Chapter 8
Page 8
Da sauran kuɗin hannunta ta siyo kayan abinci, komai da komai, ta fara amfani da ɗan ƙaramin gas ɗin da Alhaji ya siya mata, a ranar ta fara girkinta, Hauwa tana ta yi mata habaici, wanda zuwa yanzu ya rage damunta, don idan da sabo ta saba wai an zunguri mai ciki. Haka ta dinga rarrafa rayuwar har aka yi wata ɗaya da karɓar kuɗinta, shiru Yaya Sani bai yi mata zancen riba ba, sai da ta tambaye shi, da ƙyar ya ba ta dubu ashirin ya ce ba a ci ribar arziƙi da kuɗin nata ba, haka yake ba ta duk wata, wanda ba isarta kuɗin yake yi ba, ƙarshe dai a wata na ukun ta ce kawai ya ba ta dubu ɗari a cikin kuɗin za ta fara sana'a, nan fa ɓalli ya tashi, ya dinga bala'i yana cewa ba ta yarda da shi ba kenan, ƙarshe ya ce zai ba ta duka kuɗinta amma ta bar masa gida, ta tafi duk inda za ta je, jikinta ya yi sanyi, ta ce shikenan ya barta, to shi ne daga nan ya ƙara mata yake bata dubu talatin.
A ranar da ta kammala iddarta ta same shi ta faɗa masa, don ya ce mata tana gamawa ta sanar da shi yana da wani shiri, duk da ba ta san dalili ba, amma ta faɗa masa ɗin don ta ji shirin nasa.
Yaya Sani ya ce"To Alhamdulillah! Yanzu dai kin zama free kenan, miji yana fitowa za ki iya yin aurenki ko?"
Ta ce"In sha Allah!".
Ya ce"To dama akwai wani bawan Allah da nake son ki aure shi, ba wani babba ba ne, ina ga ma da kaɗan zai girme ki, sun rabu da matarsa ne, kamar na ji ma ya ce sau biyu yana yin auren, yanzun dai Allah bai kawo wata da yake so ba, yana da ƴaƴa uku, ban dai sani ba mata ne ko maza, yayan shi ne abokina, da na ba shi labarin aurenki ya mutu ya kawo shawarar kawai mu haɗa ku".
Hajara ta yi shiru tana tunani, ita ma za ta so ta samu miji ta yi aure da wuri, don ko yaya ta san zaman gidan mijin zai fi zaman gidan yayan nata, wanda take jinta a takure, kuma ta ci da kanta ta yi wa kanta duk wasu hidima, amma tana buƙatar bincike don ta san sanadin mutuwar auren na shi, don gujewa auren jeka na yi ka.
Yayan ne ya katse mata tunani da faɗin"Ya dai Hajara, ko dai ba auren ba ne a gabanki?"
Ta sauke ajiyar zuciya ta ce"Ba haka ba ne Yaya, amma akwai buƙatar a fara bincikar halinsa tukunna, aurensa biyu yana rabuwa da matan, ba mu sani ba ko daga halinsa ne, kar a zo auren ya kasa kai wa Talata ballantana Laraba, sannan ko da an tarar halinsa babu matsala, akwai buƙatar mu fahimci juna, ya zama auren soyayya aka yi ba na haɗi ba".
Tana kai wa aya Yaya Sani da yake ta gyaɗa kai kamar ƙadangare ya ce"A lallai Hajara! Da alama na ɗaure miki da yawa, to ke ashe zaman gidan ma daɗi ya yi miki, a zamanin nan kika samu mai rufa miki asiri ya aureki har sai kin tsaya wani zurfafa bincike? Na ga ma an ce wa la tajasassu! Kuma yaron nan na ce miki dai ƙanin abokina ne, zan haɗa ki da wanda zai cuce ki ne?"
Ta ce"Amma shi an tuntuɓe shi yana so na? Kuma ni ma gaskiya sai na fara ganin shi idan na ji ina son shi..."
A fusace Yaya ya ce"Shikenan Hajara, ki je ki nemi soyayya ki aura! Allah na tuba har mene ne so? Ko ba a nan ƙofar gidan kuke cin soyayyar da tsinke ba ke da wannan Alhajin? Yanzu ga shi ba a je ko'ina abun ya zama tarihi, indai kika auri mai halaye masu kyau, yana ba ki, ci, sha, sutura, magani, kuma ba ya cin zarafinki to ko babu so kawai ki godewa Allah, idan kuma kin ga da takura to ki sanar mini, sai na faɗa musu su haƙura kawai, su nema masa wata".
Hajara ta ce"A'a Yaya, ya zo ɗin dai mu ga juna, sai mu ga abin da Allah zai yi kuma".
Ya ce"Haba ko ke fa! Da ki je ki yi aure a inda kishiya za ta hana ki zaman lafiya, ba gara ki auri mara mata ba, ƴan ƴaƴasa kuma ki rungume su, yadda ba ki taɓa haihuwar nan ba, ke ma ai za ki ji daɗin riƙe ƴaƴa, kin ga za su taso kamar naki".
Hajara ta ce"Hakane Yaya, Allah Ya sa alkhairi ne". Ya amsa da amin, ya fice.
Shiru Yaya bai sake ce mata komai ba, tana ta zuba idon zuwan bazawari ta ji shiru, sai da aka yi sati biyu kwatsam sai ga Yaya ya dawo daga kasuwa da la'asar, ya shigo yana ta washe baki, ya fita da tabarma waje, babu jimawa ya shigo ya miƙowa Hajara kuɗi ya ce ta ƙirga, ta karɓa da mamaki ta fara ƙirgawa.
"Dubu ɗari da hamsin ne a nan Yaya" Ta faɗa bayan ta gama.
Ya ce"To madallah! Sadakinki ne, yanzu aka kawo, an tsayar da ranar auren sati uku masu zuwa".
"Sati uku?" Ta tambaya da mamaki.
Ya ce"E mana! Ai na yi miki bayani..."
Ta ce"A'a Yaya ba mu yi haka da kai ba, ta ya mutum bai zo na gan shi ba kawai a karɓi sadakin shi?"
Yaya ya ce"Tooo! Kenan dai Hajara ba ki amince ba, ashe duk wani tsari da nake yi don inganta rayuwarki na rufa miki asiri a banza kike kallona!"
Ta girgiza kai ta ce"Ba haka ba ne Yaya, amma ai ya kamata a ce ya zo mun fahimci juna tukunna".
Ya ce"To Hajara ba ya garin, an ce ba a nan yake aiki ba, kuma ni fa na yi duk wani bincike a kan shi, ai ina ga hakan ya wadatar, kuma zai dawo dole kafin sati ukun, zai zo ku gana".
Ta ce"Amma duk da haka, har ya amince zai aure ni, amma ko marmarin ganina bai yi ba? Kuma ko ba ya gari ai akwai waya, sai ya nemi lambata indai ba dole aka yi masa a kan auren ba, ka duba wannan lamarin Yaya".
Yaya ya ce"To kin san kowa dai da yanayin halin shi, amma zan yi musu magana, zai kira ki, ku dinga waya kafin ya dawo ɗin".
Ta yi shiru, sam ba ta ji nutsuwa da auren ba. Yaya ya tashi ya fita ya bar ta riƙe da kuɗi tana nazari.
Washegari da daddare ta ga kira da baƙuwar lamba, tun da ta ɗaga ta ji namiji ne jikinta ya ba ta shi ɗin ne, suka gaisa, ya ce"Hajara sunanki ko?" Ta amsa da e.
Ya ce"Ma sha Allah! Ni sunana Sa'id, abubuwa ne suka yi mini yawa shiyasa ban zo ba tukunna, amma ina ga gobe zan zo sai mu gaisa ko?"
Ta ce"Ka dawo garin ne?"
Ya ce"Ai dama ina nan, ni ma fa auren sai a satin nan na san da shi, zan zo dai goben".
Ta danne mamakinta, suka ɗan yi fira, har take jin labarin ƴaƴan shi. Washegari ya zo da daddare suka ƙara gaisawa, cikin manyan kaya yake, yw zambaɗa turare, amma sam ba ta yarda da kamalarsa ba, bai jima ba ya yi mata sallama ya tafi.
Za ki samu complete a kan 700
***