6
*DUHU BAYAN MURMUSHI*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 6.
Sarac Stars R Pen...✍️
Jabir.
Wajen ƙarfe biyar na yamma ya dawo gidan, tun a hanya yake jinsa wani iri da fargaban yadda zai isa gida babu Safiyya a ciki, haka yayi parking ya fito jiki a sanyaye maigadi ya rugo da gudu bayan ya rufe gate ya bashi makullun shashinsu yana yi masa sannu da zuwa, Jabir ya amsa yana amsa gaisuwarsa sai yayi gaba yana jin wani irin kewa da yake tabbatar masa da ya rasa wani ɓarin zuciyarsa, bai zaci zai ji irin haka ba duba da yadda Safiyya ta fusatashi jiya wanda hakan yasa shi jin haushi har ya kai mata mari a dalilin wuyan rigarsa da ta riƙe, kuma abunda bata taɓa yi ba kenan duk rikicin da zasu yi.
Ki cika min riga ta Sofyy tun kafin ranki ya ɓaci.
Raina sau nawa ya ɓaci.? wlh bazan sake ka ba muddun baka tsaya munyi magana ta fahimta ba, haka kawai ka mayar dani kamar mahaukaciya tun ɗazu ina ta magana ni kaɗai, Jabir na gaji.! wlh na gaji.!! Na rasa wani irin taurin zuciya ne kake da shi kamar na kafuran farko...
Bata ƙarasa maganar ba ya zabga mata mari tare da tureta ya fincike rigarsa tayi baya kamar zata faɗi, sai ta zube a kan guiwarta tana wani irin kuka mai gunji.
Safiyya saki kike so ko.?
Eh ka sake ni na gaji.! ina buƙatar farin ciki nima ba zan zauna da kai da son zuciyarka ba, shekara uku ina binka ka yarda na haihu amma kaƙi kullun sai kawo min uzuri wanda zallar son ziciya ne a ciki, nima ina buƙatar na rayu da farin cikin da kake yi masa kallon matsala.
Ta ƙare maganar tana miƙewa tare da dukan ƙirjinta.
Wlh ko kaine autan maza na haƙuri da kai ba zaka kashe min rayuwata a tsaye ba.
Shi kenan na sake ki saki ɗaya a matsayin gargaɗi, domin na tabbatar baki da inuwar da zaki raɓa sai a wannan gidan, tabbas zaki dawo ki bani haƙuri, sannan ki sani anan gamsheƙarki yake.
Ya ƙare maganar yana nuna mata yatsa manuniya tare da karkaɗa shi ya wuce cikin ƙunar zuciya ya fice daga gidan gabaɗaya. Safiyya wani abu taji ya daki kanta kamar guduma a sa'ilin daya furta kalmar saki, sai jikinta yayi wani irin sanyi wanda da kyar taja ƙafarta ta zauna a Cushing, ta shiga sauke numfashi mai nauyi jikinta yana rawa, bata taɓa kawo zata ji irin haka ba idan ya saketa, tabbas a yadda take ji a zuciyarta kamar ta miƙe ƙafa ta cigaba da zama in ya dawo ta bashi haƙuri su sasanta, amma kuma furucin daya yi mata bayan sakin sune suka tunzura ta har take jin zata nuna masa tabbas ta rabu da shi har abada, zata rayu ko babu shi, sai taji kwarin guiwa ta miƙe tana zarya a falon, ta ɗauki wayarta da ke kan center table ta kira yaya Ali bugu ɗaya ya ɗauka, ta kira sunansa cikin rauni, wanda sai da ya saka shi miƙewa dan ya tabbatar ba lafiya ba.
Yaya Ali, Jabir ya sake ni yanzu saki ɗaya, ka sanar dasu baffa.
Alhamdulillahi Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi, ki fara haɗa kayanki kin ji, Kuma karki saka kanki a damuwa domin komai muƙaddari ne daga Allah. In Sha Allah hakan alkhairi ne a gareki.
Nagode yayanmu.
Abunda ta iya cewa kenan ta kashe wayar. Shi ne yaya Ali ya bar wajen aikinsa ya je gida ya sanar da Baffa, wanda a jiyan Baffa ya tura motar kwashe kaya. A lokacin da Jabir ya dawo gidan cikin dare wajen ƙarfe goma ya samu ta fara fito da kayan amfaninta tsakar falo, ya tsaya turus yana mamakinta, duk a zatonsa idan ya dawo ƙila ta shiga cikin hankalinta zasu zauna suyi sulhu amma sai yaga saɓanin haka. Ya ƙarasa kitchen da ya ji motsinta, ya riƙe ƙofar yana cewa.
Me kike nufi naga kina haɗa kaya.?
Baffa ne ya aiko da mota idan sun ƙaraso zuwa safe zasu kwashe kayan.
Hmmmm babbar magana, har kin sanar musu kenan, dama nasan duk abunda kike min da sa hannunsu a ciki. Babu matsala na san zaki dawo ai.
Ya ƙare maganar cikin gadara ya ɗage kafaɗa ya wuce. A lokacin ya sauke numfashin dawowa daga tunanin abunda ya faru jiya.
Tabbas zaki dawo Safiyya, na baki sati ɗaya, idan baki dawo ba na ƙara miki mako biyu, idan nan ma baki dawo ba to na baki wata guda, na tabbatar zuwa lokacin hankalinki ya dawo jikinki zaki san muhimmanci na a rayuwarki.
Ya ƙare maganar yana hura iska mai ɗumi daga bakinsa sai ya buɗe ƙofar falon ya shiga ciki, kujerun falon suna nan kamar yadda suke dama nashi ne shi ya zuba, waɗanda suke Kano ne nata ya san suma zasu kwashe su, amma yana jin kwarin guiwar cewar komai zai dawo a muhallinsa bisa yaƙinin Safiyya sai ta bawa iyayenta kunya, shiyasa baya jin wani damuwa sosai dan shi kaɗai yasan irin gubar soyayyar daya shayar da ita babu namijin da zata samu haka a gunsa, ya riga ya yi raga-raga da zuciyarta da soyayyarsa, sai ya saki murmushi dan tabbas shima zai rama abinda tayi masa ne ta hanya guda, shi ne zai ƙara auro a cikin ƙanƙanin lokaci yadda zata tabbatar da cewar yana da madafa ba ita ce Autar mata ba, ya ƙarasa kitchen yaga an kwashe komai sai tsirarun abubuwa wanda yake shiya siya da kuɗinsa, bai yi mamaki ganin Safiyya ta bar masa su ba dan shi ne ya faɗa, kuma yasanta da baƙar zuciya zata barsu ko dan ta nuna masa ta isa. Wayarsa da ya yi ƙara shi ne ya saka shi kawar da tunanin ya ciro daga aljihunsa ya duba, Ummi ce mahaifiyarsa ta kira shi, ya bar kiran ya katse kafin ya kirata, ko da ta ɗaga cewa tayi.
Safiyya sun tafi ko.?
Sun kwashe komai Ummi ta bar ni da kewa, amma kuma wlh ba zan bi bayanta ba sai ita ce zata kawo kanta dan nasan ina da muhimmanci a cikin rayuwarta. Ni aure ma zanyi yanzu haka akwai wacce na fara nima anan Abuja, sai dai bamu gama fahimtar juna ba.
Idan kayi haka shi ne ka tabbatar min da kai jinina ne, Jabir ka barta daga ita har iyayenta zasu yi danasani. Amma ni ina da wacce na zaɓar maka, Zaliha 'yar ƙawata Hajiya Maryam, nafi so ka auri wacce muka sani gaskiya.
Amma Zaliha ta gama karatu ne naga tsarar Ikilima ce fa, nifa bana son raini ne.
Au rainin me Jabiru.? ana maganar aure, kuma ai Zaliha ta girmewa Ikilima da shekara guda, yanzu tana shekara ashirin da biyar ta kusa gama bautar ƙasa ma.
To shikenan bazan ƙi zaɓinki ba dama wancen yarinyar naga tana ja min aji da jin kai, kuma Zaliha zata iya maye min gurbin Safiyya tunda tana da kyau itama.
Sosai ma ai harta fi Safiyya farar fata, yanzu kayi ƙoƙari ka shigo Kano cikin satin nan ka je ku gana, sannan nima Gobe In Allah ya yarda zanje na samu Hajiya Maryam da magana, dama fa kwanaki ta kawo min maganar ko mu haɗa ku ne, nace tukuna muga kamun ludayin Safiyya, tunda taƙi zama sai ka yi auren ka koda ta dawo tasan cewa kana da wata matar ba ita kaɗai bace balle ta samu zarafin yi maka wulaƙanci.
Nagode Ummi kuma da so samu ne, ina so nan da wata biyu ayi komai a gama.
To me zamu jira.? Abu ne na gida tunda an san halin kowa ba ɓata lokacin yin bincike. Allah ya tabbatar mana da alkhairi kuma karka saka damuwa a zuciyarka kaci abinci ka riƙa bacci, kaji na faɗa maka.
In Sha Allah Ummi nagode.
Tace to kafin ta kashe kiran ya nufi ɗakinsa dan ya watsa ruwa yaji daɗin jikinsa, sai ya shirya kuma ya tafi cin abinci, maganar da yayi da Ummi shine ya ƙara masa ƙarfin guiwa da jin cewar Safiyya bata isa ta saka masa damuwa ba, zai cigaba da walwalarsa kamar komai bai faru ba dan yana da tabbacin dole zata dawo gare shi.
*****
Mujaheed.
Wajen ƙarfe tara da mintuna aka kwaɗa sallama a ƙofar gida, baba da fitowarsa kenan falon ya kammala wanka harya shirya cikin jallabiya na bacci, ya miƙe ya fito yana amsa sallamar ya saka takalmi ya fita waje, koda ya fita ya tadda malam Mati da Na'ibi a tsaye, baba ya ƙarasa ya basu hannu suka gaisa sai ya ce cikin kulawa.
Na'ibi kai ne da kanka.? ai da ka aiko har gida zan zo na same ka.
Kar ka damu malam Musa dama kan batun wannan yaron ne Mujaheed muka zo. Ɗazun malam Mati yazo min da wata magana shi ne nace bari mu zo tare mu faɗa maka dan a yiwa rufkar hanci.
Subhanallahi me kuma Mujaheed ɗin ya yi.?
Cewar baba cike da damuwa, Na'ibi ya Kalli Mati.
Kayi masa bayani ko.
To Malam. Yauwa abunda ya kawo mu ina so ka jawa ɗan wajenka kunne ya daina yiwa mutane fitsari a ƙofar gida saboda kar Tarbiyyar yaranmu ya taɓu, ɗazun nan da safe yaron nan ya taƙarƙare ya buje jiki yana fitsari a ƙofar gidana, to Sadiya 'yar wajena ta fito zata je Islamiyya sai tayi arba da shi, kuma tace taga al'auransa a waje zahiri abun dai babu daɗin faɗa, shi ne nace gwara na sanar da Liman to ban samu haɗuwa dashi ba sai na faɗawa Na'ibi shi ne yace muzo mu faɗa maka, Ato kaji.! Dan gaskiya in yana haka to za a samu matsala tunda muna da yara mata gasunan burjuk a unguwa kar ya shiga tsorata su.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to dan Allah kuyi haƙuri In Sha Allah zan yi masa magana hakan ba zai sake faruwa ba. Ku ƙara haƙuri lamarin Mujaheed wlh nima ƙara bani tsoro yake yi domin kullun babu sauƙi.
Ya ƙare maganar a raunane kamar zai fashe da kuka, Na'ibi ya ce cikin kulawa.
A cigaba da addu'a In Sha Allah zai samu lafiya kuma a ɗaure ana kula da Tarbiyyarsa tunda kwakwalwar ba dai-dai take ba, wala'alla ko mai yaga ana yi koda abu ne mara kyau zai ce zai yi, idan ya haɗu da 'yan shaye-shaye sai su koya masa kaga lamari ya ɓaci, shiyasa wannan gararamba da yake yi bayi da amfani.
In Sha Allah za a kula, Allah ya datar damu.
Cewar baba cikin yanayi na ɓacin rai dan sam maganar Na'ibi bai yi masa daɗi ba.
'A bar shi yaji da ɗaya mana ba sai an ƙirƙiro masa wani alkaba'iran ba.'
Duk wannan zancen a zuciyarsa yayi a fili kuma ya ƙara basu haƙuri yayi musu godiya, a haka suka rabu baba ya shiga gida ransa a ɓace, a tsakar gida ya tadda mama tana jiransa ya shigo, kuma labarin zuciya a tambayi fuska.! ta gama fahimtar duk abunda aka faɗa masa to tabbas ba mai daɗi bane.
Allah yasa lafiya.?
Ƙarar Mujaheed aka kawo min.
Kai Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wai kullun dai Mujaheed, yanzu kuma me aka ce yayi.?
Mama tayi maganar kamar zata fasa kuka dan damuwa, baba ya kwashe labarin komai ya faɗa mata, mama ta shiga tafa hannu tana salati.
Yanzu malam Mati bai ji kunyar kawo maka wannan maganar ba, kuma shima Na'ibi da mutuncinsa ya biyo shi. Mujaheed da bashi da cikakken hankali me zai kai shi tunanin lalata musu yara. Allah ya isa.! dan wannan sharri ne kawai, yace dai yayi fitsari a kwatan gidansa karya ƙara bawai ya jingina hakan da lalacewar Tarbiyyar Yaransu ba.
Sai ta ƙare maganar tana fashewa da kuka, jikin baba ya ƙara yin sanyi ransa yana suya.
Haba Uwale ke ce me ƙarfafa min guiwa akan lamarin Mujaheed, yanzu idan kina kuka wajen waye zanje naji sanyi.
To malam lamarin ne har da niman yi masa sharri, abun ne da cuwo.! Mujaheed kwaya nawa yake shekarunsa sha takwas fa kawai, koda yana da hankali meya sani balle ma babu hankalin.
Nima shi na gani, Allah dai ya kyauta. Ina yake ma ko har yanzu bai dawo ba ni wlh yawan yawo da yake yi ɗin nan yana damuna.
To ya zamu yi masa, ko turkeshi zamu yi kamar wani dabba, idan baka manta ba farkon matsalarsa yawan kaɗaita kansa da yake yi ne masomin komai.
Mama ta ƙare maganar tana share hawaye, baba ya jinjina kai.
Tabbas gwara ya shiga mutane wataƙila abubuwan zai fi yi masa sauƙi. Muje ciki dan na fara jin bacci.
To ya batun rufe ƙofar gida.?
Ki bar masa shi a buɗe in ya dawo zai shigo.
Cewar baba daya yi gaba yana shiga cikin ɗaki, mama ta taɓe baki tana ambaton Allah ya kyauta sai ta koma ciki itama dan ta yi shirin bacci, Mujaheed daya gama jin hirarsu ko kaɗan bai damu ba duk da akansa ne suka yi maganar, sai ya fito ya nufi kitchen ya soma buɗe-buɗe, anan ya ci karo da abincinsa a kwano, wannan karan ba laifi da ɗan yawa tasa masa, sai ya ɗauka da ruwa ya fito ya zauna ya ci, daya gama ya koma ɗakinsa ya kwanta ba jimawa sai bacci. Mama da tun dama tasan yana nan kuma taji motsinsa a tsakar gidan sai ta cewa baba ya dawo dan haka ta fito ta rufe kitchen, taje ƙofar gida shima ta rufe kafin ta dawo zuwa bedroom ɗinta ta kwanta tana mai lumshe ido da lissafin bikin Aina'u dan shi ne ya fi tsaya mata a zuciya, ta ƙosa ayi a gama ko zata samu natsuwa hankalinta ya dawo jikinta, dan babban burinta ta kawar da ita a gabanta sai ta fara yiwa Zahra tanadi dan itama ta fara gurma shekarunta sha ɗaya.
Rahma ce.