BAKİN ALKALAMI…….

Chapter 10

by @maidambu41


 Hajiya Asma'u mace ce mai zafin kishi, mace ce me matuƙar izza da isa, sannan gefe guda tana da wani bakar al'ada a ranta ita matuƙar baka kai matsayin mijinta ba to ita ta rena Matarka, bata mu'amala da matan abokan Alhaji Mustapha Ladan. Ba ruwanta da kowa sai kanta da Yaranta haka ta dasa musu a ransu.  


   Muhammad Mustapha Muhammad, wanda a yanzu suke kiranshi da Abba Babba, shine Babban danta. Sai Yusuf aka. kiranshi Abban tsakiya, sai Abba Karami Harisu, sai Zaituna wacce suke kiranta Baaba Zaituna, Sai Turai, wacce suke kiranta Baaba Turai, Sai Atikah ita ce autarsu. 


      Kaf ahalin Ladan idan ka gansu kaga wanda suka jibanci jinin larabawa, domin sun kasance wasu irin ahalin masu kyau da haiba. Duk inda suka shiga dole ka jira su kyau, kwarjini, uwa Uba ilimi da duk inda suka shiga a duniya sai an ji ba kamarsu. Zaitunah tana auren dan sarkin Agadaz, wanda ya kasance attajiri kuma basarake mai jiran gado Mahaifiyar Hamidah da Humairah,

            Mijin Turai wacce tsakanin kyau da fatarta da zubin halittarta yasa ake kiranta turai, domin tafi kama da turawan hatta gashin kanta madadin baki ja ne sosai. Tana auren wani babbar Soja a nan Niamey, Danta ne Fahad,  sai Atikah tana auren wani babban attajiri a zinder, ita ce mahaifiyar Mufidah, Annur da wasu Yaran. 



Alhaji Muhammad Mustapha Muhammad ladan, wanda ya kasance babba a cikin Yaran Hajiya Asma'u da Alhaji Mustapha Ladan, Allah bai bashi wadata kamar sauran yan uwansa ba, asalima sai da ya kai kusan shekaru ashirin da takwas kafin ya auri Maamah wacce suka jima sosai kusan shekaru goma sha biyar, kafin Allah ya basu Naanah Asma'u, bata cika shekara daya ba aka haifi Khamilah, tsakanin Khamilah da Mairoh, wata sha biyu. Tsakanin Mairoh da  Faɗime shekaru hudu me kyau, 




 Alhaji Issufa wanda shine Mahaifin Mustapha Babban jami'in gudanarwa da kudin shigar kasar ne, wanda yayi zurfin karatun boko tare da Matarshi Hajiya Hadiza wacce ita kuma Babbar malamar kwalejin Kimiyya da fasaha na Niamey ce, suna da Yara hudu abinka da yan boko,  Yaransa sun haɗa da Mustapha Yusuf Ladan yana buga wasan ƙwallon golf ne, babban dan wasa da duniya take ji da shi.  Sai Asma'u wacce suke kiranta Husnah likita ce tana aiki a babban Asibitin Niamey, tana da aure da Yara biyu. Amar da Amra,  sai Salahudeen yana London yana karatun lauya, sai Autarsu Nadrah ita ce kusan saar Khamilah. 



Alhaji Haris Mustapha Ladan, Mahaifi ga Adam Ladan, Yana tare da matarsa Hajiya Haulat, Alhaji Harisu dan kasuwa ne kuma ɗan kwangila da yake shigo da kaya wasu bisa ka'ida wasu ba bisa ka'ida ba. Matarsa Balkisu mahaifiyar Adam ita kanta yar kasar Aljeria ce, aiki ya kawo Mahaifinta Agadaz daga nan suka zauna. Ta rasu wurin haihuwar Adam. 


   .Maraya ne da bai san dadin Uwa da Uba ba, domin Ubansa abinda ya saka a gaba duniya da abin cikinsa.. Alhaji Haris yana da Yara biyar. Adam wanda ya mai da shi karen farautarsa. Sai Fuad wanda shima dai Allah ya taimaka yana aiki a kamfanin kwangilar Uban, sai Asma'u, sai Amin. 


  Dukkaninsu babu wanda Allah bai yiwa rufin asiri yadda ya dace ba, sannan suna da wata irin kyashi. Domin da su taimakawa Abba babba sun gwammaci su bashi bashi. 


***

Abin ya fara ne lokacin da Abba Babba ya ce shi ba zai yi karatun boko ba. Amma ta bangaren Addini har mamaki mahaifinsu yake. Ya zaɓi bangaren Mahaifinsu kasuwanci da kiwon Raƙuma. Idan ka ga Abba Babba a lokacin da yake matashinsa sai ka san Allah yayi halitta. Domin daga shi sai Turai,kyau asali. Duk da kasancewar yaki karatu amma fa yana da zafin nima domin sai Allah ya saka masa albarka duk abinda ya taɓa zai yi albarka. 

       Dayawan manyan mutane sun sha zuwa nimawa Yaransu aurenshi, amma yaki shi kanshi Mahaifinsu Alhaji Ladan yans matukar alfahari da shi domin yana da kashin arziki. Hajiya ta saka buri domin a lokacin hango kanta take a matsayin wata mace mai daraja saboda yadda Yaranta kowa ke aure cikin gidan attajirai da mulki. 


     Haka kannensa duk suka yi aure, wani ikon Allah har Issufa ya haifi Mustapha,  amma shi a lokacin bai yi maganar aure ba, lokacin da Mustapha yake da shekara daya a duniya, Alhaji ladan ya zo mata da maganar auren Abba Babba, kuma wani abinda ya mata ciwo wai wata yar malamai ba wasu attajirai ba. Kai ita bai dame ta ba kamar da aka ce mata zuri'ar gidansu Zarma ne kuma mahaifiyar Rakiya bahaushiya ce daga Kano. Nan Hajiya tayi tsalle tace bata yarda ba, da yake Mijinta namijin gaske a lokacin. A tare aka yi aurensa da Harisu, Mahaifin Adam da mahaifiyarshi.   Wani abin da ya faru shine daga Maamah har Bilkisu sai Allah ya jinkirta musu haihuwa,  kuma da yake Maamah ta fito babban gida da aka san addini sai haka bai dame ta, ita Bilkisu ne dai aka yi ta niman maganin lokacin, shekara biyar da aurensu Allah ya bawa Bilkisu cikin Adam. 


           Wanda ta sha Azaba daga laulayi, har zuwa haihuwar. Kamar yadda take rokon Allah ya bata haihuwa ko tana raye ko tana mace, sai gashi dakyar aka zaro kan Yaron, domin ta rasu a wurin haihuwarsa. Adam ya tashi a hannun kakarshi domin yana da shekaru biyu Alhaji Haris ya kara aure, ya auri Haulatu domin ta kula da Adam amma haka bai samu ba. 


..... 


Duk wani tashin hankali, b'acin rai ba wanda Maamah bata gani ba wanda a lokacin sai da aka bata Mahmoud saboda mahaifiyarshi ba lafiya, amma haka Hajiya tayi ta fitina da bala'i aka mai da Yaron don ya girme Adam da shekara biyu, tsakaninsa da Mustapha akwai tazara, sai dai dukkansu kusan kansu daya ne. 

    Basu da inda suke cin abinci da wasa sai gidan Maamah, asalima a bakin Mahmoud suka ji Maamah. Akan zaman Mahmoud kuwa sai da Mahaifin Hajiya ya shiga maganar kafin ta hakura. 


     Abin ba dad'i, gori cin fuska da wulakanci babu wanda Maamah bata gani ba. Karshe har cewa suka yi tana da kashin tsiya daga zuwanta Abba babba ya talauce, mahaifinsa bai taɓa kallon Maamah Rukayyah haka ba. Rayuwar ta cigaba da tafiya har tsawon shekaru goma, a lokacin ita kanta Maamah rayuwar gidan akan dole take yi ga kuma Mahmoud, ga ƙarin nauyin Adam wanda yasa kome ya jagule mata. Tun Adam yana Yaro ita ta fara hango lalacewar Yaron na farko shine duk inda za'a ajiye abu zai ɗauka, sai ta fahimci har da yunwa.  Sai tayi kokarin nuna mishi kullum yazo yana amsar abinci sau uku a rana. Wanda baya samu shi kenan sai ya samu damar idan ta bar gidan ubansa zai zo nan Amarewat ya ci abinci, sannan ya wuce gidan kakansa na wurin Uwa ya kuma ci. 


    Anan kuma ya kuma haduwa da shaidanin kawu me suna Faisal ya shiga koya mishi yadda zai nime namiji dan uwansa, a hankali Adam ya tashi da wannan halin Hajiya bata sani ba sai wata ranar Alhamis, da yake yana zuwa bangaren Maamah yayi barci ashe Mahmoud yana barci ya shiga jan wandonsa abinda ya janyo Mahmoud ya farka ya rufe shi da duka. Aka raba su me ya faru Mahmoud ya ce yana taɓa mishi wanda a lokacin Abba babba da Maamah suka zaunar da shi, dakyar ya bude baki ya gaya musu dalilin haka fada suka mlshi sosai tare da nuna mishi illar abin Maamah tace ya mata alƙawarin ba zai kara ba Allah yana ganinsa idan ya kara. Haka ya mata alƙawarin ba zai kuma ba. 


       Daga karshe gaban Hajiya ya dawo bakiɗaya da zama, a wannan lokacin Hajiya tayi ta cusa masa haushin Mahmoud da Maamah.  Rashin uwa da kyakkyawar riko ya lalata Adam wanda har zuwa Makarantar sakandare, domin kuwa ya hadu da Yara marasa ji kafin ya tafi Bodin school, dama Mustapha iyayensa suna da rufin asiri kuma suna Niamey da zama hutu yake kawo su. A makarantar ma kama shi aka yi da wani Yaro suna lalata aka kore shi, a lokacin Abba babba ya dauke shi, sai abin ya mishi yawa haka aka tura shi katsina a can ya cigaba makaranta wata islamiyya Bodin school. Ya dawo ya samu Maamah ta haifi Yarinya mace, sai dai yadda yaji aka nuna tsanar yarinyar shima ya kara bashi damar jin haushinta. Kuma abin haushi Mahmoud hana shi kula yarinyar yake domin baya taɓa barin Yarinyar ta zo wurinsa. 


Akwai zuwansa hutu suka tafi rijiya diban ruwa, ai kuwa Mahaukacin kare ya zo yayi kan Naanah Asma'u da gudu, Adam kaɗai ya tsaya domin daga Mahmoud har Mustapha guduwa suka yi suka bar Naanah Asma'u da bata wuce shekaru huɗu ba, karen nayi kanta, shi ma ya dauki bokitin ƙarfen da ya zo da shi yayi kan karen ai kuwa karen ya juyo kanshi. Har sai da ya yaga mishi rigarshi ya kwarzane fatar cinyarsa. Haka yayi ta buga mishi bokitin wanda ya janyo dole ya kyale su ya gudu, sai da ya gudu Mahmoud ya zo ya dauke ta yana faɗin. "Bude idanunki ya gudu!" Tun daga wannan ranar ya tsani Mahmoud ko don kusancin nan ya hana su, 

   Haka idan zasu tafi islamiyya suke goyanta,  su hana shi wasa da ita, a gidan ma Hajiya bata son yana jan Naanah Asma'u kamar sauran Yaran. Domin kiri-kiri Hajiya take gayawa Naanah Asma'u ita ba jinin gidan bane sai dai ko sauyata a ka yi daga asibiti. Tsangwama da tsana da Naanah Asma'u ta sha a hannunsu. Shima kuma ganin yadda aka sakota a gaba yasa ya daina kula ta. 

   Har ya koma makaranta. Duk zuwansa hutu sai ya tafi da wani alamar shaida a jikinsa akan Naanah Asma'u, akwai wani zuwansa lokacin Hamida da Mufidah sun tsokano wani kurma, inda suka tura Naanah Asma'u, ai kuwa Kurman ya biyo su garin ta boya ta shiga ɓangaren hajiya, ai kuwa ta korota, shi kuma ya fito daga can dakinsu Kurman yana jifa dai a gaban goshinsa, kuma Kurman ya shigo zai rufe ta da duka, haka ya kama.hannunta suka shiga lungu da ya kaita gidansu. Tana ganin y sake ta ta shige dakin Maamah da gudu ta wuce kasar gado.  Ai kuwa bayan tafiyar Kurman Hajiya ta zo ta kama ta. Tayi mata mugun duka, wanda a lokacin ta dake ta da kafa a kirji. Shine dalilin fara numfashinta wnada aka zata asthma ne. Hajiya bata hada Adam da kowa domin soyayyar da take mishi ya taka rawar lalacewarshi. Kuma Hajiya ta gaya mishi Naanah Asma'u a rayuwarsa kamar masifa ce, akwai wani sharri da yake bin ta shiyasa duk haduwarsu sai tayi mishi sanadin da yaji ciwo. Da wannan shima ya saka a ransa Naanah Asma'u bad luck ce a rayuwarsa.

    Haka yanayin ya kasance har zuwa shekaru bakwai bayan ya gama secondery school yaki dawowa Agadaz saboda yasan yana dawowa ba wani tarban arziki zai samu ba, a Katsina ya samu wata makaranta ta hanyar abokinsa Ansar,  ya samu makarantar a can kasar Ireland a can ya karanci fannin kimiyyar halittu wato anatomy,  hutunsa na farko lokacin da ya zo ya ga Naanah Asma'u, kawai abu daya ya sani su zuri'ar gidansu basu boya, kasancewarta baka tow akwai wanan cat eyes a tare da ita. Yana tsaye a kofar gida yana kallon yadda kome ya sauya ya ganta yara sun rufeta da duka, kuma yaran da basu kaita ba. Dauke kai yayi ya tsani ya ga mutum yana nuna lalaci.

   Yasan da ace Mahmoud ko Mustapha suna nan da basu mata haka ba,tunda ya ji labarin

Mahmoud yana Pakistan yana karatu domin, Mustapha Kuma Egpty. Dauke kai yayi yana ganin suka mata duka sai lokacin ya ga sun zo sun wuce ta gabansu,  daga can inda Naanah Asma'u take kwance kanenta ne. Suka zo daya cikinsu ta dura musu zagi tare da diban dutse tana wurga musu  a ransa ya jinjina musu. 


          Tun daga ranar ya fahimci fa duk cikin Yaran da suka daki bakar yarinyar dukkansu jikokin Hajiya ne, tabe baki yayi. 


   Haka rayuwarsu ya cigaba da tafiya ya gama hutun ya koma bai kara dawowa ba, sai bayan shekaru goma. Shima da ya dawo ya ce ya gama aiki.


_____

Bayan shekaru goma.


Duk Yaran suna karatu, wanda Maamah take fadi tashi da Mahaifinsu. Duk da Hajiya ta washi Yaranta kada Naanah Asma'u ta ji labarin. Yaran sun taso da tausayin iyayensu. 


       Bikin Husnah da aka yi, babu wanda ya gayawa Maamah za ayi shima da yake shi ma Abba Babba zai bada auren Husnah haka yasa aka gaya mishi, amma yadda take talaka nan ko ta kanshi basu bi. Gashi nan shine mai kula da duk wani harkansu na kiwo da kasuwancinsu shine a kai. Haka da za'a kai Amaryan yasa Maamah ta shirya zata kiri-kiri Turai da Atika suka ce ba zata ba ta zauna baa bukatarta. Haka yasa bakiɗaya Maamah ta saka a ranta matukar ba Hajiya ce zata bukaci ta shiga harkansu ba ruwanta. Dama Mamar Adam ce kawai take da kirki.  


   A yanzu Naanah Asma'u da take da shekaru goma sha takwas tunda ta gama secondery school bata karatu, sai abu take sayarwa a waje. Wani abinda yake bawa kowa mamaki shine bata da magana duk abinda kake ji baka isa ta kalle ka ba. Asalima tsoron maganar take. Haka yasa bata da ko abokin fada, dama masu iya janta da rigimar kenan Hamidah da Humairah ko Mufidah, ko Asma'u. Sai Allah yasa Mairoh ƙarfi ne da ita da masifa gashi bata daukar kaye kome zaka mata bata yarda da faduwa ba. 


      A lokacin sanyi tana kofar gida tana sayar da abin karyawa. Motar Mustapha tayi parking ya jima bai sakata a idanun ba akalla shekaru goma kenan d wani abu. Lokacin da ya fito ya ga tana bawa kowa abin karyawa suna bata kuɗin, kamar an ce ta d'ago kai suka yi ido hudu. Kasa ɓoye dariyar murna da farin ciki ya bayyana a fuskarta. Duk da shima ita take kallo amma mamaki ya kasa ɓoyewa a fuskarsa taya Naanah Asma'u ta kare da sayar da abinci.  Haka ya shiga bangaren Maamah da take ta zuba abincin ana fitar da shi. Faɗime tana cin abinci,?Mairoh ta gama wanke kayan abincin tana karkade hannunta. Suka gan shi murnar da suka yi ya kasa ɓoyuwa a ransu. Taburma suka shimfida mishi suka gaishe shi tare da barin gidan, ita kuma ta shigo tana satar kallonshi. Wani abu ya ji ya daki zuciyarshi, kamar a sokawa mutum allura. Sake d'ago kai yayi ya ga ta dauke kai kamar bata ganshi ba. "Maamah na same ku lafiya?" Ya ce a hankali, fitowa tayi daga kitchen din suka sake gaisawa. Sakawa Naanah Asma'u tayi ta kawo mishi abinci, yadda ta zubo haka yake kallonta ido cikin ido. "Hmm ba magana!" "Uhm" ta fada tana wani irin murmushi.  Yana cin abincin yana jan Maamah da hira, tare da tambayarta dalilin barin Naanah Asma'u a gida, murmushi tayi kawai.