MATAR GIDA PAGE 41
MATAR GIDA 041
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCAITION
P41
Ɗalha ya dauki sama da mintina biyar ya na abu ɗaya tun Amirah na basarwa har ya kai ga ta basa haɗin kai sosai ta yi kewarsa,haushi da tsanarsa da take ji cikin zuciyarta kafin aurensa da Unaisa,kwanakin bayan nan ta nema ta rasa kulawa da yake nuna mata ita da yaranta ya sa ta nime tsanar ta rasa,yanzu haka wani irin shauƙin sonsa take ji cikin zuciyarta da ita kanta bata san sanda hakan ya faru ba,a hankali ta kai hannu ta riƙe wuyarsa ta fara mayar masa da martani,Ɗalha ya kai hannunsa cikin rigarta cikin wani irin salo Amirah ta gama sakar masa jiki sai yadda ya yi da ita,sun kwashe lokaci me tsawo a haka kafin daga bisani suka jiyu muryar Fauziyya tana faɗin ''Mumy..Mumy zan sha ruwa'' da kyara Ɗalha ya iya raba jikinsa da Amirah yadda ya haɗa goshinsu waje ɗaya yana sauki numfashi da sauri da sauri a hankali ya kai hannunsa kugunta ya haɗa da nasa ya daura kansa a kafaɗatar,Amirah na son fita ta duba Fauziyya ganin bai da niyyar barinta ta fita ya sa ta ce ''zan je na bata ruwa'' ta yi magana a hankali sosai yadda shi kaɗai ya ji abinda ta faɗa runtsa idanu Ɗalha ya yi har sannan bai gama.dawuwa dai dai ba ya kai baki saitin kunne ta ya ce ''ok..y'' ya yi magana a rarrabe har sannan yana riƙe da ita gam ganin baida niyyar sakinta ya sa Amirah ta shiga koƙarin raba jikinta da nasa ƙara riƙe ta ya yi gam kafin ya yi magana da muryarsa da bai fita da kyau ya ce ''why?" shiru Amirah ta yi saboda bata fahimci tambayar ba,jin ta yi shiru bata ce komai ba ya sa ya ce ''me yasa ba ki gyara ɓangaren ki da kan ki ba? tun da lyan Salame da yarinyarta are busy'' shiru ya yi tare da ɗago kansa daga kafaɗarta ya zuba mata idanunsa da suka koma ƙananu sun yi ja sosai tsabar yadda yake jin feelings, ta ƙasa haɗa ido da shi kawai ta ce ''babu'' hannayenta duka biyu na wuyansa,kanta ƙasa ta yi magana,kwantar da murya ya yi kafin ya ce ''ki gyara gobe'' shiru Amirah ta yi tana jin yadda numfashi sa ke sauka a fuskarta da ɗumi, ƙasa magana ta yi ganin yana shirin sake haɗa bakinsa da nata cike da hikima ta kawar da fuskarta gefe ta ce ''uhmm'' kawai ta iya furta,Fauziyya da ta gaji da laluban Mumynta ta sake kuka,sautin kukan Fauziyya ya sa Amirah ɗago idanunta ta zuba wa Ɗalha idanunta cikin nasa yana kallonta a hankali ya ce ''je ki dubata'' ya faɗa tare da sakinta Amirah bata tsaya ɓata lokaci ba ta fita daga bayin saboda sosai Fauziyya ke kuka,bayan fitar ta daga bayin kunna fitilar ɗakin ta yi nan take haske ya gauraye ɗakin sai a sannan Fauziyya ta buɗe ido duk kukan da take tun ɗazu idanunta a rufe suke,hannu ta miƙawa Amirah alamar ta dauke ta,daukar ta Amirah ta yi ta shiga aikin rarrashinta Amirah na shirin fita daga ɗakin zuwa parlour dan daukarwa Fauziyya ruwa Ɗalha ya fito daga bayi fuskarsa jiƙe da ruwa da alama wanke fuskar ya yi,Fauziyya ta mika masa hannu alamar tana son tafiya wajensa fuskarsa Ɗalha dauke da murmushi ya karɓi Fauziyya daga hannu Amirah zama ya yi bakin gado idonsa kan Fauziyya ya ce ''wa ya sa ta kuka? wa ya ɓata wa princess ɗita rai?" cikin tsatsamar hausarta ta ce ''Mumy'' Ɗalha ya buɗe baki alamar mamaki ya ce ''Mumy?" Fauziyya ta kwaɓi fuska ta ce ''eh'' kallonsu kawai Amirah ta yi ta fita daga ɗakin,bayan fitarta daga ɗakin kitchen ta nufa tare da kunna fitilar kitchen daga haka ta dauki gorar ruwa ɗaya daga katan ɗin ruwa dake ajiye gefen firiji,bayan fitar Amirah daga kitchen ganin Ammi ta yi ta fita daga ɗakinta sanye cikin wata rigar bacci ta daura zani kan rigar,idanun Ammi cike da bacci ta kalli Amirah tare da fadin ''me ya sami Fauziyya take kuka? me take bukata?" Ammi ta kare magana tana hamma, da sauri Amirah ta ce ''ruwa take son sha'' ''shi yasa take kuka haka? to yi maza ki bata'' Ammi ta faɗa tare da nufan hanyar kitchen
Ɗalha ne ya fito daga ɗaki riƙe da Fauziyya idonsa kan Amirah bai lura da Ammi dake tsaye can kofar kitchen ba ya ce ''ba ki samo ruwan ba ne?" shiru Ammi ta yi tana kallon Ɗalha da Amirah lokaci guda tana mamakin su harda parlourn babu haske sosai hakan bai hanata gane Ɗalha ba,karasa shiga parlour ya yi ya zauna kan kujera sai a sannan hankalinsa ya kai inda Ammi ke tsaye Ammi bata ce masu komai tana tsaye,jiki babu kwari Amirah ta ja ƙafa zuwa inda Ɗalha ke zaune ta miƙa masa ruwa ya sa hannu ya karɓa tare da buɗe ruwan yana bawa Fauziyya sai sunne kai ƙasa yake bai san Ammi na parlour ba da ya sani da bai fita daga ɗakin ba,ita dai Ammi bata ce masu komai ba ta shiga kitchen ta bar su zaune parlour kamar masu zaman makoki,sosai Fauziyya ta sha ruwa nan take ta koma bacci ganin haka yasa Ɗalha ya daura ta hannu Amirah daga haka ya fita daga ɓangaren,Amirah kamar jira take Ɗalha na barin parlour ta tashi ta shiga ɗaki harda juya key,Ammi ta gama abinda ya kai ta kitchen ta fito hannuta riƙe da kofin shayi taga parlour babu kowa taɓe baki ta yi kafin ta nufi ɗakin Amirah ta buga kofa a hankali tare da sallama Amirah da ta shimfiɗa Fauziyya kenan ta jiyu muryar Ammi tana sallama, amsar sallamar ta yi tare da buɗe kofa a takaice Ammi ta ce ''in kun gama da kofar ku rufe'' Ammi bata jire cewar Amirah ta bar wajen,Amirah kanta ƙasa ta je ta rufa kofar entrance daga haka ta wuce ɗakinta,a wannan dare bacci ɓarawu ne ya dauki Amirah ta yi ta juye a gado bata san da wani ido zata kalle Ammi gobe ba,a can wajen Ɗalha kowa bayan komawarsa bangaren sa ƙasa kwanciya ya yi a ɗakinsa karshe ɗakin Unaisa ta je ya kwanta tare da rungumeta ta baya,washegari tun tara na safe Ammi ta tura Iyan Salame da Salame ƙyauyensu ta ce su je su yi kwana biyu sai ta nime su da fari Iyan Salame ta shiga damuwa gani take kamar wani laifin ta yiwa Ammi sai da ta kwantar mata ta nuna mata babu komai su je kawai in tana buƙatarsu za ta kira su,unin wannan ranar Amirah bata samu hutu ba aiki ta uni yi da ta gama wannan zata yi wancan haka dai ta yi ta yi ga kunyar ganinsu da Ammi ta yi jiya duk ta bi ta tsargo ko sau ɗaya Ammi bata nuna ta san wani abu ya faru jiya ba ko a fuska Amirah kaɗai ke ta jin kunya,a can wajen Ɗalha da Unaisa kowa bayan wayewar gari kamar yadda Ɗalha ya saba karfe tara ya fita ya siya masu abinci kafin ya dawo ya yi wanka yana zaune cikin parlour yana cin abinci hannusa riƙe da waya yana duba wani E mail da aka tura masa daga ofis Unaisa ta fito daga ɗaki tana tafiya tana jan ƙafa kallo ɗaya Ɗalha ya mata mayar da ldonsa kan wayarsa sanye take cikin wani riga da wando na bacci yau kwanar riga uku a jikinta ko ba a faɗa ba kallo ɗaya zaka mata ka fahimci rabonta da wanka ta kwana biyu,yau ma kamar kullum hular kanta a karkace sumarta rabi a rufe rabi kuma yana waje,tun ranar da suka dawo daga asibiti Ɗalha ya fita harkar ta bayan ta yi masa rashin kunya ta ce baza ta yi girki ba sai bayan wata ɗaya ga kuma maganganun da ta faɗa kan Ammi Ɗalha ya ji sonta ya fara fice daga zuciyarsa bayan rashi wayo harda rashi sanin cewon kai duk suna damun Unaisa wannan dalilin yasa ya jingina lamarinta,ko labarin zuwan Amirah da yara bai mata ba,waje ta samu ta zauna tare da daukan take away da tana da tabbacin dan ita ya siyu ta ja gabanta ta buɗe,mayar da dubanta ta yi ga Ɗalha taga hankalinsa na kan waya murya can ciki ta ce ''good morning'' kullum haka take gaida shi in sun haɗu da safe in kuwa basu haɗu ba to shikenan ya wuce sai gobe,dauke numfashi Ɗalha ya yi dalilin warin bakin Unaisa da ya doke hancinsa a natse ya yunƙura tare da miƙewa tsaye,zama ya yi a kujera ɗan nisa da ita kafin a takaice ya ce ''morning'' taɓe baki Unaisa ta yi tana mamakin sabbin halaiyar da fito da su a kwanaki biyu nan, ta ga sai wani share ta yake in ta yi masa magana a takaice ya ke bata amsa,ko kadan hakan bai dameta ba dadi ma hakan ya yi mata tunda yanzu ya daina damunta maganar wanka da sallah,hankali kwance ta fara cin abinci,bugun kofar bangaren aka fara daga waje Ɗalha ya jiyu muryar Afef da Rayyan suna faɗin ''Daddy ka buɗe mana kofa'' fuskar Ɗalha dauke da murmushi ya miƙe tsaye tare da nufar wajen kofar ya buɗe masu,da gudu suka shiga sun faɗa jikinsa rungume su Ɗalha ya yi yana dariya galala Unaisa ta yi tana ƙarewa yaran kallo sosai yaran sun yi mata kyau,kayan jikin su tsaf babu datti ga wani sassanyar ƙhamshi dake fita daga jikinsu kallo ɗaya ta yi masu ta fahimci yaransa ne tsananin kama da suka yi da shi babu inda suka baro shi,amma sun yin haske saɓanin shi da yake baƙi,a natse ta cigaba da cin abincinta idonta kan yaran sai faman tsalle tsalle suke a jikinsa Ɗalha ya kalle ta da gefen ido kafin ya cewa su Afef ''je ku gaishi Anuty ku'' sai a sannan hankalin su ya kai kan Unaisa,duk sun kafeta da ido sosai ta yi masu kyau gata fara ta fi Mumynsu haske nisa ba kusa ba,Rayyan ya kalle sumarta da ya fito daga hula ya ce ''Daddy she has a long hair..l like it'' ya kare magana yana sakarwa Ɗalha murmushi shima murmushi ya yi kafin ya ce ''ka fiya surutu Rayyan just go ka gaishe ta'' Rayyan ya ce ''ok'' ya faɗa tare da nufar inda Unaisa ke zaune shi ko Afef har sannan yana tsaye yana kallonta Rayyan ya je har gabanta ya durkusa kafin ya ce ''good morning Anuty'' ya faɗa yana tura yatsun sa biyu a baki kayan jikinsa da kuma ƙhamsi da yake yasa Unaisa bata san sanda ta sakar masa murmushi ba ta ce ''morning how are you'' a takaice Rayyan ya ce ''fine'' ya faɗa tare da barin wajen ya koma jikin Ɗalha,sai a sannan Ɗalha ya kalle Afef ya ce ''me ka ke a nan?oya go and great your Anuty'' Afef na wasa da ƙasan rigarsa idonsa kan Unaisa tana sakar masa murmushi ta miƙa masa hannu alamar ya zo maƙe kafaɗa Afef ya yi kafin cikin sauri ya koma kusa da Ɗalha ya kai bakinsa saitin kunnen Ɗalha ya ce ''she white'' yana nufin baturiya dariya Ɗalha ya yi kafin ya ce ''no she not" dan jimm Ɗalha ya yi kafin a daƙele ya ce ''she is shuwa..shuwa arab'' shi dai Afef har sannan ya ƙasa daina kallon ta da kyar Ɗalha ya samu Afef ya gaida Unaisa yana gama gaisuwar ya nufi kofa wai zai je Mumy Ɗalha ya tashi ya buɗe masa kofa ya fita da gudu,bayan fitar Afef Ɗalha ya shirin kulle kofa Rayyan ya ce shima zai tafi wajen Mumynsu bayan fitar su ne Ɗalha ya koma ya zauna inda ya tashi ita dai Unaisa hankalin ta kan abinci kasan zuciyarta tana mamakin Ɗalha da bai faɗa mata zuwan yaran ba to wai wa ma wa ya kawo su,tana tsaka da tunanin ta jiyu muryar Ɗalha ya ce ''hutu suka zo,sun gama jarabawa,daman nan suke zuwa hutu duk sanda suka samu hutu'' shiru Unaisa ta yi tana nazarin maganar da ya yi mata can ta ce ''da wa suka zo'' idon Ɗalha kan waya ya ce ''da matata Amirah mahaifiyarsu'' taɓe baki Unaisa ta yi tana ƙara maimaita kalmar matata da ya faɗa a zuciyarta to ita ba matarsa bace,shiru ta yi bata sake cewa komai ba can ta ce ''to ya ya za a yi? sun zo amma ba ka faɗa min sun zo ba'' a takaice ya ce ''babu yadda za a yi, ban faɗa maki ba saboda ba ki tambaya ba'' har cikin zuciyarta bata ji dadin yadda ya amsa mata ba a hankali ya aji wayarsa kan kujera yana mayar da dubansa gareta ya ce ''me yasa ki ke tambayar ya za a yi,ki da ki ka ce baza ki yi girki ba'' Unaisa na shirin basa amsa ta ji kunne ta na mata wani irin kaikayi abincin da take ci ya ɗan yaji,tooth pick da aka sa cikin ledar take away Unaisa ta dauka ta fara sosa kunnenta da shi wani katon bakin datti ta ciro daga kunnen kamar wacce ta shekara bata share kunne ba,a kan idon Dalha ta ciro dattin daga kunnenta mamaki ne ya cika Ɗalha lokaci guda zuciyarsa ta fara tashi yaji amai na taso masa da wani irin sauri ya bar wajen yana toshe bakinsa taɓe baki Unaisa ta yi ta bishi da ido har ya shiga ɗaki, tooth pick da take riƙe da shi ta sa cikin ledar take away tana cigaba da cin abincinta hankalin ta kwance,image ɗin Rayyan da Afef na idonta har ta gama cin abinci tana tunanin yaran daga yadda a ka yi masu dressing ga kuma ƙhamshi da suke sai sannan ta tuna rabonta da wanka tun ranar Laraba kwana uku kenan,taɓe baki ta yi shiga magana ita kaɗai ta ce ''shi yasa yake damuna da maganar wanka da brush ashe aljanar tsafta ya auro har wani ƙhamshi yaran ki yi'' rai babu daɗi Unaisa ta gama cin abinci bayan ta gama ne ta tashi ta wuce ɗakinta sai yau ta yi wanka da brush ta sauya kayan jikinta
SHUUKRAN