SULTANİM

Chapter 1

by @msssamher590

SULTANIM

      Na

Mss Samher



Instagram mss_samher

Tiktok mss_samher

Wattpad mss_samher





Page1



TUNATARWA: Neman yardar Allah a dukkan ayyukan da mutum yake yi shi ne ginshiƙin rayuwa ta mai kyau. Duk aikin da aka yi domin Allah, ko min ƙanƙantarsa, yana samun girma da albarka a wurinsa. Amma aikin da aka yi domin burge mutane, ko son zuciya, kan rasa darajarsa a lahira, ko da ya yi kama da alheri a duniya.



Daga cikin falalar neman yardar Allah akwai:

Samun albarka a aiki, Kwanciyar hankali, Kariya daga riya da girman kai, Samun lada a lahira. Allah ta'ala yasa mudace.



Bismillahirrahmanirrahim



Fateema Ishaq Imam shine asalin sunanta, Ya Baffa kuma ya sanya mata NADRAH.



Malan Ishaq mutun ne mai mutunci, sanin ya kamata da wadatar zuciya, kasancewanshi mutun mai ilimin addini yasa mutanan unguwarsu suke ganinsa da qima da kuma daraja.



Su biyu iyayansu suka haifa kafin mutuwarsu Ishaq wanda shine babba sai ƙaninsa Haroon, Ishaq yayi aiki tuƙuru wajan gina rayuwar dan uwansa kasancewarsa mutun jajirtacce kuma mai neman na kansa.



Haka rayuwa taci gaba da tafiya musu Haroon na kokarin karatu shi kuma Ishaq yana samar da kuɗin da ake buƙata komai yana tafi yadda sukeso Haroon yana tausayin ɗan uwansa ganin faɗi tashin da yakeyi akansa idan yayi magana sai kawai Ishaq yayi murmushi yace



"bana dawani wanda yafika zan iya sadaukar da komai dan inganta rayuwarka kuma zan cigaba da tsaya maka har sai kayi nasara in sha Allah.



Hakan yana ƙarawa Haroon kwarin gwiwa da alwashin kula da ɗan uwansa anan gaba cikin yardan Allah.



Bangaran Ishaq bai zauna haka bah ganin boko bazai yiwu musu duka bah saiya zaba cigaba da zuwa zaurukan koyar da karatun addini bayan asuba da kuma na bayan magrib zuwa isha.



Haroon ya kammala karatunsa cikin amincin Allah adaidai lokacin kuma Allah ya haɗashi dawani babban mutun inda ya bashi babban matsayi a company.

Kokari, jajircewa da rashin wasa da aiki sune takobin nasaran Haroon a aikinsa. Cikin shekarun da basu wuce uku zuwa huɗu bah Haroon ya gama tsayawa da ƙafafunsa inda ya fara cin gashin kansa yana kawo kaya daga koh ina a faɗin duniya.



Haroon ya mallaki motoci biyu kuma ya kammala gina makeken gidansa a nan millennium city dake nan cikin garin kaduna, ya samu yayansa da maganan auran wata yarinya da sukayi makaranta tare mai suna Sa'adatu.



Ishaq yayi farin ciki dan haka ya shige masa gaba tare da taimakon Baba Liman, kasan cewar a shirye yake kuma suma gidansu Sa'adatu suna da arziƙinsu hakan ya saka cikin wata biyu akasha bikin Haroon da Sa'datu.



Bayan shekara ɗaya Sa'adatu ta haifi ɗanta namiji inda Haroon yasaka masa suna Ishaq suna kiranshi Baffa, sosai Sa'adatu tayi  bakin ciki acewarta kura da shan bugu gardi da kwace kuɗi, ba'a saka sunan mahaifinta bah za'a saka sunan wani chan daban, Haroon kam koh a jikinsa saboda Ishaq bango ne a rayuwarsa.

Tun daga wannan lokacin Sa'adatu ta dauki tsana ta daurawa Ishaq tare da alwashin cireshi a rayuwarsu.



Haroon ya gyara gidan da yayanshi ke zaune tare da samar masa duk abunda yake buƙata ya takura masa sosai akan yayi aure saidai kullun ya kance masa lokaci ne beyi bah.



Bayan shekara biyu Baffa yayi wayau sosai domin babu inda baya zuwa da kafansa. Yayin da Sa'adatu ke ɗauke da wani cikin, Allah ya haɗa jininsa da Ishaq domin idan sukaje gidanshi da kuka suke komawa gida ya dinga kiran sunan Babaa babaaa hakan yana ƙara kona zuciyar Sa'adatu.



         Ranan wata laraba bayan sallan isha Baba liman ya muqaci magana da Ishaq, bayan sun gaisa liman ya fara magana kamar haka 



"Ishaq alfarmanka nake nema dan Allah idan zaka iya nasan kai mutun ne mai natsuwa da kyawawan ɗabi'u, tabbas da ace inada ɗa namiji da babu makawa shine zai sharemin hawayena. Cikin girmamawa Ishaq yace



"Baba Liman nima ɗanka ne domin kuwa matsayin uba muka ɗaukeka umurni kawai zaka bani. 



Kamar yadda kasani Amina banice na haifeta bah shekara 19 da suka wuce na tsinceta, yarinyace mai hankali da natsuwa tun bayan rasuwan mai dakina wacce ta riƙeta Amina ke fuskantar zangwama ga ahalin gidana bazan iya jure ganinta a wahala bah kaine kaketa zuwamun arai Ishaq amma bazan maka dole bah kaje kayi tunani.



Ajiyar zuciya ya sauke dan a zahirin gaskiya yarinyar ta dade tana burgeshi, kuma rashin asalinta bai daukeshi a matsayin matsala bah cikin natsuwa yace" na amince baba, kuma koh yaushe a shirye nake. 



Nan dai suka tsayar jibi bayan sallan juma'a za'a daura auran kawai. 



A daran Ishaq ya sanar da ɗan uwanshi, da farko yaso yaƙi amincewa amma ganin yanaso kuma dama abinda ya yake buƙata kenan hakan yasa ya haƙura kawai, a washe gari Haroon yazo unguwar yaso ya bashi ɗaya daga cikin gidajanshi ya zauna amma Ishaq yaƙi, acewarsa bai kamata abar gidan da iyayansu suka bar musu babu kowa bah, babu yadda zayyi dan haka ya haƙura, saidai an sake gyara gidan da duk abunda daya kamata.





       Ranan juma'a bayan idar da sallah aka sheda auran Ishaq tare da amaryansa Amina, koda labari ya iske iyalan liman haushi da takaici ne ya kamasu domin kuwa kowa yasan Ishaq da ƙimarsa  kowan nansu zaizo a bada yarsa bah wanchen tsintacciyar bah, Baba Liman da kansa ya kai amina ɗakinta bayan ya mata nasiha.





Bayan bikin Ishaq da wata uku Sa'adatu ta haihu wanan karanma namiji ne inda yaci suna Mahmud, Sa'adatu kam farin cikin da dake ciki baza'a misaltashi bah koh yanxu tasan wutsiyan raqumi yayi nisa da akala tunda babu Ishaq babu gadon mijinta.



Bangaran Ishaq kuwa saida suka shekara bakwai kafin Allah ya azurta Amina da samun ciki, gori kam tashashi har ba'a magana tun tana damuwa harta daina saboda yadda Ishaq ke kwantar mata da hankali da nuna mata komai lokaci ne.

Ranan wata alhamis da asuba nakuda yakama Amina basufi minti 15 da zuwa asibity bah tahaifi yarinyanta mai matuƙar kama da ita kyakykyawa ma sha Allah.



Haroon na samun labari ya tattaro iyalansa suka taho asibity, Baffa da Mahmud har rige rigen zuwa wajan baby sukeyi.

Babyn dake hannun Abba Baffa ya kurawa  ido yace



"Baba me sunan kanwar tamu? 



Murmushi ɗauke akan fuskan Ishaq yace"  Abbanka ne zaisa mata suna.



Maida dubansa yayi ga Haroon yace" Abba mai sunanta?



Fateema Abba ya faɗa a hankali (sunan mahaifiyarsu kenan).



Mahmud yace" suna mai daɗi she will be my favorite sister.



Baffa yace" Amma zamu kirata Nadrah koh Mama? ya kare tambayar yana duban Amina dake kwance kawai tana kallonsu.



Murmushi tayi tana faďin

"Yadda yayansu yace haka za'ayi. 



Duk dariya sukayi banda Sa'adatu da tayi wani kuntun murmushi dan murnan da Abba da yaranta sukeyi ya fara qular da ita, Baffa ya dauko jaririya ya nufota yana faďin



"Umma Nadrah fah tana da kyau wallahi.



 Abba yace" kodai zamu riƙe maka ita tun yanxu...…