Wutar ƙaiƙayi

Chapter 5

by @sadiyaabdulrazak954

PAGE 5


  Na ɗaga kiran da sallama, na ji muryar mace ce ta amsa, muka gaisa na ce"Ban gane mai magana ba. Kuma a ina kika samu wannan layin?"

Cike da yauƙi ta ce"Dama bai zama lallai ki gane ni ba, don ba ki san ni ba, kuma na tabbata za ki san ni, nan ba da jimawa ba".

"Wane ne ya ba ki wannan layin!?" Na sake tambayarta a tsawace.

Ta ce"Masoyina Salman, shi ne ya yi mini kyautar layinki".

Na yi wata dariyar takaici, na ce"To ke wannan har wani abun fariya ne? Idan ban da tsiya nawa ne layi da ba zai mallaka miki naki sabo ba? Wannan ma ai ya raina miki hankali".

Ta ce"Kin ga shashasha! To ke ba ki san isar ce ta saka ya ɗauki layinki ya ba ni ba? Ni ce na ce masa shi nake so, kuma ya ɗauka ya bani, wannan kaɗai ya isa ya nuna miki matsayina a wajen shi".

A fusace na ce"Matsayin banza! Ai yana kallon matsayin naki ya take ya bar ki a titi, ya dinga zarya a gidanmu babu dare babu rana, sannan ya biya sadaki ya kawo ni gidansa ya rufe, ai kuwa ni ya bawa babban matsayi ba ke banza karuwar titi ba!".

Da alama ranta ya ɓaci, don daga muryarta na gane ta ce"Ni kike cewa karuwar titi? Ni?"

Na ce"An faɗa miki ɗin, wace ce ke? Kuma me za ki iya? Asararru wanda ba ku da aiki sai bin mazajen mutane".

Ta yi wata dariya kafin ta ce"Sai kin ji ni". 

Ta kashe wayar, na ja kujera na zauna a kitchen ɗin, na yi shiru ina tunanin kalar mijin da nake aure, na ji zafin wannan abin da ya yi mini sosai, a kan me zai ɗauki layina ya ba wa wata? Na share hawayen da ya sakko mini, na tace taliyata na zuba na koma falo, tura abincin kawai nake yi, zuciyata ta cunkushe.

A ranar na yi sa'a ya kwana a gida, bayan mun gama cin abincin dare, na kalle shi na ce"Ina da magana da kai".

Ya ce"Ina jinki".

Na ce"Wannan layin nawa da ka ce ya ɓata yana ina?"

Ya ce"Ai na ce miki ya ɓata, to ta ya zan san inda yake?"

Na sauke numfashi na ce"Ni ban yarda ya ɓata ba".

Ya ce"To sai ki nemo shi".

Na ce"Wacce ka ba wa kyautarsa ta kira ni ɗazu, ashe har wata tana da matsayin da za ta juya ka? Har ta ce maka ka ba ta layin wayar da nake amfani da shi, kuma ka ɗauka ka ba ta ɗin? Sannan kuma ka ba ta lambata? Wannan ai cin fuska ne, da kuma nunawa duniya ni ba komai ba ce a wajenka".

"Ni fa ban ba wa kowa layin nan ba, wallahi neman shi na yi na rasa, wa ta ce miki sunanta?" Ya ƙarasa da tambayata, sam babu wata damuwa a tare da shi.

Na nuna masa, ya ɗauki wayarsa ya fara shigar da lambar, sai sunana ya bayyana, ya kira, ta ɗauka nan takr ta ambaci sunan shi, suka gaisa har suka shiga hira, amma ban ji ya tambaye ta inda ta samu layin nan ba, ya kashe ya kalle ni ya ce"Wannan wata yarinya ce, ƴar Niger, ƙila ko satar mini layin ta yi, ki manta kawai, ba ga wani ba kin fara amfani da shi?"

Takaici ya kama ni, na ce"To ta yaya har za ta satar maka layi? Abin da ƙila a aljihunka yake? Kenan buduruwarka ce".

"Ki bar zancen nan haka Zinatu kin ji, ta shi mu je gida mu gaisa da su Mama". Ya faɗa yana tashi ya ɗauki mukullin mota, ni ma ina son zuwan, don haka kawai na haƙura da zancen na bi shi muka tafi.

Muka je aka gaisa aka yi raha aka yi dariya, don Salman yana da surutu sosai, kuma sakewa yake yi kamar ba gidan surukansa ba, ya yi ta zuba zance. Sai tara da rabi muka baro gidan, a hanya na tuna da rana na ce ya siyo mini agwaluma, don tun da na samu cikin nan nakan saka shi ya siyo mini, sai ya kawo mini ita fal leda na yi kwanaki ina sha. Na ce"Ni mantawa ka yi ba ka siyo mini agwalumar ba?"

Ya ce"E na manta".

Na ce"To mu je ka siya min".

Ya ce"Ai ba hanyarmu ba ce, kuma yanzu ma sun tashi".

Na ɓata rai na ce"To mangwaro".

Ya yi ƴar dariya ya ce"Zinatu dare fa ya yi, Allah Ya kai mu gobe kawai".

Na ce"Allah sai ka samo mini ɗaya daga cikin waɗan nan a daren nan".

Ya yi shiru, har muka ƙarasa ƙofar gida, ya buɗe mota ya fita, ni kuma na coge na ƙi ko motsi. Ya zo ya buɗe gefena ya ce"Ki fito mana".

Na ce"Ni fa Allah ba zan fito ba, kawai mu je ka siyo mini".

Da alama ya ƙosa, ya ce"Zan rufe ki a motar nan fa na yi tafiyata".

Na yi kamar ban ji shi ba, don sosai na ji ina son shan agwalumar.

Ina kallo ya saka mukulli ya rufe ni a motar, ya buɗe gidan ya shige, ya saka sakata, na yi zaton gwada ni yake yi, yanzu zai fito ya ba ni haƙuri ya lallaɓa ni na shiga, amma abun mamaki sai na ji shiru, tun ina kallon ƙofar da jiran na ji ta motsa har na saddaƙar ba zai fito ba, ina nan zaune zuciyata cike da ƙunci har ƙarfe goma da minti arba'in ta yi, wato dai sha ɗaya ta kusa yi, hawaye ya zubo min, na ɗauki wayata na kira shi, ya ƙi ɗauka, barikin ya yi tsit sai haushin karnuka, tsoro ya kama ni, na fara kuka, ƙarshe sai maƙociyata na kira a waya, na faɗa mata, ta saka mijinta ya kira shi, sannan ya fito ya buɗe yana murtsika ido yake cewa"Yo ni ba kin ce ba za ki fito ba? Ai da kin bari gobe idan ma su agwaluma sun fito sai na zo mu je a samo miki, wallahi har bacci ya ɗauke ni".

Takaici ya hana ni cewa komai, ina shirin fitowa ya ce"To duba kujerar baya akwai leda ki ɗakko".

Na juya, na ga leda, ina janyowa na ga agwalumar ce a ciki, na harare shi, na fita, ya yi dariya ya ɗakko ya biyo ni da ita, yana cewa"Tun da tana fa na siyo, kawai dai gwada ki na so yi, don na ga ƙarshe yadda za a yi, to ashe ba za ki iya kwanan motar ba".

Ni dai ƙala ban ce masa ba, na je na kwanta, wai ni irin shagwaɓar nan na so yi masa, ashe shi ba za a yi haka da shi ba, na ɗauki alƙawarin ba zan sake yi masa hakan ba, a yadda na gane halinsa tsaf zai bar ni na kwana a motar, don shi ya firgita ni ba komai ba ne a wajensa.

 Akwai ranar da daddare bayan sallar isha'i, ina zaune na ji an banko ƙofar gidan da ƙarfi, gabana ya faɗi, na yi tsuru-tsuru, ban saka sakata ba saboda ya yi mini waya ya ce zai dawo gidan yanzu, jin shiru ba a sake wani motsi ba sai na tashi na leƙa a tsorace, da yake tsakar gidan da hasken wutar nefa, ina kallon ƙofar zauren na hango bindiga an zuro ta amma ban ga mutum ba, ƙirjina ya yi wata irin bugawa ga ƙaramin ciki, na koma ɗaki a guje na rufe ƙofa, ina karanto duk addu'ar da ta zo bakina, babu jimawa kuma na ji dariyarsa yana ta ƙyaƙyatawa, ya zo yana buga ƙofar ya ce"Ke matsoraciya ce ashe, to zo ki buɗe mini".

Na sauke ajiyar zuciya, na je na buɗe ina ta fushi, shi kuma ya yi ta dariya.

 Haka rayuwar ta cigaba da tafiya, Salman bai fasa halinsa ba, dob ban fasa duba wayarsa ba, wani sabon salo kuma da nake fuskanta shi ne yawan kirana da ƴan matansa suke yi, suna zagina, har da ma su iƙirarin sai sun kashe ni, wasu kuma su ce sai auren ya mutu, abun yana ɓata mini rai, ni dai gani nake kamar shi ne yake ba su lambata, ko kuma dai ba su wayar tashi yake yi har suke samun damar ɗaukar lambar tawa, duk wacce ta zage ni ramawa nake, mu yi kaca-kaca da su, ita kuma wannan da ya ba wa layin nawa shiru ba ta sake kirana ba, har na manta da ita, na zata dama kurari kawai take yi mini, hmmm ashe zuwa ta yi ta yo mini shiri, nan gaba za ku ji illar da ta yi mini.

Haka rayuwar gidana ta cigaba da gudana, tsakanina da Salman yau fari gobe baƙi, mu yi faɗa mu yi daɗi, abun ya kai yanzu idan ya tafin nan bai waiwayo ni ba, ba ya ma ɗaga wayata, ƙarshe ma sai yake saka ni a blacklist, na yi ta kira ba ta shiga, wani lokacin na shiga damuwa, wani lokacin kuma na yi gefe da shi, na yi ta harkokin kasuwancina, don kullum kasuwata buɗewa take yi, Alhamdulillah! Musamman da nake ba wa ƴan albashi bashin kaya, kamar su man gyaɗa, magi, suga da sauransu.

Lokacin da na shiga watan haihuwata, mun gama tanadin komai na haihuwar, ya ba ni kuɗi na sayi duk wani abu da za a buƙata, hatta kuɗin zuwa asibiti suna nan a ajiye, lokaci kawai ake jira.