Chapter 9
by @maidambu41
Ji tayi ranta yana zafi, yarinyar da ba ruwanta. Juyawa tayi zata fita Mahmoud ya tsare hanya yana girgiza kai. "Maamah kiyi bincike kafin ki yanke hukunci, shi ya shigo gidan Mairoh ta gan shi a cikin dakinsu, me yazo yi? Me yake nima a dakin yan mata bayan ba mutane a gidan?" Kalaman Mahmoud sun yi tasiri a ran Maamah amma kuma yadda take kallon Adam bata jin har abada zai keta haddin Yaranta. Musamman Naanah Asma'u yarinyar da ko sunanta baya kira. Shiru tayi tana fadin. "Nasan wacece Hasiya nasan waye Adam ba shaidarshi zan bada ba amma da bai ga wani abu ba bai shigo gidan ba." Juyawa tayi ta shiga dakin tana kallon yadda take kwance, wani irin karaya tayi tana son Naanah Asma'u sama da sauran Yaranta. Bata taɓa yarinyar da rayuwarta ya hada hanya da kaddara ba sai ita. Bata son yin kuka a gaban Yaranta balle su ɗauka Naanah Asma'u ba zata kai labari ba ne.
Ɗakinta ta wuce, ban daki ta shige ta zauna tare da rufe ban ɗakin ta rufe kofar tana jin zuciyarta yana suya amma haka ta yi alwala ta fito ta ayi sallah. Har zuwa karfe shida Abba babba ya shigo ya samu gidan sai a hankali. Ya gama abinda zai yi ya wuce massalancin yana fitowa Mahmoud da Adam suka rufa mishi baya tare da Sadisu da wasu abubuwan da likitan da ya dubata. Suka shiga cikin gidan. A daren abinda aka haɗa shine monitor din yadda xai yi aiki tare da wani karamin inverter, sannan aka jona mata duk wani wireless din da zai taimaka mata wurin numfashi, tare da iskar jan numfashi.
"Duk wannan na menene Adamu?" Shafa kanshi yayi ya ce mishi. "Likita zai maka bayani Abba!" Ya juya ya bar gidan akwai abu a gabanshi amma shi yanzu abinda yake rokon Allah ya mishi yadda zata farka daga wannan dogar suman da tayi. Waje ya tsaya jikin motarshi yana jin kanshi babu chargi so yake ya zuki wiwi ko zai samu damar lissafin da ya dace. A can cikin gidan kuwa likitan ne ya zauna ya musu bayani ya ce musu. "A yadda muka fahimci abinda ya janyo mata nauyin numfashin shine an zarge mata wuya ko nace an shaƙe ta ko an danne numfashinta, ba don ya kawo ta da wuri ba da bamu san me zai faru ba. Amma ta farka in sha Allah zuwa nan da wani lokaci zata farka bakiɗaya. Amma yana da kyau ku kula da rayuwarta domin ciwon yaci karfinta ya kuma cinye kaso masu yawa ga karfinta." Shiru yayi, yana kallon yadda suka kafe shi da idanun. Amma wani abu da ya sani shine gargadin da Uban kowa ya mishi. Ya mike zai tafi Mahmoud ya ce mishi. "Likita baka gaya mana kome game da ciwon ba? Wani irin ciwo ne haka?" Kallon juna suka yi da Sadisu kafin ya ce mishi. " Ku sami wanda ya kawo ta zai muku bayani!"
. Sannan ya fita daga gidan ma bakiɗaya, duk suka fito sai Mahmoud da ya zo ya zauna a gabanta yana me rike hannunta cikin tsananin tausayi. "Naanah Asma'u!" Idanunta a rufe har lokacin bata wani san me yake faruwa ba.
Haka a bangaren Ya Almu waya suke da Mairoh ta gaya mishi abinda yake faruwa, hankalinsa ya tashi duk da azumin da za a tashi gobe. Haka ya ce mata yana hanya.
-- Har asibitin Adam ya mai da likitan sannan ya biya su abinda suka mishi. Duk wannan abinda ya faru sanadin wadancan yan iskan ne. La Coffee shop ya nufa ya je ya samu a can cartel ɗinsa. Manya jami'an tsaro ne da suka zo kwalbewa, fasa kwalba yayi duk suka juya suna kallonshi. Zuwa yayi ya ja kujera ya zauna yana kallonsu. "Zaki ba da wata manufa aka tura su gidanku ba. Kasan dai nan" wani irin abu yaji yana haura mishi kanshi kamar me aljanu haka ya dauki kofi daya a wurin ya damke sai da ya fasa da hannunsa. Ya sake kama wani ya fasa, ya kuma riko na uku zai fasa da sauri yaran bar din suka riko hannunsa. "Don Allah kayi hakuri!" "El Mayor!" Inji wani Bature ya kira sunansa daga can yana kallonshi. Ciwon lips ɗinsa yayi da yake rawa kamar sanyi yake ji ya nuna jami'in tsaron ya ce mishi. "Ka godewa Allah kakin jikinka yasa na kyale ka domin duk inda aka tafi wa kasata kake yiwa hidima, ban da haka sai na ci zarafinka!"
"El Mayor! Ka fara soyayya ne? Naji ance ia zama motar kwana kwana daga gidanku zuwa asibiti!" Fashewa da dariya suka yi bakiɗaya suka nuna shi da yatsa. Yana zuwa bai wata wata ba ya dauki kwalbar giyar da yake gaban baturen ya rosa mishi a kai. Sannan ya kara daukar wani ya fasa mishi. Dariya mutumin ya fara yana faɗin. " Haba yanzu na ji magana. Ga shi" ya ciro wata kwali babba kudi ne a cikinsu. Ya ce mishi. "Daga dongu zuwa dongu! Ina son duk rintsi ya shiga maƙotarku" Shiru yayi yana faɗin kuɗin. "Ba zan yi aikin ba!" Murmushi yayi ya kara wata kwalin kuɗin. Murmushi yayi ya kalli kwalin a karo na biyu ya gansu fresh da su sai wani kamshi suke ya zauna tare da cewa. " Ba xan yi ba! " Wani kwalin aka ƙara. Murmushi yayi tare da cewa. "Miye a cikin kwantanen?" Yadda ya zauna ya daura daya akan daya. "Akwai makamai! Da kuma sabin kayan sanyi" "ka kara wani abu domin nan wurin kasuwar bukata ce an jima wasu zasu zo su daura nasu akan wannan!" Yana maganar fadar haka ya mike zai fita.. "Amma kasan yadda kayan zai fita kuwa?"
"Ina da tirela uku na abincin agaji, ya juya yana d'aga kafadarshi. " Idan ya maka ka ƙara."
Shigowar wasu mutane uku, suka nufi La Mayor tare da mika mishi hannu, dakatar da su yayi ya nuna musu inda zasu zauna. Ya zuba musu ido da kyau kafin ya ce musu. "Cinikin naku ne ko na nawa?" Dariya suka tare da cewa. " Duk abinda kace shine namu, idan ma kaso biyar zaa bamu cikin dari zamu ɗauka kuma zamu yarda." "Ku bishi ya nuna muku kaya tare da Yarana!" "An gama ranka shi dade!" Suka nufi hanyar waje da da mutumin ya mika mishi hannu. "Idanuna yana kan ka!" Dariya yayi yana faɗin. "Tunda muka fara harkalla ka taɓa kamani da wani laifi ne?" "Nasan irin halittun da nake rayuwa da su." Ya fada yana ɗaukar goran ruwa ya sha.. "amma!" D'aga mishi hannu yayi tare da nuna mishi hanya. Bayan fitar baturen sai ga team ɗin jiya da suka shiga cikin gidansu.
"La Mayor!" Banza ya musu yana zaune a gaban Bar din idanunsa yana kan goran ruwan. "Kazo mana Ladan!" Fir yaki zuwa domin ya rigada da ya fusata. Tasowa manyan jami'an tsaron suka yi zuwa inda yaƙe. "Amma me yasa ba zaka zo ba sulhu muka zo nima fa." "Sulhu?" Ya tambaye shi a dan fusace, girgiza kai yayi ya ce mishi. "Eh Adam Ladan!" "Su bar nan kafin raina ya idda baci!" "Amma!" "Su fita!" Ba musu suka juya yana ɗaya cikin team ɗin ya ce.
"Wai dan ta'adda ake karewa?" Juyawa yayi ya ce musu. "Waye ya fadi haka?" Juyawa suka yi same gayen daren shekaranjiya ne.
.... "Ni ne nan! Akwai abinda zaka yi ne?" "Kai Mansur baka da hankali ne?" Murmushi gayen yayi ya ce mishi. "Ita wannan yarinya yaushe zaka kawo min ita?" Wani irin wuta ya dauke, a hankali ya sauka daga kujerar da yake ya cire rigar jikinsa ya dauke hannunsa da ya ji ciwo dazun ya nufe shi. Da sauri suka shiga tsakaninsu. "Adam Ladan kayi hakuri!" Kasa magana yayi yana sosa kanshi kafin ya ce mishi. "Ka gudu da kafarka da duk wnada ya yake naka!" Daga haka ya saka kai ya fita daga bar ɗin.
Kai tsaye gidan Hajiya ya nufa, har lokacin da gari ya dauka za a fara azumi jikinshi a mace yake. Bangarenshi ya shiga wanka yayi tare da alwala. Babban damuwarsa yarinyar ta farka. Tunda yayi sallah ya zauna a kujerar parlourn yana ta aiki ƙaramar laptop dinsa. Buga kofar parlourn aka yi ya mike yana miƙa, bude kofar yayi. Abba babba ya gani tsaye. " Sannu abba!" Ya furta a hankali. Yana me bashi hanya ya shiga cikin dakin. "Nazo tambayarka ne mai ya faru da Naanah Asma'u?" Shi ya manta ma bakiɗaya da yazo ya sami Matarshi ta shaƙe wuyarta. Shiru yayi kafin ya ce mishi."ita da matar gidanka ce!" "Ka gaya min me ya faru don Allah?" Cikin rashin damuwa da halin da Abba Babba zai shiga ya ce mishi "shaketa tayi"
Wani irin shiru Abba Babba yayi kafin ya juya kanshi cikin wani irin yanayi da karaya ya ce mishi. "Adamu!" Yasan rokonsa zai yi akan ya gaya mishi meke damunta. Dauke kai yayi yana kallon wani wurin na daban. "Meke damunta?" Dama yasan abinda zai faru kenan murmushi yayi a ransa. Sunkuyar da kai yayi ya ce mishi. "Kayi hakuri da abinda zai fito daga bakina, ina son na gaya maka cewa bata da lafiya sosai!" D'ago kai yayi yana kallon Abba babba, "Me ke damunta!" Shiru ne ya cika dakin kamar ba kowa sai karar fankar dakin da yake kara "kikiki" "Don Allah!" "Abba babba ciwon zuciya!" Damke hannunsa yayi cikin kidima tare da mikewa. "Tun yaushe?" Sai kuma ya nufi hanyar fita a matuƙar tsorace. "Zaka je ka gayawa Maamah ne? Idan kuma ita ta shiga wani hali fa? Wannan ba abin tashin hankali ba ne, ka fahimci ciwon amma makara an rigada an makara domin bai zama dole ciwon ya barta na tsawon shekaru ba." Juyawa yayi a matuƙar tsorace ya ce mishi. "Kamar ya? Kansa ce s zuciyar? Duk da bai yi karatu ba amma yasan yadda ake mutuwa a cutar da aka ce an kayyade maka lokaci ai ba ƙaramin al'amari bane." "Ba Cancer ba ne, ciwon zuciya ce wanda aka yi ta renonsa a matsayin cutar numfashi. Tun fil azal ya dace ayi jinyar ciwon yanzu kuwa ya cinye kaso mai girma na rayuwarta."
Gyad'a kai Abba Babba yake kamar kadangare, saboda yadda maganar take shigarsa. "Yanzu ba zata warke ba kenan?" Shiru Uban kowa yayi yana kallon wan mahaifinsa yadda yake zufa kamar wnada yake haɗiye garwashin wuta, tare da ruwan korawa ba barkono. "Idan zata warke sai dai anyi mata dashen wani zuciyar, wanda yake kirjinta ya kusan tashi aiki!" Zama Abba yayi a kasa dabas, yau ya ga ranar ilimi. Yau ya ga ranar amfanin arziki. D'ago idanunsa yayi da suka yi jajjur ya motsa busashen lebbansa ya ce mishi. "Kuɗin aikin zai kai nawa?" Ya tambaya duk da yasan bai ajiye ba, kuma bai bawa wani ajiya ba. " Zai kai miliyan goma na CFA!" Haɗiye yawun bakinsa yayi kifa kanshi a tafin hannunsa. Yafi minti goma sha biyar a haka kafin ya mike yana fadin." Allah ya kyauta." Daga haka ya bar parlourn ya wuce bangarensa. A hankali yake takawa har zuwa dakin Maamah. Ya zauna a bakin gadon yana kallon yadda kome yake zuwa mishi da tsanani ga Hajiya ga Naanah Asma'u.
Da yake Maamah tana wurin Naanah Asma'u, har zuwa lokacin da za ayi sahur tazo ta haɗa musu abin sahur ta haɗa na Uban kowa aka kai mishi. Can wurin minti talatin sai gashi ya zo, ya je kanta ya ga har lokacin da taimakon monitor din take numfashi, hannunsa riƙe da Mug na tea. Sai da ya jima sannan ya bar dakin. A parlourn ya samu Maamah. Sahur gaishe ta yayi ya fita daga bangaren.
Bayan fitarshi Abba babba ya shiga dakin ya zauna a gefen Mairoh tana kallonshi. "Abba kuka kake?" Ganin yadda yake share kwalla da bayan hannunsa. "A'a tausayin baiwar Allah nan nake da take cikin ƙaddaran rayuwa nake." "Allah ya kawo mata mafita;" inji Mairoh,
***
Wai su waye family Ladan Tuareg. Kabilar turawa sun wanzu na tsawon karnuka masu yawan gaske. Kabilu ne da suka bazama a yankin arewacin masu gabashin Afirka, inda suka hada Nijar, Aljeria, maroko, Libya, da sauran yankin da suke da iyaka da ƙasashen Larabawa. Ana kiransu African berber, yayinda wasu suke kiransu da people of blue shade, Tuareg sun kasance alumma da suke rayuwa a yankin da yafi sahara, shi yasa suke dayawa a yankin arewacin nijar.
Tuaregs suna da wata shigar da suke da ita na yadi ruwan shudi wato indigo, mazansu suna saka kayan tare da farin rawani,a takaice mu muna kiransu da Buzaye. Toureg sun kaso gida biyu akwai farare masu sirki da larabawa, ka akwai babakensu da suka kasance asalin yaƙin kudancin Nijar zuwa arewacin Nijeriya, wasu suna da alaƙa mai girman al'ummar Katsina zuwa Katsinar maradi. A gefen arewa masu gabashin Najeriya kuma wasunsu suna da alaƙa da wasu mutanen yankin Borno.
.. Tuareg al'umma ce da take rayuwa kamar Fulani masu yawo a dazuzzuka, amma su a yankin sahara suke yawo saboda kiwon raƙumasu. Allah ya albarkaci rayuwarsu da hidimar rakumai, mutane ne masu karfin tattalin arziki musamman rakuma. Ana kiransu maabota raƙuma. Akwai wata al'adar da suka gadawar kansu, al'umma ce bata yarda da kowa ba sai alummarta. Suna da wata dabi'a tun yarinya tana shekaru bakwai ake zaɓar mata mijin da zata zauna da shi. Koda kuwa bata sonsa zata zauna da shi a haka. Kuma a haka suke rayuwa a cikin wannan tsarin. Zamani ya tafi yadda ba a zata duniya ta cigaba mutanen da suke rayuwa a yankunan Sahara sun watsu a birni, sune a wasu manyan wuraren aikin gwamnati. Suna da dama can ilimin addinin Musulunci domin suma suna cikin mutanen da Muslunci ya shigar musu tunda dama mutane ne masu yawo a cikin sahara. Basu yarda da auren wata kabila domin basu cika yarda da a kawo musu wata ƙabila cikinsu. Shi yasa basu cika yawa a cikin al'umma ba. Suke iya yankin da suka fi yawa. Ba kamar Fulani da suka kasance a ko'ina ba. Wannan dabi'arsu ya saka su rasa wasu abubuwan dayawa daga cikin har da rashin yaɗuwar al'ummarsu. A yau al'umma Tuaregs sun kasance manyan mutane a yankin arewacin nijar zuwa sauran kasashen.
***
Alhaji Mustapha Ladan, ya kasance Tuareg wanda ya haɗa jini da babban gidan sarauta Tuareg da suke Arewacin Morocco, sai dai rigimar rayuwa tasa ya dawo kasar Nijar duk da dama can Mahaifiyarshi yar yankin Timia, amma shi ya zaɓi ya dawo garin Agadaz da iyalinsa wato Hajiya Naanah Asma'u, wacce ta kasance ya ce ga kawunsa a anan Timia. Alhaji Mustapha Ladan mutum ne da yake da daraja, domin tun da Kuruciyarshi ya dawo nijar. Ya cigaba da rayuwa a gaban Kawunsa da dangin mahaifiyarshi.
Tunda ya dawo Timia bai ƙara waiwayen Morocco ba, ya rungume dangin mahaifiyarshi, Alhaji Mustapha Ladan, mutane da Allah ya mishi baiwa da kasuwanci duk da yazo Timia da rakumai masu yawan gaske, kusan garke hudu nashi na kanshi....