Chapter 33&34
by @deeyamerh10
đź’–đź’– SOYAYYAR ZUCI đź’–đź’–
(Love and Romantic story)
Written
By
Deeyamerh
07070647239
Page 33&34
Fatima ta matso kusa da Suhaima da sauri domin tayi mata bayani Amma ina.... Suhaima tai saurin daga mata hannun“Kar ki zo kusa da ni.”
"Fatima don Allah ki ba ni dama in yimiki bayani.”
Me za ki ce?” Suhaima ta tambaya cikin ɓacin rai. “Akwai wani bayani da zai canza abin da naji da kunne na ne?ko kuwa zaku cigaba da rai na min hankali ne?why Fatima?nayi tunanin kice mafi kusanci bayan Abba Ammey na da zataga abinda zai cutar dani wajan kareni Amma,tasaka karasawa domin wani kuka da ya sarketa juyawa zatayi Amma Fatima ta ruko mata hannun cikin sauri.
"Dan Allah suhaima ki tsaya kiji domin da akwai abinda kina ji zaka kisan wllh bani da laifi,sannan Bros Sha'ayan yayi haka ne domin Abu biyu,na farko ya boye Miki ne domin a wanna lokacin baki da lokacin soyayya Duba da Ammey bata kusa dake,Ni na fada masa domin Ammey ita ce komai namu,Na biyu kuma,kina karatu domin Abba shi ya ne mine ya saka ya mike wanna zance Domin ba iya Boye Miki akai ba har ma da Auran da Aka daura Miki dashi wanda Ayi hakan ne dan Abark ga Ammey domin Abba yace a jikinsa yake ji zata dawo gareshi,duba da yadda kika rayuwa a cikin gidan ku kamar bayyawa duk abinda yake faruwa Abba yasani Wannan yasa Abba yace a rufe zan cen ,Amma wallahi Allah banyi niyar cutar da ke ba, ki yarda Dani. fashewa da kuka Fatima tayi domin tsan abun dole a gigita duniyarta.
Suhaima shiru tayi tana kallon Fatima kamar wata sukuwa domin gani take kamar zata ga abinda Fatima ta fada mata a kan fuskarta,"Aure aka daura mun da wanda ban taba gani ba?to meyenayi ba Abba?Aure ba wasa ba Fatima da aure nake soyayya da wani?nacewa Allah me umm?kuka ta sake fashe wa dashi sosai tana rungume Fatima dan Wllh jitake kamar wasa.
Gun gumeta Fatima tayi ta ja numfashi mai zurfi, kafin ta ce"Na san abin da yayi Miki ya sa kika yi fushi to ba haramun yayi ba,Kuma na san da ba nice na fito ba za'ayi muku kallon mara tarbiya Sai Allah yasa nice,Nima a inda nasan an daura Miki Aure,nazo zan wuce naji Dady yana fadawa Mama cewa yanzu aka daurawa suhaima Aure da dan Abokin su,Amma ba wanda ya sani taja bakinta tayi shiru,sannan ba kowa bane face Sha'ayan,saisai naji mama tana murna da hakan. To kinji abinda naji shiysa ko da na ganku banji komai ba domin nasan waye Amma kiyi hakuri dan Allah.
Suhaima ta kalle ta tace"Ba ni na shirya abin da ya faru ba. Kuma ban taɓa tunanin zan ji wanna labarin mai matukar rikitarwa ba,Da na san abin da zai biyo baya kenan da ban fada soyayya da SECRET LOVER ba, Domin Ba zan boye Miki ba ina sonsa jinake kamar wani shashi na jikina nane,Fatima bazan iya rayuwa da SH ba domin zai aure Ni ne kawai Amma zuciyar tana ga SECRET LOVER Dan Allah a warware Auran ta fada cikin kwalla.
"Cikin sauri Fatima tace Amma me ya sa kika bari kika fara sonsa Suhaima?
“Saboda na shine yake dauke mun duk wata kewa da nake ji,shine yake jin duk wani motsina a zuciyarsa,a duk lokacin da nake cikin kunci shine mai yaye mun,Na kasa sanin yaushi nafara sonsa domin SOYAYYAR ZUCI nake masa mai sa zuciya fashewa,da zan iya da nashiga duniya neman Sa domin da gasken gaske ina sonsa da kaunarsa Na yi tunanin zan iya magance karfin SOYAYYAR da nake maka Amma abin yaci tura,ina cikin bulayin neman sa sannan ace mun Ina da Auran wani akai na?tabbas su Abba sunyi kurkuran bayar dani domin ina da wanda nake so.
Kallonta kawai Fatima take yi Domin duk haukan da takeyi akan mutum daya ne to idan taji shine to yazatayi kenan?ganin tunanin bazai kai mata ba ya tace"Amma abu ɗaya nake roƙonki ki yarda da ni a kai ban taɓa nufin cutar da ke ba,tabbas wannan zabin da Abba yayi Miki shine zabin da kika dade kina nema dan haka ki kwantar da hankalinki a sannu zaki gane hakan.
Suhaima ta yi shiru na wasu daƙiƙu.
“Me ya sa ba ki gaya min tun farko ba?”
“Saboda na ji tsoro.”
“Tsoron me?”
“Tsoron kada ki ƙi fahimtata. Tsoron kada ki ɗauka cewa na ci amanarki.”
Suhaima ta sauke idanunta. Fushin har yanzu yana nan, amma kalaman Fatima sun fara karya masa ƙarfi.
Fatima ta ƙara da cewa.
“Idan har kin ga na yi miki laifi, zan amince. Amma ki saurare ni kafin ki yanke min hukunci. Ni ma abin ya dame ni. Kuma ban so abin da ya faru ya sa ki ji cewa ban damu da mutuncinki ba.”
Suhaima ta share hawayenta a hankali.
“Ban ce ban yarda da ke ba…”
“Amma kina fushi da ni.”
“Eh,” Suhaima ta amsa cikin sanyin murya"saboda kinsan komai koda bana sonsa zan kare masa hakkin Auran sa akai na Amma Kinga irin shigar da take jikina?kenna abinda yasa yayi mun daukar amarya ranar cocktail party kenan? Shiyasa da kika dawo baki cemun komai ba?
Fatima ta gyada kai"eh duk nasani shiyasa nai Miki shiru domin yana da hakkin yin haka ko ma fiye da shi,sannan ko me napep din nan ai shi ya turosa.
Suhaima ta yi shiru, tana kallota fahimci cewa da gaske Fatima take Domin bin da ya faru tasani,Haba shiyasa yake ce mata Madam sai yanzu tagane,ko ma shi ne dalilin da yasa kwata kwata bata kula samari.
Duk wani abu da Fatima ta sani sai da ta fada mata Domin tasani kuma ta koyaye domin Auran nan babu fashi shi ahto.
Dinner da da bada su aka kara saba dan gadanan gida sukai dan yake zazzaɓi ya ruf suhaima.
________
Sha’ayan tun da yafige motarsa bai tsaya ko ina ba sai Airport dan Gara yayi nesa da kasar ko zaiji sanyi a ransa domin Abin da Suhaima ta yi masa ya tsaya masa a rai fiye da yadda yake so ya nuna,kiran waya yayi yace wa driver yazo ya amshi motarsa.
Ba'adau lokaci ba sai gashi yaxo key din
Motar ya bayar sannan y shige cikinna.
List din Ya duba flights É—in da ke akwai.
Sai idonsa ya tsaya akan Dubai,karfe 9:00 PM jirhin zai tashi ba wai dan yana da wani muhimmin aiki a can ba.
A'a ,Yana son kawai ya yi nesa da mutanen da suka sa ransa ya ɓaci,Musamman Suhaima.
Ya ɗauki passport ɗinsa, ya miƙa wa ma'aikacin check-in.
“Sir, you’re travelling alone?”
Sha’ayan ya ɗaga kai.
“Yes.”
“Destination?”
Ya yi É—an shiru kafin ya amsa.
“Dubai.
A lokacin da aka sanar da boarding ɗin jirgin ƙarfe tara, Sha’ayan ya zauna a kujerarsa, hannunsa ɗauke da wayarsa.
Saƙonni da dama sun shigo,Amma babu ɗaya da ya buɗe, sunan ta ya kurawa ido,Ya dade yana kallon sunan,Zuciyarsa tana wani irin nauyi.
Jirgin ya tashi daga filin jirgin, yana barin ƙasar a hankali.
Sha’ayan ya kalli hasken garin da ke ƙasa har ya ɓace daga ganinsa.
Sai ya lumshe idanunsa,Fuskarta kawai yake kalla da irin yadda take tsiwar ce masa zata rungume wani. wannan daren yazo masa da wani irin lissafi na daban,yana murnar ganinta ita tana murnar fada masa wani da ban,da Auransa kanta.
Wannan dare ka kasance mai tsaho a gun Ma'abuta zuciya daya,Domin ya kasa dai na tunaninta da yadda yayi kiss din ta,haka ma a bangaran suhaima komai ya tsaya mata,domin komai a matsayin bako yazo mata gashi na wata hanya da zata iya haduwa da SH bare suyi shawarar yadda zasu yi dan wllh bazata iya kallon idonsa tace bata sonsa,Amma ya duba abinda xuciyarta take so.
🔥🔥🔥🔥🔥
Karfe 7:35 na safiyar Dubai.
Jirgin ya sauka a Dubai International Airport cikin nutsuwa, amma zuciyar Sha'ayan ba ta da wata nutsuwa ko kaÉ—an.
Tun daga lokacin da ya bar wajen dinner a Kano, bai sake magana da kowa ba. Fushin da Suhaima ta dasa masa ya rufe masa zuciya gaba É—aya.
Da ya sauka, ya ɗauki wayarsa yana kallon screen ɗin na ƴan daƙiƙu.
Sunanta ne kawai ya bayyana a zuciyarsa.
Suhaima.
Ya danne lips É—insa, ya kashe screen É—in.
“Not now…”
Ya faÉ—a a hankali.
A wajen airport kuwa, motar da aka shirya masa tuni tana jiransa.
Bayan kusan mintuna arba'in da biyar, motar ta isa Palm Jumeirah.
A gabansa ya bayyana wani katafaren gini mai ɗaukar ido—Atlantis The Royal.
Sha'ayan bai ko kalle shi da mamaki ba. Ya saba da irin wannan rayuwar. Amma duk da haka, ganin irin wannan wurin ya dace da yanayin da yake ciki—mai tsada, mai nisa da hayaniyar mutane.
yana shiga lobby É—in, ma'aikatan hotel suka tarbe shi cikin girmamawa.
“Good morning, sir.”
Ya É—aga kai kawai.
“Morning.”
Babu murmushi.
Babu sake fuska.
Babu wata magana mai yawa.
An kai shi ɗakinsa, aka buɗe masa ƙofar.
Room É—in ya kasance babba, mai kyau, taga mai faÉ—i tana kallon Arabian Gulf, komai a ciki yana nuna tsantsar luxury.
Ya ajiye wayarsa,Ya hau cire suit É—insa a hankali, ya zauna gefen gadon,a wannan karon ne gajiyar tafiyar ta fara sauka masa.
Amma duk da haka...
fushinsa da Suhaima bai ragu ba.
Ya jinginar da kansa a gefen gado ya lumshe idanunsa,hotonta ya sake bayyana cikin zuciyarsa.
Murmushinta.
Muryarta.
Da kuma abin da ta yi masa a wannan daren,idunsa buÉ—e da sauri.
“Why do you keep coming back to my mind?”Ya furta cikin takaici.
Toilet ya shiga yasakarwa kansa ruwan sanyi domin shine dai dai da yanayin sa,sai da yayi wanka sannan ya dauro alwala duk wata sallah da ake binsa sai da yaramata Sannan ya dau wayar cikin room din domin yana so a kawo masa coffee.
A Kano kuwa, Suhaima ba ta san cewa fushin da ta jefa zuciyar Sha'ayan ya kai ya bar ƙasar ba,Kuma abin da ba ta sani ba shi ne...
wannan tafiyar ba za ta zama ƙarshen komai ba,ha salima Ita ce farkon wani sabon babi na soyayyarsu.