Chapter 11
by @maidambu41
Maamah irin mutanen nan ne masu tsayawa a iya matsayinsu, Yayunta da Hajjama sun sun so tsayawa Naanah Asma'u tayi karatu. Sai dai kalaman Abba babba yasa taki domin a duk lokacin da ya gaza yana fada yana jin kunyar ya kalli Yaransa har ya amsa sunan Mahaifinsu domin bai da wannan damar tunda ya gaza daukar nauyin karatunsu. Wannan mutunci da ƙimar yasa Maamah taki yarda wani ya taimakawa Naanah Asma'u. Ba wai tana jin daɗin ganin Yarinyar a zaune ba sai dai tana jin ciwon abinda zai saka a taɓa kimar Mahaifinsu.
Gashi wani abinda yake kara d'aga mata hankali Naanah Asma'u ta gama makaranta tun tana da shekaru goma sha shida, sannan tana cikin Yara masu tsananin hazaka wanda har ake tunanin zasu kasance masu karatu a bangaren kiwon lafiya. Ita kanta ta fahimci burin Yarinyar ta karanci abinda ya shafi haka. A lokacin da Adam ya dawo yayi ƙoƙarin tsaya mata amma ta fuskanci idan yana yana son jefa rayuwar yarinyar cikin matsala da matsin lamba, ya ce zai yi wani motsi bs ita ba mahaifiyarsu ma bata tsira ba daga tashin hankalin Hajiya. Ga mahaifinsa da kiri-kiri ya gayawA Abba Babba da cewa. "Na ji Naanah ta gama makaranta kuma tana zaune ko?" Gyada kai Abba Babba yayi ya ce mishi. "Eh ina jiran wasu abubuwan ne su yi sauki na biya mata koda kwaleji ne!" Ya fada yana sunkuyar da kai. "Idan haka bai samu ba, akwai wani Alhaji badamasi abokina ne Matarshi ta rasu ta bar mishi yara bakwai zata iya auren!"
"Idan ba zaka iya taimakawa ba, na meye sai kayi tallar yarshi? Fisabiilillahi! Ba kana da yar da tafi ta a shekaru sai ita wannan da bata wuce kayan tsaraba ba." Ya fada yana barin parlourn, shiru suka yi Hajiya ta ce mishi. "Uban kowa kenan ai Yaran Rakiya basu bukatar dogon ilimi ko sun samu ba zasu yi amfani da shi don taimakawa Ubansu ba, shi yasa nayiwa Bebi magana yarta hasiyah da mijinta ya rabu da ita a daura auren da makaho, bai da kudin karatun Yara, amma ai nasan Harisu zaka taimaka mishi domin da ciwo ace bai da ɗa namiji!"
Haka suka hana shi kudin da zai biyawa Naanah Asma'u karatu amma aka bashi kudin aure har da Jari, kuma ta shata mishi layi idan ya taimakawa Rakiya da Yaranta Allah ya isa.
Wannan shine dalilin da wasu abubuwan suke zaune, Uban kowa ya kai mishi kudi amma sanin cewa abinda Uban kowa yake yi ba ta arziki ba ce ya ce ya bar shi yaki amsa.
Haka suke cigaba da zama aure kuwa yaki yinsa sai kaucewa yake.
Numfashi Maamah ta ja tana fadin." Kasan karatu sai mutum yana da hali, ita kuma abu ya hadu mata da ciwo shi yasa muka hakura tayi fama da jinyar da take da shi. "
Girgiza kai Ya Almu yayi ya kalle ta, fuskar nan dauke yake da wani lullubebben sirri, hakuri da juriya ne aka kwance a fuskarta. Bayan sun gama hira ya tashi zuwa bangaren Hajiya da Adam suka haɗu ya dauke kai kamar basu san juna ba, kowa shegen sama ne. Haka yasa shi wucewa bangaren Hajiya. Shi kuma Uban kowa ya wuce bangaren Maamah. Yana zuwa ya ja kujera ya zauna. "Ina son abinci!" Maamah ta san iya adadin da yake so ta fada mata, jikinta yana wani irin rawa ta shiga zuba mishi. Har ta kawo bai kula ta ba. Duk abinda suke yi akan idanun Maamah suke yi. "Maamah yau an bada na sadaka?" "A'a!" A hankali ya fara ci yana kallonta kasa kasa, yadda take rawar jiki da shiga hankalinta. Cokali biyu ya ci ya mike tare da ajiye mata cfa dubu uku, ya ce mata." A rabawa Yara!" Har ya nufi waje ya tsaya cak ya juya yana kirga kudin da suka rage mishi. "Don Allah idan da hali a dakatar da sayar da abincin nan" ya ajiye mata wasu kudin masu yawa. Sannan ya fita, yana barin gidan Naanah Asma'u ta sauke ajiyar zuciya. "Kina tsoronsa ko?" Bata ce kome ba ta cigaba da aikinta.
A bangaren Hajiya masifa ta fara yiwa Almu shi kuma mutum ne da baya ɗaukar jidali ya ce mata. "Zan tafi ni bana son tashin hankali!" "Tow sai ka sauka bangaren Rakiya?" "Eh na sauka wani abu ne?" Yadda yake mai da mata magana da zafi da zafi yasa ta sauko ta fara mita kuma ta bashi hakuri duk abinda ta bashi ya ce ba zai ji ci ba. Mikewa yayi ya bar parlourn ai kuwa ta fita zuwa wurin Maamah tayi ta zaginta da cin mutuncinta. Kafin ta dawo wurinta. Shi kuwa yana fita bangarensu ya nufa, dakin Adam ya fara shiga yayi wanka ya shirya Tsaf, yana cikin shirin sai ga Adam ya shigo. Wani irin kallon suka yiwa juna, Adam ya wuce yayi abinda xai yi ya dauki key din ɗaya ɓangaren ya ajiye mishi ya fita.
Shima haka ya gama ya dauki key din ya nufi bangaren ya ga yayi kura, fita yayi ya nufi bangaren Maamah ya ce mata. "Maamah ko zaki bani aronta ta taya ni kintsa bangarena?" Gyada kai tayi tare da cewa. "Ki dauki mask." Haka ta dauki tsintsiya da abin goge ta nufi wurin shima ya zauna a bangaren Maamah suna ta hira har zuwa sha daya sannan ya koma ya samu tana ta aikin ta gama sha tana goge parlourn. Tsayawa yayi yana kallon yadda take aiki cikin nutsuwa amma kuma ba sauri. Zuwa yayi ya amshi abin goge ya fara goge kasar, da gangan ya saka ruwa yadda zai taka ya zame, aikuwa yana yin haka ya kuwa zame, yadda ta d'ago kai a razane, sai ta ga yana murmushi. Dauke kai tayi tana murmushi. Wannan shine mafarin duk wata Alakar da aka kulla da zuciya.
Duk yadda zaka iya bada labarin shakuwa da kulawar da Ya Almu yake bawa Naanah Asma'u tow kayi karya kace yana mata kaza domin gobe zai lullube wnada yayi da wanda ya fishi. Da zai koma Hajiya taji labarin da Naanah Asma'u zai koma tayi fada tayi masifar ko inda take bai kalla ba ya wuce da ita Niamey.
.
Bai yarda ya bar nijar ba sai ta ya gama mata kome har da jarabawar da zata yi na shiga Universite Abdou Moumoiuni, yana kasan Canada a lokacin a can yake buga wasa Hajiya ta saka shi a gaba tunda ya biyawa Naanah Asma'u kudin makaranta sai ya biya mata umara, haka ya biya mata. Taje a lokacin Maulidi. Watan Naanah Asma'u biyu da zana jarabawar shiga jami'ar, don har ta dawo gida. A wata na kudi sakamakon ya fito sai a lokacin Uban kowa ya ji labarin abinda yake faruwa. Yaji zafi sosai domin shi yaso daukar wannan nauyin aka hana shi. Mahaifinsa har da masa barazana.
Ranar wata talata da dare Abba Babba yana waje yana shan iska da ɗan butarsu yana shan shayi. Ya zo ya zauna bayan ya gaishe shi. Mika mishi leda da kudi yayi ya ce mishi. "Kayi hakuri na so nayi yadda zata koma makaranta, sai dai Allah bai nufa ba, gashi a saya mata kayan abinci idan tana da buƙatar kuɗi kada ta tambayi kowa ta tambaye ni!" Abba babba yasan ko Naanah Asma'u zata mutu da yunwa ba zata taɓa tambayar shi ba. "Ka bar shi Adam kada Hajiya ta ji labarin nan!" "Wannan daga cikin gumina na halak ne ba daga dukiyar da ta zame min haram ba ne ka amsa Hajiya kuwa ai sai k gaya mata zata sani!"
Godiya Abba babba ya mishi tare da amsar kuɗin, koda ya shiga cikin gidan ta gayawa Maamah bata ce uffan ba. Da ya gayawa Naanah Asma'u abinda Adam ya ce girgiza kai tayi bakinta yana rawa. Kai hatta jikinta rawa yaƙe. "Na gode a bar shi! " Ta faɗa.
Washe gari suka shiga kasuwa sayayya. Wani irin rikicin daba ne ya kaure. Gashi ita da Khamilah da Mairoh suka shiga kasuwa, yadda ƙarar sare juna da suka yake tashi yasa ta rud'e, abinda yasa aka yi ta gudu. A lokacin da suka isa gidan sun sami Uban kowa a kofar gidan. "Kai meye haka?" " Ana fada a kasuwa ne muka bar Didih a can?" Kura musu idanun yayi kafin ya cigaba da wanke hannunta. Kallon hanyar da suka fito yayi ya ga yadda mutane suke ta guje guje, mikewa yayi ta tsare wani mutum da mashinsaa, ya ce mishi." Sauka" ba musu ya sauka ya bashi mashin din ya hau tare da bugawa ya nufi cikin kasuwar. Wurin yayi tsif babu al'amar mutane kowa ya gudu domin rayuwarsa. Zaga kasuwar yake. Yana faɗin. "Ke Jikar Mustapha Ladan!" Sau uku yana faɗar haka can sai gata ta fito daga wani shago. Ganinshi ya kara mata tsoron abinda yaje faruwa. Zuwa yayi gabanta ya tsaya da mashin din.. ai kuwa yaran suka fito da gudu da makamai, kashe mashin din yayi ya tsaya a gabanta "dauko min sandar can?" Ba musu ta dauki tare da mika mishi. A hankali ya nufe su. Rike rigarshi tayi.. "sake min!" Da sauri ta sake shi.. ya juya sandar ya nufe ba tausayi yayi ta musu dukar da zasu jima suna jinya. Guduwa wasu suka yi yana juyawa yaga daya cikin Yaran ya nufe ta. "A'a fa!" Ya fada da ƙarfi. Taka dutse yayi ya murza kafin yaron yakai ga ya yanketa shi kuma Allah ya bashi saa ya jife shi da dutsen dole ya faɗi can. Ya isa gabanta yana mai kunna Mashin din ya hau, kallonta yayi yaga tana rike hijab ɗinta. Zai bude baki yayi Magana kawai yaji yaron nan ya yanke shi da wuka. Ai kuwa sauka yayi ya damke yaron ya shiga dukansa sai da ya karya mishi hannu.. ganin yadda jinin yake zuba ta rasa me zata yi kawai ta ciro dankwalin kanta, ta daura mishi.
Bayan ta daura mishi ta hau bayan mashin din suka dawo gidan, ganinta a bayanshi yasa Abba babba ya sauke ajiyar zuciya. Sauka tayi ta nufi cikin gidan, duk yadda aka tambaye ta mai ya faru bata iya fada ba, kawai ta ce ba kome ne. Kwanaki tsakani suka wuce Niamey da Abba Babba, inda suka samu Husnah ita ta shiga gaba aka gama mata kome, inda zata ƙarancin medicine, zabi ne da Ya Almu ya bata domin a bakin Mairoh ya ji me take so.
A hankali kauna da shakuwa, ya shiga bin zukata mutane biyu nan. Duk wanda zai baka labarin abinda yake faruwa yayi karya. Watanta hudu suka yi hutun farko, a ranar da zata dawo a ranar Ya Almu ya zo. Tayi murna domin zuwan da yayi, bikin Humairah za'ayi kanwar Hamidah. Kuma har shi aka gayyata. Da yake a hostel take zama. Da ta dawo gidan ta haɗa kayanta. Ta ganshi a parlourn Mammy yana cin abincin. "Naanah Asma'u baki ga Yayanki bane?" Mammy ta tambaye ta, kunyarshi da nauyinsa yasa ta komawa can gefen kujerar parlourn ta zauna kanta a sunkuye ta ce mishi. "Ya hanya?" Iya wannan kalaman ta furta, "Alhamdulillahi" ya fada yana murmushi. A hankali ta mike zuwa cikin dakinsu. Inda ta samu nadrah da kawarta suna hidimarsu, tunda tayi sallama ta wuce inda kayanta yake tayi ta haɗawa. "Gashi inji Addah Husnah!" Amsa tayi ba laifi tunda ta zo tana samun kyautatawa daga yan gidan har da mahaifiyarsu da Baffanta. "Na gode!" Ta furta tana mai hada kayan a cikin akwatinta. "Nadrah itama yar Family dinku ce?" Murmushi tayi ta ce mata. "Me kika gani?" "Kawai yanayinta ne ya sha banban da naku!" "Tana da kyau amma baka ce ba?" "Eh!" Ya fada tana kallon Naanah Asma'u da take jin su amma aikin gabanta take yi. "Bata hira ne?" "Hmmm tana yi mana, kin ga yadda take love da Ya Almu, duk yadda kika so ki ji me suke cewa sai humm ko hmm! "
Dariya yarinyar tayi, ita kanta tashi tayi ta bar musu dakin.. washe gari kamar yadda ta shirya sai ta samu shima haka ya shirya suka bar garin. Tun a hanya Khamilah take gaya mata Ya Moud ya dawo daga Pakistan. Sai ta rasa inda zata saka kanta don farin ciki.. murmushi kawai take yi tana wasa da yatsunta.
"Hmm!" Satar kallonshi tayi, a kunyace. "Uhm!" Ta furta tana kallon gefen hanya, ajiye mata wani kwali yayi akan cinyanta. Juyawa tayi tare da kallon shi, murmushi yayi yana kallon hanya. A hankali ta shiga buɗe abinda aka naɗe kwalin da shi kafin ta isa asalin kwalin. Sarkace ta white gold, da abin hannu da kunne, sai sarkan kafa.
"Na gode!" Ya furta tana kallon abin, sakawa tayi a jaka tana murmushi. Sau biyu suka tsaya a hanya daga nan basu tsaya a ko ina ba sai a Agadaz. Sun iso da dare, a gajiya koda ta shiga cikin gidan. Sallah tayi da wanka tuni tayi barci.. washe gari, gidan kakanninta ta wuce ba zata iya jiran Ya Moud ba, tana ganinsa ta fada kanshi ya rungume ta yana dariya. Itama haka zama suka yi suka ta hira yana janta da hira. Dama ko da baya nan shine abokin shawaranta. Kai karewa a gidan ta kwana. Don dama ta saba tana zuwa ta kwana. Sai da ta wuni Ya Moud ya ɗauke ta a sabon motarshi da aka. fara kawowa kafin ya zo. A lokacin da suka isa gidan sun samu an cika domin. Akwai bikin da za a yi na kawayen amarya wani abinda ya bata mamaki shine yadda ta ga wata mata a cikin gidan Bayan Maamah a dakinsu take tambayar Mairoh tabe baki tayi ta ce mata.. "wancan tsohuwar tasa shi yayi aure!" Daga haka bata kara cewa uffan ba.
Ita kanta Amaryan tana tare da su Hajiya, kusan hidimar bikin ita take taya su. Da yamma duk wani abinda sauran Yan mata suka yi sai ganin Naanah Asma'u aka yi da shi, ba abinda ya fi basu haushi kamar gold din wuyarta. Ai kuwa zaginta tun ana yi a bayan idanunta har suka fara kasancewar hidimar a kofar gidan za ayi. Maza da mata Maamah tayiwa su mairoh da Khamilah Faɗime. Tun safe ya saka ta gaba suka je aka gyara mata gashin kanta har da su Mairoh. Anyi musu jan lalle da baki ita ce dai aka yiwa ja.
Ai sai kallon ya koma kanta, tunda suka fito kofar gidan, Hajiya Turai ta hanata zama je ki dauko kaza yi kaza, kai abubuwa kala kala, lokacin da ta dawo ta zauna bata san me ya faru ba. Ashe Hanifah ganin inda ta zauna nan Almu zai zauna asalima kamar ya ajiye mata wurin zaman ne, shi kuma yana tsaye tare da Fuad suna magana.. Hamidah ta dauki ruwan zafin shayin da suke zubawa kowa. Ta kwara mata, a hankali yayi taku biyu ya kare ruwan zafin ya zuba a bayansa. Murmushi yayi mata. Wanda yayi dai-dai da ihun mutane.. da yake ana dab da kiran sallah ne. Ai kuwa take aka tashi taron tunda har dare ne za a cigaba. Duk kannen Ubansu suka taru a gaban Almu ai ko babu kome yana musu hidima. Marin da Hajiya Turai ta kifawa Hamidah yasa wurin ya kara ɗauka. Ai kuwa Hajiya Zaitunah ta d'ago Naanah Asma'u da ba ruwan ta suka nufi bangaren Hajiya da ita tare da marinta ai ita ta ja me bakar kafa mummuna tazo wai ta burge kowa ne. Cin zarafi kala kala.da kyar ta samu ta kwace kanta ta fita da gudu, sanin ciwo lungu dare yayi bata shiga ta wurin ba, don Hajiya ma tace a rufe lungu, kiran da Hajiya Atikah ta mata tare da cewa a rikota. Ta ji an fisgeta zuwa lungun. An danne mata bakinta tare da cewa. "Shiii!" Ai bata san lokacin da ta sake fitsari a jikinta ba. Sarkan kafarta ne ya fita daga kafarta. Tana kokarin jan numfashinta, hannu ya saka a cikin aljuhun rigarshi ya ciro inhale ya danna mata a baki. A hankali ta fara sauke numfashi. Sake ta tare da juya baya a hankali ta bar wurin jikinta a mace. Juyawa yayi idanunsa ya sauka akan abu me kyau yana sheki.. sunkuywa yayi ya dauka.. abun kafarta ne wato. A cikin aljuhun wandonsa ya tura.