Chapter 5
SULTANIM
Na
Mss Samher
Instagram mss_samher
Tiktok mss_samher
Wattpad mss_samher
Page5
Turus tayi ganin Ya Baffa tsaye, bakinta har rawa yakeyi wajan furta “Ya baffa, su Baba sunfita tun ɗazu basu dawo bah.”
“Sa hijab kizo muje” yafaɗa a sanyaye.
Ƙirjinta ne yabuga da ƙarfi amma babu fuskan tambaya, dan haka tasaka hijab tabi bayansa.
Ganinsu a gidan Abba ga mutane dayawa a tsakar gidan yasa ƙafafunta suka fara rawa, zuciyarta na bugawa kamar zata faso ƙirjin.
“Ya baffa…” ta kira a firgice.
Bai amsa ba saidai idanuwansa sunyi jajur. Ya kama hannunta a hankali suka shiga cikin gidan.
Kai tsaye yawuce da ita ɓangaran Abba “ki zauna anan ina zuwa.”
“Don Allah Ya baffa…. Meyake faruwa ne?” ta tambaya muryanta na rawa.
Abba ne ya shigo yana faɗin “Baffa jekayi alwala, ina saukowa.”
“Da toh”, kawai ya amsa yafice.
Abba ya ƙarasa tare da jan hannun Nadrah suka zauna atare, ita kam da ido kawai take binsa dan kwakwalwarta yana daf da daskarewa.
Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, sannan ya kalleta da tausayi.
“Mamana…”
Muryansa ta tsaya na ɗan lokaci, Nadrah ta riƙe hannunsa da ƙarfi hawaye na taruwa a idanuwanta.
“Don Allah kafaɗamin Abba, ina Mama da Baba?”
Kiyi haƙuri Mamana, Allah ne yabamu su, kuma shine ya karɓe su. yanxu addu’armu kawai suke buƙata.
Ta tashi da sauri tana girgiza kai.
“Bangane me kake faɗa bah Abba, Baba yacemin yanxu zasu dawo.
Ƙoƙarin jan numfashi takeyi da ƙarfi amma iska yaƙi shiga ƙirjinta da ƙarfi tafurta
“Mamaaaa! Babaaa!”.
Ta faɗi ƙasa sumamma.
Ahankali take buɗe idanuwanta da suka mata nauyi, ta runtsesu naɗan wani lokaci saboda yadda suka mata nauyi kamar anzuba barkono.
Ƙoƙarin tashi tafara amma yadda takejin jikinta kamar babu ƙashi, Mahmud dake gefanta yafara ƙoƙarin ɗagata rungumeshi tayi tare da fashewa da kuka bai hanata bah dan shima daurewa kawai yakeyi.
Baffa yashigo ɗakin ɗauke da cup a hannunsa miƙa wa Mahmud yayi yana faɗin
“Bata tasha.”
Kanta kawai take iya girgizawa yayin da hawaye suka cigaba da zuba a saman fuskanta.
Baffa dake kallonta zuciyarsa cike da tausayi ajiyar zuciya ya sauke mai nauyin gaske, karban cup ɗin yayi daga hannun Mahmud sannan ya ranƙwafo yakai shi bakinta.
Dago idanuwanta da suke jawur ta ɗaura akan fuskan Baffa yadda fuskanshi yake bazata iya masa musu bah dan haka tafara bude bakinta ahankali tana sha saidai ta shanye gaba daya sannan yabar ɗakin.
Mahmud ya matsa kusa da ita a sanyaye yace
“Kiyi haƙuri Nadrah.. komai zai wuce in sha Allah.”
Kalamansa sunyi mata nauyi fiye da ƙarfin da take dashi. Sabon kuka ya kuɓuce mata kanta ta ɗaura saman cinyarsa kuka takeyi sosai irin na wanda ya rasa mafita.
Hannunsa dake kanta yake shafawa a hankali, baisan wace kalma zayyi amfani da ita wajan kwantar mata da hankali bah, abin da kawai ya sani shine rayuwarta bazata ƙara zama iri ɗaya bah.
KWANAKI UKU BAYAN JANA’IZAR
Abba ne zaune a babban parlorn baƙi tare da Dady, cikin jimami Dady ke faɗin
“Kayi haƙuri Alhaji haroon, haƙiƙa baku kaɗai akayiwa mutuwa bah ɗan uwanka mutumin kirki ne suna matsayi mai kyau in sha Allah.”
Abba ya gyada kai a hankali, idanuwansa sun cika da hawaye amma bai bari sun zubo bah. Murya mai nauyi yace
“Allah ya saka da alkairi. Ciwo ne baba amma dole mu karɓi kaddara, uba na rasa bah ɗan uwa bah. Nan Abba ya labartawa Dady wasu daga cikin sadaukarwan da Baba yamasa.
Dady ya sauke ajiyar zuciya yace “ lallai samun ɗan uwa irinsa a wannan zamanin sai an tona, Allah ya masa rahama ya kyautata bayansa! kuma yarsa ɗaya kace?.”
Abba ya amsa da “Eh” Dady ya jinjina al’amarin tare da masa fatan Allah ya basa ikon riƙeta da amana.
Sun jima suna tattaunawa kafin Dady ya masa sallama bayan sun gaisa da Umma.
Abba ya kalla Umma dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya hankalinta kwance “Nadrah taci abinci kuwa” ya tambaya yana kallanta.
Gaskiya bansani bah nadai saka Talatu takai mata tafaɗa cikin ko inkula.
Miƙewa yayi ya nufin ɗakin batare da yacewa Umma komai bah.
Abba ya tsaya gaban ƙofar ɗakin Nadrah na yan ɗaƙiƙu kafin ya tura ta a hankali. Akan Tray ɗin da aka ajiya saman wani stool idashi ya fara sauka wanda koh budeshi batayi bah sannan ya kai idansa ganta.
Kwance take yayin da jikinta ke lulluɓe da bargo, kusa da ita ya ƙarasa ya kalleta da tsananin tausayi.
“Mamana…” ya kira a hankali.
Tashi zaune tafara ƙoƙarinyi Abba ya taimaka mata tare da zama gefanta, Cikin ƙarfin hali tace
“Sannu da shigowa Abba.”
Kin tabbatar ni Abbanki ne?. Ya tambaya yana kallonta.
Da mamaki ta ɗan kallesa sanan ta gyada masa kai. Cikin kwantar da hankai Abba ya fara magana
“Kiyi haƙuri mamana. Ki kwantar da hankalinki sannan kiyi musu addua, na tabbatar suma baza suji dadin yadda kika takura kanki haka bah. nayi miki alqawarin bazaki taba kukan maraici ba domin ni da babanki duka abu guda ne.”
Murya na rawa tace “Abba meya samesu. Baba yacemin yanxu zasu dawo fah” ta ƙate faɗa tana fashewa da kuka.
Anan Abba ke labarta mata wani taro aka gayyaci Baba kuma kowa zaije da iyalinsa. Inda tun a hanyar zuwa wata babbar mota ta haukan motar su Baba, Kafin mutane su taru a wajan motar ta guda sannan sukuma….. a take a wajan Allah….. ya karbi abinsa…” ya kare faɗa a raunane.
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un… shi kawai Nadrah take iya maimaitawa. Abba ya dafa kafarta yace
“Yanxu kwantar da hankalinki da zakiyi shine zai ƙara musu natsuwa a masaukinsu, sosai Abba ya kwantar mata da hankali kuma taji zuciyarta ta samu natsuwa.
Hannunta ya kama sukaje parlor ya zaunar da ita a dining yasa Talatu ta kawo mata abinci, yana nan zaune saida ya tabbatar taci sosai sannan ya tashi ya barta bayan ya sake kwantar mata da hankai.
Tana shirin barin dinning ɗin Umma ta ƙaraso kallo ɗaya tayiwa Nadrah ta ɗauke kai, Nadrah tace
“Barka da fitowa Umma”
“Yawwa” Umma tafaɗa batare data kalleta bah.
Jikinta a sanyaye ta nufi ɗakinta, wanka tashiga ta wanke jikinta sosai kwana biyu kenan batayi wanka bah.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya Mahmud da Abba suna ƙoƙarin kula da ita dan bata cika ganin Baffa bah tunda bah wani fita parlorn ma takeyi ba.
Yau sati biyu kenan da rasuwan su Baba kuma yayi daidai da ranan da Abba zai wuce china shida Mahmud…..