Chapter 9
Tun daga ranar bai sake zuwa ba, amma kullum yana kiranta a waya su gaisa, ita dai sam ta kasa nutsuwa da auren, bayan sati ɗaya auren ya rage sati biyu kenan, sai ta samu Yaya Sani da zancen kuɗinta, don ta yi kayan ɗaki, sai kuwa ya fitittike ya fara faɗan ya za a yi ta kashe ɗan kuɗin da ake juya mata tana samun riba da shi? Da mamaki ta ce"To Yaya na ga dama dai ina yi ne saboda na ci abinci na rufawa kaina asiri, yanzu kuma tun da ka yarda da wanda zan aura ai na san ba zan rasa abinci ba, kuma idan ban sayi kayan ɗaki ba a haka za a kai ni gidan mijin babu komai?"
Ya ce"Abin da za ki duba Hajara ba mu san gobe ba, idan har kika zauna haka taro ko sisi ba sa shigo miki rayuwar ba za ta yi miki daɗi ba fa, shi wannan bawan Allah da za ki aura, na san ba zai rasa katifa a ɗakinsa ba ai, sai ki haɗa sauran kayan kitchen ɗinki, kina da zanin gado da labule, ki je ki harhaɗa ki yi zamanki, ke fa ba buduruwa ba ce ballantana wani ya yi miki gori, ke koma an yi miki gori sai me? Idan kika duba rayuwar ma gabaɗayanta nawa take, duka fa mu gawa ne a tafe, yau mu ne gobe ba mu ba, zaman aure za ki yi fa ba ƙyale-ƙyale ba".
Sosai ranta ya ɓaci, ta ce"Yaya kai fa namiji ne, ba ka san komai a kan wannan abin da kake so na yi ba, a gaskiya ni fa indai ba zan yi kayan ɗaki ba to sai dai na fasa auren, ka mayar masa da sadakinsa kawai".
Tana rufe baki ya yi farat ya ce"A yau ga shirmen banza! To ni ba na manta ma da sadakin wajenki ba? Haba Hajara yanzu dubu ɗari da hamsin ba za ta ishe ki kayan ɗaki ba? Ke kuwa me kika ɗauki rayuwar duniya? Kayan gado ko na dubu saba'in ya ishe ki, ki sayi katifar dubu hamsin, talatin ɗin ki samu kujeru ko sakan ne ki siya, ba kina da kayan kitchen ba?"
Ta haɗiyi yawun takaici ta ce"Yaya rayuwa fa ta canza, wannan lissafin da kake yi ko sakan ɗin zan siya sai dai marasa kyau".
Ya ce"To ni ki ba ni kuɗin ki gani idan ban siyo miki ba".
Ta yi murmushin takaici ta ce"Haba Yaya! Kana neman riƙe min kuɗi, ni da haƙƙina sun ƙi fitowa, kuma na sake ɗaukar wasu na ba ka?"
A zabure ya ce"Kenan nufinki na cinye miki kuɗi ko Hajara!?"
Ta ce"Ni fa ba haka nake nufi ba, kawai ni dai wannan lissafin naka bai yi mini ba, saboda haka ka ba ni ko rabin kuɗina ne na san abin da ya dace na yi". Daga haka ta tashi ta bar shi a wurin.
Sati ɗaya suna kai ruwa rana, sai da ta fitittike ta ce ta fasa auren, sannan ya ba ta dubu ɗari da ƙyar, ta haɗa da sadakin ta sayi kayan gado sakan da katifa ita ma sakan ɗin, ta kaɗe tsofaffin tarkacenta, tana jiran ranar aure. A satin auren ango Sa'id ya zo sau biyu sun gana, sam ba ta ji wani shiri ta ɓangarensa ba, kamar yadda ita ma ko walima ba ta shirya ba, saboda ba ta ɗaukin auren ma.
Goma na safe aka ɗaura auren, ƴan'uwa na kusa da maƙota sun shigo, Yayan ya ba da shinkafa, ita kuma ta ba da kuɗin cefane aka yi girki, da daddare tsirarun ƴan'uwa suka raka ta ɗakinta, don babu ma wacce ta faɗawa auren cikin ƙawayenta. Bayan an watse an bar ta ita kaɗai a gidan, ta tashi ta je ta saka sakata a ƙofar, ta tsaya a tsakar gidan tana haske-haske da fitilar wayarta, ƙaramin gida ne, mai ɗaki biyu, sai kitchen da banɗaki, sai a lokacin ta lura da katifa a tsakar gidan, ta ƙarasa da mamaki ganin har da jakar bakko guda biyu, kamar wacce aka yi mata umarni ta buɗe, ta ga kayan sakawa ne a ciki, sai ta ji ba ta ji daɗi ba, ta san dai ma su jere ne suka fito da su, suka bar masa a tsakar gida, saboda sai yau aka yi jeren, katifa ce babba mai kyau, amma sai tsami take yi, ta ja bakkon ta yi ɗakin gadon da ita, ta ajiye da niyyar sai gobe ta saka masa a cikin sif, ta nemi bakin gado ta zauna tana jiran shigowar ango.
Shiru-shiru tun tana zuba ido har ta fara ƙosawa, ba ta ankara ba ta ga sha biyu ta yi, sai abun ya fara ba ta tsoro, ta nemo lambarsa ta kira shi, tana ta ringin bai ɗauka ba, har sau uku, ta saka sakata a ɗakin ta yi addu'a ta kwanta, bacci mai cike da rashin nutsuwa ya ɗauke ta.
Can cikin baccin ta ji ana buga ƙofar gidan da ƙarfi, ta tashi zaune a firgice, ta janyo wayarta ta duba lokaci, ta ga biyu da rabi na dare, tsoro ya kama ta, duk da tana tunanin ko shi ne ya dawo, ta kira lambarsa, bugu ɗaya ya ɗaga ya ce"Hajara ki zo ki buɗe mini mana".
Ta sakko daga gadon ta je ta buɗe, tana haska jikinsa don tabbatar da lafiya yake ko akasin haka, "Ya dai? Na ga kina haska ni".
Ta na rufe gidan ta ce"Babu komai, kawai dai tunanin inda ango zai je nake yi, a ce sai yanzu ƙarfe biyu da rabi zai shigo".
Bai ce komai ba, ya wuce ciki, ta bi bayansa, idonsa yana sauka a kan katifar da ke waje, ya juyo a fusace ya ce"Kutt! Wane jahilin ne ya yasar mini da makwancina!?"
Gabanta ya faɗi, ta ce"Ban gane ba! Sababbin kayana a ka jera, kuma da safe zan shigar maka da ita ciki"
Ya ce"Amma wannan ai jahilci ne a ce katifata ta kwana a waje, wannan an tozarta ni wallahi!" Sai ya ja dogon tsaki, ya shiga ɗakin, Hajara ta dafe zuciyarta tana daidaita nutsuwarta kafin ita ma ta shiga. Ta tarar da shi yana cire kaya, da mamaki take ta bin shi da kallo ganin ya tuɓe zirr ko gajeren wando bai bari ba. "To kin tsaya a kaina! Ga kazarki can!" Ta kalli ledar da yake nuna mata wacce ya wulla ta gefe tun shigowar shi.
Ta je ta zauna a ƙasan gadon mamaki da fargaba sun cika ta, musamman da ta ga ya fice tsakar gida a hakan da yake, ta sauke gwauron numfashi, da guntuwar yunwa a cikinta, don haka ta buɗe ledar, kaza ce guda a ciki, sai pure water guda biyu, ta fara cin kazar a sanyaye kamar mara laka, sai gani ta yi yana turo katifa cikin ɗakin, gabaɗaya ya rufe su da katifar ita da kazar ta tashi da sauri ta lafe a jikin sif, ya ɗora ta a kan gadon da ya sha zanin gado sai ƙamshi yake yi, ya haye ɗaram ya kwanta, kuma har yanzu babu kaya a jikinsa.
"Idan kin gama sai ki zo ina jiranki ko?" Ya faɗa ba tare da ya kalle ta ba.
"To ina zuwa". Ta faɗa tana ficewa daga ɗakin, ɗakin kujeru ta afka har tana tuntuɓe ta saka sakata tana sauke numfashi, tunani ta shiga yi na wane irin miji ta aura haka? Anya kuwa yana da cikakken hankali? Tabbas an lulluɓe mata kura da fatar akuya, yanzu ita ta ina za ta fara zama da wannan mutumin? Sam ba zai yiwu ba.
Bugun ƙofar ɗakin ne ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, ta miƙe tsaye a razane tana rarraba ido, don kamar zai ɓalla ƙofar ma. "Ke Hajara!" Ya kira ta a fusace.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Yaya ka cuce ni!" Ta faɗa tana fashewa da kuka.