SULTANİM

Chapter 4

by @msssamher590

SULTANIM

     Na

Mss Samher

 

Instagram mss_samher

Tiktok mss_samher

Wattpad mss_samher

 

 

Page4

 

Ma’aikata na gaishesa wasu suna masa sannu da zuwa hannu kawai yake daga musu harya isa office ɗinsa.

 

“Architect: Umar Faruq Muhammad Hameed” shine rubuce a jikin door and desk name plate ɗin office dinsa, Hisham ne ya shigo riƙe da tarin files a hannunsa Faruq dake kallonsa ya yamutsa fuska yana faɗin

 

“Aikin kenan bazama a bar mutun ya huta bah”

 

Hisham yace “you most be teasing me har wani hutu kake nema bayan wanda kasha.” 

 

Banza ya masa sai wani bata fuska yakeyi, nan dai Hisham ya masa bayanin duk abubuwan daya kamata yasani dan sun kammala duka project ɗin daya bari a kasa har sun fara sabbi.

 

 

Kaduna

 

Abba ya kallah Baffa dake shirin barin dining yace

 

“Kayi kokari ka tura musu message ɗin saboda a fara aikinka da wuri.”

 

“I will, In sha Allah.” Wannan yana ɗaya daga cikin manyan burinshi bada aikin gina company ɗinsa a 

Prime Stone Builders.

 

Umma tace “Kai tarayya da mutanan arziƙi akwai dadi yaro ƙarami sai kuɗi Allah ya basu.

 

Kallonta kawai Abba yayi batare da yayi magana bah dan tuni su Baffa sun bar wajan.

 

Saida tagama santinta sannan Abba yace “Nan da sati biyu ne tafiyata zuwa China kuma tare da Mahmud zamu tafi wannan ƙaran ina tsammanin zan dade akalla wata hadu zuwa biyar.

 

“Shikenan Abbansu Allah ya kaimu kuma Allah ya bada abinda za’aje nema.

 

 

Mama ce ta kira Nadrah a karo na uku Jin shiru yasata nufi ɗakinta zaune take akan ɗan karamin gadonta ta zabga tagumi ƙarasawa Mama tayi ta zauna tare da dafata idanuwanta dasuke cike da kwalla taɗago kawai saita rungume Mama tafashe da kuka.

 

Ahankali Mama ke shafa bayanta harta fara sauke ajiyar zuciya Mama tace

 

“Meke damunki Nadrah tun safe nake ganinki haka yanxu kuma kin shigo ɗaki kina tunani harda kuka menene matsalar? ta ƙare tambayar tana ɗago fuskanta.”

 

Muryanta a sanyaye tace 

 

“Mama bansani bah amma zuciyata babu dadi kuma sai mafarki marasa dadi nakeyi kwana biyun nan, tayi maganar wasu hawaye nazuba akan fuskanta.

 

Cikin sanyin jiki Mama kefaɗin “Ya isa haka irin waɗannan abubuwan duk suna faruwa amma addua akeyi kiyawaita maimaita Hasbunallahu wani’imal wakeel kinji Khairan in sha Allah.”

 

Nan dai Mama ta kwantar mata da hankali, Sai bayan Isha Baba yashigo gida saboda yanxu shine limamin babban masallacin unguwar akwai hidimomi sosai a kanshi.

 

Mama ta kawo masa ruwa da abinci tana masa sannu da zuwa, numfashi ya sauke yana faɗin 

 

“Jagoranci ba matsayi bane kawai, nauyi ne da sadaukarwa.

Ina Nadrah?, banji ɗuriyarta bah ya ƙare tambayar yana ɗan waige waige. 

 

Nan tabashi labari abun daya faru dazu yace ta kira masa ita, zama tayi kusa da Baba ahankali ta furta

 

“Sannu da zuwa Baba banji shigowarka bane.”

 

“Fateemah”

 

Da sauri ta ɗago jinya kirata da sunan da bai taba kiranta dashi bah.

 

Sosai Baba yamata nasiha tare da nuna mata muhimmancin addu’a da haƙuri, jikin Nadrah yayi sanyi kuma ƙasan zuciyarta nacike da tsoro da fargaba.

 

Ta dauki kusan kwana uku a wannan yanayin kafin ta warware gaba ɗaya, wata irin soyayya takeyi wa iyayanta na ƙololuwan matakin ƙarshe.

 

 

Abuja

 

Agajiye Faruq yake dan haka ƙarfe huɗu daidai ya bar office, sai daya shiga part ɗinsa yayi wanka sannan yazo bangaran Mami. 

 

Ita kaɗai ce a parlorn su Zaina sunje gidan wata ƙanwar Mami, kusa da ita ya zauna tare da ɗaura kansa saman cinyarta

 

“Mamina barka da gida”

 

Yawwa yaron mami ya office i guess kagaji saboda idanka yanuna haka. Tayi maganar tana shafa sumar kansa. 

 

“Mamina yunwa” ya furta ahankali. 

 

“Abu” mami ta kwalama kira. kawoma yarona abinci, a ranta kuma tana tunanin wace mai sa’arce zata samu ɗanta😹.

 

Wacce Mami takira da Abu tafito daga kitchen ɗauke da tray saida tajera masa a dining sannan taƙaraso parlorn tana faɗin 

 

“Alhaji ƙarami barka da shigowa.” 

 

Ɗaga kanshi daga chinyan Mami yayi yace

 

“Jiya kamar banganki ba”

 

Yau nadawo daga ƙauye Alhaji karami. 

 

“Okay! ya faɗa a taƙaice”

Bata tsammaci wata maganan bah dan haka ta bar parlorn.

 

Saidaya gamacin abinci sanna yadawo gurin Mami, a natse tadubeshi tace

 

“Ya maganan da Dad ɗinka ya maka he’s very serious this time around saboda koh jiya da daddare yamin magana.”

 

Idansa ya lumshe kamar ammasa dole a magana yace 

 

“Mamina please”

 

“Shikenan tunda bakasan maganan amma wallahi duk abun daya taso karka nema Mami kuma, tana kaiwa nan tabarshi zaune ta wuce ɗakinta.

 

Koda ya fita sallah bai dawo bah saida akayi isha kuma part ɗinsa ya wuce, saida yayi shirin bacci sannan yadawo parlor football yake kalla amma bawai dan yana ganewa.

 

Wayarsa da aka kirane ya dawo dashi daga duniyar tunanin dayake ciki Hisham ne dan haka ya ɗaga daga chan ɓangaran Hisham yace 

 

“Yaran Mami ina ka’ajiye wayar inata kira tun dazu”

 

Ya akayi?.

 

Hisham yasan halin Faruq sosai he’s his only bestfriend tun suna school dan haka har shirunsa yana ganewa yasaba da halinsa na rashin son surutu da hayani dan haka suke zaune lafiya dan Hisham nada haƙuri.

 

Hisham yace “Swafiyya ta kirani, please man ka saurareta am sure she will explain her self.

 

“Bana buƙata”

 

“Hey man nasan you love this girl just give her a chance. Daga haka ya yanke wayar dan yasan bah lallai ya amsa shibah”

 

Swafiyya kam she keep calling kozai ɗauka, around 10pm har bacci ya fara ɗaukansa saboda mutun ne bai baccin wuri yaji wayarsa guntu tsaki yaja gani mai kiran but he decided to pick.

 

Daga chan ɓangaran Swafiyya tayi ajiyar zuciya murya a sanyaye tace

 

“Am really sorry babe”

 

“Swafiyya!! Ya kira sunanta da wani irin murya daya tilasta mata lumshe ido.

 

“Are you still going to Australia?” Tambayar tazo mata a bazata amma cikin ƙarfin hali tace 

 

“Babe lemme exp…. Tsawan daya daka mata yahanata ƙarasawa cikin fushi yace 

 

“Swafiyya are you going or not?”

 

Cikin aro jarumta tafurta

 

“Yes of course i’m going”.

 

Yanke wayar yayi tare da kasheta gaba ɗaya yana furzar da wani irin iska mai zafi daga bakinsa.

 

 

Yau juma’a misalin ƙarfe biyu da rabi Baba ya shigo da hanzari, fitowar Mama kenan daga ɗaki sanye da hijab ganin Baba yasa tasaki murmushi tana faɗin

 

“Na shirya Malan.”

 

Nadrah dake zaune saman kujera yar tsugunno idanuwanta akansu Baba ya dubeta yace

 

“Mamana mekike kallo?, murmushi tayi tace

 

“Babu komai Baba! Allah ya tsare yadawo daku lafiya”.

 

Shafa kanta Mama tayi suka Amsa da Amin tare da barin gidan.

 

Har wajan karfe biyar su Mama basu dawo bah haka yasa hankalinta fara tashi jin motsin anshigo gidan yasata fita da sauri……..