Chapter 7
PAGE 7
A haka na yi arba'in, na koma gidana jikina duka babu daɗi, Salman ya nuna mini ya yi kewata don ya ji daɗin dawowata sosai, yana nunawa Sabreen so sosai, shi kansa ya lura da yanayina na rashin walwala amma da na ce masa babu komai haka ya rabu da ni, satina ɗaya da komawa na shirya na tafi Jigawa gaida Ummansa, ta ji daɗin zuwana kamar yadda ta saba, kwana biyu zan yi, tun a ranar da na je ta sa ake yo mata siyayya ta kayan haɗin maganin mata, ta yi mini daka da gumba, da ta ba ni a kunyace na karɓa, ta yi murmushi ta ce"Zinatu kin san fa halin mazan zamanin yanzu, sai kana gyarawa, musamman idan ka fara haihuwa, ke ƴata ce duk yadda zan yi wa ƴata haka zan yi miki, saboda haka ki ma daina jin kunya, Allah Ya ƙara muku zaman lafiya".
Na amsa da amin, na yi mata godiya, ta yi mini tsarabar abubuwan amfanin girki kamar yadda ta saba, na tafi ina jin daɗin dacen suruku.
Satina biyu da komawa wataran na tashi da ciwon kai, kwana biyu ina shan magani abun babu sauƙi, daga nan sai na fara zazzaɓi, ga kasala da take damuna, jikina kullum kamar an yi mini duka, ga shi shi ma Salman har ya gama marmarina ya koma gidan jiya, sai ya tafi aikinsa ya bar ni da Sabreen, girki ma ba kullum nake yi ba, sai dai na lallaɓa na je gidan Hajiya Hadiza na ci, haka dai har zazzaɓi ya kwantar da ni, a dole aka kai ni asibiti, aka saka mini ruwa kwanana ɗaya aka sallame ni bayan an sayi magunguna, to fa daga nan sai jikin yake ta gaba-gaba, a je asibitin a dawo, ga ɗanyen goyo wanda ba ka saba ba, duk sai na rame na yi zuru-zuru.
An kwana biyu rabon da wannan ƴar Niger ɗin ta kira ni, yau da safe ina kwance Sabreen ta yi bacci ni ma ina hutawa da zazzaɓi a jikina, sai ga kiranta, na ji gabana ya faɗi, take wani ƙunci ya zo zuciyata, na rasa nutsuwata, yau na ji fargabar ɗaga wayarta, amma kuma sai na kasa ƙin ɗagawar, na ɗaga a sanyaye ban ce komai ba, ta ce"Hello kina ji na!?"
Na tashi zaune ina cewa"E" kamar an yi mini dole.
Ta ce"Zinatu kike ko wa?"
Na tsinci kaina da faɗin"E Zinatu".
Ta ce"Na yi miki gargaɗi a kan masoyina kin ƙi ji, ni kaɗai ce ya kamata na zama mace a gidan auren Salman, tun da kin ce za ki iya da ni mu je zuwa, na rantse da Allah indai ni haifaffiyar ƴar Niger ce sai na ga bayanki, idan kina son rayuwa to ki tattara wannan ƴar magen da kika haifa ki koma gidan ubanki! Ki rabu da auren Salman ko ki mutu, don kuwa kwana uku na ba ki, muddin na ji kina gidan wallahi sai na saka rayuwarki a kwale-kwale".
Ba ta jira cewata ba ta kashe wayar, zuciyata ta dinga bugawa, dama sai na kasa ajiye wayar na fara kuka, na daɗe a haka kafin tashin ƴata daga bacci ya katse ni, na ɗauke ta ina jin tausayinta, don har na fara hasashen yadda za ta gudanar da rayuwar maraici.
A hankali abun ya dinga gaba, ranar da Mama ta zo duba ni ta ga jikin ta ce gaskiya gida zan koma, shi ma bai yi musu ba, aka tattara ni aka mayar gida, ana ta magani da yawon asibiti a banza, jiki sai gaba yake yi, baƙin da fatata ta fara yi ne ma yake ƙara ba wa ƴan'uwana tsoro, na rame na yi baƙi sosai.Salman kullum sai ya zo duba ni, sotari ma a nan yake cin abinci, saboda police station ɗinsu babu nisa da gidanmu, kuma yana sakin kuɗi sosai a jinya. Watarana da ba zan manta da ita ba, da yamma ina zaune a falo ni da Mama, wannan ƴar Niger ta kira ni, sai da na kalli Mama na ga hankalinta yana kan tv sannan na ɗaga wayar a sanyaye, ko sallama ba ta yi ba ta ce"Kina ina!?"
Na ce"Ina gidanmu".
Ta sheƙe da dariya ta ce"Ki jira ni".
Na ajiye wayar ina tunanin zuwa ta yi ko me? Ana sallar magriba cikina ya hau wani mugun ciwo, na ɗauki lokaci ina murƙususu kafin yawu ya fara taruwa a bakina, da sauri na fita daga ɗakin, kafin na ƙarasa banɗaki amai ya kece mini, na dinga yi babu ƙaƙƙautawa, Mama ta zo tana yi mini sannu, tana haska aman gabana ya faɗi, wani baƙin amai ne kamar ruwan kwata, na gama na wanke bakina, Mama ta zuba mini ruwa ta kai min na yi wanka, na koma na kwanta ina jin ciwon cikin, wunin ranar ban iya cin komai ba, sai ruwan shayi, don haka yanzu ma shayin ƙanwata Binta ta haɗo ta miƙo mini, na sha rabin kofin, ina ajiyewa wani aman ya ƙara taso mini, yanzun kuma koren amai ne na yi ta kwara shi, ranar dai haka na kwana ina ta yi, babu wanda ya yi bacci a ɗakin.
Da damuwa Mama take ce mini"Ni fa Zinatu wannan abun ya fara ba ni tsoro, rashin lafiya ba ya jin magani? Idan an yi test a ga babu wata cuta a jikinki?"
Hawaye kawai nake yi na kasa cewa komai.
Tun daga ranar kuma jikina ya rikice, duk wanda ya gan ni sai ya tausaya mini, ganin kamar zan mutu ya sa ƙanwar Babana ta ce ya kamata a canza mini magani, a saki asibitin nan, a nemi na musulunci, haka aka tattara ni aka kai wajen mai maganin Islamic, ya haɗo mini uban magunguna Salman ya biya kuɗin, cikin ikon Allah sati ɗaya kacal sai ga sauƙi yana ta samuwa, a hankali na fara warwarewa, haskenw ya fara dawowa wanda da har na yi zaton shikenan na zama baƙa, cuta ba mutuwa ba ce, na warke tass, na fara murmurewa, amma sai dana gama shan magungunana sannan na koma gidana.
A ranar muna zaune a falo da Salman a hankali nake bugar cikinsa a kan buduruwarsa ƴar Niger, nan nake jin ashe da ta zo ne ta kama ɗaki a sabon gari, da sunan ta nutsu ta daina kula kowa don shi ya aure ta, daga baya da ta ga ba aurenta zai yi ba shi ne abun ya juye ya zama rashin kirki, shi ma ta yi masa barazanar dole sai ta ga ƙarshen auren nan.
To ni dai tun a ranar na saka ta a blacklist, kuma na kama ibada, zikirin safiya da na maraice ba ya wuce ni, komai ya dawo min daidai, na koma makarantata, har yanzu shi yake kai ni, bai fasa hidimta mini ba a kan karatu, ko yana da uzurin da zai hana shi kai ni, sai ya kira ni ya jaddada mini lallai na tafi makaranta, sosai yake so na yi karatu.
Akwai wata Aisha ƴar ajinmu, buduruwa ce, na girme ta, tana son Sabreen sosai, tana taya ni rainonta, hakan yana taimaka mini a makarantar, tun ina ba wa Salman labarinta har ya santa, saboda idan ya shigo da ni a mota sai ya kawo ni har inda za mu yi lakca, saboda haka Aisha tana ganinmu za ta taho da sauri ta ɗauki Sabreen, hakan yana yi masa daɗi, sai su gaisa ya yi mata godiya, daga baya ma sai ya zamana kullum zai ba ni dubu uku da ya saba ba ni, ita kuma ya ba ta dubu ɗaya, wataran dubu biyu, akwai lokacin da muna zaune da daddare nake ta mita kan cewar wayar Aisha ta lalace, ina so na tambaye ta abin da za mu yi gobe, idan ba mai muhimmanci ba ne ba zan je ba, ya ce"Ai gara dai kawai ki je ɗin, kar wani abun ya wuce ki".
Na ce"To".
Ya ce"Bari na fita yanzu zan dawo kar ki rufe gidan".
Cikin sarewa da halinsa na ce"To kuma idan da sabo ai na saba, yanzu ba sai ka tsara ni ba, ka tafi duk inda za ka je ka kwana".
Bai ce min komai ba ya fice, kafin na yi bacci ya dawo, tabbas na ga ya shigo da leda, amma ban gane meye a ciki ba, ya saka ta a sif ɗinsa, ni ma ban zurfafa bincike ba, muka kwanta.
Washegari da za mu tafi makaranta na ga ya ɗakko wannan ledar, bai ce mini komai ba, ni ma ban tambaya ba, muka tafi, sai da muka ƙarasa sannan ya ɗakko ledar yana ce mini"Waya na siyawa Aisha".
Sai da na ji gabana ya faɗi, na ce"Waya kuma?"
Cikin haɗin ko'inkula ya ce"Ba kin ce wayarta ta lalace ba?"
Na ce"Amma a kan me za ka siya mata waya?"
Ya ce"A kan tana son ƴata, kuma kuna mutunci".
Muka fito, yau ba ta ma ga zuwanmu ba, sai da na shiga na kira ta, ta zo suka gaisa tana karɓar Sabreen daga hannuna, na karɓi wayar na miƙa mata ina murmushi na ce"Ga waya inji Abban ƴarki".
Ta zaro ido da alamun mamaki, kafin ta yi murmushin farinciki ta ce"Na gode sosai Abban Sabren".
Ta riƙe hannuna ta ce"Ki taya ni godiya!".
Ya ce"Babu komai".
Ya miƙo min dubu huɗu, ya ce na ba ta dubu ɗaya, sannan ya shiga mota ya tafi.
Bayan mun zauna a wayance na karɓi wayar na duba kwalin tsaf, na bincike cikin wayar don na ga ko ya ajiye lambarsa a ciki, ko wani abu na rashin gaskiya, amma ban ga komai ba, na ba ta wayar tana ta murna.
A ranar sai na wuni a sanyaye saboda na san halin shi, na fara tunanin yana son Aisha ne.
Tun daga lokacin na dinga bibiyar wayarsa da ta Aishan, ban gano komai ba, don haka na watsar, ba bar shi a kyautatawa ce kawai yake yi mata.
Akwai ranar da Habiba ta zaunar da ni musamman ta yi mini magana a kan Aisha, Habiba ƴar group ɗinmu ce, ina ce mata Anti saboda ta ta girme ni, take ce mini"Yanzu ke Zinatu ba kya tunanin wani abu zai iya shiga tsakanin mijinki da yarinyar nan Aisha? Ki duba yadda take ta liƙe miki, tana ɗaukar ƴarki, ƙila fa duk ba don Allah take yi ba, kin san fa ƴan matan zamanin nan, ta ga miji ɗan kyakkyawa da kuɗi da mota, ta ga yana kyautata miki, kuma tana ganin yanayin suturarki ke da ƴarki, tsaf ta za yi sha'awar aure shi".
Duk da ni ma a baya na yi wannan hasashen amma sai da maganarta ta tsorata ni, na ce"In sha Allah babu abin da zai faru, mu kyautata mata zato".
Anti Habiba ta ce"To Allah Ya sa, amma dai ki kula".
Ni dai ko a fuska ban canzawa Aisha ba, muna ta mutuncinmu.
Watarana Anti Habiba ta yi fashin zuwa makaranta, sai washegari da ta zo take faɗa mana jiyan ba a nutse take ta, ƙaninta a ka kama, har yanzu yana rufe a station, tana faɗar sunan station ɗin na ji na su Salman ne, nan take kuwa na ce"Ai kuwa indai ba wani babban laifi ya yi ba kar ku wani damu, zan saka Abban Sabreen ya shige masa gaba, don a nan yake aiki".
Ta ce"Wallahi babu wani laifi, yawon dare dai suka ce".
Na ce"In sha Allah zan yi masa magana".
Ta ce"Da kuwa mun ji daɗi, Allah Ya saka da alkhairi".Duka ƴan wajen sun ji daɗi, nan suka hau tsokanata da matar ofisa ni kuwa ina dariya kaina yana fashewa.
Da na koma gida, da rawar ƙafata na sanarwa Salman, ya ce to na faɗa mata idan ta je station ɗin ta neme shi, nan take na kira ta a waya na faɗa mata, haka kuwa aka yi washegari ta je, ban san dai yadda suka yi ba, amma da yamma ta kira ni tana yi mini godiya ta ce ƙaninta har ya dawo gida, na ji daɗin hakan kuwa, da Salman ya dawo na yi masa godiya.
Bayan an kwana biyu har na manta da an yi wannan abu, kwatsam wataran kamar almara na ga zoben Salman a hannun Anti Habiba, wata azurfa ce mai kyau da farin dutse a jikinta, tun kafin aurenmu take hannunsa, don haka na gane ta sosai, ba abun mamaki ba ne don ta yi wa Anti Habiba daidai, tun da mace ce mai ƙiba, shi kuma Salman ba shi da ƙiba siriri ne irin jikin fulani, don ko ni na fi shi auki, na yi wa azurfar nan kallon tsanaki, na jinjina kai.
Na koma gida zuciyata tana ta azalzata, ina ta so Salman ya dawo na duba hannunsa, a ranar bai kwana a gida ba, don haka dole na haƙura na yi kwanan tunani, sai da safe da ya dawo na duba hannunsa da sauri, gabana ya faɗi ganin hannunsa wayam babu zobe, kamar na tunkare shi da zancen a yi ta ta ƙare sai kuma na danni zuciyata, don ina son na samu ƙwaƙƙwarar hujja a kan hakan, don haka fatana yanzu shi ne kawai na samu damar bincikar wayarsa.