MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 42

by @maimunabala209

MATAR GIDA 042



SHUUKRAN/022


YOTA ASSOCAITION




P42


Da gudu Rayyan da Afef suka shiga parlourn Ammi,Ammi dake zaune cikin parlour ta daura Fauziyya a kafarta tana bata tea a baki ta ɗago ta kalle yaran ganin yadda suke sauki numfashi yasa Ammi jefo masu  tambaya ''daga ina kuke?" ta yi tambaya idonta a kansu Rayyan ne ya fara magana yana sauki numfashi ya ce ''wancan gida muka tafi wajen Daddyn mu'' ya ƙara magana hannayensa duka biyu daure kan gwaiwa kamar me ruku'un sallah har sannan yana sauki numfashi da sauri da sauri,Afef ya ƙaraso inda Ammi ke zaune ya zauna kusa da ita sosai kamar zai shiga jikinta ya kwantar da murya tare da faɗin ''Ammi akwai farar mata a waccan gidan,Daddyn mu ya ce Anuty mu ce sumar ta dogo'' dai-dai lokacin Amirah ta fito daga kitchen sarai ta ji abinda Afef ya faɗa amma sai ta yi kamar bata ji ba,tun da Ɗalha ya auro Unaisa bata taɓa ganinta ba ko sau ɗaya kuma bata ma son ganinta,dauke kai ta yi daga kallon Afef da ke bawa Ammi labarin Unaisa ta mayar da dubanta ga Ammi ta ce ''na sauki miyar,na haɗa lemon yanzu'' Ammi ta kalleta daga yadda ta yi magana kaɗai yasa Ammi ɗaga ido ta kalleta ta karasa magana kamar za ta yi kuka kishi na cinta sosai amma sai ta ɓoye,wani irin tausayin Amirah ne ya ziyarci Ammi lokaci guda hakan yasa cikin kwantar da murya ta ce ''a'a ki barshi sai zuwa anjima'' jiki babu kwari Amirah ta karasa shiga parlour ta samu waje ta zauna tare da ɗaukar wayarta ta kunna data ta shiga kallon vidoe a face book Rayyan ya karasa shiga parlour zuwa yanzu numfashinsa ya sauka,Ummu Abiha da Sumayya dake wasa da toys ɗinsu can kuryar parlour Rayyan ya je ya tsaya yana kallonsu kafin ya ce ''Ummu zo mu je na kai ki wajen Anuty mu,ta yi fari ta fi Mumy fari'' wani irin zafi zuciyar Amirah ya mata lokacin da ta ji abinda Rayyan ya faɗa amma sai ta danne zuciyarta ta cigaba da kallon da ta ke,Ummu Abiha da ta yi nisa a wasa ko kallon Rayyan bata yi ba tana cigaba da wasan ta,tun safe da Amirah ta fara aiki ba ita ta gama ba sai karfe shidda,duk yaran ta yi masu wanka a karo na biyu ta canza masu kaya itama ta yi nata wanka,ba ƙaramin gajiya ta yi ba har yanzu ta ƙasa fahimtar dalilin da yasa Ammi ta bawa su Iyan Salame hutu,Amirah na shirin tayar da Sallah Sudais ya shigo ɗaki yana wasa da yatsun sa kansa ƙasa kamar wanda ya yi laifi kallo ɗaya Amirah ta masa ta fahimci akwai abinda yake so hakan yasa ta tambaye sa ta ce  ''me kuma ya faru?me ka ke buƙata?" a hankali Sudais ya ɗaga ido amma ya ƙasa haɗa ido da mahaifiyarsa sai ya ƙurawa darduma da take tsaye a kai ido yana wasa da ƙasan rigarsa ya ce ''masallaci muke son zuwa'' numfasawa Amirah ta yi a tunanin wani abun zai faɗa tunawa ta yi da akwai masallaci gefen gidan Ammi duk sanda suka zo Kano sau da yawa nan suke zuwa sallah har Ɗalha da Dady ba tare da kallon inda yake tsaye ba Amirah ta ce ''to sai kun dawo da an idar ku dawo gida'' da wani irin sauri Sudais ya fito daga ɗakin  yana faɗin ''to Mumy'' daga haka ya fita a guje,gaba ki ɗayan su suka tafi masallacin har Fauziyya,a can masallaci suka haɗu da Ɗalha bayan idar da sallah Ɗalha ya haɗa kansu zuwa gida,suna gaba yana biye da su bayan shigarsu gidan ne Rayyan ya mintsili Sudais yana nuna masa bangaren Unaisa,Sudais ya kalle Ɗalha ya ga su yake kallo kawai ya ce ''Daddy za mu je wajen Anuty mu'' Ɗalha na danna waya ya ce ''ok'' da gudu suka yu bangaren Unaisa har Fauziyya Unaisa dake tsaye cikin parlour waya saƙale a kunnenta ta ji muryar yara suna mata sallama a ƙofa tare da bugun kofar katse wayar Unaisa ta yi tare da buɗe kofa nan ta gan su tsaye su bakwai ras,kafin auren ta da Ɗalha ko sau ɗaya bata taɓa jin son yaran ba hasali ma basa gabanta amma yanzu bata san me ya shiga kanta ba kawai yaran suna burge ta kallon Rayyan da Afef ta yi ta ga an sauya masu kaya sun yi tsaf da su wannan ƙhamshi da ta ji jikin Afef da Rayyan ɗaxu da safe yanzu haka ƙhamshin ke fita daga jikinsu,kallo ɗaya za ka yiwa yaran ka fahimci mahaifiyarsu na ƙokari wajen kula da su,bata san sanda ta sakar masu murmushi ba ta ce ''ku shigo'' duk suka shiga Sudais ne ya fara gaida ta kafin sauran,bayan Unaisa ta zauna ne ta shiga tambayar su sunayensu ɗaya bayan ɗaya duk suka faɗa mata Unaisa na ta kallon jan lalle da aka yiwa Ummu Abiha da Sumayya da Fauziyya ƙafa da hannu, sosai lalle ya kwanta a fatar su yi masu kyau sosai,dake  duka yaran suna da hasken fata hakan yasa lalle yi masu kyau sosai,basu wani dade ba suka ce mata za su tafi Unaisa ta ce ''to'' bayan fitarsu Unaisa ta dade zaune tana tuna maganganun Ɗalha kafin ya auro ta yadda ya yi ta kushe Amirah a wajenta kullum cikin ƙorafi yake kan Amirah ƙazama ce bata kula da yara yadda ya kamata,sannan bata kula da gida,doguwar ajiyar zuciya Unaisa ta sauke kafin murya can ƙasa ta ce ''munafuki''daga haka ta miƙe tsaye tana daukar wayarta ta nufi ɗakinta har sannan mamaki kwance fuskarta murya can ƙasa ta ce ''har wani lalle ta yi masu ga wani shegen ƙhamshi da suke,wai ita ga mai tsafta'' ta faɗa tana shiga ɗaki zuwa yanzu Unaisa bata san takamaimai abinda take ji kan Amirah da yaranta ba son yaran take ko kishi take da uwarsu
















Karfe takwas na dare dai-dai Ammi ce tare da Amirah da yara zaune cikin parlour Amirah na ma Ammi tausa yayin da yara sun fara bacci,kasancewar yau babu nepa yasa sun yi bacci da wuri,hasken tocilan Ammi ne ke  haska parlour Ammi da Amirah na hira yayin da Ɗalha na zaune yana danna waya ko sau ɗaya bai sa baki a hirar da suke ba,hasali ma ransa a ɓace yake tun sanda ya ji Ammi ta cewa Amirah ta shigar da yara ciki saboda sauro lokacin ya fahimci yau ma wajen Ammi za su kwana,hakan yasa ransa ɓaci,suna nan zaune Dady ya shigo bakinsa dauke da sallama hannusa riƙe da leda da ya yiwa su Sudais tsaraba duk suka amsa masa sallama Ammi ta tashi ta karɓi ledar hannusa tare da yi masa sannu da dawowa,bayan Dady ya amsa sannu da dawowar da Ammi ke masa ne lokaci guda ya mayar da dubansa ga Ɗalha da Amirah ya amsa sannu da dawowar da suke masa daga haka ya mayar da dubansa ga Ammi inda ya ce ''mai gyaran solar bai zo ba ne?" Ammi dake tsaye gefinsa ta amsa masa da ''eh bai zo ba'' kallon Ɗalha ya yi da har sannan yana danna wayarsa Dady ya ce ''Ɗalha haka za mu kwana cikin duhu?" Ɗalha ya yi shiru tare da ajiye wayarsa gefe yana kallon Dady,Dady ya daura da ''a je a siya mai a zuba a inji'' sai a sannan Ɗalha ya yi magana ya ce ''to Dady'' daga haka ya miƙe tare da barin parlour,bayan fitar Ɗalha Dady ya fita daga parlourn zuwa ɓangarensa,bayan fitar Ɗalha daga parlourn Ammi inda ya paka motarsa ya nufa ya shiga mota ya ja ya fita daga gidan,kusan gidajen mai huɗu ya tafi duk sun tashi a karshe dai ya tsaya wajen masu siyarwa a bakin hannya ya siya lita goma daga haka ya wuce gida,ɗakin inji ya shiga zuba mai a cikin inji kafin ya tayar,canza layi ya yi daga nepa zuwa gen,ko kallon side ɗin Ammi Ɗalha bai yi ba ya dauki take away guda biyu daga motarsa ya wuce bangarensa,nan parlour ya ajiye take away daga haka ya wuce ɗakinsa,wanka ya yi bayan fitarsa daga bayi ya shirya kansa cikin jallabiya blue,kwanciya ya yi bayan ya kashe fitilar ɗakin har sannan zuciyarsa babu dadi, a hankali ya rufe idanunsa yana karanto addu'a bacci,wayarsa ce ta yi ƙara alamar shigar saƙo daukar wayar ya yi ya duba yaga E mail aka tura masa ba tare da ɓata lokaci ba ya buɗe E mail, letter ne dauke da sunansa an tura sa training a legos,ranar monday za a fara training ɗin kenan gobe zai bar Kano wata ajiyar zuciya Ɗalha ya sauke tare da gyara kwanciya,washe gari karfe goma na safiyar Lahadi Ɗalha ne zaune cikin parlourn Ammi Unaisa na gefen sa   sun shiga yiwa Ammi sallama Amirah da ke cikin ɗaki tun sanda ta ji shigowar su ta shiga bayi ta rufe kofar da key,su Sudais na kewaye da Ɗalha Ammi ta kalle Sudais ta ce ''je ka kira Mumyn ku ka ce mata Daddyn ku zai wuce'' da gudu Sudais ya nufi ɗakin Amirah,ya buga ƙofa har ya gode Allah Amirah bata buɗe kofa ba ganin lokaci na tafiya yasa Ɗalha ya cewa Ammi za su wuce zai kira Amirah a waya,Ammi da kanta ya gama kullewa ta kalle Ɗalha da Unaisa ta ce Allah ya kiyaye masu hanya da ameen suka amsa mata daga haka sun fita daga parlourn har wajen mota su Sudais suka yiwa babansu raƙiya,Amirah dake kulle cikin bayi sai da ta tabbata Ɗalha ya bar gidan kafin ta buɗe kofar bathroom ta fito zama ta yi bakin gado ta yi tagumi tana tunani zuciyarta babu daɗi,ta sani ita ta kara masa kwanaki ta ce ya yi sati biyu ɗakin Unaisa amma yanzu ta ji babu daɗi da ta ga za su sake koma Kaduna tare,ta dauki a ƙalla mintina goma zaune cikin ɗaki kafin daga bisani ta tashi ta fita daga ɗakin, nan parlour ta tarar da Ammi zaune waya kare kunneta,waya take da Iyan Salame waje Amirah ta samu ta zauna tana kallon Ammi bayan Ammi ta gama waya ne Amirah da har sannan idonta a kan Ammi ta ce ''har hutun nasu ya ƙare?" Ammi ta ce ''eh jibi za su dawo'' dan jimm Ammi ta yi kafin ta mayar da dubanta ga Amirah ta ce ''me yasa ba ki fito kun yi sallama da mijinki ba?" Ammi ta ƙare magana tana kafe Amirah da ido,a natse Amirah ta ce ''l was in the bathroom shi yasa'' shiru Ammi ta yi bata sake cewa komai ba,Ammi ta riga ta fahimci Amirah ba ta son haɗuwa da Unaisa hakan yasa ta yi shiru ita dai Amirah tana ta mamakin Ammi ta ƙasa fahimtar dalilin da yasa ta bawa su Salame hutu jiya,yau kuma ta kira su ta ce su dawo aiki jibi,abinda Amirah bata sani ba shine saboda Ɗalha Ammi ta tura su Iyan Salame ƙyauye ta yi hakan ne saboda ta lura da Ɗalha a matse yake ita kuma akwai shirin da take yiwa Amirah baza ta bari Ɗalha ya same ta yanzu ba 













SHUUKRAN