuna.”

Babu irin tambayar da ba su yi mata ba a kan ta faɗa musu wanda ya yi mata ciki, amma ta tsaya kan kalamanta na cewa babu kowa. Fiye da awa suka shafe a wajen suna ta abu ɗaya, har suka gaji.

Salma, wadda ta fahimci sam Waheeda ba ta fahimci yadda ake samun ciki ba, ta riƙe hannayenta biyu tana kallon kyakkyawar fuskarta cike da tausayi.

“Ba riƙe hannu ke sa mace ta ɗauki ciki ba, Heedat. Ummah ta faɗa miki haka ne saboda gudun irin wannan rana. Ta faɗa miki haka ne domin ki nesanta kanki da duk wani namiji da ba muharraminki ba. Shin, ki tuna… kin taɓa kwanciya a katifa ɗaya da wani namiji? Kun cire kaya kin kwanta a jikinsa?”

Runtse idanu Ummah ta yi da ƙarfi. Ba ta taɓa tsammanin akwai ranar da za ta zo a yi wa ’ya’yanta irin wannan tambayar ba. Saboda irin tarbiyyar da take iya ƙoƙarinta ta ba su, sai ga shi wai yar autarta ta ce wannan abu ya faru da ita.

Shiru Waheeda ta yi, ta shiga tunani. Nan take abin da ya faru a waccan ranar ya fara dawowa mata ɗaya bayan ɗaya.

Jikinta ne ya hau rawa. Ta sa hannaye biyu ta toshe bakinta.

Ganin haka da suka yi, sai suka san ta tuna.

A kausashe Baba Karami ya ce

“Wanene shi?”

Dago jajayen idanunta ta yi ta dube shi, wasu sabbin hawaye na sake zubowa a kumatunta. Murya a karye ta furta

“Besty ne…”

Wani mugun kallo ya watsa mata.

“Wani shegen ne kuma Besty?”

Follow me for more interesting chapters 🥰🤌🏻