Chapter 6
*RIKICIN DUNIYA...*
©️ Meenat A. 'Yandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
CHAPTER 6
..."Kasim!" Wasila ta karasa maganar murya na kyarma.
"Kinyi mamakin gani na ko? Ki daina mamaki. Zuciyata ruhina komai nawa ya rikirkice bani da wani buri da ya wuce Inzo in yi tozali da ke. Gobe nayi niyyar zuwa amma na kasa duk da insecurity da Ake fama dashi haka na bugo hanya domin in zo inyi tozali da ke"
Ya karasa maganar yana mai sakar mata murmushin da ya karasa tafiya da ita.
"Kasim! Da gaske ba mafarki bane kai ne nake gani a kofar gidanmu?"
"Mafarki kuma wasila? In ma mafarki kike ki bude ido ni ne da kaina"
"Amma Kasim!"
Da sauri ya tsallake ƙatuwar kwatar data raba tsakaninsu. "Amma me, don Allah kada ki ce baki so na"
"Ina tsoron yadda Nadiya zata fassara mu. Ka ga ni bana son tashin hankali, zata iya cewa munci amanarta ko kuma ka yaudareta"
Ta karasa maganar cikin kissa tamkar zata fashe da kuka.
"Mtsww! Nadiya kuma? Look Wasila ki daina kawo min sunan wata mace muddun muna tare, bana ji bana ganin kowa face ke"
Ya karasa maganar yana mai kare mata kallo.
Wani irin sanyi ta ji har cikin zuciyarta. Ba shakka aikin Bakurmi ya fara aiki.
Sunanta da ta ji ya kira ya sakata ɗago kanta da sauri.
"Za ki aure ni"
Jin maganar tayi ta dakar mata zuciya lokaci ɗaya ta ji kakafuwanta na kokarin kayar da ita.
“Ni kuma Kasim baka ganni bane, diyar talaka gaba da baya. Anya da gaske kake aurena za ka yi?"
Wata irin rikicewa ta hango a fuskar Kasim. Kafin ta yi wani yunkuri zubewa yayi bisa guiwowinsa.
"Zan mayar da ke attajira kai duk wanda ya raɓeki zai gogi arziki. Please ki ji tausayina ki amince zaki aureni."
A rikice ta kamo hannunsa ta miƙar da shi tsaye.
"Ka rufa mini asiri a matsayinka na ɗan masu kudi a zo a iske ka a tsugune a gabana. Na amince zan aureka sai dai matsala daya ce"
"Wace matsala ce fada mini koma meye zan magance miki shi"
"Shi aure ya na bukatar kudi Sosai mahaifana kuma ba su da kudi, dole a saka aurenmu nesa"
"Hmm!"
Ta jiyo sautin ajiyar zuciyar daya sauke
"In Dan wannan kada ki damu domin ba matsala bane, Ni zanyi komai. Yanzu haka nadama nake yi ta tun farko me ya kai ni wurin Nadiya, bayan kin fita kyawu kin fita diri kai komai ma kin fita"
Dariyar mugunta Wasila ta yi. "ALLAH ko Kasim?"
"Sosai ma. Yanzu abinda za a yi shine, tunda dare ya yi ki Bani numberki sai ki koma gida. Ni kuma zan kwana ne gobe ma zan dawo in ganki wata kilama bazan tafi ba sai nayi kwana biyu ina ganin ki."
Baki ta turo cike da kissa. "Bani da waya data Mama nake amfani, ita ma taje gidan biki aka sace ta"
"Ayya to wannan ba matsala bane. Zuwa gobe zan siyo waya In kawo miki. Ba yadda zanyi amma duk da haka amshi wannan Samsung din ban cika aiki da ita ba dayan sim dina ne ciki. "
Hannunta har kyarma ya ke yi ta amsa tana godiya. Kudi masu yawa ya kwaso ya bata.
Da gudu ta shiga gida yana bajewa a tsakar gida "Umma duniya sabuwa"
Guɗa Umma ta kwala tana mai zama gefen Wasila. "Yar nan! Duk wannan kaɓakin arzikin daga ina?"
"Hmm! Daga Kasim mana"
Fiddo idanuwa Umma tayi cikin mamaki ta furta.
"Kasim kuma, kina nufin har aikin Bakurmi ya ci?"
"Kwarai kuwa Umma. Yau Kasim har duka mini ya yi, kai dole ma a kara masa kudi"
"Ai na fada miki Bakurmi sha kundun ne Indai wurin aiki ne. Yanzu ya ku ka yi da shi?"
"Ya ce a matse ya ke ayi aurenmu, zai turo magabatansa tun kafin mu gama exam. Sannan zai jika kowa da arziki ko rabata akayi sai an Dangwale arziki, duk wata hidima da kayan da iyaye ke yi ma diya ya ce shi zai yi mini."
"Wayyo dadi kashe Ni, koda ya ke kar ka kashe ni ka barni inci arzikin wannan duniyar ta yadda zan mike kafa inyi bake-bake"
"Yanzu ba komai bane wannan duk somin taɓi ne Umma"
"Amma Wasila ya aka yi Kasim ya san gidan nan?"
"Wannan kuma ai tsohon zance ne. Kin manta shi da Nadiya sun taba zuwa gidan nan?"
"E, tabbar anyi haka"
Kiran wayar da ya shigo wayarta ne ya tabbatar Mata da Kasim ne domin My number ta ga an rubuta. Dauka ta yi ta nufi daki tana ma Umma alama da tayi shuru.
Gidansu Nadiya
Layin Kasim Nadiya ke kira amma fada mata ake waya yake da wani. Hankalinta ba karamin tashi ya yi ba musamman data tuna duk yau bai nemeta ba.
"Nadiya lafiya kije naga kin tasa abinci gaba kin kasa ci?"
"Inna akwai damuwa. Duk ya Kasim bai nemeni ba, ni kuma idan na nemeshi bani samun shi"
"Kiyi masa uzuri wata kila wata sabgar suke yi kinsan masu kuɗi da hidindimun arziki"
"Kila kuma haka ne, bari zuwa a jima sai In sake kiransa. Abin da ya saka duk na tayar da hankalina bai taba yi mini irin haka ba, kowace safiya da sakonsa nake farkawa kafin kiran waya ya biyo baya. Amma yanzu kin kwantar mini da hankali wallahi."
Ta karasa maganar tana sauke ajiyar zuciya.
"Salamu alaikum ance ana Sallama da Jamila In ji Sahabi"
Matashin yaro ya fada.
Tsoki Inna Tayi.
"Allah wadaran naka ya lalace. Raƙumin dawa ya ga na gida, ke dai na fahimci kome zan fada miki ba za ki taba gane abin da nake guje miki ba. Waye sahabi wanda kudin koyarwar da yake yi ta Laraba da ake bashi, shi kansa ba zasu rike shi bare har ya iya rike ki, amma a haka kika rumtse ido kina fadar sai shi saboda shi ne ɗan autan maza ko?"
"Inna ki rabu da ita jiki magayi. Tuwo labarin wuta yake ji a tambayi tsire asha labari. Indai auren talauci ne da ƙafafuwanta zata gudu ta dawo"
Jamila dake tsaye jin irin ciin mutumcin da da ake yi ma Sahabi. Da kyar ta fita.
Kallon fuskarta da yayi lokaci daya ya fahimci abinda ke faruwa, dama can ya sani Inna da Nadiya sun tsane sa Mahaifinta ne kadai ke kaunarsa.
Hakuri ya bata yana mai yi mata nasiha ta kara hakuri komai lokaci ke gareshi, In sha Allah wata rana sai labari.
Sabuwar waya a keypad a cikin kwalinta tare da sabon Sim CARD ya mika mata.
Cikin farin ciki ta yi godiya sai da ya tabbatar da ta shiga gida daga bisani ya kama tashi hanyar.
Jikinta har ciri yake ta shiga gidan tana kwalawa Inna Kira.
Kwalin wayar ta mika mata tana dariya.
"Inna yanzu ya bani ita"
"Aikin ɓur in ji tusa. Yanzu ke wannan wayar rakani kashi ko ni uwarki aka ba ita ai an gama rena mini wayo bare Ke budurwa mai jini a jika."
Amshe zancen Nadiya ta yi. "Don Allah ki rabu da ita, shi ne har kike wani kwalama Inna Kira dama wannan yar iskar wayar ce ya baki?"
"Inna don Allah me ye laifin Sahabi bafa rokonshi nayi ba shi yayi niyya ya kawo mini. Sannan wallahi har cikin raina na ji dadin wannan wayar nasan duk lokacin da Allah ya hore masa zai sai min wanda tafi wannan"
"Ki rabu dasu Jamila! Ko daya kada ki dauki abin da suke fada, Allah shi ke azurtata kowa duk bawa baya wuce arzikinsa. Ni kuma banga aibun Sahabi ba yaro ne mai nutsuwa da hankali ga addini ko bayan raina na sani zai rike ki da amana"
Dariya Inna ta babbake da ita. "Ka ga Malam ka ci gaba da dorata a keken ɓera, Indai talauci ne ga ta gashi. Ni kaina da za a dawo da hannun agogo baya bazan dauke ka ba."
"Ki ci gaba da duk abin da kika ga dama. Shi Allah ba azzalumim bawa ba ne"
Yana kaiwa nan ya shige daki.
Wayarta da Inna ta jefar ta dauka ta nufi daki. Daren ranar tayi kuka tamkar ranta zai fita, daga karshe ta yo alwallah ta kaina kukanta Allah har bacci ya kwashe ta.
Nadiya kuwa tuni tayi bacci sai faman juyi take.
A tsakiya daji ta tsiinci kanta, ba gida gaba bare baya. Mace ta hango tsaye cikin bakaken kaya hannunta rike da sharbebiyar wuƙa tayo kanta a guje...
Meenat A. 'Yandoma
***