SULTANİM

Chapter 3

by @msssamher590

SULTANIM

     Na

Mss Samher

 

Instagram mss_samher

Tiktok mss_samher

Wattpad mss_samher

 

 

Page3

 

Manzan Allah S A W yace: shaidanu suna nisantar gidan da aka karanta suratul baqra a cikinsa har na tsawon kwana uku

mala'iku sukanyi duba izuwa sararin duniya,yayin da suka kalleta suna hangota ne baqiqqirin basa ganin komai face hasken gidaje ko guraren da ake karanta alqur'ani a cikinsa.

 

 

 

Part ɗinsa yaje yayi wanka tare dayin sallah sannan ya shirya cikin wasu ɗanyan yadi kaftan kalar chocolate brown a parlornsa ya samu Hisham daya shigo yayi sallah, bangaran Mami suka koma gaba daya.

 

Koda suka gama cin abinci parlor suka dawo aka cigaba da hira kiran da mahaifiyar Hisham ta masa yasa ya musu sallama ya wuce.

 

Dady yace “Umar kasan maganar da mukayi before tafiyarka, ina kan maganata wallahi idan baka motsa bah zan baka mamaki.

 

Mami tace “ Ayi hakuri yarona ya huta daga zuwansa. Barin wajan Dady yayi bayan ya tabbatar musu da abin daya faɗa.

 

Ɗan guntun murmushinsa ya sake kamar koh yaushe a hankali ya furta

 

“Don’t worry mamina it comes to an end in sha Allah “

 

 

Kaduna

 

Anayin sallan la’asar Mahmud yazo, Nadrah ta shirya already, sanye dake da black abaya tayi rolling mayafin, tayi kyau saita fito kamar balarabiya. 

Mahmud dake kallonta murmushi ya kasa bari fuskanshi, saida ya saita motarsa a titi sanan ya ɗan dubeta yace 

 

“You look stunning”

 

Murmushi tayi wanda yasa kumatunta lotsawa kyawawan dimples ɗinta suka bayyana, cikin muryanta mai sanyi tace

 

“Thank you Ya mahmud”

 

Rift Valley Girll House Restaurant suka fara zuwa, ya mata odern shawarma, milkshake da signature steak salad, shi kuma lemon drift da burger. Sun ɓata lokaci sosai a wajan.

 

Kamar koh yaushe siyayya mai yawa Mahmud ya mata kayan sakawa dana kwalliya da sauransu, sun iso gida ana kiraye kirayen sallan Magrib ita kadai ta shiga shikuma ya shiga masallaci, saida sukayi isha sanan suka shiga gidan tare da Baba.

 

Mama tace “Mahmud baka gajiya Allah ya saka da alkairi yasa kufi haka.

 

“Amin Mama babu komai ita kaɗaice ƙanwar danake da” bai wani jima bah yawuce gida.

 

 

Abuja

 

Zaune yake a cikin motarsa ƙirar Mercedes Benz GLB, kyakkyawar budurwa ce ta nufo motar sai yauƙi takeyi doguwa ce tana da haske amma ba sosai bah, bude motar tayi ta shiga fuskanta dauke da murmushi tana faɗin 

 

“Wow, one whole year! i’m so happy to see you again dear”

 

Idanuwanshi ya zuba mata hannu tasa ta rufe fuskanta  tace

 

“And yet you are still in my heart”

 

Murmushi mai ɗan sauti yayi cikin calm voice ɗinsa yace 

 

“I miss everything about you”

 

Dariya tayi sosai sannan tace “ babe i’m extremely excited guess what?”

 

“Hmmm don’t keep me waiting!”

 

“I got admission for my master’s program in Australia! Can you believe it?”

 

Jin yayi shiru yasa cikin sanyin murya tace  

 

“Are you not happy? Babe this is a big step for me”

 

“And you’re telling me now ya faɗa yana kallonta”.

 

Am sorry but i’m just trying to surprise you.

 

“Okay! am leaving”

 

Babe please 

 

“Swafiyya we’ll sort out this tomorrow. Good night”

 

Sanin bazai saurareta bah yasa tafita tana kallonsa har ya bar haraban gidan ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta furta 

 

“I can’t afford to lose this opportunity, I’m really sorry babe”

 

 

Bayan ya isa gida ya dade a cikin mota yana tunani so he waited for her to finish university and now she want to leave for master’s, ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin

 

“She have to choose! Me or her Master’s.”

 

Bai iya shiga ɓangaran Mami bah ya wuce part ɗinsa a waya ya kira Zahra yaceta kawo masa tea.

 

Saida ya gama shirin baccinsa sannan ya jawo wayarsa calls ɗin Swafiyya ya tarar tare da messages wayar ya kashe gaba daya dan kansa har wani ciwo yake masa.

 

 

Washe Gari

 

9am daidai yafito, ya shirya cikin ƙananan kaya farin T-shirt da jeans blue. A dining ya samesu bayan sun gaisa shima ya zauna Mami tace

 

“Jiya kuma sai baka dawo bah hope lafiya kake”

 

Yeah Mamina kawai gajiya ne.

 

Dady yace “Yawwa Umar, ina wannan abokin nawa dake Kaduna Alhaji Haroon yaronsa Baffa yanaso ya bada aiki a company ɗinka”.

 

“Tohm yabi process ɗin da kowa yakebi” Faruq ya faɗa yana goge hannunsa da tissue.

 

Dady yace “Shikenan zan faɗa masa but please check your gmail at your earliest convenience.

 

“Hisham ne yake kula da wannan kuma zanyi magana dashi in sha Allah”, daga haka ya musu sallama ya fice.

 

Bai tsaya koh ina bah sai Prime Stone Builders, Hisham da shima isowansa kenan suka gaisa sannan suka nufi ciki…….