SULTANİM

Chapter 2

by @msssamher590

SULTANIM

     Na

Mss Samher

 

Instagram mss_samher

Tiktok mss_samher

Wattpad mss_samher

 

 

Page2

 

An karbo daga abu hurairah Allah ya qara yadda da shi yace:manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gareshi yace: kalmomi guda biyu,masu sauqi akan harshe,mafiya soyuwa agurin ubangij,masu nauyi akan mizanin ma’aunin ayyuka sun: SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI,SUBHANALLAHIL AZIM.

 

 

 

Shigowan Nurse yasa Umma ta karbi Nadrah tare da haɗiye maganar da yazo bakinta.

 

Bayan ta gama duba mama ta tabbatar musu zasu iya tafiya komai lafiya.

 

Har dare su Umma suna gidan badan ranta yaso bah saidan umurnin Abba, washe gari Abba yasa aka nemo mai taimakawa Mama dan bazai yiwu taje gidan Baba liman bah ballema yanxu da baya raye.

 

Haka Mama taci gaba da rainon Nadrah cike da kulawa duk bayan kwana biyu zuwa uku Abba yana kawo su Baffa dan suga Nadrah.

 

    

      BAYAN SHEKARA 17

 

Abubuwa da dama sun faru cikin waɗannan shekarun. Ciki kuwa akwai bunƙasar arziƙin Abba wato Haroon. Yana ɗaya daga cikin jerin mutane sha biyar da sukafi kowa kuɗi a jahar Kaduna.

 

Kuma yana ƙoƙari wajan tallafawa al’umma wanda ba kasafai ake samun irin wannan haɗin kai tsakanin arziki da alheri bah.

Cikin shekarun nan Abba ya kafa cibiyoyin kasuwanci waɗanda suka samar da aikinyi ga matasa da dama.

 

 

Ɓangadan Baba ma akwai cigaba da dama, domin kuwa shi ne limamin babban masallacin dake nan cikin unguwa. Mutum ne mai dattaku da sanin ya kamata, wanda ke jan hankalin jama’a ba wai da kalamansa kaɗai ba, har da kyawawan ɗabi’unsa.

 

A tsawon shekarunsa na jagoranci, Baba ya kasance ginshiƙi wajen shiryar da matasa da kuma tunatar da al’umma muhimmancin tsoron Allah da zaman lafiya. Hudubobinsa suna cike da nasiha, haƙuri, da ƙarfafa zumunci, abin da ya sa mutane ke matuƙar girmama shi.

 

Zumumci dake tsakanin Abba da Baba kuwa sai sambarka domin Haroon ya riƙe ɗan uwansa tamkar Uba.

 

Sa’adatu (Umma) tayi duk wani abu daya kamata wajan cireshi a rayuwarsa kamar yadda tayi alƙawari, amma sai take ganin kamar kansu kullun haɗuwa yakeyi, ga ƙaunar dake tsakanin yaranta dasu Baba, yaran suna jin daɗin zama da shi, suna sauraron maganarsa, suna girmama shi fiye da yadda take zato. 

 

Wannan ƙauna tasa wani lokaci tana jin kamar Baba ya fi kowa kusanci da zuciyar yaranta. shine abinda yafi komai ɗaga mata hankali.

 

Bugu da ƙari Nadrah, yarinya ce kyakkyawa ga natsuwa, ganin yadda yaranta ke rawan ciki a kanta musamman Mahmud yasa Umma ƙara tsanar ahalin Ishaq, dan ko ƙasa da sama zata haɗe guri ɗaya bazata yarda ta haɗa zuri’a da tsintacciyar mage bah.

 

Lokacin da Baffa yafara sanin ciwon kansa saiya zama mutun mara surutu, bayasan hayani saɓanin Mahmud, daya kasance mai kazarkazar dasan shiga jama’a.

 

Hakan yasa indai ba makaranta ba to Mahmud yana gidan Baba wajan Nadrah.

 

         ********

Faɗawa jikin Mama dake zaune akan daya daga cikin kujerun parlorn tare da rungumeta tana faɗin 

 

“Finally munyi hutu zan zauna tare da Mamana a gida.

 

Ya salam nikam Nadrah yaushe zakiyi hankali kawai kifaɗo ɗaki haka babu sallama, sake lafewa tayi a jikin Mama, a hankali ta furta

 

“Na matsu naganki ne kuma sannan nayi miki albishir yarinyanki ta girma SS3 zata shiga idan mun koma.

 

Dariyan da sukaji yasa duk suka kalla ƙofa, Baba ne ya shigo yana faɗin 

 

“Bismillah kushigo mana.

 

Abba ne tare dasu Mahmud, Barin jikin Mama tayi tana faɗin 

 

“Sannu da zuwa Abba”

 

Yawwa mamana nazo a daidai kenan tunda naji sakon kin girma da kunne na ya ƙare faɗa yana faɗaɗa murmushinsa.

 

Gaisawa duk sukayi Mama ta ƙara da fadin” Yayansu naji ka kammala karatunka Allah yasa albarka ya kawo rabo mai amfani.

 

Murmushin gefan baki Baffa yayi cike da miskilanci yace

 

“Amin Mama.

 

Fira suka cigaba dayi har aka kira sallan la’asar, koda suka idar gidan suka dawo  lokacin Mama ta kammala haɗa musu abincin da sukafiso wato tuwan shinkafa miyan zogale.

 

Wannan karan a tsakar gida suka shinfiɗa tabarma, abinci sukeci cike da nishaɗi da ƙauna.

 

Sai dare suka bar gidan bayan Mahmud yace Nadrah ta shirya gobe zaizo sufi ta, hakan ya zama mata jiki tun tasowanta lokaci zuwa lokaci yana zuwa ya dauketa suje ya mata siyayya.

 

 

Zaune take a kayataccen babban parlor ɗin gidan ƙafa ɗaya kan ɗaya tare da kallon agogo akai akai, jin sallamarsu yasata ɗagowa tazuba musu ido ranta a matuƙar bace.

 

Abba ne ya haye sama yana faɗin 

 

“Good night boys” koh kallah inda take beyi bah danya lura kwana biyun nan rigima takeji.

 

Rai a bace Umma tafara magana

 

“Wato nayi duk abunda da zanyi koh sau nawa nake faɗa muku kudaina dare a gidan chan idan shi abban naku ban isa dashi bah ku ai dolanku kuji maganata kuma na rantse idanma akwai abunda kuke shiryawa kuyi saurin warwareshi dan bazan taba  aminta bah.

 

Tana kaiwa nan tabi bayan Abba, Tabe baki Baffa yayi dan ya rasa gane dalilin masifar Umma shikam Mahmud murmushi yayi mai cike da ma’anoni kala kala.

 

 

    ABUJA

 

Jirgin ƙarfe huɗu ne zai sauke shi tun safe ake shirye shirye a gidan, Mami dake saukowa daga strais fuskanta yalwace da murmushi tace

 

“Zahra ina Zaina hope kun gyara part din yayanku da kyau kunsan halinshi.

 

Zaina ce tafito ɗaki tana faɗin “twin sis shalelen mami fah zai dawo tun wuri munemo inda zamuje.

 

Zahra tace “you spoke my mind dear. 

 

Ummm bani zanji daku bah Allah ya kawomin yarona lafiya he will deal with you.

 

Nnamdi Azikiwe International Airport 

 

A hankali yake tafiya hannunsa ɗaya yana jan suitcase, sanye yake cikin kananan kaya riga sky blue da wando khaki, sunyi masa kyau inda suka fito da hasken farin fatanshi, dogone sosai yana da ɗan jiki daidai nashi, matuƙar kyakkyawa ajin ƙarshe.

 

Hannu yasa ya shafo lallausan sajen dake kwance akan fuskansa, fararan idanuwansa da suke koh yaushe a lumshe kamar mai bacci ya ɗan budesu a hankali. Hisham ne ya nufosa yana murmushi rungume juna sukayi Hisham yace

 

“Welcome man it’s been a year.

 

Murmushi kawai yayi masa suka nufi mota.

 

Asokoro sunrise water park 

Daidai wani katafaran gida sukayi horn mai gadi ya wangale gate suka shiga.

 

Zahra da zaina dake tsaye suka nufi motan, fuskarnan a ɗaure kamar koh yaushe yafito

 

“Welcome Ya Faruq we miss you” suka faɗa atare.

 

Kafaɗar Zaina yadafa tare da kama hannun zahra cikin muryansa mai cike da tsantsar natsuwa yace

 

“Ƴan biyun Mami sun ƙara girma”

 

Shigowansu yayi daidai da sakkowan Mami da hanzari ya ƙarasa ya rungumeta ajiyar zuciya ta sauke tana faɗin

 

“Yabo da godiya su ƙara tabbata ga ubangijin daya dawomin dakai cikin ƙoshin lafiya, Allah ya maka albarka”

 

“Amin ya Allah Mamina i really miss you”

 

Kansa ta shafa tace “yanxu kaje kayi wanka kayi sallah sai kazo kaci abinci.

 

Hisham ya karbi zancen da faɗin “Mami kodai ni nakoma ne.

 

Dariya duk suka saka har Abba da shigowan shi kenan yace “ Ai Hisham ni kaina haƙuri nakeyi idan akace Umar yana gidan nan, Aure kawai zanyi masa na huta.

 

Rungume juna sukayi shida Abba kowa zuciyanshi cike da farin ciki…….