FARASHIN ABOTA

23

by @nafisatusasaal01

*NAFISATU_SASAAL*
     ***


23

Dogayen yatsunsa biyu ya ɗaga ya yi min alamar na zo.

Mamaki ne ya bayyana a saman fuskata, da kuma tsoron sanin cewar da zarar na matsa kusa da shi zai gane ni.

Ko taku biyu ban yi ba, aka kirashi a waya..

Hannunsa ya ɗagamin tare da yi min alamar na wuce ciki.

Ƙafafuwana suna harɗewa na shiga ciki gidan..kai tsaye sashensu Fatima na shiga..

A rumfarsu na samu Mamansu tana kwashe dafaffiyar shinkafa dafadukan da yaji busasshen kifi a cikin kula.

Yawu na haɗiya ina murmushi na ce;

"Mama ina kwana?"

Ɗagowa ta yi tana kallona da murmushi kwance a saman fuskarta ta ce;

"Lafiya ƙalau. Aikuwa yanzu nan Fatima ta shiga sashen su Aunty, kin san su Saifi saukar dare suka yi jiya, maza ki je tana can..lafiya dai kika baro mutanen gidan na ku ko?"

Amsa mata na yi da "lafiya ƙalau, Inna ta ce ma a gaisheku"

"Muna amsawa" ta faɗa daidai lokacin da ta ƙarasa kwashe shinkafar a cikin kula.

Zan juya ta miƙomin bokiti tana cewa, na kai wa Aunty ta ajiye mata...ina tafe ƙamshin shinkafar na yi min yawo a hanci.

Da sallama na shiga sashen, babu kowa a ɗan ƙaramin tsakar gidan, don haka na nufi hanyar parlonta.

Takalma na gani, ciki har da ƙaton takalmin Armani double sole kamar yadda aka rubuta a jiki, kana gani kasan ƙafar namiji ne.

Sai da na fara yin bismillah, sannan na yi sallama.

Muryoyi sama da na mutum ɗaya ne suka amsamin.

Ban shiga kai tsaye ba, sai da na gyara zaman mayafina kaina.

Da Fatima na fara cin karo daga bakin ƙofa..zan zauna a kusa da ita, a ƙasa..

Aunty ta nuna min kujerar zaman mutum biyu tana cewa;

"A'a Hindatu kar ki zauna a ƙasa ki ɓata kayanki dawo nan ki zauna"

Murmushi na yi a kunyace na yunƙura  zan miƙe na ji ɗaya a cikinsu tana cewa;

"Aunty fa wajen zaman.." bata ƙarasa ba, Aunty ta dakatar da ita ta hanyar cewa;

"Na sani"

Ƙarasawa na yi zan zauna na ga waya tafkeke(Tablet) a gefe, don haka na ɗan raɓa a gefe na zauna.

Gaishe su na yi ɗayan bayan ɗaya kamar yadda na saba, suka amsamin fuska a sake..

kafin su fara tsokata da yau na yi kwalliya, ko dan na ji Sammani ya dawo ya na gari ne?

Kunyace ta kamani, na saka gefen mayafina na rufe fuskata ina murmushi..anan na fahimci wataƙila ba su san Aunty ba ce tayi min kyautar kayan.

Ko minti biyu ban yi da zama ba, na ji fitowar mutum da muryarsa da ba zan taɓa mantawa ba ya na cewa;

"Aunty na gwada yaƙi yi, it seems kamar network ne babu"

Bai lura da ni ba, sai da ya zo zai zauna, ina kallon Aunty sai kallonmu take tana murmushi..

Tsayawa ya yi yana kallona da irin kallon da nake ganin kamar ta ƙyama ce a baya, sai dai tsayuwarsa a daf da ni, ya sa na fahimci yanayin idanunsa ne yasa nake ganin haka.. 

Girarsa ɗaya ya ɗage ya ɗan motsa leɓensa zuwa gefe ɗaya duk da haka yana kallona kamar dai so yake yi ya tuna ina ya sanni..

Ɗan murmushi ya yi, mai kyau ya ce;

"Filthy! right?"

Dariya mutanen parlon suka kwashe da shi.. ɗaya a cikinsu ta ce;

"Yau dai Hindatu ta yi wanka, batun rashin tsafta kuma babu shi"

Ina jin haka, na gane dai dagaske kalmar filti ƙazanta ya ke nufi..

Sai na fashe da kukan kunya da takaici.

Kafin Aunty ta fara ƙorafi..ya yi sauri ya ɗauki wayarsa da ke ajiye a gefena ya yi hanyar fita..yana ji tana kiransa ya ƙi juyowa yana ce mata baƙi zai gani a waje, yanzu zai dawo.

Daƙyar suka lallasheni na yi shiru..har da ce min indai zan biyewa halin Saif sai ya saka min hawan jini..

Har na yi zaman hour huɗu a parlon Aunty muka yi sallah muka ci abinci bai dawo ba..

Ina nan zaune ni ƙadai bayan kowa ya fita, Fatima ma ta tafi sashensu yin wanka  na jiyo muryar Sammani ya na sallama..

Amsa masa nayi, ya shigo cikin ƙananan kayansa masu kyau..sai ƙamshi yake yi, har wata ƴar ƙiba ya yi.

Ya na ganina ya zaro ido yana murmushi..

Da alama yayi mamakin ganin yadda na fito tsaf da ni.

"Rabin raina, dama kina nan gidan?"

Ya faɗa yana ƙaraso tsakiyar parlon.

Murmushin jin daɗi na yi, ina gaisheshi.

A kujerar da ke fuskantata ya zauna yana ƙaremin kallo sai  murmushi yake yi.

Kafin ya kai ga cewa wani abu, Aunty ta yi sallama.

Ɗan zamowa ya yi daga saman kujerar ya na gaisheta.

Fuska a sake ta amsa tana yi masa yaya hanya?

A nan dai suka fara hirar da sam ba fahimta nake yi ba.

A cikin hirar tasu na ji tana tambayarsa ina Saif?

Ɗan dariya ya yi ya ce;

"Wallahi tun da ya fito jama'a suka lulluɓeshi, da ƙyar sha, da zamu rabu da shi dai ya ce zai je dutse, anjima kaɗan zai dawo, wataƙila ma ya na kan hanya"

Ɓata fuska Aunty ta yi, da alama  ba ta ji daɗi ba..sai dai bata ce komai ba akai ba.

Kallona ta yi, ta ce; 

"Hindatu dan Allah karɓowa Sammani abun sha a sashen Goggo(mahaifiyarta)"

"Toh" na ce mata ina miƙewa.

Ina kallon yadda Sammani ya ke ta bi na da wani irin kallo.

Ina zuwa sashen Goggo ko zama ban yi ba, aka ba ni ruwa da lemo na juyo.

Zan shiga sashen Aunty kenan na hango Saifi, da wasu kayan daban ba wanda ya fita da su da su ba, da alama kafin ya bar gidan ya shiga sashen mazan gidan ya sauya kaya.

Ina shirin zan juya da sauri, ya ɗago muka haɗa ido..

Tsayawa ya yi, ya na kallona..nima sai na ji na kasa tafiya, haka na tsaya a waje ɗaya, kaina a ƙasa zuciyata ta na ta bugawa  da sauri da sauri...

Ina jin sanda ya fara takowa zuwa inda nake..tsabar tsoro ƙafafuwana har rawa suke yi.

Lokacin da ya matso daf da ni, wani irin ƙamshi mai sanyin daɗi ne ya fara shiga hancina..duk da haka kaina na ƙasa ina kallon takalmansa sau ciki kalar baƙin da ya yi matuƙar da cewa da shigarsa..

Hannunsa dake ɗaure da agogo ya miƙo zai ƙarbi ruwan hannuna, da muryarsa da ke nuna alamar gajiya ya ce;

"Ina fatan ba ki saka datti ba"

Ɗago kaina na yi sama domin samun damar kallonsa..

Sai na ga shima, gashin da ya kwanta a saman goshina yake kallo..

Ni gaba ɗaya ban san ma ina da saurin kuka ba, sai da na ji wani kuka na shirin tahomin... zan yi ƙasa da kaina..ya ɗora yatsansa manuniya a saman laɓɓansa ya rage girman idanunsa alamar na yi shiru..

Ɓude ruwan ya yi, ya fara sha har lokacin yana tsaye..bayan ya gama sha..

murya ƙasa-ƙasa ya ce;

"Na gode" daga haka ya shige ya barni tsaye ..

Da bango wajen na jingina, murmushin jin daɗi ya ƙwacemin..sai na ke jina kamar ba ni ba, kamar wata sabuwar mutum ce da ban.

Na jima a haka idanuna a lumshe ina ta murmushi kamar wacce aka yiwa wani gagarumin kyauta..

Muryar Sammani ce ta dawo da ni hayyacina..

"Hindatu me kika tsaya yi a nan?"

Da sauri na gyara tsayuwata ina ce masa babu komai..

Ɗan jim ya yi alamar tunani..sai kuma can ya saki murmushi ya ce;

"Hindu kin ga yadda kika sauya kuwa? Ai ban san haka kika koma ba, da na yo miki tsaraba kala-kala"

A lokacin sam ban fahimci ina kalaman Sammani suka dosa ba, don haka na yi murmushi kawai ba tare da na ce komai ba.

Gefen fuskarsa ya shafa ya ce;

"Amma karki damu idan zan ƙara dawowa dole na yo miki tsaraba"

Lemon hannuna na miƙa masa.

Ya karɓa yana cewa;

"Ba ki karɓo ruwan ba?"

Kaina na girgiza, kafin na ce wani abu mu ka jiyo muryar Fatima a bayanmu.

Baki Sammani ya washe ya na ƙare mata kallo, lokacin da yake amsar gaisuwarta, saɓanin na ta fuskar da babu fara'a sam..

Kallona ta yi ta ce;

"Yaushe zaki tafi gida?"

Daidaita fuskata na yi, saboda yadda na ga ta ta fuskar babu wasa na ce;

"Sammani ne da man ya tsayar da ni"

Shiru ta yi kamar ba zata ce komai ba, har ta juya sai ta kuma ta dawo tana kallona ta ce;

"Ai ba ke ya kamata ki biyo shi ba, shi ya kamata ya zo gidanku, don haka ki taho na rakaki gida"

Sammani kawar da zancenta ya yi ta hanyar yin ƴar dariya ya ce;

"Da alama Fatima baki yi farin cikin ganina ba"

Ba ta ce masa komai ba..zai ƙara yin magana.

Mu ka jiyo muryar Aunty tana cewa;

"Hindatu dama baki tafi gida ba? Me kike yi a nan?"

Ga mamakina da sauri Sammani ya bar mu a tsaye ya yi hanyar fita..yana sosa ƙeyarsa.

Mu kaɗai ta gani a tsaye, na san kuma ta ji muryar Sammani, ba ta tambayemu yana ina ba, ta ce na kama hanya na tafi gida..kar Inna ta ji ni shiru..

Sallama na yi mata, ta ce In sha Allahu zata aikomin da tsarabarta da Saif ya kawomin.. 

A raina na ce tsarabar da zaki ba ni dai..

Mu na tafe a  kan hanya Fatima tana mitar ban da Sammani ya rainamin wayo, ya rasa a ina zai tare ni mu yi hira sai a gidansu, maiyasa bai fara zuwa gidanmu ya ganni ba?..

Kafin mu isa gida babu kalar shawarar da bata bani akan kar na kuskura na sakar masa fuska ba..Ni dai a cikin zuciyata kawai jin ta nake yi..

Domin ni a lokacin gani nake yi..babu wani abu da Sammani ya yi ba daidai ba..

Ko da zan ƙara rakata sai da ta ƙara ja min kunne na kiyayi Sammani..

Da daddare ina zaune a ɗaki, yaro ya yi sallama..wai Sammani ya zo gaishe da Baba..

A lokacin Baba yana masallaci, don haka Inna ta ce na fita kafin Baban ya dawo..

Ban wani tsaya ɓatawa kaina lokaci ba, na zura hijabi akan atamfar jikina na fita..

A tsaye na sameshi, sai ƙamshin ƴan gayu yake yi.

Zan gaisheshi ya tari numfashina da ce wa;

"Hindatu ya ya zaki fito a haka, ina Abayar ɗazun, maiyasa ba ki saka shi ba... gaskiya ki koma ki je ki saka kin ji rabin raina?"...✍🏻

Anya ba Sammani ne ya siyi Abayar nan ba?😂