Fargar Jaji

Chapter 1

by @fulani2


*Da sunan Allah mai Rahama Mai jinƙai. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga Fiyayyen Halittu Annabi Muhammadu RasululLah (S.A.W) da matayensa 'ya'yansa da kuma Sahabbansa da jikokinsa baki ɗaya.*

  *Allah ka ƙara haskaka ƙabari da kuma ruhin Mahaifiyata Hajiya Zhara'u M. Abdullahi Yabo. Tare da Malamina Yayana M. Abubakar Abi Allah ka jajjada Rahamarka a garesu tare da dukan Musulmi baki ɗaya Saboda Alfarmar Annabi (S.A.W) Ina baran addu'a a gare su ga duk wanda ya ga littafin nan.*

  *Haƙƙin mallaka (m) Aisha Abbdullahi Yabo

Wani irin sanyi ƙafafunta suka yi da har ta kasa ci gaba da tafiya, ta faɗi tim! Kamar wacce aka sarewa gwiwoyin ƙafa, tafiya suke yayin da take ji tamkar ba tafiya suke ba. Zuciyarta ciki da tsoro da tararraɗin abin da za su tarar.

Suwaiba da take janye da ita ta juyo da sauri, “Ya haka, Aisha? Ki tashi mu tafi tun kafin ya kai ga illata miki ’ya!”

Wani irin tsinkewa ta ji zuciyarta ta yi, idanunta suna zubar da hawaye ta ce, “Ji nake ƙafafuna tamkar ba nawa ba.”

Riƙo ta yi tare da tayar da ita tsaye tana faɗin, “Ki ƙarfafa wa kanki, babu abin da zai faru da ita. Ki yi sauri, don ba mu da lokaci.”

Suna zuwa Suwaiba ta yi ƙarfin halin buɗe ƙofar ɗakin, tayi sa’a ƙofar a buɗe take. Ta ja hannun Aisha da ta zama tamkar mutum-mutumi. Suna shiga, wayam, babu kowa sai shirgin tufafinsa da kuma yangalallar katifarsa.

Kallon Suwaiba take a tsorace, wacce take bin ɗakin da kallo, fuskarta ɗauke da mamaki.

“Wallahi da idona na ga ya shiga da ita cikin ɗakin nan.”

Durƙushewa tayi a wajen tana kuka, “Na shiga uku, ina to ya kai mini ’yata!”

Kamar wacce aka tsikara da allura ta miƙe tsaye, ta fita ɗakin da gudu tana ihun kiran Hussaina.

“Hussaina! Hussaina, ina kika shiga ne!? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Na shiga uku!!”

Suwaiba da ta bi ta bayanta ta rufe mata baki tana faɗin, “Kin ga, daina wannan kururuwar. Kar ki tara wa kanki jama’a. Ki kwantar da hankalinki, ba mamaki abin da nake zato ba hakan ɗin ba ne, ko ya aike ta ne.”

“Ya aike ta? Kamar ya ya aike ta? To tana ina, shi ɗin ina ya je?!”

Hayaniyarsu ce tasa jama’ar unguwar fitowa suna tambayar lafiya. Suwaiba tayi shiru tana rarraba idanu. Tsoranta ɗaya, kar a zo abin da take zato ba hakan ɗin ba ne, ta shiga bakin ’yan unguwa, uwa uba mahaifiyarsa. Ta tabbata masifar Inno har wajen hukuma sai ta kai ta da sunan tayi wa ɗanta sharri.

“Wai me ya faru ne ku ka tsaya cirko-cirko da ku? Aisha, lafiyarki kuwa? Ki ke wannan kukan, ko mutuwa aka yi miki?” Wata dattijuwa take tambayarta hankali tashe.

Durƙushewa tayi a wajen tana kuka ta ce, “Hussaina ce Suwaiba ta gani tare da Idiris a ɗakinsa, yanzu kuma mun zo babu ko ɗayan su.”

Nan fa jama’ar wajen suka hau salati.

“To ke, ya aka yi kika ƙyale su?”

Aka yi mata tambayar kusan a tare.

“Uhm! Na je na kira uwar ne don ta tabbatar kar a ce sharri na yi masu.”

Ta basu amsa jiki a sanyaye.

“Ai kin yi wauta da sanda kika gansu sai ki masa magana, ba wai ki ƙyale su ki je kiran uwar ba. Yanzu to ga shi nan ba a san a ina ya kai ta ba.”

“Wallahi Inna Mairo, ban yi zaton zuwa na kira Aisha mu dawo zai tafi da ita wani wuri ba. Na yi hakan ne saboda yankan hujja.”

Tayi maganar a ruɗe.

“To ai ga yankan hujja nan. Kin ga ni, tunda garin kiran nata yanzu kuma sun yi sama ko ƙasa. Anya kuwa kin tabbatar su ɗin ne?” Baba Isa yayi mata tambayar tare da kafeta da idanu.

“Wallahi Baba, yadda na gansu, Ubangiji sarkin sarauta ya nuna mini Annabi, hakan!”

Aminiyar Inno ta zame jiki ta je ta faɗa mata abin da yake faruwa. Ta fito babu ko mayafi.

“Ina munafukar take ne? Kai ku gafara, ku bani hanya don Allah!”

Ta kutsa cikin jama’ar ta cakumi wuyan Suwaiba tana faɗin, “Munafuka! Algunguma! Munafuncin naki ya tashi daga kan kowa ya dawo kaina. To, ta Allah ba ta ki ba, wallahi na fi ƙarfinki!”

Da ƙyar aka janyeta. Jikin Suwaiba ta koma gefe tana mayar da numfashi tare da shafa wuyanta, don kuwa ta ji shaƙa. Sai fizge-fizge take.

“Ku barni na illata shigeya ɗan nawa ne za tayi wa sharri!”

“Ke Inno, ki kama kanki. Kowa ya sani a unguwar nan, Idiris yadda kika san bunsuru, hakan yake wajen bin ’ya’yan mutane. Kar ki wani naɗa tabarmar kunya da buri. Ki bari har sai an ga yarinya, an tabbatar da ba sa tare, sannan ki yi duk abin da za ki yi.”

Cikin Jibril tayi tana kumfar baki, “Kai, kama kanka! Ko uwarka bata isa na faɗa ta faɗa ba, bare kuma kai da a haifi na haifi ka. A gadon uwarka ka kama shi da mace!!?”

“Battar uban nan! Gadon uwata kika ce! Sai da a kan guts...”

Saurin rufe masa baki Baba Isa yayi, “Kar na sake jin bakin ka, ka ji na faɗa maka ko!”

Aisha har yanzu tana durƙushe a wajen, sama-sama take jin hayaniyar mutanen gaba ɗaya. Hankalinta baya a wajen. Tashi tayi tana jan ƙafa kamar wacce ta yi sha. Ta rasa ina za ta nufa don nemo ’yarta.

“Kun ga wannan kace na ce ɗin duk ba zai kawo mana mafita ba. Ku zo mu je a duba su.”

“Mu je, Hamisu. Ai wallahi idan har ya tabbata Idiris na tare da Hussaina, sai lahira ya fi shi jin daɗi, daga kanta ya daina taka ’ya’yan mutane. Ku mu je!”

Jibril yayi maganar tare da riƙe hannun abokinsa Hamisu.

Da ƙyar aka shigar da Inno cikin gida. Wasu matan na tausarta, sai zage-zage take. Nan fa aka ba za ma neman Hussaina lungo da saƙo. Duk inda aka san tana shiga a cikin maƙota, an je, ba ta nan.

Gaba ɗaya Aisha ta fita a hayyacinta. Duhun magarib ya sanyo kai. Jibril ya ce, “Maman ’yan biyu, ku yi haƙuri, ki tafi gida. Za mu yi sallah mu ci gaba da neman su.”

Gyaɗa kanta tayi cikin sarƙiwar murya wacce ta ci kuka ta ce, “Na tafi gida, na yi me? Ba zan iya ba. Muradina na ga ’yata. Ya Allah ka kiyaye mini yarinyar nan. Allah ka tsare ta daga sharrin bawan nan naka, Ya Allah!”

Ta fashe da wani irin marayan kuka.

Rungumeta Suwaiba tayi tana kuka tana faɗin, “Ki yafe mini. Wallahi da na san ba za mu dawo mu same su ba, da ban bar su a tare ba. Tabas na tafka kuskure.”

Baba Isa ne ya ƙaraso wajen da suke. Kallonta yake cike da tausayi. Tabbas Allah kaɗai ya san irin halin da take ciki a matsayinta na uwa.

“Jibril, kun duba ko’ina kuwa?”

“Baba, mun duba duk inda muke sa ran ganinsu. Sam babu amo, babu labarinsu. Shi ne na ce su je gida. Idan mun yi sallah, za mu ci gaba da neman ta. Ita Maman ’yan biyu ta ce babu inda za ta tafi.”

Ajiyar zuciya Baba yayi kafin daga bisani ya sassauta muryarsa cikin lallashi ya ce, “Ki yi haƙuri, Aisha. Ku tafi gida. A dai wannan ɗan takin da muke ciki, addu’a ita ce abin da ya fi dacewa da ki nace wa yi a matsayinki na uwa. Da yardar Allah, ana yin sallah za mu sake fita nemanta. Ki kwantar da hankalinki, kin ji ko? Babu abin da zai sameta.”

Ba don ta so ba, hakan ta juya tare da sauran matan suka koma gidajensu.

Zaune take a kan darduma ta idar da sallah. Ta ɗaga hannu ta kasa faɗar komai sai fashewa tayi da kuka. Hassana tana gefenta, Hafiza na jikinta, wacce da ƙyar ta samu ta lallashita tayi bacci.

Kallon uwar tayi tana kuka ta ce, “Da gaske ne, Ummi, Hussaina ta ɓata?”

Kallon Hassana tayi da idanunta da suka yi luhu-luhu saboda kuka. Kawar da kanta kawai tayi, ta kasa cewa da ita komai.

Abdul ne ya shigo gidan a ruɗe yana ƙwala mata kira tun daga tsakar gida.

“Aisha! Aisha!! Aisha, kina ina ne!!?”

Tana jinsa, sai dai ko motsawa ta kasa yi daga wajen da take. Ba ta da ƙum da niyar amsa masa. A sukuwanne ya shigo ɗakin yana ƙarasawa wajanta, ya fizgota tare da tayar da ita tsaye. Kallon juna suke ido cikin ido. Cikin ɗaga murya ya ce, “Gaskiya ne abin da aka kirani a waya aka faɗa mini!?”

Shiru ta masa, sai dai kallo take masa mai cike da tsana.

“Tambayarki nake, gaskiya ne Idiris ya ɗauki Hussaina?!”

“Kuna ina? Ku zo an ganta!!”

Wani matashi da ya shigo gidan a guje ya faɗa cikin ɗaga murya.

Ture shi tayi, ta fita da gudu. Ya bi bayanta. Hassana ta kwantar da Hafiza ta bi bayan iyayen nata.

Ko da suka ƙarasa wani kangon gida da yake ƙasan layi, mutane sun taru, manya da yara, maza da mata. Kasa ƙara sa wa tayi, ƙafafuwanta suka dinga rawa, zuciyarta ta dinga bugawa fat! Fat!! Fatt!!!

Abdul ne yayi ƙarfin halin kutsawa cikin mutanen ya ƙarasa wajen. Tana kwance rairan cikin jinin da yake kwararowa ta ƙasanta kamar an yanka babbar dabba. Durƙushewa yayi wajen.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Hussaina!!”

Baba Isa ya dafa kafaɗarsa ba tare da ya iya furta ko da kalma ɗaya ba. Shi kansa hawaye yake zubarwa. Haƙiƙa an mata rashin imani.

Ƙarajin Abdul yasa ta yanki jiki ta faɗi a wajen.

“Shi kenan ya illata mana rayuwa!!”

Wata mata ce ta ɗagata tare da rungumota jikinta. Ta ƙarasa da ita gaban Hussaina. Idanunta na ganin yanayin Hussaina, ta durƙushe gabanta tare da tallafota, ta rungumota jikinta tana jijjigata.

“Hussaina! Wayyo Allah, na shiga uku! Na bani, na lalace! Ni Aisha, me zan gani!!!”

“Ki yi haƙuri, Aisha. Ki dinga salati. Haƙiƙa akwai firgice. Ko mu da muke maƙota, abin ya girgiza mu, bare kuma ke da kike uwa.”

Wata tayi maganar cikin kuka.

Yanki jiki tayi ta faɗi tana rungume da Hussaina a jikinta.

“Ina ga fa suma tayi, ku dubata,” cewar Baba Isa.

Abdul ya kalleta a firgice. Wani irin abu yake ji a zuciyarsa mai matuƙar nauyi. Tun da yake a rayuwarsa bai taɓa shiga tashin hankali da tararraɗin rayuwa irin wannan ba. Baƙar rana mai cike da baƙin tabon da ba zai taɓa gogewa ba a tarihin rayuwarsa.

Da rairafe ya ƙarasa wajen. Rungumesu yayi yana wani irin kuka da sabbatu.

“Don Allah ku tashi. Idan kuka mutu, ina zan sa raina! Ku tashe ni daga wannan mummunan mafarkin, don Allah! Ku taimakeni ku tashe ni! Wayyo Allah, na shiga uku!!”

’Yan sanda ne suka ƙaraso, wanda tun ɗazun ɗaya daga cikin mutanen da suke wajen ya kira su a waya.

“Ku matsa daga hanya, ku matsa!”

ASP Rufa’i yasa aka ciro Hussaina daga jikin Aisha. Babu inda yake motsi a jikinta. Yayi umurnin da a ɗauki hotonta da kuma wajen.

“Su waye waɗannan ɗin?” ASP yayi tambayar idanunsa a kan su Abdul.

Jibril ya ce, “Iyayen yarinyar ne.”

“Ok. DSP, ku ɗauke yarinyar da mahaifiyarta a kaisu asibiti. Yanzu za mu biye bayanku, mu kuma dinga waya.”

“Ok, Sir.”

Ya sara masa.

Wasu mata ne suka tallafi Aisha da ƙyar a ƙasa ta mota. DSP Badmasi ya cicciɓe Hussaina, yasa ta a mota. Abdul ya yunƙura da ƙyar ya tashi, yayi taku ɗaya zuwa biyu, ya ji an riƙi rigarsa. Juyowa yayi, Hassana ce ta masa ƙuru da idanu.

“Abba, shikenan ba zan sake ganin Hussaina da Momy ba, kamar yadda Innar su Na’ima ta tafi aka daina ganinta? Me ya ji wa Hussaina ne, jini yake zuba a jikinta?”

Durƙusawa yayi gabanta, ya rungumota jikinsa. Zuciyarsa tayi wani irin rauni, ya sake wani irin kuka. Itama kukan tasa.

“Za su dawo, In Sha Allah. Za ku dinga wasa kamar yadda kuka saba da ’yar’uwarki. Mamanki ma za ta dawo. Ki daina kuka, kin ji ko?”

Kallonsu ake cike da tausayi.

ASP ya matso kusa da shi ya dafa kafaɗarsa.

“Ka yi haƙuri. In Sha Allah, za mu yi iya ƙoƙarinmu wajen ganin mun gano ko waye yayi wa ’yarka wannan cin zarafin. Ko akwai wanda ya ga ko waye? Sannan kuma ya aka yi aka gano tana wajen nan?”

“Uhm! Ban san me ya faru ba. Ni dai ina cikin gari, maƙocina ya kirani ya faɗa mini abin da yake faruwa, shi ne na garzayo na dawo gida. Ina zuwa ne aka zo aka faɗa mana ai an ganta a nan ɗin.”

Jibril ne ya matso kusa da su ya ce, “Ranka ya daɗe, bayan mun yi sallah magarib ne muka fito nemanta. Mun zo shigewa tanan ɗin sai muka ga ya fito yana sanɗa. Hakan yasa muka yi ƙoƙarin kama shi, amma yana ganinmu sai ya gudu.

“To, mun yi ƙoƙarin binsa, sai dai cikin rashin sa’a mun kasa cimmasa, ya ɓace mana. Hakan yasa muka dawo nan ɗin, sai muka sameta cikin jini.”

“Waye shi ɗin wanda kuka gani? Sannan ku nawa ne sanda kuka gan shi?”

“Idiris ne. Ɗan unguwar nan ne. Muna da yawa gaskiya, za mu kai mu goma ko ma fiye.”

“Kun kuma tabbatar da shi ɗin ne?”

“Tabbas shi ne. Ai mun masa farin sani, Ranka ya daɗe, tunda duk ’yan unguwa ɗaya ne mu. Sannan kuma akwai wacce ita ce ta fara ganinsa da yarinyar, Suwaiba.”

Hamisu ya bashi amsa cike da tabbaci.

“Ok. Ina Suwaiba? Sannan ina su iyayen Idiris ɗin?”

“Dukansu suna gida.”

“Ku yi haƙuri, za mu tafi da ku police station. Za mu shigar da bayanan nan naku. Kar ku damu, ba wani abu ba ne, kawai bayanin ku za mu shigar.”

“Ba komai, Ranka ya daɗe. A shirye muke da mu ba ku haɗin kai don ganin an ƙwatar wa yarinyar nan da haƙƙinta.”

“Na ji daɗin hakan sosai.”

Ya dawo da dubansa kan Abdul.

“Za ka biye mu, mu tafi asibiti. Sajan Tukur, ku tafi da waɗannan office, har ita Suwaiba da iyayen Idiris ɗin. Duk ina buƙatar ganinsu a office.”

“Ok, Sir.”

Tun da aka zo aka bata labarin abin da ke faruwa, duk tabi ta ruɗe. Sai kai da kawo take a ɗan tsukakken tsakar gidan nata.

“Shi kenan yaron nan ya janyo mini masifa. Yanzu ya zanyi ni, Inno?!”

Zuwa tayi ta janyo mayafinta a kan ƙyauren ɗaki, tamkar wata taɓaɓɓa, ta fito gidan. Ita kanta ba ta ce ga inda za ta je ba.

Tana fitowa tayi tozali da masu baƙin kaya ’yan sanda. Ta juya a sukuwanne za ta koma ciki, suka yi saurin yi mata ƙawanya.

“Kin ga, ki zo mu tafi ba tare da gardama ba. Idan kuma kika sa mana gardama yanzu sai jikinki ya gaya miki!”

Ba ta da mafita bayan ta biye su ɗin. Dama Hausawa kan ce ɗan kuka shi yake janyo wa uwarsa jifa. Tayi maganar a ranta tana mai ƙara fashewa da kuka.

Tun da suka dawo gida, bata iya ta koma fita ba. Duk da labarin ganin Hussaina ya sameta, sai dai yanayin da ta ji an ce an ga Hussaina a ciki sai ya ƙara tayar mata da hankali. Tana ji a ranta, koma me ya sami yarinyar nan laifinta ne. Da a ce tun sanda ta gan shi da ita ne ta je ta masa magana, da duk hakan bai faru ba.

“Kukan me kike kuma? Ai koma meye laifinki ne. Sai ki tashi ki tafi. ’Yan sanda na jiranki a waje, za su tafi da ke.”

Kallon mijin nata da shigowarsa kenan tayi a firgice ta ce, “’Yan sanda kuma?”

“Su fa. Dama ai baki shi ke yanki wuya. Duk wanda ya ce ba zai gani ya ja baki yayi shiru ba, ƙarshensa kenan. Kuma wallahi ni ba ruwana, ƙafata ba za ta taka Police station ba!”

“Na shiga uku! Don Allah, Malam, ka taimake ni. Ka yi masu magana su tafi su ƙyale ni.”

Buga ƙofa aka yi. Kallon ƙofar tayi a tsorace tana zaro idanu kamar wacce tayi wa sarki ƙarya.

“Kin ga, ni ba ruwana. Suna jiranki, ki maza ki fita tun kafin su shigo!”

Ɗaki ta shiga ta ɗauko hijab ɗinta ta fito. Yaranta na kuka, kallonsu kawai tayi ta kawar da kanta. Haƙiƙa yau halinta na shirin janyo mata masifar da ba ta san a ina za ta tsaya ba.

Riƙe yaran yayi yana lallashinsu. Ta fita tana waiwayensu.

A mota ɗaya aka saka su, aka nufi Police station da su. Mutane kowa sai mayar da zance suke.

“Ki daina kuka. Za su dawo da yardar Allah. Mu je gidana.”

Maman Na’ila tayi maganar tana mai riƙe hannun Hassana. Abdul ya roƙi alfarmar ta zauna a wajanta kafin su dawo.

“Hafiza na gida, na barta tana bacci.”

“Ok, mu je mu ɗaukota.”

Fulani