Fargar Jaji

Chapter 2

by @fulani2



Suna zuwa asibitin suka nufi emergency, sun tarar da su DSP a tsaye, daga gabansu kuma likitoci ne suka yi cirindo a kan Hussaina, sun mata ƙawanya.

"Ya a ki ciki ne?" ASP ya yi tambayar, idanunsa a kan DSP.

"Tun da muka zo dai suna a kanta har yanzu ba su ce komai ba."

"Ina ita uwar?" DSP ya buɗe baki zai yi magana, karajin Aisha ya karaɗi emergency ɗin, wanda hakan yasa bai iya furta ko da kalma ɗaya ba. Suka nufi wajanta da sauri. Hankali tashi, Abdul ya riƙo hannunta.

"Ina 'yata? Don Allah ku ce mini babu abin da ya sameta. Mafarki ne nake, ku tashe ni daga wannan mummunan mafarkin!!"

Rungumeta ya yi, jikinsa ya kasa cewa ko da uffan saboda ji yake bakinsa ya bushe, yawon bakinsa sun ƙafe tamkar an sa gum an datsi laɓɓansa. Ƙwaci jikinta ta yi daga riƙon da ya yi mata, ta sauko daga kan gadon da sauri tana faɗin, "Ina 'yata!!!"

Nus suka tasu suna ƙoƙarin riƙita ta, yi saurin ja baya kamar kububuwa.

"Ku nuna mini 'yata, na ce!!"

"Kin ga ki kwantar da hankalin ki. In Sha Allah 'yar ki za ta samu lafiya, kin ganta can ana duba ta," ASP ya yi maganar cikin lallashi tare da nuna mata wajen da ake duba Hussaina.

Abdul ya matsa kusa da ita, ya kai hannu zai riƙita ta, ja da baya kaɗan tana kallonsa, idanunta a waje cike da tsana ta ce.

"Kar ka kuskura ka matso wajen da nake, bare har ka yi gigin taɓa ni, azzalumi macuci! Ko me ya sameta kai ne ummul haba'isi!!"

Tsayawa ya yi yana kallonta, takaici suka haɗe masa da baƙin ciki. Wani irin ɗaci yake ji a cikin bakinsa. Ta yaya zai zama silar wargaza rayuwar 'yarsa da kuma su kansu? Don me take son ɗora laifin komai a kansa?

Likita ne ya kira su dukansu, suka tafi da sauri. Aisha ta tashi cikin jin jiri ta ƙarasa wajen da suke. Masu jinya da mijinyatan da sauƙi ya fara samuwa, sai kallonsu suke ciki da tausayin wannan rashin imanin da aka yi wa ƙaramar yarinya.

"Ina mai ba ku haƙuri, maganar gaskiya ko da kuka zo, rai ya riga da ya yi halin..."

Faɗuwa ta yi a wajen ba tare da ta iya jin sauran maganar ba.

"Wayyo Allah na, bani na lalace! Mutuwa, me yasa za ki mini haka!? Wayyo Allah ka ɗauki raina na huta da ganin wannan baƙar ranar! Idris ka cuce mu, Allah ya isa tsakanina da kai. Allah me yasa z..."

Wata dattijuwa da take jinyar jikanyarta ta yi saurin zuwa wajanta, rufe mata baki ta yi cikin matuƙar tausayi da tausasa murya ta ce.

"Haba yarinyata, me yasa kike abu kamar ba Musulma ba? Dukan mai rai tabbas sai ya ɗanɗani zafin mutuwa, kullu nafsin za'ikatul maut. In ji Allah. Haƙika akwai cin rai da yadda lamarin ya kasance, amma idan har kika yi haƙuri za ki ci ribarsa duniya da lahira. Ki yi addu'a, kin ji 'yata."

"Innalillahi wa inna Ilaihi raji'un, Allahumma ajibni fi musibati wa ajibni khairan minha, Hasbunallahu wa ni'imal wakil, La'ilaha illallahu Muhammadu RasululLah SallalLahu AlaiHi WasalLam!!"

Tun daga waɗannan kalaman kalma ɗaya ba ta iya sake furta wa ba. Hawayen idanunta suka tsaya cak, ta kwantar da kanta jikin dattijuwar.

Abdul jiri ya tashi, ɗaukarsa DSP ya yi saurin riƙo shi. Kallon Hussaina yake, idanunsa na zubar da hawaye masu zafin gaske.

Bayan sun gama auni-auninsu da rubuci-rubuci, aka ba su gawar. Dattijuwar ita ta kai Aisha har mota, tana ƙara yi mata nasiha, suka nufi gida da ita.

"Oh ni Suwaiba, yau tsegumi ya kai ne ya baro, yau ni ce a police station, baƙin tarihi!"

"Kin ga ki kwantar da hankalin ki, ba wani abu za a yi miki ba. Kawai bayanai muke so ki ba mu na abin da kika sani gami da faruwar lamarin nan," cewar ofisa.

Haɓar zanenta tasa tana share hawayen da ke zarya a fuskarta, ta fyace majina.

"Ke muke saurare."

Cikin kuka ta zayyane masu iya abin da ta sani. Bayan ya gama rubutawa, aka dawo kan su Jibril, bayar da bayanin komai suka yi kamar yadda suka sani.

"Shi kenan za ku iya tafiya, amma ku kwana da shirin, koyaushe za a iya neman ku."

"In Sha Allah a shirye muke, a duk lokacin da aka buƙaci ganin mu za mu zo," cewar Jibril.

Sun juya za su tafi, Inno ta biyu bayan su. Tsawa ya daka mata.

"Ke, wa ya ce da ke ki tafi!?"

Ta juyo a tsorace tana faɗin, "Ranka ya daɗe, na ji kun ce ne mu tafi ai shi yasa."

"Su na ce su tafi, ba da ke ba. Ke kina nan har sai ɗanki da ake zargi ya bayyana kansa, sannan za mu sallame ki."

Kuka ta fashe da shi kafin daga bisani ta ce, "Wallahi idan zan shekara a wajanku, na tabbatar da Idris ba zai taɓa zuwa nan ɗin ba, saboda taurin zuciya ne da shi wallahi. Sannan ranka ya daɗe, kai da kanka fa ka ce zargi ka ga babu tabbacin shi ne. Kenan zamana a wajanku tamkar zalunci ne."

"Idan kika ce za ki mana rashin kunya a nan ɗin, sai nasa a naɗa miki na jaki. Sajan Mery, ki sa mini ita a sil!"

"Ok Sir," ta amsa tare da fitowa daga bayan kanta, ta ja Inno tana ihun kuka.

"Wallahi Suwaiba, idan har na fito, sai kin tabbatar da ba ki da wayo daga kaina, ba za ki sake yi wa ɗan wani sharri ba!"

Da sauri Suwaiba ta fita, don ita kam a tsorace take. Turata ta yi cikin sil, tana rufe ƙofa ta ce, "Ba ma son hayaniya, ko ki mana shiru ko yanzu jikin ki ya faɗa miki!"

Rufe bakinta ta yi tana ƙoƙarin haɗiye kukan.

"To, to, na yi shuru."

Bayan sun tari abin hawa, Suwaiba ta dube su ta ce, "Wallahi ni fa ban da ko sisi da zan biya na adaidaita."

"Ba damuwa, mu je sai na biya mana gaba ɗaya," cewar Hamisu da yake ƙoƙarin shiga.

Yadda ta ga rana, hakan ta ga dare, idanunta a kan Hussaina. Yau Hussaina ce ke a kwance, babu inda yake motsi a jikinta. Hussaina ce ke kwanan keso ta sanadin azzalumin maƙoci da azzalumin uba.

Mahaifiyar Abdul ce da kusan tare suka iso gidan, tare da gawar, don tun a kan hanya ya kira ya faɗa masu. Ta zo ta tashe ta daga gaban gawar, ta nufi falo da ita.

"Ki yi haƙuri Aisha, babu mai wuce ƙaddararsa. Tun da har Allah ya rubuta cewa ta hakan zai karɓi rayuwarta, babu wanda ya isa ya karkare hakan daga alƙalamin ƙaddararta."

Kanta kawai ta iya gyaɗa mata. Tashi ta yi ta fita waje, alwala ta ɗauro, ta dawo cikin falonta. Shimfiɗa darduma ta yi, ta fuskanci gabas.

Umma ta kalle Abba da yake a kwance kan gado, tamkar babu abin da ya faru. Ranta a ɓace ta ce, "Wai Alhaji, me kake nufi ne?"

Shiru, babu amsa. Girgiza ƙafafunsa ta yi.

"Alhaji!"

Juye ya yi tare da yin miƙa yana faɗin, "Mene ne?"

"Tambayata ma kake, tun da mahaifin Abdul ya kira ya faɗa ma ƙaddarar da ta samu Aisha, ka ƙi zuwa, ka ƙi bari na je. Haba, sai ka ce wacce ba ta da kowa a garin nan. Wani irin rashin tausayi ne wannan?"

Tashi ya yi ya zauna, idanunsa a kanta.

"Saboda hakan ne za ki tasheni bacci? To, kamar dai yadda na faɗa, ba zan ba kuma duk wanda na isa da shi ba za shi ba, faƙat!"

Girgiza kanta ta yi.

"Innalillahi wa inna Ilaihi raji'un! Wace irin zuciya ce da kai? Ko me A'isha ta yi, ya kamata ka haƙura, komai ya wuce. Abdul ne mijin da Allah ya zaɓa mata, ba mu isa mu sauya hakan ba. Sannan wani ba ya haifar ɗan wani. Mu godewa Allah da muke a raye, rabo bai zama sanadin yankewar numfashinmu ba. Tun da aka yi auren nan, ka hana mu zuwa wajanta, idan ta zo ma babu wani farin ciki da take samu daga wajenmu."

Shiru ta yi tana share hawayen da yake fuskarta.

"Daga yanzu ba zan sa ke yi maka wannan biyayyar ba. Ina son 'yata, dole ce tasa kawai na kawar da kaina daga gareta saboda bin umurninka, amma daga yanzu wallahi na daina. Gobe zan tafi gidan, ba za a yi wannan rashin tausayi da ni ba. Na tabbatar da tana cikin halin da za ta buƙaci mu a kusa da ita. Wallahi tafiya zan yi!"

Ta ƙarasa maganar tare da bin hanya za ta fita.

"Ki tabbatar da idan har ƙafarki ta taka gidan, ba bisa yawon bakina ba, ban yafe ba!"

Yana faɗa ya koma ya kwanta. Juyowa ta yi da sauri tana kallonsa, gyaɗa kanta kawai ta yi ta fice ɗakin, rai a ɓaci.

Sai safa da marwa take cikin ɗakin, ta rasa wace irin zuciya ce ne da Alhaji da ba ya yafiya. Zama ta yi gefen gado ta yi tagumi, hawaye masu zafi suna zubo mata.

'Shin da me yake so Aisha ta ji raɗaɗin mutuwar, ita wacce aka yi sanadin katsewar numfashinta sanadin zalunci ko kuma da wufantar da ita da suka yi a matsayin su na iyayenta?'

Riƙe kanta ta yi, tausayin 'yarta na ɗawainiya da ita.

Zabura ya yi daga baccin da yake yana salati, wanda salatin nasa ne ya tashe ta daga bacci. Laluba makunnin fitila ta yi ta kunna, haske ya mamaye ɗakin. Tagumi ta ga yayi cikin damuwa ta ce, "Lafiya kuwa, Love?"

Ajiyar zuciya ya yi kafin daga bisani ya ce, "Babu komai, ki koma ki kwanta kawai."

"Haba, ya za ka ce da ni ba komai? Don Allah, me ya faru?" Ta yi masa tambayar kamar za ta yi kuka.

Sauku da ƙafafunsa ya yi ƙasa.

"Mafarkin A'isha na yi cikin wani babban rami mai matuƙar zurfi, tana ihun kuka tare da miƙo mini hannunta tana neman taimakona. Ina ƙoƙarin ceto ta ne na farka."

Tsaki ta yi.

"Dama saboda wannan ne ka tsorata ni? Hum, ka dai ji tsoron Allah, ka dinga tuna wa ita ɗin matar wani ce."

"Na fi ki sanin matar wani ce kuwa, sai dai ki tuna ita ɗin ƙanwata ce. Hakan kuma ban isa na hana kaina mafarkin da ba ni ne na janyo ya zo ba."

Tunzuro baki ta yi gaba.

"Da ba ka sa ta a ranka ba ai ba za ka dinga mafarkinta ba, ba kuma yau ka saba yi ba. Ai tun da na sha jin ka na mafarkin ta da kiran sunanta."

Komai bai ce da ita ba. Ya sauka daga kan gadon, banɗaki ya shiga.

Ta koma ta kwanta tana masifa.

"Ni Halima, na ga abin da ya fi zare tsaye. Ni da wannan masifar, ba gara a ce kishi nake da ita ba? Tana gidan wani, amma ka ƙi cire tunaninta a ranka. Koyaushe ƙara cusa mini baƙin ciki kake da ita."

Jim kaɗan ya fito, yana sharci ruwan fuskarsa, da alama alwala ya yi.

Sauya kayan jikinsa ya yi, wajen da yake ibadarsa ya je, zai kabbarta sallah wayarsa ta fara ringing. Tsayawa ya yi cak, a yayin da zuciyarsa ta dinga bugawa fat! Fat!! Fat!!!

Da sauri ta tashi tare da duba wayar da take gefen filo. Ganin mai kiran yasa ta koma ta kwanta tana jan dogon tsaki.

Tana faɗin, "Jaraba, da daren ma sai an hana mutum sake wa."

Jiki a sanyaye ya je wajen da wayar take a ajiye. Kiran ya tsinke. Yana dubawa ya ga sunan Ummana. Wani irin sanyi ya ji, ƙafafunsa sun yi zama. Zama ya yi gefen gadon da sauri.

'Kar dai rasuwa Aisha ta yi, shi ne fassarar mafarkinsa? Don in har lafiya babu abin da zai sa Umma kiransa cikin wannan sulusin daren.'

Ya yi tambayar a zuciyarsa, tsoro ya sake samun mazauni a zuciyarsa.

Kira ya yi, tana shi ga aka ɗaga. Kukan Umma ne ya karaɗe masa dodon kunnensa.

"Ummana, me ya faru?" Ya yi tambayar hankali tashe.

"Nasir, Aisha ce..."

Zuciyarsa ta yi wani irin bugawa da har sai da yasa hannu ya dafa saitin zuciyarsa. Jin ta yi shiru tana ci gaba da yin kuka.

"Me ya samu A'ishan?"

"Yarta Hussaina ce, wani azzalumin ya yi mata fyaɗe, wanda hakan ya yi sanadin da yarinyar ta rasu."

Tashi ya yi zaburi yana faɗin, "Innalillahi wa inna Ilaihi raji'un! Fyade, ta kuma rasu! Innalillahi wa inna Ilaihi raji'un!"

"Abbanku ya hanani zuwa, ya ce shi ba zai je ba kuma kowa ba za shi ba. Shin hakan adalci ne a gareta? Kai kaɗai na san za ka yi masa magana. Don Allah ka ruƙar mana shi ya barni, ko da ni ce na je. Don Allah."

"Ki yi haƙuri. Zancen babu wanda zai je ai duk bai tasu ba. Zan zo Kaduna, har Abba zai je yanzu zan tashi, In Sha Allah."

"A'a Nasir, kar ka biyu daren nan, ka bari zuwa gobe sai ka zo."

"Ki dai yi mini addu'a."

Ya tsinki kiran ba tare da ya bari ya ji me take faɗa ba. Kiran direbansa ya yi, wanda a gidan yake kwana. Yana ɗauka ya ce, "Iliya, ka fito da mota za mu tafi Kaduna."

"Lafiya kuwa Yallaɓai, tafiya da sulusin daren nan?"

A gurguje ya masa bayanin abin da ya faru. Bai ƙara sa jin salatin da Iliya yake yi ba, ya tsinki kiran.

"Ka kuwa san ƙarfe nawa yanzu da za ka kama hanya? Ka tafi ƙarfe biyun dare fa," ta faɗa, idanunta a kan agogon da ke manni a kusurwar ɗakin.

"Na sani da biyun dare, da ranar duk na Allah ne. Shi yake tsari bayinsa a kowane lokaci."

"Eh, amma duk da hakan da ka bari sai gobe, sai ka tafi, tunda mai faruwa ta riga da ta faru."

Yana zura takalminsa ya ce, "Addu'ar ki kaɗai nake buƙata. Na san kin ji duk abin da ya faru, idan kuma za ki ƙi tashi mu tafi..."

"A'a, a sauka lafiya."

Kaɗa kansa kawai ya yi, yasa kai ya fita. Bin ƙofar ta yi da idanu, zuciyarta kamar za ta fashe dan takaici.

"Ni ban taɓa ganin marar zuciya irin Nasir ba. Duk abin da ta yi masa, ya kasa cire ta daga ransa. Idan an yi magana, ya wani raina wa mutane hankali da zumunci, ƙanwarsa ce ita. Mtsww!! Yanzu ina yin wata magana, zai ce ban da imani, ban da tausayi da abin da ya sameta."

Ta koma ta kwanta, zuciyarta na suya.

'Ko mata uku zai aure, ba ta jin za ta damu irin yadda take jin damuwa a kan Aisha. Ina ma ita ɗin ce ta mutu da kowa ma ya huta!'

Ta yi maganar a zuciyarta.

Ya fito haraba ya samu har Iliya, direba, ya fito da mota. Suka kama hanya. Bai san ta yaya zai iya kwantata irin ciwon da yake ji gami da abin da ya faru ba. Ji yake kamar 'yar cikinsa ce aka yi wannan zaluncin.

Faɗa Abba ya hau yi kamar babu gobe.

"Don me za ki kira shi ki ɗaga masa hankali, ki sa ya biyu hanya cikin dare!"

"Abba, ka yi haƙuri, ba laifinta ba ne." Nasir ya yi maganar kansa a ƙasa.

"Idan ba ta kira ka ba, ka san me yake faruwa bare har ka biyo dare ka zo? Kar ka sake wannan gangancin, biyu dare ka yi tafiya mai tsayi, musamman a kan abin da ba ya da muhimmanci."

"Ka yi haƙuri," Umma ta yi maganar murya a sanyaye.

Tashi ta yi za ta fita.

"Ki zauna, magana nake so za mu yi," cewar Nasir.

Komawa ta yi ta zauna a kan kujerar da ta tashi. Gyara zamansa ya yi, idanunsa a kan Abba da ya haɗi fuska gabas da yamma. Duk sai ya ji jikinsa ya yi sanyi. Hakan ya yi ƙarfin halin buɗe baki.

"Don Allah, don son Ann..."

Ɗaga masa hannu ya yi.

"Ka ga, kar ka haɗani da abin da ya fi ƙarfina a kan abin da ba zan iya yi ba. Na faɗa mata a jiya, kuma a yanzu ma zan maimaita. Wallahi, ba wanda zai tafi. Idan har waninku ya tafi, ba da yawona ba, ban kuma yafe ba. Ko me ya faru, ita ce ta janyo wa kanta. Ai duk wanda ya ce zai hana uwarsa kwana, shi ma ba zai taɓa yinsa ba."

Tashi ta yi a zuciye, ta kalle shi ta kaɗa kai ta bar falon. Bin ta da kallo Nasir ya yi kafin ya dawo da kallonsa kan Abba. Idanunsa na zubar da hawaye, ya matsa kusa da Abba da yake zaune a kan kafet, riƙo hannayensa ya yi, zai yi magana ya tari numfashinsa.

"Wallahi Nasir, kan maganar nan za mu samu saɓani da kai, ba na buƙatar ta.!"

An shirya gawar, maƙota da 'yan uwan Abdul duk sun cika gidan. Aisha tana zaune daga gefe, hannunta riƙe da cazbi tana ja. Hassana da Hafiza suna kwance jikinta. Hassana ta ci kuka sosai har muryarta ba ta fita.

"A'isha, ko za ki kira iyayen naki? Shiru, babu wanda ya zo. Ga shi tun jiya muna hanyar zuwa nan ɗin, Alhaji ya kira Abbanki ya faɗa masu," Maman Abdul da ta matso kusa da ita ta yi maganar murya ƙasa.

Tana gyaɗa kanta ta ce, "Ba zan kira su ba. Na tabbatar da ba za su zo ba. Sun jima da binne ne a wajen su. Ni ba rayayya ba ce a wajen su. Ni ma daga yanzu na ƙara tabbatar wa da kaina ni ɗin marainiya ce, da ban da kowa sai waɗannan."

Ta nuna yaran tare da kife kanta jikinsu. Sai yanzu ta samu hawayen suka zubo mata.

Fulani