DUHU BAYAN MURMUSHI

8

by @rahmakabir13

*DUHU BAYAN MURMUSHI*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 8.

Sarac Stars R Pen...✍️

Yin sana'a ko aiki garkuwa ce ga mace muddun kina kiyaye dokar Allah kuma kin tsaftace zuciyarki sai Allah ya dafa miki. Ƙalubalen Safiyya bana rashin ci ko sha bane ko rashin kulawa ba, ƙalubalenta na yawan buƙata ne wanda tun asali Jabir ya sabar mata, sannan kuma tunda ta dawo take fama da zubar jini lokaci zuwa lokaci wanda yasa ta ƙara ramewa tayi haske, kullun suna cikin zaryar zuwa asibiti tana shan magunguna har sauƙi ya fara samuwa a hankali, sai ƙalubale na gaba shi ne ta saba da cin abincin da ranta ke so ta dafa taci ko su fita suci a gidan abinci, duk da anan gidansu akwai rufin asiri amma kuma abincin da suke ci na yau da kullun ne sai na gargajiya, babu irin abincin turawa ko cin nama akai akai ko cin daɗi da kwalama, hakan yasa duk 'yan kuɗin data zo da su suka ƙare wajen siyan kayan ciye-ciye, musamman da bata jure cin karin safe na gidan ta gaji da shan kunu da ƙosai ko doya, idan kuma tea zasu sha ba yadda take so bane, wani lokacin sai ta aika an siyo mata madara ta ƙara. Wata guda da dawowarta amma ta gundura da zaman gidan shiyasa wani lokacin sai take ji kamar tayi tsuntsuwa ta koma gidanta amma kuma Jabir bai bata damar haka ba, dan tun sa'ilin data dawo bai taɓa kiranta ba ko da flashing ne, sannan bai yi mata magana ba a WhatsApp kuma tana ganin status ɗinsa yana ganin nata amma basa magana, wani lokacin sai taji kamar tayi masa magana amma kuma in ta kira me zata ce masa, sannan ma in ta tuna da zancen da yayi mata akan zata dawo ta bashi haƙuri sai taji ta sare, soyayyar sa yana ta nuƙurƙusarta har yau ba zata ce ta daina ba sai dai haushinsa da take ji, wanda da zarar ya zo sulhu babu ja zata sauko ta koma ɗakinta, duk da a baya tana ganin ta rabu da shi har abada ashe na ɓacin rai ne ba zata iya ba.

***

Jabir.

A ɓangarensa kuwa shima yana cikin damuwa na rashin ji daga Safiyya dan duk a zatonsa sati biyu yayi yawa zata waiwaye shi, amma sai gashi an shafe wata guda shuru bata tuntuɓe shi ba, sai dai tunaninsa ya bashi 'yan uwanta ne suka cigaba da yi mata famfo shiyasa ta nuna masa taurin kai, amma a yadda yasan Safiyya tana da rauni kuma tana son shi sosai, ya tabbatar zata dawo gare shi, sai dai a yanzu abu ɗaya ne zai zaburar da ita ta dawo ɗakinta in ta ji zancen aurensa, dan magana ta kankama har an tsayar da rana nan da sati biyar, wato wata ɗaya da mako guda, zuwansa Kano sau biyu amma bai yi tunanin yaje ya ga Safiyya yayi bikonta ba, domin Umminsa ta gama yi masa famfo akan karya kuskura yaje ya saukar da kai su ƙara raina shi, gwara ya barta ta gwaru a gidan in ta gane zaman ba daɗi to in ta dawo masa zata kiyaye ɓacin ransa tabi umarninsa, a cewarta ma ya haƙura da ita kwata-kwata tunda haihuwar ta zai iya zama musu matsala ita kuma tana son jikoki daga gare shi, shiyasa ta ƙara bada ƙaimi wajen aurensa da Zaliha har aka tsayar da rana suka fara shirin biki, dan tace yanzu ne zai mori aure, ya auri lafiyayya wacce ba zata haifo masa matsala ba. Kuma ya gamsu da maganar ummi amma banda zancen ya haƙura da Safiyya domin har gobe yana sonta, yana fatan su shirya su komawa aurensu, amma fa dole sai ya tabbatar da Safiyya ta aje burinta ta bi zaɓinsa, kuma a yanzu daya ji shuru bata nimeshi ba ya tabbatar idan zancen aurensu yaje kunnenta zata kira shi, dole ma zata nima sulhu su shirya kuma hakan ba zai sa ya fasa auren ba, dan itama Zaliha yana sonta kuma ta kasance irin kalar zaɓinsa dan bambancinsu da Safiyya kamanni ne, amma ta surar jiki kusan duk ɗaya suke da kaɗan Safiyya zata fita tsawo da kumari, wanda yasan itama Zaliha in ta samu cikar ɗaki zata yi kumari. A cikin ɗan lokacin da aka haɗasu soyayya suke gudanarwa mai tsafta, dan sosai Zaliha ta bashi dama saboda ita dama tuntuni Jabir yana burgeta, shiyasa babu ja ta amince da auren, kullun suna maƙale a waya ko WhatsApp chart, shiyasa ma Jabir bai damu sosai da rashin Safiyya ba domin Zaliha tana ɗebe masa kewa.

Lokacin da biki ya yi saura sati uku a sannan har an bugo katin biki wanda suka shirya event kala-kala, dan ummi ta shiryawa bikin sosai, ta sayar da ɗaya daga cikin filin gadonsu ta zuba a sha'anin, suka haɗa a kwati seti biyu cike da kaya, abu dai na masu hannu da shunu, dama mahaifinsu Jabiru Alhaji Aminu mai kuɗi ne babban ɗan kasuwa kuma ma'aikacin gomnati, bayan ya rasu ne suka samu gado mai tsoka, dan su huɗu ne Yaransa, Jabir ne babba sai Nura ke bi masa sannan Ikilima da Rahma autarsu. To bayan rasuwar babansu Ummi ta ƙara aure tana auren wani malamin makarantar secondary, matarsa ɗaya da yara shida, bashi da ƙarfi sosai shiyasa yake biyo ummi gidanta a duk ranar kwananta, kuma ta ɗauke masa ciyarwa sai ɗan abunda ba za a rasa ba in ya kawo suyi amfani da shi, bata haihu da shi ba sunan dai yana miji amma Umma ke mulkarsa domin arzikinta yasa ya amince da auren ta, saboda ita ce ta nuna tana sonsa tun farko shiyasa, su Jabir basu so auren ba amma data dage sai suka barta tayi kuma cikin ikon Allah auren nata sai ya zame musu garkuwa dan babu mai yi musu kallon 'ya'yan mace, Nura shi ne ya cigaba da kula da kasuwancinsu yayin da yana cigaba da karatunsa na masters a fannin kasuwanci, bai yi aure ba amma yana da niyya dan har ya fara nema, Ikilima kuma tana jami'a aji na uku yayin da Rahma take secondary aji biyar, yara ne da suka taso cikin gata duk da mahaifinsu ya rasu amma basa cikin maraici musamman da Malam Hafiz mijin Ummi ya zame musu uba, kuma sauran 'yan uwan babansu suna iya ƙoƙarinsu akan lamarinsu dan suma suna da rufin asiri. Maganar auren Jabir ma sune suka yi ruwa da tsaki har aka bashi auren Safiyya, wannan da zai ƙara ne ummi ta bawa malam Hafiz dama ya shige gaba wajen auren, sai dai ta sanar da 'yan uwan baban cewar zai ƙara aure mijinta ya yi komai, suka saka albarka da addu'a.

Ikilima suna zaune da Ummi a falo suna ta duba kayansu na fitar biki da aka fara amso wasu daga wurin ɗinki. 

Ummi banga Shaddata ba fa. 

To Ikilima ai ba a gama kawo ɗinkin ba. Kuma da sauran kwanaki tunda saura kwana ashirin yau. 

Hakane, amma ummi wai ni ko yaya ya sanar da Safiyya kuwa.?

Anya bai faɗa ba, kuma bana so ma taji a bakinsa, ke ni ina fatan ma aurensu ya rabu kenan bana son wata alaƙa ta kuma haɗasu, kinsan har yanzu tana cikin idda to da zarar sun fara magana wataƙila su shirya kafin auren azo magana ya nima rugujewa tunda yana mugun sonta, shiyasa nake ta yi masa famfo akan karya kuskura ya kirata ya rabu da ita har sai ta nime shi da kanta su shirya, kin ga kuwa abu ne mai wuya tunda har iyayenta suka jagoranci kashe mata aure ba zasu taɓa bari ta koma ba. 

Hakane kuma, ni wlh tausayi ma take bani, data yi haƙuri ta bi yadda yaya Jabir ya tsara musu da ba azo wannan maganar auren nasa ba. 

Cewar Ikilima cikin damuwa, Ummi ta galla mata harara. 

Kina nufin baki son aurensa da Zaliha. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Ikilima.! karki zama mai fuska biyu mana, ko Zaliha ba ƙawarki bace da kike wannan maganar. 

Ummi nifa tausayi ta bani shekara takwas da aure ace su rabu, gashi sun samu rabo bai jima ba ya rasu. Allah dai ya zaɓa musu bafi alkhairi amma ni ina son zamansu ya dawo dan bani da matsala da Anty Safiyya tana da kirki. 

Ba shakka ai saiki je kiyi bikonta ta koma ɗakinta ko, Rahma ɗauko min wayata in zaki fito ɗaga dakin nan. 

Ummi ta ƙare maganar cikin buɗe murya ga autarta, Ilkima ta fahimci ran ummi ya ɓaci sai ta saki murmushi. 

Allah ya huci ran ummi nima ina farin ciki da wannan auren da za ayi, baki ga yadda nake ta gayyatar Kawayena ba.

Ke dai kika sani da munafurcinki. 

Ummi ta faɗa tana cigaba da duba ɗinkinta, Ilkima ta miƙe riƙe da kayan ta kala biyu ta wuce zuwa ɗaki ta aje, ta zauna a gefen gado ta aje kayan sannan ta shiga duba numbern Safiyya a wayarta, data zo kan number kamar zata danna sai kuma ta fasa dan bata san ta ina zata fara yi mata bayani ba, kuma tana so tayi mata bayanin auren Yayansu dan ya dace ta sani ko zata yi tunanin komawa ɗakinta, dan gaskiya tana mugun son su koma aurensu tana son Safiyya saboda kirkinta sam ba tada matsala, wani tunani ya faɗo mata sai ta yi saurin shiga WhatsApp ɗinta ta duba numbern Safiyya sai ta shida tayi mata sallama taga yayi makin biyu, alamar tana online sai ta shiga wajen gallary ta ɗauko hotun katin auren Yayansu ta rubuta a ƙasa kamar haka. 

Anty dan Allah kiyi ƙoƙari ki shirya da yaya ki koma ɗakinki kafin aurensa, ni dai ina so ki koma ɗakinki. 

Sai ta tura mata, tana gamawa ta miƙe ta saka kayanta a wardrobe ta ɗauki wayar ta fito falo ta shiga da sabgoginta. 

****

Safiyya. 

Tana kan tiktok ne sai mama ƙarama ta kirata tsakar gida shi ne ta fita, daga nan bata dawo ba ta cigaba da kama mata aikin abincin rana sai da suka tsayar da sanwa kafin ta koma ɗaki lokacin wajen sha biyu da rabi, sai ta shiga bayi tayi fitsari daga nan ta ɗauro alwala ta fito ta shimfiɗa dadduma ta gabatar da nafila wanda a lokacin an kira sallar azahar, ta zauna tayi lazumi kafin ta miƙe ta gabatar da farilla, bayan ta idar ta jima tana zaune tana addu'a, data gama sai ta miƙe ta naɗe sallaya ta aje da hijab ta hau gadon, ƙiri-ƙiri ta mayar da ɗakin mama ɗakin baccinta dan in mama bata da girki tare suke kwana, in kuma itace da Baffa to mama a turaka take kwana, mama bata hanata kwana a ɗakinta ba duba da tana buƙatar a bata kulawa da rarrashi, sai lokacin da anty Indo ta zo ne take cewa ta koma ɗakinsu Kausar mama ta shigar mata tace babu ruwan ta, yadda Safiyya take jin daɗin in Anty Indo ko yaya Ali suna niman takura mata mama ce ke shigar mata ta tsawatar. Ta kwanta kafin ta ɗauki wayar ta cire a key nan ta ga notification da number ɗin Ikilima a saman wayar na WhatsApp, sai ta shiga app ɗin ta buɗe cike da mamaki, dan tun da ta dawo gida babu wani daga gidansu Jabir da ya yi mata magana ko da kiran waya ne, sannan ma babu wanda yazo gidansu da sunan biko, yadda suka zuba ido basu zo ba nan ma gidansu haka suka zuba ido babu wanda ya nima Jabir ko wani nasa, kafin ta sauke hoton data turo mata sai da ta fara karanta saƙon dake ƙasa, gabanta yayi wani irin mummunar faɗuwa wanda sai da numfashinta ya sauya, ta shiga fizgo shi da ƙarfi dan kamar yana yi mata wuyar ja da fitarwa, cikin rawar hannu ta buɗe hoton ta soma binsa kamar wacce ta warke cutar makanta, zahiri Jabir ne zai yi aure kuma tunda Ilikima ta faɗa tasan ba zata taɓa yi mata ƙarya ba dan basa ma irin wannan wasan, zuciyarta tayi mata nauyi, dama ta daɗe da saka wannan tunanin a cikin ranta akan Jabir zai nima ƙara aure nan gaba tunda ita ga tsarin daya sakata na ba zata haihu ba sai nan gaba, to tabbas ko dan saboda ummi ta samu jika zai yi tunda tasan tana son jikoki, wato ya so ya cigaba da zama da ita ya kasheta shi ya raya kansa, hawaye mai ɗumi ya sauka a kuncinta sai ta fita daga WhatsApp ɗin ta shiga wajen kira, yau dai dole ta karya billenta ta kira shi, number Jabir ta saka domin ta haddace ba zama ta tsaya dubo shi daga contact ba, ta danna masa kira. Jabir yana tsaka da aiki a office yaji kira daga wayarsa ya ɗauka yaga Safiyya ce, sai da yayi ƙayataccen murmushi dan bai yi wani mamaki ganin kiranta ba domin yasan dole zata kira shi, musamman in ta ji labarin aurensa duk da bai faɗa mata ba amma yasan zasu ji tunda maganar aure baya ɓoyuwa, ya ɗaga da sallama amma sai yaji muryarta cikin kuka. 

Yanzu Jabir akan ka zo kayi bikona muyi sulhu ka mayar da aurenmu shi ne ka zaɓi yin aure dan ka ƙuntata min ko. Dama na jima da wannan tunanin dole za a zo gaɓar da zaka ƙara aure tunda ni kaƙi yarda na haihu saboda kar na haifo matsalar da zai zame maka kaya dan baka gama tara arzikin da zaka kula damu ba, babu komai Allah yana kallon komai kuma ka gama nuna min halinka. 

Haba Safiyya ya kike magana kamar ni ne kaɗai mai laifi, kema kinsan ba zai yuwu ki haihu ba duba da daga ni har ke bamu shirya hakan ba, kuma wannan auren Ummi ce ta haɗa shi wai kar na zauna babu mata tunda iyayenki sun mara miki baya wajen kashe aurenki. Wlh har gobe ina son zama dake, ina sonki, idan kin yarda akan tsarin dana yi mana, yanzu ba sai anjima zan kamo hanyar kano na zo har gida na mayar da aurenmu mu dawo Abuja tare. 

Ya ƙare maganar yana sauraren nishin kukanta, mamaki ya gama cika Safiyya da jin wai bai sauya ra'ayinsa ba, ta yi murmushin takaici tace. 

Kana nufin har yanzu kana kan bakanka kenan, lallai Jabir kana da son kanka da yawa, ai kaci moriyar ganga dole ka nima mai lafiyar da zata haifa maka yara lafiyayyu, to bari ka sani wlh nima ina nan akan bakata kar kaga na kira ka kayi zaton na gaji da zaman gidanmu ne, na kira dama naji tabbacin aurenka kuma naji nagode. 

Tana gama faɗar haka ta kashe wayar ta aje akan gado ta fita tsakar gidan cikin sauri hanya yana haɗe mata saboda hawayen daya cika mata ido bata gani sosai. 

Rahma ce.