27
MASIFAFFAN NAMIJI..!*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty💞*
_Gabadaya Shafin na yau Sadaukarwa ne gareki Bestyna *SA'ADATU ALKALI D/TSAFE..*❤️Ina Rokon Allah yayi Riko Da Duka Hannayenki Halinki na gari ya Biki..Alherin Allah yakai miki Har gadon Barcinki.._
*027*
"Tunda Mama Taji mganar Kai Abdullahi kara da Hajiya Sa'a tayi ikirari sai Hankalinta ya Tashi ammh bata Nuna ba sanin Halin Abdullahi na kafiya da Dakiya Tasan bazai Fasa ba kuma Bazai yarda anemi Sulhu ba sai dai in Hajiya Sa"an ne da kanta Ta nemi Sulhu.
Shiyasa Tun Safe batare da ta gayama Kowa komai ba ta Fita ta bar Gidan Auwal da jidda nata Tambayanta inda zata tace Ba Dadewa zatayi ba yanzu zata Dawo Tana Fita Bata zarce ko"ina ba sai gidan Baba Wada ta sameshi acikin Dakinsa,Inna Abu Ta Shiga tagayamai Zuwa Mama ita tamata iso Har Cikin Dakinsa Bayan sun gaisa ne Mama taKoramai Jawabin komai Ta Karishe da Fadin"Don Allah ina so ka Shiga Mganar nan Mallam..Kasan Halin Abdullahi bashi da Taushi Kuma Ra"ayi ne Dashi Gwara ka Shiga maganar kafin Hajiya Sa"a ta aikata Abunda tace kuma abubuwa suzo basu yi Dadi ba.."
Baba Wada yace"Ashha..Abu dai Baiyi Dadi ba...Ai ba"a Haka yanzu da baki gayamin ba Shi Abdullahin shuru zai yi kenan..?karki damu Insha Allahu hakama Bazata Faru ba ai shi Aure wani Abu ne na Ubangiji kuma Sulhu alheri Insha Allahu Tunda kin nemu Da na Shiga Mganar zan Shiga.."Mama Taji Dadi tayi ta godiya sai Bayan Tafiyarta ne Baba wada ke korama Inna Abu Abunda ke Faruwa baki ta Rike Tana Fadin"Oh ni Abu yau naga Abunda yafi zare tsayi..?Kajimin karfin Hali Barawo da Sallama wato Ita Tayi kudi bari ta Nuna ma Mutane karfin arziiki..Toh in ta Fasa kai Abdullahi kara Kotu Ta Raina Ubanta kuma Auren Hauwa"u da Nazifi ba Fashi da yardan Allah.."Kallonta kawai Baba wada yake yi yana Kada kanshi Afili ya Furta.."Mata..!Mata..! Sai a barku kawai.."
Kai Tsaye Baba wada ya Kira Abdullahi a waya yace in ya tashi Daga wajen aiki ya Biyo yana son Ganinsa Haka kuwa akayi yana Tashi kafin ya Karisa gida, ya Biyo Tare suka Shiga Sallar mangariba sai da suka Fito kana Baba wada yamai mganar da Mama Tayimai Kai Tsaye Abdullahi yace"Eh Baba..Ku barta ta kainin Kotun ina Jiranta Wlh.."
Baba wada yace"A"a baza"ayi haka ba Abdullahi in Rai ya baci Toh Hankali ke Nemoshi..Bazamu Biyemata ba ita mace ce mai Rauni kuma Zuciyarta bata da wani Dogon Nazari In ma mgana zamu yi ai ba da ita zamuyi ba..Tana da Wakilai da waliyyai akwai Iyayenta maza na Bangaran Uba dana Uwa Saboda haka na yanke Shawaran zan kira Nazifin da kaina namai Bayani Ko Ranar asabar ko Lahadi dukkamu zami Taci Chan samaru gidan Uban ita Sa"an Mu samu Koda wani Babba wanda ya isa da ita mu koramai Jawabi na Tabbata Shi zai Fahimcemu harma kaga an samu Masalaha.."Kamar Abdullahi zai yi Gaddama sai kuma ya Duba Matsayin Baba Wada awajensu Shiyasa ya amince da Shawaran Baban wadan suka rabu kan Sai ya Kira Nazifin sunyi mgana.
Nazifi kuwa Dama Jidda ta gayamai komai Domin ajiyan yayi ta Kiran wayarta bata Dauka ba sai zuwa Chan ta Kirashi Cikin Damuwa Tana kuma kuka sai yake Tambayanta lafiya ita kuma ta Gayamai Shima bai wani Damu ba sai ma yakama Dariya Har Jiddan taji Haushi sai kuma ya koma yana Lallashinta da Bata baki,koda yaji bai Kira Abdullahi ba Domin ya Tabbatar wannan ba wata mtsala bace awajenta kuma Mganar zata kaishi kara wannan Shirmen banza ne kawai shiyasa ya Share Mganar ko Abdullahin bai kira ba Sai kuma gashi Baba wada ya Kirashi yana mai Bayani Jin haka yasa Bai nunamai yaji mganar ba suka Rabu da Baba wada kan Ranar asabar zai Shigo Saboda in ya Shiga makaranta bazai Dade ba Baba wada yace Shikenan Bari suyi mgana da Abdullahi.
Koda Baba wada ya Kira Abdullahi yamai bayanin yadda sukayi da Nazifi bai Ce komai ba yace Allah ya kaimu Duk da Ranar Shima zai Shiga Cikin makaranta Ammh bazama zai yi ba,Nan suka Rabu kan sai Ranar asabar din.
Ranar asabar kuma Tun 7am Na safe Nazifi ya Shiga Cikin makaranta,Yabar sakina agida Jiya tazomai Weekend ammh ya Fita ne ma Tana barcinta Shi kuma bai Damu da ita ba Domin yanzu kowa ta kanshi yake,Bukata indai ba Sakina ta Nuna Tana Bukatarsa ba bai Cika Zafafama kansa ba azumi ne yana Kokarin yi kuma sanin bazai samu abu ba Toh sai ya Dangantashi Da baya so kawai ya Shiga Harkokinsa Dayake kuma Baya samun zama daya dawo gida Sai barci sai kuma gobe yanzu kuma jidda ta Shigo Rayuwarsa Su Raba Dare suna waya Hankalinsa kwance In yana officema suyi waya kuma Alhamdulillah Tana Debemai kewa Sosai Shiyasa yau din ma Daya Fice bai bi takanta ba Tunda ya Leka Dakinta yaga Tana barci kamar wacce tayi aiki. aikin Datayi Dayane aikinsa kuma ita ta nuna She is ready shiyasa kowa ya Sauke nauyin kowa yana ma Tunanin kila shi ya Dawo da ita ko kuma Domin Taga ya Daina Nuna Damuwa da ita ne kamar Baya Ohon mata,acikin Ranshi yasama ko Mganar Auransa Ya taso bai da Matsala Domin sai ka Damu da mijinka kake Jin Labarin zai yi Aure ka Nuna Damuwarka Toh Sakina dai Baya gabanta Ballatana ma ta Damu Shiyasa yake taHarkokinsa ko ajikinsa bai yi Tunanin ya Tattauna komai da ita ba sai Abun yazo kusa.
Koda ya Shigo Zarian Har Abdullahi ya Shiga Makaranta ya Fito nan gidan Baba wada suka Hadu,ko Gidan Mama Abdullahin bai Shiga ba Daman ba Da mashin Dinsa yazo ba Tana gida Ta Haya ya hau yaje makaranta ya Dawo Nazifi na zuwa Gida kawai ya Shiga suka gaisa daasu Inna Abu ya Fito suka wuce Baba wada ke ta Nuna Hanyar Tunda bai manta ba,da zasu zo neman Auran Sa'an Shida marigayi Usaman Direba suka zo,Duk da kuma an kara gine gine,Gidan yaso ya bace Masa sai kuma ya gane sai gasu Kofar gidan Mahaifin Hajiya Sa"a anihin Babban Gidansu.
Yaro suka aika sukace don Allah a musu sallama da wani Babba ba Jimawa sai ga wani Yaro matashi kamar sa"anin su Abdullahin ya Fito bayan sun gaisa sai Baba wada ke kara Tambayanshi nan ne gidansu Sa"adatu,wacce taje makka..? Yace eh nan ne gidan sai Baba wada yace Toh don Allah yana so yayi musu sallama da wani Babba Cikin iyayen ita Sa"an sai Matashin yace gaskiya Duka sun Rasu sai wani kanin Babanta Guda Daya Baba isuhu Shine mahaifinsa ammh Shi baya Fita sai dai su Shiga Saboda yana Fama da Ciwon kafa Jin haka yasa Baba wada yace yaje yayi musu iso Suna son ganinsa ne Ba Gaddama ya koma Ciki bai Dade ba yazo yayi musu Jagora zuwa Cikin Gidan har Dakin da Baba isuhu ke kwance yana Jinya.
Suna Shiga Dakin Baba wada ya ganeshi Saboda yana Daga Cikin wadanda suka basu auran Sa"an,Bayan sun gaisa sun mai ya Jiki sai ya nuna Bai ganesu ba Baba Wada ne ya gyara zama yayi mai Bayani Sosai yarda zai gane Kai ya Fara gyadawa yana Fadin"Masha Allah..Anyi haka kuwa..Kwanaki ai har nan din Sa"ar ta kawomana yar wajen nata mai ma Sunanta ma..?
Baba wada yace"Hauwa"u suna Kiranta Jidda.."Yace" kwarai an yi haka kuwa Sannunku da zuwa.."Baba wada ya amsa da yauwa kafim Matashin nan ya Dawo da Ruwa da lemo,Basu bi ta kanshi ba Baba wada ya Fara kora Jawabin Abunda ke Tafe dasu Sai da ya gama kana Ya kara da Cewa"Shiyasa mu ka yanke Shawaran gwara muzo Gidan Iyayenta domin mu samu Babba wanda zai Shiga mganar Kasan mgana da mata sai a Hankali Tunda an kasa Fahimtar Juna.."Baba isuhu yayi Shuru kafin ya Gyada kai yana Fadin"Topha..Haka akayi..?gaskiya Sa"a bata kyautaba kuma Tayi Rashin Hankali Kuma mu nan bata gayamana ba Koda yake sai Tayi sati bamu ganta ba Daga ita Har Kanwarta lariya Suna Chan Sunyi Gidajensu suna zaune sai sun lekomu kana ammh Duk da Haka zan Shiga mganar Tunda har yau matsayin Uba nake garesu bari Mugani.."Yafada yana kwalama ma Matashin Daya kawosu Kira mai Suna Musa Sai gashi ya shigo kallonsa yayi yana Fadin"Kana da Lambar Sa"adatu..?
Kallon Babansa yayi yana Fadin"Yaya Sa"a Ta Chika..? Yace mai eh sai yace yana da itaDa sauri yace"Yauwa maza ka Kiramin Ita kabani na mata mgana ba.."Ba musu ya Kirata Dayake Tana da lambarsa har gidanta yana zuwa tana mai alheri Tana ganin kiran ta yanke ta Kirashi Shi kuma Bayan sun gaisa Yace Baba isuhu ke son mgana da Ita sai ya mikamai Bayan Sun gaisa Baba isuhu yace in Tana gida Ta kariso yanzu yana son ganinta bata kawo komai Tace gatanan zuwa.
Cigaba da Tattaunawa akayi Tsakanin Baba Wada da Baba isuhu,Har ya nuna mai Nazifi a matsayin Mijin da Jidda Zata aura yayi ta saka albarka ko Minti Talatin ba"ayi ba sai ga Hajiya Sa"a tayi matukar mamaki Data ga su Baba wada,Sai kallon Abdullahi Take yi Shi kuma sai ya kauda kai Zama tayi suka gaisa da Baba isuhu kana ta waiga suka gaisa da Baba wada kafin Baba isuhu ya Fara yi mata Fada da Nasiha mai Ratsa jiki ya Dade yana Nutsar da ita Kafin ya Dora da Fadin"Sa"adatu Taya zaki Hana araya Sunar ma"aikaci..?ke ba abun Farincikin bane Yarki ta samu Miji kamar wannan ba..? Yara nawa ke neman Dakin kan nasu basu samu ba ammh ke kin samu kina wasa da Damarki haba Sa"a Don Allah kibari kinji ko..? Ke yanzu Uwace ba yarinya bace bai kamata kina Irin wannan Abun ba Don Allah ki Janye wannan mganar ta zuwa kotu haka sam bai Dace ba ai kun zama Daya yanzu keda Kika bar kasar nan baki Dade da Dawowa ba bq Abun ki Godema Allah bane Masha Allah yarinyarki tataso Cikin gata kamar Tana gabanki toh menene Abun damuwa..? Ai Abun Farinciki ne ace yau sa"a kina Raye kin kai yarki Dakin Auranta kin saka mata albarka."
Kanta na kasa ta Dago sai da ta karema Nazifi kallo Dakyau kana ta muskuta Tana Fadin"Baba nifa bana ki bane..Mganar karatun Jidda ne ina da Burin Tayi karatu gaskiya.."Baba wada yayi mirmishi yana Fadin"Toh wa kika ji yace bazata Cigaba da karatunta ba..? Na tabbata Nazifi zai iya biyama Jidda ne ko nawa ne tayi karatu Saboda haka baki da wannan mtsalam.."Kai Tsaye Sa"a tace"sai yayi alkawari bana so sai na amince kuma Daga Baya mganata ta Sauya.."
Dariya ta kama Baba wada ya murmusa Baba isuhu yace"To Shikenan kai kayi mata alkawarin zaka bar Yarinyarta ta Cigaba da karatunta Tunda Bukatarta kenan.."Nazifi ya kalli Abdullahi shi kuma ya Dagamai kai Sai ya Sunkuyar dakai yana Fadim"Insha Allahu..Indon wannan ne tuni mun gama mgana da Jiddan da Tuntuni ma Tagayamin mtsalan da bamu kawo yanzu ba.."
Baba isuhu yace"kinji ko..? Don Allah sa"a datu adinga Hakuri kinji ko..?ina Fatan shikenan ba wata mgana.."Kai ta gyada Tana Fadin"Insha Allahu Baba nagode.."Yaji Dadi ya Dinga saka mata albarka,Kudi ta Debo a jakarta ta zube gabanshi ta Fice suma Kudin suka bashi kafin su mai Sallama Yayi ta godiya yana saka musu albarka,kana suka mai sallama suka Fito a Tsakar gidan suka Hadu da Hajiya Sa"a Nazifi ne ya tsaya ga gaisheta da Umarnin Baba Wada ko bakomai Surukarsa ce ta Chanchanchi Darajawa Dakyar ta amsa sai Hararan Bayan Abdullahi take wanda ma Bai san Tanayi ba.
Nan dai gidan suka Barta suka koma Daga nan Gida suka maida Baba wada kana Daganan suka koma Gidan Abdullahi sukaci Abinci Wanda Harira ta taimaka Hafsah tayi Daganan Nazifi ya kara Dubata masha Allah tayi kyau taki kiba kamar ba ita ba Daganan kuma suka Wuce Wajen ginin Nazifi chan sukayi sallar Azahar,ginin Shima yayi nisa Sosai ammh Nazifi yace kafin bikin in bai gama ba Haya zai kamama Jidda Shima Abdullahi Sunje Gra,Shima kadan ya Rage gida bai kamallah ba, An gama komai SauraFenti da kuma intelock din tsakar gida da kuma Kayan wuta,Ammh acikim Ranshi yana Tunanin kila komai ya Tsaya kenam sai kuma Bayan Bikin Jidda Tunda Hidimarta ce ke gabansa Allah Barshi bayan anyi sai ya maida Hankali ko loan zai iya ci a Wajen aikinsa Ya karisa komai kafin Hafsah ta Haihu Allah barshi a rika Cireewa a albashinsa.
Sai 2pm na Rana suka Rabu da Abdlullahi a gidan Mama ya barsa ya koma gida Shi kuma ya Shiga Dakin Auwal jidda tazo ta sameshi sukayi Hira Duk dai kan mganar tsare tsaren Biki ne La"asar nayi yayi mata sallama Ya wuce bayan ya zo mata da leda guda na Shopping din kayan kwalliya jidda sai wani yanga ake Mariya da Auwal na mata Dariyan Da tace bataso Mama ce ke Shiga Cikin mganar tace akyalemata autanta Da Daddare sai ga Baba wada yazo Shi ya kora ma Mama yadda komai ya Gudana yace ta kwantar da Hankalinta komai ya wuce taji Dadi Har ranta Tana ta mai godiya.
*******
Tafe Tafe kwana Nesa Wuni yana karewa muna Shiga kwana,kwana yana karewa muna Shiga Satittika,Satittika yana kwarewa muna Shiga Shekara da Haka muke Cinye Sauran kwanakinmu a Duniya Bamu sani ba Allah ka Bamu Dacewa Ameen.
Gashi yau Bikin Jidda Sauran Sati Hudu Cif ta kowani Bangare Shirye Shirye keta Gudana Ta Bangaran Abdullahi Kuwa Kudi ya Bada Mama da Ita kanta Jiddan da Subai"atu suka je Jaji suka Zabo mata Kujeru da gado da Katifa masu kyau da Tsada, masu kyau Ita kuma Zannira tayi mata Gadon karfe da kuma kayan Kallo sai Subai"atu datayi mata Fridge,da Labulai sai Center Cafet,Hajiya Sa"a kuma Taga ba Sarki sai Allah ta saki Tunda dai Auran nan na yarta ce ba na wani ba Tuni ta watsar da komai ta shigo Cikin gida anayin komai da ita,shi kanshi Nazifin yanzu a gidanta ya zama Dan gida Tunda Tun bayan Faruwar haka indai yazo Zai Dauki jidda Ta rakashi Suje ya gaisheta Tun Tana wani basarwa Har tazo taDaina Hakama Hajiya Lariya itama yaje gidanta wajen Sau Biyu Sun gaisa ita ta sakama Jiddan ta Rakashi Family Hause din Mamarsu ya gaisheshi Suka ganshi Harda Babban gidansu na na Barayin Inda su Nazifin suka Taba zuwa Wani Lokacin ma in ya Shigo Garin a Chikan yake samunta in taje ma Sa"ar Weekend,Yanzu kuma Tsakanin Jidda da Nazifi wata irin Soyayyace mai karfi da Shakuwa ta Shiga Tsakaninsu in ka gansu sai kace Damam chan Masoya ne Nazifi dan Rayuwa ne yasan kan Mace Sosai kawai waje ne bai samu ba sau yanzu matukar so da kulawa yake nuna ma Jidda itama Haka sai dai Tana Kokarin Bashi Girmansa a matsayinsa na abokin yayanta gefe Daya,kuma Suna Shan Soyewarsu.
Goggo Habiba 50k ta kawo Gudummuwa Da nata dana Ya"yanta Domin Bata da bakin Godema Ya"yan yayan nata Kowani Sha"ani da Jiikinsu da aljihunsu ake musammanma Yaya Abdullahi sai Ammi ma 50k Hafsah ta kawo Mama taji Dadi Harda Hawayen Dadi,Sai Umman Sadiq itama ba"a barta a Baya ba 30k ta aiko ma Abdullahi tace Gatata Gudummuwar nan Mama ma yan"uwanta sun Hadamata Dubu 50k Dashi a kahada akaje kano akayi ma Jidda Siyayyar kayan Kitchen da Duk Abun ya kamata Tunda Flat House ne mai Dan Girma Nazifin ya kama anan Famwaki Tunda ginin dai bai gamu ba nan za"a yima Jidda Jerenta in sun gama Cin amarsun zai mai data kaduna,Daman Dubaran Hakan in ya tashi komawa Sabon gidansa basai an Wahala ba Tunda wanchan gidan Sakina Ta Cikashi da kayanta sai ya barmata Sai ya yanke Hukunci na Zaria gidan Jidda ne,In sunzo basu da mtsala wajen Sauka Chan kaduna kuma ko Dakinsa Zasu zauna Suyi Rayuwarsu Cikin Soyayyah da kaunar Juna.
Hajiya Sa"a Tazo Ta Tambayi Mama Abunda Ba"a siya ba Mama tace komai an Siya sai Abunda ba"a rasa ba Wannan Dalilin yasa Mama ta mata Bayanin komai kawai sai takoma Gida sukayi mgana da Lariya sukaje suka Siya katifa da Fridge Babba mai Biyu sai Gas na Zaune mai Shidda,sai Labulai da kuma Zannuwan gado,Dama tana da wasu Datazo mata dashi Daga Chan Saudiya,sai wasu Expansive kololi masu kyau da Tsada Data kara mata,sai Home Theater,Sauran Abubuwa dai masu Tsada ta Siya dasu Dinning Kuma Bayan sun yo Siyayyah Direct Gidan Mama ta wuto Dashi Mama nata Godiya Sosai Abdullahi ma Dayazo ya gani bai ce komai Ba Duk da yanzu ba irib da Bane suna gaisawa sama sama da Hajiya sa"an.
Bangaran Amarya da kawayenta Kuwa Rumana ne sai wasu Wadanda suka gama Makaranta Tare,sai Mariya 50k suka nema ya basu na Walima da Shagalin Biki,Kayan akwati kuwa Wata matar abokinsa ta Hada komai akwatuna Bakwai,Shake da kaya sai Wanda yagani Da kanshi ya kwaso ya kai gidansu Su Inna Abu suka gani,Sai da Biki ya Rage Saura kwana Goma kana Aka Hadu aka kai kayan Yan"uwan Inna Abu da makota sai kannensa Suka kawo kayan Gidan Mama acikin masu karban kayan Harda Hajiya lariya Sa"a dai Tana gida Masha Allah kaya Sunyi kyau Sosai Dayake Abun Gidane haka aka gama ganin kaya ana saka albarka Sunci Sunsha Harda Tukwaici aka basu suka Ki karba sai da Zannira ta matsa kana suka karba Dayake Tazo Ranar da za"a kawo kayan Dasu Hafsah wacce Cikinta dan Wata Shida gayinan ya Fito yayi Girma kamar CikinFari.
Baba wada ne ya Kira Nazifi yana Tambayanshi yako gayama Matarsa Sakina yace "A'a ammh Cikin Satinan zai gayamata.."Fada Baba wada ya Fara mai yana Fadamai bai kamata ba Tana da Hakki ya gayamata zai kara aure yace Insha Allahu zai gayamata Dama yayi Niyyar sai ya samu wasu Kudi a Hannunsa ne ya Damkamata Na siyayyarta in ta karba Shikenan in bata karba ta Rasa Da Haka suka Rabu da Baba wada Wanda shi Daman ya Riga ya Bari sai in tazo Weekend din wannan Satin Tunda Rabonta da kaduna wajen Sati uku kenan Toh a ina zai ganta..? Shiyasa bai Fadamata ba har yanzu...!
******
*Kaddara ta sake Hadasu...*
Yau Ta kama Jumma"a wacce tayi Daidai da Saura kwana Takwas Bikin Jidda da Nazifi da misalin karfe 6:30pm na yammah a Kofar main get na ABU SAMARU,yan makaranta ne Birjit suna Tsaye wasu kuma Suna Tafiya ne,Ayayinda wasu kuma ake ta zuwa Daukansu,Kowa dai kagani yana ta Haraman komawa gida ganin Ga Mangariba ta kawo Jiki kuma Dare ya Fara Shiga.
Tana Tsaye a bakin Titin Duk inda Hankalinta yake yakai kololuwar Tashi ganin Duhu yayi bata samu Bus ba,Koda tazo duk sun Cika,agogon Fatan Dake Hannunta ta kaima Duba Lokaci Daya ta saki karamin Tsaki acikin Ranta tana jin Takaichin Rashin samun accomadation da batayi ba,dayake ta Shiga aji Hudu da ta samu mai zai jamata wannan Jiran,Yanzu ita Tunaninta ma Daya koda ta samu Abun Hawa Lokacin da zata bata kafin ta kai gida Shine Abun Tunaninta,Sake sakin Wani Tsakin Tayi tana gyara zaman gyalen Abayar Dake Jikinta.
Doguwar mace,wacce ke sanye da wata bakar abaya da gyalensa tayi Rolling,sai Kafarta sanye da wani bakin Takalmi mai tudu Katadarta Rataye da wata bakar Jaka sai Hannayenta Dauke da wasu manyan littafai na karatu Fuskarta sanye da wani Farin gilas na gayu,Daga ganin Fuskarta Tana Cikin Damuwa Duk da bata son Hawa mashin Sai ta yanke Shawaran Bari kawai ta Hau mashim Din Tunda bata da mafita Hannu ta sanya tana Tsaida Masu mashinan ammh su kansu sunki Tsayawa.
Fitowar Abdullahi kenan Daga Cikim makaranta Shima ya tsaya yin wani Abu ne yasa yakai yammah haka,Ya fito kenan yana Kan Mashin dinsa kamar wasa ya Hangota tana Tsaye kamar tana Tsaidashi har ya wuce Sai kuma yayi wani Tunani kawai ya Juyo yana Tunanin mace ce kuma ga Dare ya Kawo Jiki Tana Bukatar Taimako Shi kanshi bai Taba Daukan wata mace a mashin dinsa ba in ba Hafsatu ba ammh sai gashi yau ya tsaya gaban Wata mace yana Tambayanta inda zata Abunda bai san ya akayi hakan ta Faru ba.
Littafin Masifaffan Namiji free book ne amma ga waɗanda ba za su iya jira ba akwai Completed document 1k ne biya ta wannan acct ɗin 5040273639 Moniepoint Jamila Umar.
Ko tuntuɓa ta wannan lambar ***
*Janafty*