Chapter 10
PAGE 10
Tunani kawai nake yi, shi ya kamata na fara yi wa magana, ko ita? Kuma ma ta ina zan fara yi masa? Shin zan faɗa masa na ga zoben shi ne a hannun Habiba ko kuwa na ji recordin ɗin wayarsu? Zuciyata ta dinga zafi, na fara tsanarsa wannan maganar ba wacce zan zubawa ido ba ce, abun akwai baƙinciki, saboda haka na yanke kawai zan tunkare shi mu yi ta, ta ƙare a yau.
Ina shirin tashi na ji ya ƙwala mini kira, na sakko tsam na fita na shiga falo, sai na tsaya na harɗe hannu a ƙirji ina kallonsa fuskata babu walwala sam.
Na lura bai gane yanayin da nake ciki ba, tun da dariya ya yi ya ce"To an so gigita ni kenan aka yo wannan shigar aka yi mini tsaye a ka".
Na haɗiye yawun takaici na ce"Au da gaske ni ina da abin da zan gigitaka?"
Ya ce"Kamar ya?"
Na ce"To ai gani na yi idan har maganarka daga zuciya ta fito bai kamata na dinga ganin wasu halayen daga gareka ba".
"Waɗan ne kenan?" Ya tambaya a nutse, da alama ya gane abin da nake nufi.
Na zauna a kujerar da take kallon tashi, sai bakina ya gagara furta komai, ina ta danne zuciyata daga raunin da take son yi, amma ta fi ƙarfina, don sai da hawaye suka zubo mini, na goge ina ƙarfafa kaina, da ƙyar na iya cewa"Salman wane ne kai?"
Ya yi kalar mamaki ya ce"Ban gane wane ne ni ba?"
Na ce"Ok, ba ka san kanka ba ko? Wannan ba abun mamaki ba ne ba".
Na ce"Wace ce ni? Kuma mene ne matsayina a wajenka?"
Ya ce"Zinatu wai me yake faruwa ne? Na kasa gane inda kika dosa".
Na ce"Ni ma ba ka san wace ce ni ba kenan, kuma ba ni da wani matsayi a wajenka, shiyasa kake yin komai da zuciyarka ta raya maka".
A wannan karon shiru ya yi, bai ce mini komai ba, sai dai bi na da ido kawai.
Na ce"Salman wace alaƙa ce a tsakaninka da ƙawata Anti Habiba?"
Cikin sakan ɗaya alamun razana suka bayyana a gare shi, ya ƙi ce mini komai.
Na ce"Hmm! Amma dai ka san matar aure ce ko? Kodayake ƙila kai da itan ba ku san darajar aure ba, kun manta ba a gidan duniya za a dawwama ba, akwai madakata. Salman yanzu shaharar taka har ta kai ka tsallake karuwai, ka tsallake ƴan mata da zawarawa ka faɗa kan matar aure? Da matar aure kake soyayya Salman?"
Na dakata ina jiran amsar shi, sai dai bai ce mini komai ba, don haka na cigaba"Na san komai da yake tsakaninku, abun ya kai har za ka iya cire zoben hannunka ka ba ta kyautar shi".
Na yi dariyar takaici na ce"Wallahi ka ba ni mamaki, kai yanzu ko tsoro ba ka ji ni ma wani ya ce yana sona? Ba ka jin tsoron ranar da mijinta zai gano ku? Ko dayake ai ba ku ji tsoron Allah ba ma, ballantana mutum, to a gaskiya ba zan ɗauki wannan ba, na gaji haka, abun ya isa!". Na ƙarasa da ƙarfi.
Har yanzu kamar da dutse nake magana.
Na ce"Salman wannan abin da ka yi tamkar cin fuska ne a gare ni, ƙawata wacce muke tare!? To gaskiya zan saka manya a maganar nan idan har ba ka rabu da ita ba, zan ɗauki nawa matakin!".
Na fice, ganin da gaske ba zai kula ni ba, to idan ban fita ba ya zan yi? Shi ba ɗana ba, ballantana na rufe shi da duka, na koma na kwanta ina hawaye.
Na ji ficewarsa daga gidan, sai na yi zaton ko fushi ya yi, ban yi zaton zai dawo ba don haka na je na rufe gidan, sai dai babu jimawa ya dawo, ya shigo ya kira sunana"Zinatu ga wannan".
Na juyo na kalli ledar da yake miƙo mini, kamar na yi banza da shi, sai kuma na daure na sakko daga gadon na karɓa na duba, kaji ne da lemuka, na je kitchen na ɗakko faranti da kofi na juye, na kai masa falo don can ya koma, ina ajiyewa na koma ɗaki, ina jin sanda ya gama ya yi wanka ya zo ya kwanta, an ɗauki lokaci har na yi zaton ya fara bacci, sai na ga haske ta wayarsa, alamar ana kiranshi, ya tashi ya fice daga ɗakin, sai na ji ban yarda da shi ba, ƙofar falo ya tura ya shiga, ni ma na sakko na mara masa baya, saɗaf-saɗaf na ƙarasa ƙofar falon na tsaya, sai na ji yana cewa"Ki yi haƙuri ga gobe nan, ko da safe za mu yi waya".
Dama na san za a rina, ban ankara ba na ji motsin fitowarsa, don haka na yi hanyar banɗaki, haka muka kwana muka tashi ni raina a jagule, shi kuma na rasa inda ya dosa, yadda dai na lura kamar ma sam bai damu ba.
Washegari na zauna duka na gama jin recording ɗinsu, hankalina ya tashi sosai da jin irin shaƙuwar da suka yi, a wayar suna yawan tsayar da wajen da za su haɗu, sassaucin da na ji a zuciyata ɗaya ne, ban ji sun ambaci hotel ko wani gida ba, shi yasa nake kyautata zaton ƙazamar mu'amula ba ta haɗa su ba, amma muddin na yi sake tabbas za ta iya kai wa ga hakan, don haka dole na ɗauki mataki.
Haka Asabar ta yi, ya kai ni makaranta kamar yadda ya saba, ina shiga ƙunci ya shiga zuciyata, na ji gabaɗaya ma na tsani makarantar da karatun, saboda ba na son ganin Anti Habiba sam, ai kuwa ina ƙarasa idona a kanta ya fara sauka, abun mamaki muna gaɗa ido na ga ta ɓata rai, ta ɗauke kai, sai kuma ta tashi da sauri ta yi hanyar fita, na bi ta da kallon mamaki, lallai tana da ƙarfin hali, da alama ya sanar mata na sani, shi ne za ta fara nuna mini kishi muraran saboda ba ta da kunya, sauri ta dinga yi har ta ɓacewa ganina, haka kawai na ji ban yarda da ita ba, sai zuciyata ta raya mini bin bayan shi ta yi, ƙila dama sun yi da ita za su haɗu, na ji kamar na bi bayanta, sai kuma na dake, na shiga cikin ƙawaye, amma sam hankalina ba ya wajensu, ta ɗan daɗe sannan ta dawo. Wunin ranar dai ko ƙala ba ta haɗa mu ba, washegari ma haka, sai da muka yi sati biyu a haka sannan ƴan group ɗinmu suka gano muna gaba, suka zaunar da mu don sasanci, kowa ya ƙi cewa komai, to na ce musu me? Na ce ta shiga jikin mijina suna soyayya su yi mini kallon shashasha mara amfani, ko kuwa na ce shi ne ya ce yana sonta, su dinga yi da ni su ce ban yi dacen miji ba? Ita kuma dama na san ko me za a yi ba za ta faɗa ba, tun da ai da kunya kina matar aure ki dinga soyayya da wani, wanin ma mijin ƙawarki, haka suka yi suka gaji suka ƙyale mu.
Tsawon sati biyu ban duba wayarsa ba, amma yau na yanke zan duba, saboda abun nashi kullum gaba yake yi, yanzu abun ya kai Salman yana tashi tsakar dare ya yi waya, sai na neme shi na rasa idan na farka, sai na yi sanɗa na fito na ji shi a falo yana waya. Yau ɗin ma tsakar dare na yi niyya amma fargabar kar ya tashi yin waya ya ga babu wayarsa ya saka na bar shi, sai da asuba da na idar da sallah, na kalle shi yana kwance yana baccin asara ba shi da niyyar yin sallah, na ɗauki wayar tashi na koma falo, kira na fara dubawa, nan na ga ko jiya da daddare sun yi waya da Anti Habiba, na yi ta dubawa kullum sai sun yi, abun ya ba ni mamaki, wannan wace irin masifa ce haka? Raina ya jagule, na je na ajiye masa wayarsa.
Na zauna a falon na shiga tunanin yadda zan yi, idan ma na je na tare ta ni me zan ce mata? Ni fa ba ni da irin wannan masifar, amma akwai wata ƴar'uwata wacce ita ce babbar aminiyata, gidanmu ɗaya, tare muka taso don mu sa'anni ne, ita ba ta yi aure ba har yanzu, akwai shaƙuwa da yarda sosai a tsakaninmu, sannan ita kam ta iya faɗa, don ko faɗan ƙuriciya idan aka ritsa ni ita take tare mini, saboda na yanke zan faɗa mata komai, ko za ta ba ni mafita.
A ranar na kirata a waya, ta zo gidana da yamma, har da kukana, na zayyane mata komai, har ma na kunna mata wasu daga cikin wayar tasu ta ji, Kausar ta lailayo ashar ta ƙunduma, nan ta rufe ni da faɗa tana cewa me nake jira? Gabaɗaya ta jibga mini laifin wai tun da ban ci ubansu ba, gabaɗaya ta birkice ta ce na ɗakko hijjabi, na ce"Kausar na yi me da hijjabi?"
Ta ce"Ba kin san gidanta ba? Zuwa za mu yi mu yi mata tijara, wallahi ba mijinta ba har uwarta da uwar mijinta da ubanta da uban mijinta da uwar kishiyarta duk sai sun ji komai, kuma kina da shaida ga muryar matsiyaciya nan kowa zai ji!".
Ni ma zan so hakan, saboda haka kai tsaye na amince, na rufe gida muka tafi, a adaidaita sahu tana ta tsara mana yadda za mu yi idan mun je.
Har ƙofar gidan mai adaidaita sahu ya ajiye mu, muka shiga da sallama, kishiyarta tana tsakar gida tana hada-hadar girki, Anti Habiba ta leƙo ta yi mana kallon mamaki ta koma, muka doshi ɗakin nata da sallama, ta amsa a daƙile, muka shiga, na yi tsaye kamar yadda na ga Kausar ta yi, shiru na ƴan sakanni, sannan ta ce"Bayin Allah lafiya dai ko kuka shigo min gida har ɗaki, kuka yi min tsaye a kaina?"
Kausar ta ce"Ai ba ki nemi lafiya ba, don ba ki san muhimmancinta ba, kuma gidanki da kike iƙirarin an shigo ke ma kin kusa barin shi, ya kamata ki fara ƙirgen kwanakin iddarki tun daga yanzu".
Ta ce"Me kuke nufi? Zinatu da wacce kuka zo?"
Na ce"Da irin wacce kika shiga rayuwar mijina!".
Kausar ta ce"Ke saboda daƙiƙanci da jahilci kina matar aure kike soyayya da wani!?"
"Soyayya? Da uban wa nake soyayya?" Ta faɗa tana miƙewa tsaye, ta fara zabure-zabure na tabarmar kunya naɗe ki da hauka.
"In ji ubanki!" Cewar Kausar, sannan na kunna recording ɗin wayarsu, nan take na ga jikin Anti Habiba ya yi sanyi, ta zauna a sanyaye, Kausar ta ce"Har wanda kika ba shi labarin uwarki da ubanki sun mutu akwai a nan, yanzu za mu zauna mu jira mijinki ya dawo mu zaunar da shi, shi da kishiyarki mu kunna masa, sannan mu ƙarasa gidan uban naki da kika kashe su da bakinki saboda kwaɗayin abun duniya da son zuciya su ma mu kunna musu!".
Na ƙara da faɗin"Har group ɗin makaranta sai na tura kowa ya ji!".
Nan take jikinta ya fara rawa, ta fara inda-inda ta ma rasa me za ta ce mana, da ƙyar ta iya haɗa kalmar "Don Allah Zinatu ku yi haƙuri, wallahi saharrin shaiɗan ne".
Kafin mu ce komai, muka ji tsayuwar babur ɗin mijinta, na ce"Alhamdulillah Allah Ya sa mijin nata ne, a yi ta ta ƙare".
Ta tashi a firgici, mu ma muka tashi za mu fita tsakar gidan da ya shigo yana kwaɗa sallama, ta sha gabanmu da sauri ta durƙusa gwiwowinta a ƙasa ta fara siririn kuka tana cewa mu yi haƙuri, Kausar ta hankaɗe ta ta ce"Ke kin isa! Kin isa ki saka ƴar'uwata kuka na ƙyale ki? Wallahi hawayenta ba za su tafi a banza ba!".
Muka fice, ta biyo bayanmu, daidai nan mijin nata ya ƙaraso yana cewa"Lafiya? Me yake faruwa?"
Na ce"Mu je daga ƙofar gida".
Kausar ta ce"Ki faɗa a gaban kowa har kishiyar tata ta ji".
Na ce"A'a mu je dai, ji jira ni a nan don Allah Kausar".
Na kalli Anti Habiba, na ga ta ɗora hannu biyu a ka, kamar wacce za ta fasa ihu, na bi bayan mijinta muka fita zuciyata tana zafi.
LAST FREE PAES!
A nan zan tsaya da free pages, akwai abubuwa da dama a cikin labarin nan, labarin ya faru a gaske, sai ɗan kwaskwarima a wasu wuraren, akwai tirka-tirka kala-kala, da ƙalubale da Zinatu za ta fuskanta, bari na ba ku satar amsa🤭Salman zai ƙara aure, abubuwa da dama sun faru kafin auren da kuma bayan auren, sai dai na ji ku ƴan amanata.
Littafin Wutar ƙaiƙayi na kuɗi ne akan naira 500 kacal! Ki biya ki karanta cikin aminci, za ki tura kudin ta wannan a ccount ɗin
8028966015
Sadiya Abdulrazak
Opay bank
Ki tura shaidar biya ta nan ***