Wutar ƙaiƙayi

Chapter 6

by @sadiyaabdulrazak954

PAGE 6


     Dab da zan haihu ya zo a ƙarshen wata, lokacin da nakan je Jigawa gaida mahaifiyarsa ba, muna zaune muna fira nake ce masa "Ranar yaushe ya kamata na tafi Jigawa, Asabar ko Lahadi?"

Ya yi mini kallon mamaki ya ce"To a can za ki haihu kenan?"

Na ɗan ɓata rai na ce"Kamar ya".

Ya ce"To Zinatu kina kallon yadda kika zama kamar buhun sumunti ta ina za ki fara barin gari? Watan haihuwarki ne fa, ki yi haƙuri dai sai bayan kin haihu".

Na ce"Ni fa babu abin da cikin nan zai hana ni, abin da ba kwana zan yi ba, a ranar zan dawo?"

Ya ce"Ni dai da kin haƙura".

Na ce"To da sharaɗi, indai ba zan je ba, to kai sai ka je, ka je ka gaishe ta, ka kai mata kayan da na saba kai mata".

Ya ce"Kai! Zan je, amma gaskiya ba dai a watan nan ba".

Na rasa me yasa ba ya son zuwa garinsu, hakan ba ya yi mini daɗi sam, na ce"To don girman Allah ka bar ni na je, na saba zuwa idan ban je ba Umma ba za ta ji daɗi ba".

Zai yi magana na katse shi da faɗin"Don Allah kar ka hana ni".

Ya ce"To shikenan Allah Ya kaimu Lahadin sai ki je".

Na yi murmushin jin daɗi, ina yi masa godiya.

Ranar da na je Jigawa, ita ma Umma har mamaki ta yi, bayan mun gaisa na jaɓe waje ɗaya ina shan furar da ta dama mini, ta zauna ta saka ni a gaba tana ta matsa mini ƙafafu kamar ba surukurta ba, take cewa"Haba ƴata, kin yi nauyin ma ba za ki haƙura ki huta ba? Ni har ina cewa sai mun zo barka? Sam ban tsammaci zuwanki ba".

Na yi murmushi na ce"Ai Umma babu komai, tun da zan iya, na saba zuwa idan ban zo na ganki ba, ba zan ji daɗi ba".

Ta ce"Allah sarki da kin yi zamanki wallahi babu komai, Allah Ya sauke ki lafiya, Allah Ya miki albarka".

Haka na wuni Umma tana nan-nan da ni, a gaskiya na yi dacen suruka, matar tana so na sosai, sam ba ta ɗauki duniya a bakin komai ba, ta yi ta yi mini nasihar zama da miji, haka za ta yi ta faɗa mini na dinga haƙuri, duk da ban taɓa faɗa mata Salman ya yi mini wani abu ba. Ina yin sallar la'asar na kama hanyar Kano.

Da na dawo bayan kwana biyu na je gida na taho da ƙanwata, saboda yanayin aikin shi na kwana, kar naƙuda ta taso mini cikin dare babu kowa. EDD na biyu ga wata ya nuna, a ranar kuwa tun safe nake zuba ido na ji ta inda ciwo zai fara, na ji shiru, har dare ya yi na kwanta, don ranar yana aikin kwana, da yake washegarin ranar za a yi zaɓe, ƙarfe sha biyu na dare ya kira ni a waya, na ɗaga cike da bacci, ya ce"To ya ake ciki, kin sauka lafiya?"

Na yi dariya ƴar dariya na ce"Kuma sai ka ce faɗar Allah? Don an ce yau ne kawai sai ka yarda dole yau ɗin ne? Ni ƙalau nake, don bacci ma nake yi ka tashe ni".

Ya yi dariya ya ce"Ma sha Allah! To ki koma baccinki".

Abun mamaki yana kashe wayar, sai na ji kamar wayar nan ce ta saukar mini da ciwo, nan take marata ta fara ciwo, to dama ciwon mara ya zame mini jiki tun ina buduruwa, saboda haka na share ban kira shi na faɗa masa ba, na kwana a haka. 

Da sassafe na tafi gidan Hajiya Hadiza na faɗa mata yadda nake ji, ta raka ni gidan wata mata nurse a nan cikin barikin, ta duba ni, ta ce haihuwa ce, amma da saura, zan iya kai wa yamma kafin na haihu, ta ce idan na koma gida kar na kwanta, na yi aikace-aikace, ko kuma na yi zagaye, na kwaso na koma gida, na ci abin da ƙanwata ta girka, nan fa na zage kamar wacce na sha ƙwayar ƙarfi, na kwaso kayan wanki wasu ma a wanke suke, na shiga yi babu ji babu gani, na gama na fito da duka kayan kitchen ɗina, na wanke su tas na sake jera su, na dinga neman aiki, duk wai saboda na haihu da wuri, ciwon yana ta gaba-gaba, can bayan la'asar na yi wani tunani, na ga ya kamata na tafi kasuwa, don na rage yawan kuɗin da ya ba ni na zuwa asibiti, na ƙaro ko leshi ne na ƙara a kayana na fitar suna, tun da nurse ce za ta karɓi haihuwar a gida, ai kuwa na tashi na tafi, har na je titi sai aka ce mini ai babu abun hawa sakamakon zaɓe da ake yi, daga titin nan da ƙyar nake jan ƙafa kafin na ƙarasa gida, saboda yadda ciwon yake ƙara gaba, haka na dawo na cigaba da zagaye tsakar gida, har dare ya yi, na sake kiran nurse ɗin ta zo ta duba ni, ta ce saura kaɗan, bari ta je ta dawo.

Ina tsakar gida ina zagaye, ƙanwata tana kitchen tana yin girkin dare, muka ji an banko ƙofar gidan da ƙarfe, sannan aka fara wani ihu da hargagi mai ban tsoro, gabana ya faɗi, ina son zubawa da gudu na kasa, zaburar da na yi ta saka marata riƙewa ƙyam, na dafeta ina jan ƙafa don ceton kaina, kwatsam na ji dariyar Salman yana ƙyaƙyatawa, ƙanwata tana taya shi, ashe shi ne ya tsorata ni, duk da ya san halin da nake ciki na naƙuda, shi fa sam babu ruwan shi indai shaƙiyancinsa ya motsa ko a ina sai ya yi shi, na ɓata rai na koma ɗaki, ya biyo ni yana ba ni haƙuri, sannan ya yi mini sannu.

Babu jimawa kuma ciwon ya yi tsanani, ya karɓi wayar ya sake kiranta, tana zuwa ta ce abun ya zo, Hajiya Hadiza tana tsaye a kaina, nurse tana taimaka mini, yayinda Salman yake falo yana kwasar girkinsa Allah Ya sauke ni lafiya, na haifi ƴata mace a ɗakina, suka gyara ni tsaf, suka gyara ƴar, sannan suka kai masa ita, ya yi farinciki sosai har sai da na yi mamaki, don ban san yana son ƴaƴa har haka ba, duk da yana da wani ɗan kafin wannan amma yadda ya nuna murnarsa sai ka ce ba a taɓa yi masa haihuwa ba. 

Hajiya Hadiza ba ta bar ni ba, sai da ta dafa ruwa na yi wanka, ta gyara ɗakin tsaf ta wanke kayan jinin nan fess sannan ta tabbatar mun kwanta ni da Baby sannan ta tafi.

Washegari ƴan'uwana suka dinga zuwa ganin ƴa, an yanke shawarar sai an yi suna sannan na tafi gida wankan jego. Nan fa na ga kulawa a wajen Salman a kwananin nan, komai ya rakito ya kawo mini, kullum sai ya jibgo naman kai an dafa mini, sannan da daddare ya siyo gasasshen nama, ban da wanda zai haɗo a cefane wanda za a yi girki da shi, ya sakawa yarinyar suna Aisha, muna ce mata Sabreen.

Ya ƙara mini kuɗi, na bayar aka ƙarowa Sabreen kaya masu kyau da tsada, iyayena sun yi ƙoƙari sosai wajen haɗa mini kayan barka, don Baba ma ban da kayan sakawarmu ni da ƴar har zannuwan gado ya ƙara mini, sannan aka yi mini gara. Haka ma dangin Salman da suka zo ana gobe suna da abun arziƙi, kayan barka niƙi-niƙi, yajin daddawa har da maɗi. Salman shinkafa buhu biyu ya kawo ta girkin suna, ya siyo rago da tunkiya narka-narka, sai dai fa ƙarshe iya ragon aka yanka, don akwai wasu ƴan'uwana da muke takun saƙa da su, su ne suka zuga shi a kan ɗaya ma ya isa, a ka bar tunkiyar, wanda kuma ƙarshe bayan an gama taron sunan suka ba ta shinkafa ta ci ta mutu.

Hajiya Hadiza ta yi mini kalanda mai ɗauke da hoton Sabreen, shi ma Salman ya yo tasa sa yawa, aka yi rabo a wadace, an yi taron suna sosai kamar biki, Salman ya ɗakko wani shahararren mai DJ, wanda a lokacin ɗakko shi sai wane da wane, mai DJ ya kwaso karuwai aka baje aka raƙashe, ƴan barikinmu sun yi mini kara sosai, don ni ba ni da wuyar sabo, musamman da nake harkar maganin mata suna siya sosai. Haka aka gama taron suna, kowa ya watse, bayan kwana biyu na koma gida wanka.

 Mama ta kula da ni sosai, wanka ake yi mini mai kyau, Salman idan zai zo ganinmu ba ya gajiya da ruƙo ledoji, haka zai zauna ya ci abinci a yi ta fira da shi. Satina uku a gida, watarana ina kwance na ga an kira ni da wannan lambar tawa, wanda ni har ma na manta, na tashi zaune na ɗaga cike da masifa na ce"Baiwar Allah lafiya kike sake kirana?"

A sanyaye ta ce"Lafiya ƙalau, Maman Aisha ya kike?"

Sai na ji jikina ya yi wani sanyi ƙalau, kamar an jefe kaza da wuƙa, na kasa cewa komai. Ta ce"Ni fa kiranki na yi mu gaisa, ba da wata manufa ba, wallahi ni kawai son ki nake yi, ina so mu dinga gaisuwar mutunci ne".

Sai na ji muryarta ta yi mini daɗi, kawai na nemi duk wani tanadin rashin mutuncina na rasa, na ce mata"To babu damuwa na gode".

Ta ce"Yawwa, gobe zan kira ki mu sha fira kin ji?"

Na ce"To".

Sai ta kashe, na sauke wayar na bi lambar da kallo, ina mamakin kaina.

Tun daga wannan ranar fa sai ta fara kirana a waya, na saki jiki mu sha fira, kamar mun san juna a zahiri. Daga baya kuma sai ta fara nuna mini tana kishin mijina, akwai ranar da ta ce mini ita fa a duniya ba ta da mijin aure sai Salman, kuma ba ta da ra'ayin zama da kishiya, saboda haka ko dai na rabu da shi ko kuma ta yi ajalina.

Haka kullum za ta kira ni tana yi mini gargaɗi, da maganganu na tsoratarwa, za ta kashe ni, za ta yi ajalina, za ta nakasa ni, za ta haukata ni, za ta yi mini abin da kare ma ba zai sake shinshina ni ba, babban abin da yake damuna shi ne, indai ta kira ba na iya ƙin ɗaga kiran, kuma na kasa faɗawa kowa abin da yake faruwa, kullum cikin fargaba da tunani nake.