2
https://www.arewapen.com/book?id=6a9287eff3eaa6dc8f153f72
BAYA TA HAIHU
Ummu Maher(Miss green)
Page 2
Turo ƙofar ɗakin mahaifiyarsa ya yi cike da nutsuwa, sannan ya rufe ƙofar ya tunkaro inda Hjy take a bakin gadonta tana waya. Har sai da ya tsaya ta kammala wayar sannan ya gaisheta, ta amsa cike da son ɗan na ta sannan ta ce" Hamzah lafiyarka kuwa? Saboda na ga duk ka canja kamar kana cikin damuwa ko?.
Magana yake son yi amma ya kasa yana jin kunya, amma tuna wankin hula yana don kai shi dare yasa ya ce" eh to gaskiya ina cikin wani irin yanayi na ruɗani, amma zancen gaskiya ina cikin damuwa Ammi".
Ta ha numfashi sannan ta ce"To na ji faɗa min damuwarka Hamzah". Ya ɗan nisa sannan ya ce"Ammi ƴar gidan yayanki nake so Maryam".
Ammi ta washe baki sannan ta ce" Masha Allah, dama ranar da nake ta jira ce ta zo, a yadda Allah ya yi maka arziƙin nan bana so ace wata ka aura ba ƴar uwarka ba, saboda matan zamani kuɗi ne kawai a ransu".
Nan dai suka yi ta hirar su.
*******
"Ammi anya kuwa kuna sona, tsakani da Allah kinsan fa ni Ya Habibu nake so yanzu kuma sai ace wai na auri Hammah Hamzah? Ammi Wallahi idan kuka aura min wani ba Hammah Habibu ba zan iya rasa rayuwata saboda shi ne zaɓi..."
Tun kafin na ƙarasa Addah Hafsah ta ce" Amma ban taɓa sanin ba ki da hankali ba sai yau, yanzu tsakani da Allah meye Habibu ya fi Hammah Hamzah ne? Kuɗi, kyau, nasaba, ko mi?".
"Ya riga shi sace zuciyata saboda haka ni wallahi ba zan aure shi".
Duka Ammi ta kawowa bakina na kufce cikin fushi ta fara magana" Cigaba da faɗar abin da kike so, wawiyar yarinya sakarai, don ubanki waye yake auren wani talaka yanzu, to wallahi ko mutuwa za ki yi ba zaki aure shi ba kin ji na faɗa miki kuma Wallahi idan malam ya dawo ya tambaye ki kika ce mishi Habibu kike so Allah ya isa ban yafe..."
Addah Hafsah ta yi saurin rufe mata baki saboda kada ta ƙarasa, ni kuma na tsugunna gwuiwowina a ƙasa na riƙe ƙafafunta ina kuka me cin rai " Ammi ka da ki raba ni da shi wallahi zan iya rasa raina, ko kuma shi Yaya Habibu ya rasa ransa Ammi yanzu kin zaɓi wani a kaina?.
Ture ni can gefe ta yi, sannan ta ce" idan kin ta shi ki rataye kanki". Sosai hankalina ya ta shi na ki zuciyata tana bugawa kamar za ta fita daga ƙirjina.
Wannan wacce irin masifa ce take son tunkaro ni ya ƙarfi da ya ji ni sam ban gina tubalin rayuwata da Hammah Hamzah ba, da Habibu na gina rayuwata sannan yanzu rana ɗaya a canja min da wani wanin ma wanda sam ko da can jinina bai haɗu da shi ba.
Sai da na yini a ɗaki, ranar ko abinci kasa ci na yi babu yadda Addah bata yi dani ba amma na ce Ni sam ba zanci ba tana ji tana gani haka ta haƙura Ammi kuwa ko ta kaina ba ta bi ba ƙarshe ma cewa ta yi ko mutuwa zan yi sai na aure shi, idan ma zan kwantar da hankalina oho ita dai ko dai yaya ne ai me kuɗi ne saboda haka idan ma zan yi haƙuri na yi.
Ina zaune a ɗaki na ji ana kiran sunan Addah Sailuba, ana mata Oyoyo ni kuwa ina jin su na yi shiru na cigaba da kukana, saboda ni banga abin da ya kamata na yi ba idan ba kukan ba.
Bayan sun gama gaisawa ta shigo ɗakina, saboda an kai mata rahoton abin da yake faruwa shi yasa ma ta taho da saurinta domin a cewarta ba zan musu saki na dafe ba dole ne na auri Hammah mutum me kuɗi har haka a zauna ana mishi irin wannan. Tana shigowa ɗakin ta yi turus a ƙofar ɗaki ganina ina ta kuka duk na haɗa zufa na koma na fige tamkar kazar da aka tsoma a ruwa.
"Haba Mero ke kuwa anya ba ki da matsala akan ki? Kina ganin irin rayuwar da nake yi ai za ki so ace ba kya irin rayuwar da na ke yi, saboda kin ga dai wahalar da nake sha ke dai jiyau ce ba ganau ba". Ta dinga rarrashina ni kuwa ko kallon ta ban yi ba ballantana ma na saka ran zan haƙura na aure shi.
Ta gaji dai ta fito, Ammi ta ce " Dama kin dena wahalar da kanki, domin nasan kin san wacece Maryam da ɗan banzan taurin kai saboda haka kiyi banza da ita, shima jira nake ya zo Habibun na faɗa masa ya fitar min hanyar ƴa idan kuma ba haka ba billa-hil_azeem zai ga abin da zai biyo baya maramutunci ɗan gidan ɗan caca". Haka da Ammi ta yi ta sababinta da baya ƙarewa dama ga Ammi da mita sai ta kwana tana magana ɗaya.
Ana haka kuwa aka aiko ana sallama da ni, yaro ya ce" wai yana ta kiran wayarta ba caji".
Ammi ta yi caraf ta ce" yo ina waya za ta yi caji ya kawo mata waya burin ƙolo, saboda haka kaje ka ce masa kada ya sake zuwa wajen ta idan kuma yaƙi Allah zan sanya ƙatti su yi mai ɗaukar amarya shege me kama da amalanke".
Su Anty Sailuba suka fara dariya, saboda Ammi ko faɗa take akwai ta da abin dariya sosai.
Jin hakan yasa na fito da gudu daga ɗaki ko ɗankwali babu a kaina ina kuka ina share majina, saboda kukan duk ya haɗe fuska tamkar jaririyar da take so ta sha Mama.
Ammi ta fusgoni na yi sujjada ta ce" yawwa yi sujjada dama ba ki yi sallah ba".
Dariya suka sanya dukkansu Ammi ta ƙi barina na fita, ƙarshe ta tashi da kanta wai za taje ta yi masa warning a kaina. Da gudu na taso ta juyo bayan ta sanya mayafi ta ce" Wallahi in har kika biyo NI ban yafe ba" turus na koma na zauna, wasu zafafan hawaye suka fara zubo min a hankali. Na furta a fili " Na shiga uku, wannan wani irin azzalumi ne wanda yake son kawo ƙarshena yana don rugazamin kyakkyawar rayuwata".
A can waje Ammi ta hango shi zaune akan bencin ƙofar gida wanda samari suke zaman hira da daddare, tun daga nesa take harararsa da yake akwai solar a kofar gidan ta haske sa sosai, kyawunsa da kwarjininsa ya ƙara fitowa sosai Ammi ta yi wani Gwauron tsaki, sannan ta ce a fili " shege maye ɗan baƙin ciki ina murna za muyi kuɗi shi kuma zai zo ya kwafsa min Kur'ani baka isa ba".
Ta faɗi hakan tana me jin tsanarsa a zuciyarta. Saurin tsugunnawa ya yi gaban Ammi domin ya kawo gaisuwar surukai, amma Ammi ta dakatar da shi da cewa" kasan Allah Habibu wannan shi ne kashe di na farko kuma na karshe, kada na sake ganinka a ƙofar gidan nan tunda ba na ubanka ɗan caca bane".
Sosai ya ji maganar a bazata, a kuma gigice ya ɗago kyakkyawar fuskarsa kuma fara tas-tas amma saboda wannan mummunar maganar da ta faɗa yasa fuskar ta shi ta koma jajur, tamkar dai an zuba garwashi. Bakinsa yana kakkarwa ya fara roƙon Ammi akan ta daure ta faɗa mishi laifinsa amma ta yi banza da shi ta kama hanyar komawa gida tana huci. Habibu ya janyo gefen mayafinta fuskarsa ta jiƙe da hawaye ya ce" Ammi na roƙe ki kada ki raba ni da Maryam, Wallahi idan kika rabamu komi zai iya faruwa idan ma wani ta aura ta kasa zaman aura...
Da sauri Ammi ta juyo ta ɗauke shi da wasu tagwayen Maruka ji kake tas_tas tana huci ta ce" to dan ubanka idan kai ne me sawa ko hanawa ka hana ta zaman aure, banza ƙaton jahili kawai".
Sosai ya riƙe wajen marin tun da ya girma babu wanda ya taɓa ko da ture shi amma yau sai ga shi an mare shi, duk zafin zuciyarsa dole ne ya haƙura tunda marin ya fito ne daga wajen wanda ba zai iya ramawa ba, amma da za a kwana ana marinsa in har za a aura masa Maryam ba zai damu ba. Ya ta shi ya fara tafiya tamkar dai wanda ya fara shaye-shaye domin harhaɗa hanya ya fara yi.
Yana zuwa ƙofar gidansu ya faɗi ya yi zaman ƴan bori, ya saki kuka tamkar ƙaramin yaro dama ga shi fuskarsa ta yi jawur tamkar dai garwashi. Malam wato mahaifin Habibu yana zaune ƙofar gida suna caca ya hango ɗan na shi tamkar dai an cillo shi, da sauri ya tashi ya tunkaro shi yana ce wa" me sunan Baffah na me ya faru?.
Jin Muryar mahaifinsa ya ƙara famo mi shi babban tabon da ya yiwa giɓi a rayuwarsa, bai san lokacin da ya kaiwa mahaifinsa wani masga ba sannan ya ta shi ya fara magana kamar zautacce.
"Ina ji a jikina dama ba kai ne mahaifina ba, ina ji a raina dama ba daga tsatson ɗan caca me shan giya na fito ba, kai mahaifi ne amma ka kasance azzalumi wanda bai damu da damuwar ƴaƴansa ba tabbas da ina da dama dana goge tambarin jini ka a jikina saboda ko kusa ko kaɗan bamu dace da juna ba domin kudu daban arewa daban".
Durƙushewa ya yi a wajen ya fara sakin kuka me ciwo, irin kukan nan da yake fitowa daga cikin zuciya ya fito a fili.
Jikin mahaifin Habibu ya yi sanyi sosai, yaransa mata biyar ne sai Habibu shi ne ɗansa na biyu amma dukkanin matan nan mutum ɗaya ce ta yi aure sauran duk sun kasa Auruwa, sai an yi kamar za a yi auran sai a fasa saboda halin mahaifinsu. A saboda haka ne ma ake kiran gidansu gidan mata zallah saboda dukkansu a yanzu sun kai su yi aure amma abu ya faskara domin kuwa aure dai ya ƙi yiwuwa akwai wacce ranar ɗaurin auren ma aka fasa, sannan ita kan ta yayar Habibu maneji take a gidan auren saboda kullum kishiyarta cikin yi mata gori take ita da surukarsu a cewar su an auro musu baragurbi, sauƙinta ɗaya mijin yana sonta sosai.
A lokacin ne Malam Umaru ya ji kamar zai dena abin da yake yi ko domin rayuwar yaransa, ga yara dai tamkar su ne suka yi kansu amma shiru har yanzu sai kace wanda zai sanya su a gaba ya dafa ya ci, ga shi yara suyi ta yi masa atile suna zaginsa suma yaransu kullum a cikin yi musu gori suke musamman ma mahaifiyarsu Habibu ko gidan bikin ko suna duk ba ta zuwa saboda gori kullum tana gida ga shi ƴar gidan manya ce domin mahaifinta shi ne mai garin baki ɗaya, amma ta nace sai shi haka dai aka yi auren ba sanya albarkar manya, da farkon auren ma babu wanda yake bi ko ta ƙofar gidanta a cikin ƴan gidansu sai da ta yi haihuwa biyu ne, a lokacin da malam Umaru yake yawan dukanta ganin zai kashe musu ƴar uwa ne yasa suka ɗauke ta, amma soyayya gamon jini cikin lokaci kaɗan ya rarrashi abarsa suka dawo gidan aka cigaba da zaman doya da manja, ga yunwa ga matsin lamba daga mutanen unguwa ko kaɗan ba ta jin daɗin rayuwarsa sai ya yi caca ne yake samo musu ɗan abin da za su ci. Ana haka ne ta fara sana'ar wanki da guga aka yi sa a abin ya karɓe ta sosai ana kawo mata sosai a haka har yaran suka fara girma ga shi sai yara mata take haifa.
Goge hawayen fuskarsa ya yi, cikin lokaci kaɗan tsoron Allah ya zo masa ya ji sam bai kyautata yaransa da matarsa guda ɗaya ba, kuma bai kyautawa soyayyar da take masa ba ga shi dai duk abin da yake tana tare da shi, sai yaji ko aransa ko da sau ɗaya ne ya kamata ya sanya su cikin farin ciki ya kamata kuma ya koma ga Allah ya dinga sallolinsa na farilla akan lokaci, sannan ya nemi yafiyar Ubangiji. Haka ya shiga gidan yana mai ɗauke da sallama.
Mrs SHU'AIBU ce✍🏿